Free chapter · Read without an account

Chapter 26

by Jamila · SAKACINA KO HALIN MAZA




*SAKACINA KO HALIN MAZA?*    



  *RUBUTAWA:-*
 *JAMILA LAWAL ZANGO*

                   *SADAUKARWA GA:-*

 *SUMMY M NA'IGE*
              _(Aminiya)_             

      
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

                          *Page 26*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


A cikin motar da suka zo da ita suka sakata,sun yi tafiya mai nisa gaske sannan suka tsaya.

Duk nisar tafiyar da suka sha amma Mama da Ibrahim ba su farfaɗo ba.

Wani ƙaton gida suka shiga da su tare da kwantar da su,sannan suka fice daga gidan.

Kusan awa ɗaya Mama ta yi sannan ta farka cikin tsananin razana tana salati.Ta kalli in da take yayin da take tsananin mamaki,idanuwanta suka firfito tana mamakin in da ta tsinci kanta.

Ibrahim dake kwance ta rungume tana jijjiga shi,cikin tashin hankali tana mamakin ganin ta a wannan gida.

Ko da ya buɗe ido sai ya cika da tsananin mamaki ya kalle ta ya ce.

"Mama ina ne nan kuma mai ya kawo mu wannan gida?"

Mama dake cikin tashin hankali ba ta ba shi amsa ba,sai miƙewa da ta yi tana ƙarewa gidan kallo.

Duk da rashin ƙarfin jikinta amma haka ta miƙe ta kama hannun Ibrahim suka fito waje.

               " Madam lafiya ina za ki je."

Ta ji muryar wani mutum wanda yake tsaye a get ɗin gidan,ya na sanye da kakakin sojoji da bindiga ɗauke a hannunsa.

Mama ta ja baya da sauri tana kallon sa da tsoro a fuskarta.

" Waye kai kuma mai ya sa kake tambayata?Zan koma in da kuka ɗauko ni."

Ta ba shi amsa da muryar tsoro a fuskarta,tana ja da baya saboda ta tsorata ƙwarai da ganin sa.

" Madam ki yi haƙuri oga bai ba mu izinin ki fita ko da ƙofar gida ba ne."

Ya ce cikin ɗaure fuska ba tare da ya kalle ta ba,balle ya ga tashin hankalin da ke ɗauke a fuskarta.

" Waye kai mene ne haɗina da kai har za ka ce ba zan fita ba,sannan waye agan ka ina ruwana da shi."

Ta jera masa tarin tambayoyin da take tunanin ba zai amsa mata ko ɗaya ba.

" Wannan kuma sai ki jira har sai ya zo ki yi mi shi tambayoyi,amma ba ni da masaniya ina kan aikina ne kawai.

Mama da fari ta ɗauka wasa yake mata amma da ta dage kan dole sai ya buɗe mata,sai ta ga ya ɗaure fuska ya ɗaga zungureriyar bindigar sa,ba tare da ya ƙara kallon ta ba.

Da sauri ta kama hannun Ibrahim suka koma ciki,saboda ta tsorata da shi gani take kamar zai harbe ta.

                         " Inna lillahi!
Wai me ke faruwa ne na kasa gane komai ya Allah ka fahimtar da ni,na san cewa Baba Sani ba zai taɓa killace ni a gidan nan ba don kawai na buƙaci Juwairiya ta dawo."

Ta faɗa cikin tashin hankali tare da rashin madafa tana ji kamar ta yi hauka.

" Ina Juwairiya mai ya sa ita ba'a taho da ita ba?"
Ta tambayi kanta da tsananin mamaki yayin da ta rasa ta in da za ta fara tunani,domin lamarin ya ɗaure mata kai sosai.

" Ko masu garkuwa da mutane ne suka sace mu?"

Ta faɗa tana kallon Ibrahim da ya cika da mamaki ya na kallon daular gidan da aka kawo su.

A jiyar zuciya ya yi mai nisa sannan ya sauke tagumi ya kalli Mama,da fuskarta ya nuna tsantsar tashin hankalin da take ciki.


