Free chapter · Read without an account

8

by Sadiyamuhammadnasir · RIKON SAKAINA

RIKON SAKAINA

YA FARU A GASKE

NA

SADIYA NASIR DAN

Arewa Book

sadiya Nasir

SHAFI NA TAKWAS

"Khadija! Khadija! Uncle Naira ya soma kwala min kira da karfi yana biyo ni, ganin haka yasa nasa gudu na shiga ciki da sauri, Sahura tana kitchen hakan ya bani damar cire mayafina na fad'a toilet na zauna dirshan na saki kuka mai karfi, maraicina ya dawo min sabo, tunda nake da mahaifina bai tab'a d'aura hanunsa a jikina da sunan duka ba, amma tunda nazo gidan Baffa Kabiru komin k'ank'antar laifi sai dai naji mari, yau gashi saboda rashin gata Uncle Naira yasa hanu ya mareni kuma ya mari banza, bana da wanda zai lallasheni ko yaji damuwata. Wani irin tsanar uncle Naira ne ta d'arsu a zuciyata, take na d'auka wa kaina alwashi bani bashi har abada, a nemar Aure kenan zai iya d'aukar hanu ya mareni idan anyi Aure sai kuma yaya? Na jima ina kuka sai da naji kaina ya soma ciwo kafin na sake wa kaina ruwa na jika gashi na sosai na fito, kitchen na nufa na debi abinci lokacin Sahura ta fita harabar gida, tamkar Magani haka nake cin abinci zuciyata babu daɗi.

Uncle Naira da tsananin nadamar abinda ya aikata yabar gidan Hajiya Indo, kai tsaye gida ya koma ya haye gado ya cigaba da sak'awa da warwarewa na yanda zai gyara abinda ya b'ata, ya rasa meyasa zuciya ta debeshi har ya kai hanu jikin Khadija, wannan Mari da yayi mata na iya jagula komai, ganin tunani naso yafi karfinsa yasa ya mike ya nufi gidan giya dake cikin Barack ya saya yayi tatul, da kyar ya iya kai kansa gida ya jibge a parlor ya cigaba da sambatu yana kiran sunan Khadija anan bacci ya d'auke sa.

Ina idar da sallar la'asar Baby suka shigo tare da Hajiya, saboda in rage b'acin ran dake zuciya ta yasa ban jira Baby ta sauƙo ba na haura na sameta don muyi hira, sosai hakan ya rage min damuwar dake zuciyata.

Banbi takan wayata ba sai da na d'aura kafad'a ta bisa pillow zanyi bacci, miss calls na gani da bakon number kusan guda takwas, gaba d'aya na mance dana ba Ibrahim phone number ta, bin kiran nayi da sauri amma ba'a d'auka ba harta tsinke, ina kokarin ajiye wayar kira ta sake shigowa da number, d'auka nayi da sallama. "Aminci ya sameki a duk inda kike Khadija da fatan kin koma gida lafiya?". Sai a sannan na tuna, tsintar kaina nayi dayin murmushi nace. "Lafiya kalau Alhmdullah ya kake?"

"Lafiya amma ba sosai ba".

"Subhanallah meya faru ?".

"Bakomai kece dai kika hargitsani?"

"Ni kuma?".

"Kwarai Khadija, tunda nayi arba dake kuma nutsuwa tabar jikina, gaba d'aya sai ina jina ba'a dai'dai ba, gaskiya ke mai sa'a ce, ban tab'a jin irin abinda naji akanki game da Mace ba". "Uhumm Allah ko?".

"Eh wallahi, naso mu ɗan tattauna gashi dare tayi nasan kuma zaki kwanta saboda ki samu tashi akan lokaci kije makaranta, ni kuma ban sallami d'alibai da muke karatu dasu ba, in Sha Allah gobe sai muyi magana". "Allah ya kaimu". Ameen ya rabbi ya ambata ya kashe wayar, murmushi nayi da ban san dalili ba na gyara kwanciya, haka bacci ya d'auke ni cike da tunani iri da kala musamman akan bak'in wulakanci da uncle Naira yamin.

