Free chapter · Read without an account
Chapter 27
*SAKACINA KO HALIN MAZA?*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*
*Page 27*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
Ta na riƙe da wayar cikin tsananin tashin hankali yayin da jiri yake iban ta da ƙyar take iya buɗe ƙwayar idanunta.
Sai dai duk iya iyakan ƙoƙarinta don ta gano pattern ɗin da ta saka wayar,amma ta kasa har ta haƙura za ta kwaɗa wayar da ƙasa sai kuma ta fasa,ta ƙara kwatantawa sau biyu cikin ikon Allah a na biyun wayar ta buɗe.
Bincike ta fara yi a wayar wanda iya yinta ba ta ga wani abu da zai dasa mata zargi ba,saboda Juwairiya ta adana duk wani abin da ya shafi A.m a cikin wayar ta ɓoye shi.
Ta yi nufin ta ije wayar sai kuma wata dubara ta faɗo mata ta danna numbobin A.m.
Tana fara danna numbobin sai ga numbar A.m ta fito ɓaro-ɓaro an yi saving ɗinta da rubutun larabci,wanda iya ƙwaƙwanta ta yi ta gane mai sunan yake nufi,amma ta kasa saboda rubutun babu wasulla,ga shi karatun arabin na ta an yi ɗan cikin cokali.
Durƙushewa ta yi a gurin tare da saka wani gigitaccen ƙara,kamar wata mahaukaciya ta fara rotsa,duk wani kayan ƙawa dake cikin gidan tana ƙunduma ashar.
"Wallahi ku dawo gidan nan nice ajalin ku sai na kashe ku duka mundin na gane cin amanata kuke."
Gurin mai gadi ta nufa kasancewa yau Lantana ta na hutun ƙarshen mako da take yi.
"Kai ina A.m ya yi bayan gida a buɗe sannan Juwairiya ita ma ba ta nan?"
Jikin sa ya kama rawa dama tun da yaga Am ya fito da Juwairiya a hannun sa,ya sha mamaki ganin tana matsayin mai aiki ya ɗauko ta.
Sai ya ƙara kallonta ya ga yadda ta birkice kamar wacce aka kwanto daga turu, tana zare ido ai ba za a ji mutuwar Sarki a bakin sa ba.
" Hajiya ban sani ba da yake na zaga bayi yau na tashi da motsawar ciki."Wani wawan mari ta sakin mishi.
" Banza wawa kawai banga amfanin aikin ka ba."
Ta juya saboda ba ta cikin yanayin da za ta iya wani dogon magana.
******
A.m da ya shaƙe ta tamkar zai kaita lahira yana jin zai iya kashe ta,saboda tsabar tashin hankalin da yake ciki.Ga baki ɗaya idanun shi sun yi jajur tamkar garwashi wuta,ya canza kalar da ba ta taɓa sanin yana komawa ba.
Da ƙyar take kakari saboda wahalar da ta sha,ga kuma A.m yana shirin kaita lahira ba tare da kwananta sun ƙare ba.
" Uban me na yi miki da za ki kashe min yaro?Da kuɗina na siye rayuwarki a she ke kike hana ciki ya shiga jikinki? Na rantse yadda kika salwantar min da yaro sai na kashe ki."
Juwairiya da take jan numfashi da ƙyar idanunta sun yi gulu-gulu,domin A.m ya yi mata shaƙa ba na wasa ba.
Likitan dake tsaye yana kallon A.m da ya zama mahaukacin ƙarfi da yaji,tsoro yake ya matsa kusa da shi kar ya illata shi,amma da ya ga yana shirin kisa,sai ya matsa tare da riƙe shi da ƙarfi ya ce."Ma za ki tashi ki fita don ki ceci rayuwarki."
Duk da ba ta jin ƙarfi a jikinta amma haka nan ta ruga,daidai lokacin da A.m ya ture likitan ya faɗi ƙasa ya bugu da bango,ya ɗauki wani ƙarfe dake gefe ya ɗaga zai maka mata.