" Ba na tunanin za'ayi garkuwa damu har gida sannan aka wo mu cikin wannan daular Mama! Ki duba irin wannan gidan na masu kuɗi ne sosai.Ni dai ina zargin a kwai wata a ƙasa.Tabbas a kwai lauje cikin naɗi."

" Haka ne Ibrahim zuciyata ta fara hasasomin haka,sai dai ina zargin duk abin da ya faru a kwai saka hannun Baba Sani a ciki.Zuciyata ta fara zargin in da ya tura Juwairiya ba alkhairi ba ne,sai dai ina ɗan jin sanyi ne, in na tuna da Juwairiya yarinyar kirki ce,na yadda da tarbiyar da na ba ta sam ba na tunanin za ta aikata abin da nake zargi,duk da cewa ba'a shedar ɗan yau."

Hannu ta ɗora a ka yayin da gabanta ya faɗi ras!Sa'ilin da wani tunani ya faɗo mata.

" Kar dai a ce Baba Sani ya yi mini ƙarya ne akan aiki zai kaita,ya saka ta a hanyar banza?"

Ta tambayi Ibrahim da take tunanin bai fahimci abin da take nufi ba.
Mama ta saki ƙara tare da zubewa a ƙasa tana faɗin." Ya Allah na kasa samun natsuwa zuciyata,na shiga ruɗanin halin da Juwairiya take ciki,kar a ce Baba Sani ya ɓata mini tarbiyar da na gina ta akai,ya saka ta a harkar banza.Kar a ce da kuɗin da take aikata alfasha muke ciki."

Sai ta girgiza kanta tana kuka da ƙarfi ta ci gaba da faɗin. " Iya tsawon yaushe zan zauna a wannan gidan ba tare da na san gaskiya ba,in har Juwairiya ta canza tarbiyar da na ba ta tabbas ba zan iya yafe mata ba,domin na ci burin na ga na aurar da ke Juwairiya kar ki yi mini haka."

Da sauri Ibrahim ya taso ya rungumeta yana rarrashi ganin tana son ta fita hayyacinta.

"Mama mu bi abin da sannu-sannu kar ki aibata ta,na san cewa sam Anty Juwairiya ba za ta aikata haka ba,tabbas a kwai abin da ke faruwa.Kuma duk wanda ya sa aka kawo mu cikin wannan daular,to a kwai saka hannun Baba Sani a ciki don zuciyata ba ta yadda da irin sanyin da ya yi ba,lokaci guda ya zubda duk wani makaman sa akanta."

Mama ta shiga cikin tsananin ruɗani ƙwarai ta yi ihu ta yi kuka,tana roƙon mutumin da ya taimaketa ya gaya mata abin da ke faruwa,amma ko kallon ta bai yi ba don ba'a ba shi izinin haka ba,bayan haka shi bai san komai game da lamarin da ya faru ba.

Ganin irin kukan da Mama take yi tana kiran sunan Juwairiya ta ƙi shiga cikin gidan,a farfajiya ta tsaye tana kuka sosai ya kalle ta ya ce.

" Hajiya ba ni da nufin na cutar da ke gara ki koma ciki,don wallahi ko kukan mutuwa za ki yi ba zan buɗe miki ki fita ba.

Jin haka Mama ta ƙara sakin wani kukan ta zauna a gurin ta ƙi motsiwa,sai kuka da take yi domin kanta ya kulle.

*****

A ranar da aka ɗauke su Mama Juwairiya ta yi wani irin bacci mai nauyin gaske,ba ta tashi ba sai da ta ɗauki tsawon lokaci tana bacci mai kama da na mutuwa.

Buɗe idanunta ta yi cikin tsananin mutuwar jiki don ji take ko ɗan yatsa ba za ta iya ɗagawa ba.

Sai da aka ɗauki tsawon lokaci sannan ta samu ta iya tashi zaune.

Ɗaga idanunta da ta yi ta kalli agogon da ke manne a bangon ɗakin,da gudu ta miƙe tana salati saboda tunawa da ta yi ko sallah ba ta yi ba.