Washe gari da safe na gama shara ina k'okarin moping naji shigowar saƙo dake wayar tana makale cikin ɗankwalina, zama nayi na bud'e wayar, ganin number Uncle Naira yasa naja dogon tsaki ban tsaya na karanta abinda ya rubuta ba na goge message din nayi blocking number d'in sa gaba d'aya, haka na k'arasa aikin cike da takaici da bakin ciki, in ba rashin kunya ba har uncle Naira zai iya sake bibiyata.

Tsawon sati biyu muka d'auka Uncle Naira idan ya kira wayata bata shiga sannan idan yazo gidan baya samun ganina, wannan al'amari ya d'aga masa hankali gashi baya so Hajiya tasan maganar saboda ba zata d'auki zancen duka ba musamman akan laifin da bai taka kara ta karya ba. Tsakanina da Ibrahim kuwa shakuwa ce da soyayya mai karfi ta shiga tsakanin mu a y'an wa'innan kwanakin, kuma da zancen Aure yazo gareni, kuma hankalina ya kwanta dashi saboda Kamalar sa da kuma kwatanta bin dokokin Allah, sai dai na sanar dashi maganar Aure ba nan kusa ba saboda burin Baffa Khabiru na son nayi karatu mai zurfi, ya kuma goya min baya yace bakomai in kwantar da hankalina komai zai zo da sauƙi. A haka har muka soma final exams, a wannan lokacin Allah ya jarabci mahaifiyar Ibrahim da ciwo har ta kaita ga kwanciya a asibiti, shiyasa sam bana gane mishi saboda jinyar Mama.

Ana saura kwana biyu mu kammala exams muna hira da Sahura nake sanar da ita ciwon mahaifiyar Ibrahim kuma har ga Allah ina so naje na duba jikinta, sosai ta bani goyon baya akan haka har tace nayi ɗan sayayya na tafi dashi karma nace mishi zanje dubata, idan na dawo gida saina fad'a mishi cewar naje.

Take na d'auki shawarar ta ranar final paper muna fitowa na biya na saya fruits na wuce asibiti dake ya sanar dani har dakin da take. Ai kuwa na samu Ibrahim zuwan sa kenan, sosai ya nuna jin daɗin ganina, hakan yasa ya kasa b'oye matsayina a wajen sa ya sanar da y'an uwansa da Mahaifiyar sa nice matan da yake so ya aura, naga kauna kam agun mutanen nan, ko minti shabiyar ban yiba na fito Ibrahim ya biyo ni yace ba zan hau adai-daita ba zai kaini gida da kansa, kallon sa nayi nace "Ka san idan ka kaini gida na iya haifar da matsala ko? Kawai ka barni na hau Napep yafi min sauƙi, murmushi yayi ya dubeni. "In Sha Allah babu mai ganinki nesa da gida zan ajiye ki kizo kawai muje". Ganin ya dage yasa nace toshikenan muje, ta cikin G.R.A muka bi saboda akwai sakon da zai karba a wajen wani, a dai'dai destination hotel gefen yayi parking ya barni cikin motor ya shiga amso saƙon, ganin shago a gefe kaɗan yasa na fito saboda tsananin kishin ruwan dake damuna tun a makaranta, ban d'auki lokaci a motor yazo muka tafi, nesa da gidan mu ya saukeni muka ɗanyi hira kaɗan na mishi sallama na fito. Gidan shuru Kasancewar ko azahar ba'ayi ba, Sahura ce kawai take ɗan aikece aikace a gidan, ɗaki na wuce na cire kayan jikina na fad'a toilet domin yin wanka.

****

Sahura na kwashe shanya Uncle Naira ya shigo, a ladabce ta gaisheshi ya amsa yana shan kamshi. "Ke ina Khadija?". "Tana ciki". Ta fad'a da sauri. "Hajjaju fa?". "Tana office bata dawo ba". "Ok su Aliya na school ko? Eh ta ambata da sauri, kudi ya ciro a cikin aljihu had'e da ATM. "Please ki hau Napep zuwa bank road ki ciro min 10k, ga pin d'in ina jiranki". To Sahura tace ta nufi hanyar shiga gida ya dakatar da ita "Me kuma zaki shiga yi?".