" Na shiga uku mai ya faru yanzu fa ƙarfe ɗaya har da kwata,wane irin bacci na yi ko dai mutuwa na yi na dawo?"

Ta tambayi kanta domin wannan bacci da ta yi bai yi kama da na lafiya ba.

Da sauri ta miƙe ta shige ba yi tana tunanin to wane sallah ya kamata ta fara.

Bayan ta idar da sallah sai ta yi sauri ta ruga zuwa falo,saboda kiran curoma da cikinta yake yi.A haka dai ta ƙarasa tana mamakin jin gidan ya yi shiru,kamar ba mutane a gidan.

Ta shiga cikin tsananin tashin hankali da ta duba lungu da tsaƙo ba ta gan su ba ,sai ta fara kuka da salati tana dubawa cikin tsoro.Ta ɗauki tsawon lokaci amma ba ta ji ɗuriyar kowa ba.

Tana tsaye a farfajiyar gidan motar Baba Sani ya sawo kai.Da sauri ta ƙarasa gurin shi cikin muryar kuka don tunaninta ya fara ba ta yana da saka hannu na rashin ganin su,ko kuma shine ya ɗauke su.

" Baba Sani ina Mama na duba ko ina ban ganta ba."

Wata irin tsawa ya daka mata ya ce."Ku ji min munafuka ban sani ba,duk abin da ke faruwa ba da saka hannunki ba za ki raina min wayo."

Zare idanunta ta yi ta ce."Wallahi ba ni da masaniya akan komai mai ya faru?"

Kallonta ya yi sai ya matso kusa da ita ya fara magana cikin ɗaga murya." Jiya A.m ya sameni ya ce kun yi da shi zai kai Mama wani gari har zuwa lokacin da za ku rabu,saboda na gaya masa ta kawo min ƴan sanda."

Ya faɗa ranta a ɓace da baƙin ciki ƙarara a fuskar sa." Wallahi sam ba haka na so ba na so a ce yabar mini komai a hannuna,saboda na yi baƙin cikin irin daular da ya kaita."

Juwairiya ta kaɗu da jin abin da ya faɗa sai ta saka kuka sosai,ganin yanzu Mama ta san abin da ta aikata.

A ƙasa ta zauna tare da ƙara sakin kuka." Na shiga uku ba zan iya ƙara gaɗa ido da Mama ba,wane irin kallo za ta yi min wallahi na yi dana sani ƙwarai,yanzu idanuwana ba za su ƙara ganin ta ba har saina haifa mi shi yaro."Sai ta ji hawaye na sintiri akan fuskarta.

Sosai ta shiga tashin hankali ta na jin ba za ta ƙara iya haɗa ido da Mama ba,don ta san daga ranar da ta ji abin da ke faruwa za ta tsaneta na har abada.

Ganin irin kukan da take yi sosai kamar ranta zai fita a ranta ta na jin baƙin ciki matuƙa.

Baba Sani bai duba halin da take ciki ba ya ce." Ki kwantar da hankalin ki ni kaina na yi alƙwarin saina raba auren ku,in har na buƙaci kuɗi bai ba ni ba,wallahi saina tona asiri komai ya wargatse saboda na tsani ganin ki a cikin wannan daular,in kuma baya haihuwa ne sai ya sake ki don ba za ki zauna da shi ba."

Ba ta ce masa uffan ba har ya gama magana ya fice.

Juwairiya sai ta ji ba za ta iya zama a cikin gidan ba,domin duhun da ya yi mata yafi duhun ƙabari.

Ta yi kuka har ta ba uku lada tana ji wani irin kunyar Mama matuƙa tun kafin ta haɗa ido da ita.Take nadama ta shige ta har ta fara tunanin ba za ta taɓa yadda ta ƙara haɗa ido da Mama ba,matuƙar A.m bai aminta da ita ba a matsayin matar sa,wacce zai yi rayuwa da ita na har a bada.

Duk kiran da yake mata ƙin ɗagawa ta yi tana cikin haɗa kayanta,sai ta ji hucin mutum a bayanta,wanda ta gane A.m ne domin in dai ya zo guri turaren sa yake fara bayyana kan sa.

Kuka ta saka masa sosai tana dukan sa aƙirjin sa,ba tare da ya hana ta ba ya ƙyaleta don ya san dole ta yi,ita da take da hawayen banza ba'a taɓa ta ba ta yi kuka ina ga an rabata da Mama.

Ganin tana ta dukan sa amma ya ƙi ko motsi sai ta ƙara fashewa da kuka tare da faɗawa jikin sa.

" Mai ya sa zaka rabani da Mama anya ka yi min adalci kuwa,da wane ido kake son na kalle ta?Bayan ta san cewa na yi aure ba tare da sanin ta ba! Ni na san Mama ba za ta taɓa yafe mini ba,domin ita ba irin Baba Sani ba ne."

Ƙara rungumeta ya yi tsam a jikinsa ya na jin gangar jikinsa ya yi kewarta matuƙa.

" Ki gane ba ni da nufin na cutar da ita sai dai na yi hakanne don kar ta hanani samun farin cikina.Ina cikin damuwa sosai aurenki da na yi na yi ne don na samu cikon burina,amma kullum damuwa yake ƙara min ga Baba Sani da ya maida ni bankin sa, ga Mama sannan Zainab ta fara zargina dake jiya na shiga tashin hankali domin a kwai wanda yake bibiyarmu.Anya Juwairiya ke alkhairi ce a gareni?"

Ya faɗa yayin da idanuwansa suka canza launi saboda tsananin damuwar da yake ciki.

Da sauri ta janye jikinta gare shi tana jin wani iri zafi sosai jin abin da ya faɗa.

" Wayyo Allah na! Na roƙe ka ka cire min son sa a cikin zuciyata mutumin da nake so fiye da rayuwata,yake ganin ni ba alkhairi ba ce a rayuwarsa."

Ta faɗa a fili sai hawaye suka ci gaba da turereniya a fuskarta.
Tasowa ya yi zai riƙe ta ya buɗe baki ya ce." Sam b......"

" Don Allah ka fita daga gidan nan ba na son ganin ka! Ka fita kafin kasa zuciyata ta buga."Ta katse shi tana nuna masa hanyar fita.

Cikin zafi ya kalle ta." Ok na ji zan fita amma ki gaggauta dawowa gidana domin ki haifa min babyna mu rabu tun kafin Zainab ta fahimci komai,sannan Zainab ta sha alwashin cusgunawa rayuwarki domin ta gano gaskiyar lamarin dake tsakaninmu,don haka ki shirya duk wani cin kashi da za ki gani a gidan,sannan ba zan yi koma baya ga lamarin ba domin mu samu mu fita daga zarginta."

Sai Juwairiya ta fara kallon sa kamar wani mahaukaci yayin da take ji tabbas A.m ba ya sonta kamar yadda ya sha faɗa mata.

Wani irin baƙin ciki ya tokareta wanda y saka ta ji a ranta za ta iya bijire musu duka tare da tona asirin komai,don a yadda take jin zuciyarta ba za ta iya ɗaukar cin kashin da Zainab za ta yi mata ba.

Tabbas za ta tona komai ta fito ta nuna ma duniya ita ma matar shi ce,in yaso sai sama da ƙasa ta haɗe,haka kawai ya din ga ƙwallo da rayuwarta don kawai ya ga tana son sa.

Riƙe rigar A.m da ya juya zai fita ganin ta ƙi cewa komai da nufin ta gaya masa baƙaƙen maganganu,amma yayin da ya zuba mata idanun sa masu kama da an zuba zaiba a ciki,sai ta ji wata irin narkakkiyar dalma na son sa ya zagaye duk ilahirin jikinta,kuma ba ta taɓa ganin Mama ta yi sa in sa da mahaifinta ba.

Juwa ta yi da sauri ta yi ta shige ɗaki tare da sakin kuka mai ƙarfi.