"Mayafi zan d'auka". Ta ambata kanta a k'asa. "Su kuma wanda suke shanye fa?". "Nasu Baby ne". Oya d'auki kisa bana son b'ata lokaci ne". Da sauri Sahura tasa mayafi ta bar gidan.

Shu'umin murmushi Uncle Naira yayi yasa kai cikin gidan.

Fitowa ta kenan daga wanka ina neman kayan da zan saka na gabatar da sallar Azahar uncle Naira ya fad'o ɗakin. "Innalillahi wa'inna ilaihi raju'um na ambata saboda zuciyata data tsinke, da sauri na yaye bedsheet na lullube jikina murya a kausashe nace. "Wannan wani irin cin mutunci ne zaka shigo ɗakin y'an mata kai tsaye, sannan ka ganni ba kaya maimakon ka fita ka tsaya kana kallona?". Dariya ya fashe dashi harda tafa hanu. "Meye abin boyewa a jikin da ake raba wa Maza a hotel? Duk wani wayon ki Khadija a tafin hanuna kike, har ki mutu baza kiyi barikin da nayi ba, ashe ke Y'ar hanu ce shine kike wahalar dani? Ko kina tunanin ba zan iya biyan farashin ki bane yasa kika kasa bani had'in kai?".

"Subhanallah me kake fad'a haka uncle Naira kana cikin hankalin ka kuwa?". Mugun kallo ya watso min. "Ina tunanin ko ubanki bai zai kai ni hankali ba, kin ga bana son wahalar da shari'a gidan nan ba kowa daga ni sai ke kawai ki bani had'in kai nayi abinda zanyi na kauce, bana son wani kauce kaucen munafurci". Ya k'arasa maganar yana nufowa inda nake. Da gudun gaske na haye gado zan fita ya fisgoni da karfi, wutsil wutsil na soma na kwatan kaina Amma na k'asa saboda ya fini karfi, ganin na neman ya bud'e min tsaraici yasa nasa hakorana a kirjin sa na ciza da karfi, wani irin k'ara ya saki ya wurgani gefe, da gudun gaske na fito a ɗaki har bana ganin gabana, sam na mance towel ne a jikina na fito harabar gidan, sai jina nayi na fad'o jikin mutum, a razane na ɗago ido ganin Baffa Kabiru yasa na fashe da wani irin kuka na rungume sa. "Subhanallah Khadija lafiya? Meya faru ina zaki? keda waye?". Ya jefo min tambaya uku lokaci guda, kasa bashi amsa nayi sai ma kuka da yaci karfina. Uncle Naira rai bace ya fito yana faman kwala min kira, ganin Baffa Kabiru yasa ya tsaya turus. "Mustapha Naira....? Baffa Kabiru ya ambata muryarsa har na rawa, matsar dani gefe yayi ya kalleni sai a lokacin ya lura da ɗaurin towel dake kirjina, kukan kura yayi ya nufi inda Uncle Naira yake ya turesa suka zube k'asa ya hau cikin sa yacigaba da duka da iya karfin sa, uncle Naira ganin Baffa Kabiru na neman yi masa lahani yasa ya fara kare dukan yana ramawa, ganin jini na fitowa a hancin Baffa Kabiru yasa na saka ihu na fara neman d'auki, Sahura ce ta shigo a kiɗime saboda ihun da nake da karfi, ganin irin abinda ke faruwa yasa ta kira number Hajiya ta shaida mata abinda ke faruwa.

Da taimakon Ubangiji Allah yaba Baffa Kabiru dama yama Uncle Naira dukan daya galabaita, babu b'ata lokaci ya kira area command yace azo da motor a tattara mishi Uncle Naira. Ganin yanda na fita hayyacina yasa Sahura kama hanuna muka shige cikin gida.

Da Hajiya Indo da motor hukuma kusan a tare suka iso, sosai hankalinta ya tashi ganin irin dukan da Baffa Kabiru yama Uncle Naira kuma yasa aka tafi dashi, hankali tashe ta shige ciki ta nufi ɗakin Daddy don jin dalilin faruwar haka.......

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.