A.m ya daɗe a ƙofar gidan ya duƙar da kansa a kan sitiyarin motar sa,sosai ya jima a gurin ya na jin damuwa a ran sa.

Wayar sa ya zaro ya nemo numbar ta da ya yi saving da suna damuwata,domin haka yake kiran ta tun da ta shigo cikin rayuwar sa ta saka mi shi damuwa.

Da ya yi nufin ya kirata akan su tafi sai kuma ya tuna bai san wanda yake musu shishshigi ba,da sauri ya figi motar sa a guje ya bar ƙofar gidan,a ran sa ya na addu'ar Allah ya sa ta dawo yau saboda ya yi missing ɗin girta.

A ranar ta shirya ta koma gidan A.m saboda gidan ya yi mata babu daɗi.

Suna zaune a falo Zainab ta kwanta gaba ki ɗaya a jikin shi tana zuba mishi shagwaba,yayin da shi kuma sai biye mata yake yana ƙara saka ta cikin lambun son sa.

Hankalin sa na kan ƙofa ganin yamma ta yi ba ta shigo ba,wayar sa ya zaro ya ƙara tura mata da tsaƙon da ya tura yafi sau ba adadi kamar haka.

"Aslm mai kike yi har yanzu ba ki dawo ba,na gaya miki kar ki ƙara mintuna a gidan na maza ki dawo.Da fatan za ki bi umurnina a matsayina na mijin ki n wucin gadi."

Tun da ta ƙaranta sau ɗaya ba ta ƙara gigin ƙara karanta wa ba,duk da tsaƙon yana shigowa duk bayan mintuna.


Da siririyar sallama ta shigo wanda idanun A.m yana kallon ƙofar shigowa.Karab suka haɗa ido ya yi sauri ya ɗauke kan sa,sai ya ɗan ture jikin Zainab ya miƙe da sauri zai haye sama.

Zainab da sauri ta kalli bakin ƙofa ta kuma mai da idanunta kan A.m da ya miƙe yana danna waya zai haye sama.

                 " Honey ina za ka je."

Ba tare da ya kalle ta ba ya ce." Ba shopping kika ce zan kai ki ba?Ina son na watsa ruwa zafi nake ji."Ya faɗa ba tare da ya kalle ya ba.

Hannun sa ta kama ta riƙe tana sakin mi shi lallausar murmushi. Tare nake son mu yi jirani just one minute."

Ta juya kan Juwairiya dake tsaye kamar sanda tana kallon su."Sannu mara mutunci Mamar ta ki mutuwa ta yi da kika je kika zauna?"

Juwairiya da take jin gabaki ɗaya ranta babu daɗi ,ba ta tanka mata ba sai ajiyar zuciya da ta sauke,na alamun wacce ta ci kuka ta ƙoshi.

" Ke ni za ki kawo wa rashin mutunci banza yar matsiyata ki kula in kika ce hauka za ki yi mini,wallahi sai in kashe ki in kashe banza,na ga uban da zai tsaya miki.Ai ni duk wanda ya shiga gonata saina raba sa da rayuwarsa,kuma mu zuba mu gani shege ka fasa."

Ka sa ce mata komai ta yi ta saci kallon A.m da ya jingina jikinsa da kujerar dinning har yanzu,danne-danne yake a wayarsa ba tare ya tanka ko kallon ɗaya daga cikin su ba.

" Ni fa zafi nake ji so zan shiga ciki sai kin shigo."Ya faɗa babu ko ɗigon damuwa a ran sa.

" Yarinyar nan ta ba ni haushi fa tana sane da kuɗi nake biyan ta,amma ta je gida ta zauna Allah saina cire kuɗina don ba zan yi asara ba."Ta ce tana kallon A.m ko zai ce wani abu.

Watsa mata mugun kallo ya yi tare da jan tsuka." Duk abin da za ki yi mata ki ba ƴar aikin ki ba ce,ina ruwana wannan ya rage naki."
Yana gama faɗin haka ya haye matakalan bene ba tare da ya kalle ta ba.

" Ki yi haƙuri jikin ta ne ya yi tsanani har sai da muka kwanta asibiti k..."

"Rufe min baki shashasha." Ta katse ta cikin tsawa.

" Da ga yau duk wani aikin gida ya koma kan ki Lantana ba za ta ƙara komai a gidan nan ba,maza ki wuce underwears ɗina sun yi datti ki haɗa da na A.m ki wanke.Ta faɗa tare da kama kunninta sai kuma ta saki ta haye sama.

Tun daga wannan ranar take wahalar da ita duk wani aikin gidan ita take yi,dalilin haka ko makaranta ba ta zuwa wani lokaci,domin ƙawayen ta take kwasowa ta saka ta girki,har in za su tafi ta ba su abincin ba sai sun yi girki ba.

Wani lokacin sai ta kira ƙawarta ta ce ga za ta turo Juwairiya ta yi kwana biyu ta taya ta aiki.Ga zagi da cin mutunci komai aka yi ita ce.

Juwairiya ta yi shiru ne sakamakon tsorata ta da A.m ya yi kan in ta yi gigin tona asiri,zai cutar da Mama sannan ba zai gaya mata in da take ba.Hakan ya sa take jure duk wani cin kashi da take mata.

Kusan tsawon lokaci ta yi tana saka ido a tsakanin su haka Lantana ko tari ta yi idanunta na kanta.

A.m ya kauda duk wani abu da na zargi da shiga tsakanin su,har faɗa yake ma Juwairiya kamar bai santa ba,kuma kullum cikin sata aiki yake in dai yana gida.

Duk wani saka ido ta yi ta gaji daga bisani ta ci gaba da harkokinta dama ta san A.m ba zai taɓa iya kalon ta ba,balle yanzu da duk ta zube ta lalace saboda wahalar aiki da ƙuncin son maso wani da take yi,sai hanci da ta yi gashi kullum sai ta yi mafarkin Mama da Ibrahim.

Tafiya ta kama Zainab ba tare da wani shakku ba ta bar ƙasar bayan ta saka Lantana,ta din ga kwana a gidan har ta dawo hakan bai wani ɗaɗa A.m da ƙasa ba ya amince.

Cikin dare bayan sun yi bacci A.m yake shaƙa mata Lantana maganin bacci,wanda in ta kwanta sai safiya take farkawa.
Sai safiya ta yi ta din ga ƙorafi tana mamakin baccin da take yi ita dai Juwairiya dariya take mata sosai.
Juwairiya ta gasganta A.m ƙarshe ne gurin wayo da basira,ita kanta mamakin sa take ga wayo da iya kalami ga mace wanda hakn yake sa ta mutu ƙaunar sa.


Zaune suke a cikin makaranta ita da Hauwa Juwairiya ce ta siyo su agwaluma da yalon Bello,tana ta ci tana lumshe idanun ta domin su take son ta ci.

Hauwa ta kalle ta ganin yadda take ci kamar wata mayunwaciya.
Ganin yadda ta kafe ta da ido sai ta ɓalli agwalumar ta cige baki,saboda tsami amma haka take son sha.

" Humh ke ma ka yi mamaki kamar wata mayya haka na tashi ina son na sha agwaluma,bayan ni ba mutuniyata bace saboda tsaminta."Ta ƙara ɓalla tare da lumshe idanunta saboda daɗi.

Dariya Hauwa ta saki ta ce."Anya lafiyarki ƙalau kuwa ko dai ciki kika samu?Ni fa ina ganin kamar ciki ne da ke?"

Da sauri ta miƙe tare da yar da agwalumar cikin tashin hankali ta zare ido ta ce."Na shiga uku ciki fa da kika ce gaske ne?"

" Ina zan sani tunanin haka nake gani a jikinki yau kuma kin zo da baƙon lamari abin da ban taɓa ganin kin sha ba kike sha.To ke ya kamata ki gane yaushe rabon ki da yin ɓatan wata?"

Ta tambaye ta ganin yadda ta diririce har hawaye sun fara sintiri a fuskarta.

" Umh umh wallahi na manta tashin hankali ba zai barni na tuna ba,amma ina ganin kamar tun ina gidan Mama wayyo Allah na bani!"

"Mene ne na banuwa Juwairiya fata za ki yi Allah ya sa wannan cikin ya dasa so tsakanin ki da mahaifinsa."
" Tab!Ai wallahi in Zainab za ta iya haihuwa to ni ma zan bar wannan cikin a jikina zubar da shi zan yi ko da zan rasa rayuwata ne,nufin ki na fara irga watannin rabuwa da A.m na koma gurin Mama? Ba zan iya ba domin ban san da wani idon zan iya kallon ta ba."Ta ce cikin kuka.

" Haba wai ke mai yasa ba ƙya fahimtar magana da ɗaukar shawara ne! Ki bar cikin jikin ki na tabbata shine makamin da zai jawo kusanci tsakanin sa da mahaifin sa."

Hauwa ta faɗa cikin zafi domin zuwa yanzu ta fara ba ta haushi ganin ta cika kafiya da taurin kai.

" Na lura ba kya sona so kawai kike na rabu da farin cikina.To sai na zubar da cikin nan kuma babu wanda ya isa ya hana."

A zafafe ta furta cikin ɓacin rai tana gani n kamar ba ta son zaman ta da A.m.

" Ni ban ce ba ina baƙin cikin yadda kika ɗauki so kika ba ma namiji wai shin shine kaɗai namiji a duniya,na tabbata ko rabuwa kuka yi za ki samu namiji mai kyau ki aura,ke ma ki na da kyau."

Miƙewa ta yi tare da ɗaukar takaddun ta."In har za ki taimakamin na zubar ki zo ki raka ni asibiti,in kuma ba za ki ba ai na san hanya."

Ta nufi hanyar fita da sauri Hauwa ta biyo bayan ta duk da ba ta farin ciki da zubda cikin amma babu yadda za ta yi.

Likita ya kalle ta cikin mamaki sam ba ta yi kama da mutuniyar banza ba,amma mai ya sa take son ta zubda ciki? Da kuma ya tuna mugu ba shi da kama.

" Don Allah likita ka taimaka ka zubda cikin nan ko nawa ne za mu baka."

Juwairiya ta faɗa jikinta na rawa ta kwaso duk kuɗin da ke jakanta ta ije a teburin sa.

Duk tsoron da take ji na allura haka ta bari ya zumbuɗa mata tana cige baki,sannan ya ɗauko wani magani ya ba ta kan in ta ji ciwo ta sha guda biyu.

Tun kafin ta dawo gida take jin wani irin jiri kamar za ta faɗi! Ko da ta dawo gida kwantawa ta yi saboda ciwon da mararta take yi,yayin da ciwon yake ci gaba kamar ana tsira mata allura.

A haka ta kwana kamar za ta baƙunci lahira, duk yadda ta so ta ɗauki waya ta kira Hauwa ta gaya mata za ta mutu,saboda Zainab na nan A.m ko kallonta ba zai yi ba,amma ta kasa saboda ciwon mutuwa da take ji.

Washegari ko ɗaga ɗan yatsarta ba ta iya wa sunan Allah kawai take faɗi a bakinta da yake motsawa,tana kukan rabuwa da Mama ba tare da sun yi bankwana ba.

Jinin dake zuba kamar an buɗe famfo ya sa ta gane mutuwa za ta yi,sai ta fara maimaita kalmar shahada numfashinta na ɗaukewa.

Zainab da duku-duku ta fice asibiti saboda a kwai wani bawon Allah da za ta yi mata aiki da misalin biyar da rabi na safe,tun jiya aka so ayi aikin sai dai an kawo shi ta riga tabar asibitin,kuma ƙa'ida ne in har ta koma gida ba ta dawowa.
A.m dake zaune a falo ya na kallon news mamaki ya kama shi ganin har wannan lokacin ba ta fito ba ta ɗaura abin karya.

Miƙewa ya yi tare da saka takalmi ya nufi ɗakinta.

Halin da ya ganta ya yi masifar ɗaga mishi hankali,ba tare da wani tunani ba ya taitayeta ya saka a mota ya nufi asibiti da ita.

Da ƙyar aka samu aka tsaida jinin bayan cikin ya fita.Hankalin A.m ya tashi gani yake kamar mutuwa za ta yi wani irin tausayin ta ya kama shi,ya na jin bai yi mata adalci zai barta ta mutu a ɗaki.

Zura mata ido ya yi cikin tausayi ya na shafa kanta.Da sauri ya kamata ya riƙe tare da tallabota ganin ta buɗe ido.

Juwairiya zuciyarta ta buga ganin likita ya shigo riƙe da fayal a hannun sa,tsananin tsoro ya cika mata zuciya don ta san yau a sirinta zai tonu.

A hankali A.m ya maida hankalin shi kan likitan da ya miƙa masa fayal,ya ba masa bayani da harshen turanci duk da cewar Bahaushe ne shi.

" Ina baka haƙuri na zubewar baby don madam ta yi ɓari ne,har sai da muka yi mata wankin ciki.Ga waɗannan maganin za ka siya an sallame ta."
Wani irin tashin hankali ya ziyarce shi riƙe likitan ya yi tare da jijjiga shi." Mai ya sa ka bari cikina ya zuba ka san shekara nawa na yi ina son na haihu?Wallahi sai kun dawo min da cikina don ba zai yiwu ba!"

A.m ya faɗa ya na naɗe hannun riga zai yi dabbe gani yake kamar gazawar su ya sa cikin ya fita.

" Am sorry wallahi bamu da hannu a cikin zubewar cikin na nan! Amma na yi mamakin yadda kake son kaga ka haihu matar ka ta iya zubda cikin dake jikinta,don bincike ya nuna mana magani tasha mai ƙarfi har cikin ya fita."

Sai A.m ya kalle shi kamar mahaukaci ko bai fahimci mai yake nufi ba,ya kuma juya ya kalli Juwairiya wacce ta bayyana gaskiyar zargin da yake mata,saboda yadda ta yi tsuru-tsuru na rashin gaskiya.Wani irin shaƙa ya kai mata cikin tashin hankali.

Zainab da ke tafe a cikin motar ta tana tuƙi cikin tsananin nishaɗi,sakamakon ta yi aiki cikin nasara wanda hakan yake saka ta tsananin farin ciki a duk lokacin da ta yi aiki.
Wayarta ta ɗauka ta kira layin A.m amma har ta yi masa kira biyar bai ɗauka ba.
Ko da ta iso haka kawai sai ta ji gabanta ya faɗi.

Maigadi ya wangame mata get ta shiga ta yi parking da sauri ta shige ciki,saboda yunwa take ji matuƙa.Da fari ta so ta fara cin abinci amma sai ta ga rashin dacewar hakan ta shige wanka.

Bayan ta fito tana ɗan dube-dube a cikin dirowar gadonta sai ta ga wani magani an ɓoye shi a cikin dirowar.

Da sauri ta buɗe gabanta ne ya buga dam! Sa'ilin da ta ga sunan dake manne a kwalin maganin.

" Maganin ɗaukar ciki da wuri."Ta maimaita sunan maganin da Hausa.
" Me A.m yake yi da shi bayan ni ba na haihuwa?"

Tambayar da ta yi ma kanta kenan amma ba ta da amsarta.
Wayarsa ta gani duka uku a gida bai ɗauki ko ɗaya ba sannan ba shi a gidan.
Juwairiya sunan da ya faɗo mata a rai kenan ta saki wani irin ƙara,da sauri ta sauko har tana faɗi ta mulmulo amma ba ta kula ba.

Wayam babu ita sai wayarta dake yashe a kan gado.Da sauri ta ɗauki wayar duk da ta san a halin da take ciki ba za ta iya karanta komai ba.

              TO FA ƘARA! ƘARA!! ƘARA !!!





KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

   BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI



           SAKACINA KO HALIN MAZA 


                              TAKU 

                 JAMILA LAWAL ZANGO
                             JAMCY





  Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba ***_.


Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.






COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.