Da sauri ta fice daga ɗakin cikin tashin hankali, tana jin kamar ta sume jikinta babu daɗi,amma ya zama dole ta ceci rayuwarta,don yau ta ƙara tsoron A.m sosai a ranta.
A.m da haushi ya ishe shi ganin Juwairiya ta gudu,ya san ko ya duba ta ba zai gan ta ba,saboda asibitin bene ne ga lungunan dake cikin asibitin,ƙarfen da ya yi ninyar maka mata shi ya buga ma likitan,tare da ficewa da sauri yana neman ta.
Sai dai ya nemeta sama da ƙasa bai ganta ba ƙara ya saki cikin ƙaraji, ya rantse yau da ya ganta sai ya raba ta da numfashinta,sannan kuma sai ta gaya masa dalilin ta na zubar masa da ciki.
Ya kai ma iska naushi cikin takaici yana dunƙule hannun sa,ji yake kamar ita yake duka.Allah ne kawai ya taimake ta da ta gudu da yau sai dai wata ba ita ba.
" Wayyo Allah dama ina haihuwa da gaske zan iya haihuwa?"
Ya daɗe a gurin yana ganin kamar za ta fito daga ƙarshe ya shiga motar sa,wanda Allah ne kawai ya sa ya iso gida.
Sai dai yana shiga cikin gidan ya tsaya cikin tsoro ganin an yi ma gidan kaca-kaca,komai na gidan an fasa hatta tv dake manne plasma duk ta yi raga-raga da su.
Ko da ya shiga cikin ɗakin sa sai ya gwammace gara ɓarnar falo da ta yi akan na cikin ɗakin,saboda duk wani takaddu na shi na amfani sai da ta yaga su ta yi mi shi ɓarna sosai.
Tsayawa ya yi da mamaki yana kallon ta tsoro ma ta ba shi,ganin yadda ta wargaza gashin kanta ta zama kamar wata mahaukaciya.
Tashin hankalin da yake ciki yasa ya kasa tambayarta abin da yake faruwa,duk da zargi da yake yi akan ta gane komai.
Zainab ta ƙaraso gurin sa cikin tashin hankali,ta shaƙe shi idanunta sun canza kala,tsabar kishi cike a idanunta ji take kamar ta kashe shi,kawai ta huta domin ya cuce ta.
" Munafuki azzalimi mayaudari yau Allah ya tona asirin ka,dama amanata kuke ci kamar yadda Lantana ta faɗa min ka ƙarya ta?
A.m ɗanka kake son ya fito ta zina ?Ba na haihuwa mai ya haɗa ka da maganin ɗaukar ciki da wuri."
Duk da cewar ya ji maganar ta dake shi amma sai ya sauke ajiyar zuciya da ya tsaya iya nan ta sani.
" Zainab ki fahimce ni wallahi ba na zina kuma ba zan taɓa yi..."
"Rufe min baki mazinaci kawai? Yau Allah ya tona asirin ka na gama yadda da kai.Ni da ba haihuwa nake ba,in fact ba ni da mahaifar da zan ɗau ciki kake shan ƙwayoyin ɗaukar ciki da wuri."
Ta ja numfashi da sauke nauyayyar a jiyar zuciya,tana gumurzun kuka gaba ki ɗaya ta fita hankalin ta.
A.m da ya rasa abin yi ƙarasawa kusa da ita ya yi yakai hannu zai taɓa ta,da sauri ta janye jikinta tana mishi wani wulaƙantaccen kallo.
" Ni Allah ya tsare ni na ƙara barin ka taɓa ni da hannun zina ai..."
" Zainab!"
Ya katseta cikin ƙaraji sannan ya nuna ta da ɗan yatsa." Kar ki ƙara kirana da mazinaci in ba haka ba jikinki ne zai gaya miki."Ya ce cikin ɓacin rai.
" To meye kai in ba mazinaci ba ko fasiƙi kake son na ce maka,wallahi na tsane ka ba na son ko kallon mayaudariyar fuskar ka,dole ka sake ni ba zan zauna da mazinaci ba."
Ta ce tare da ƙara cikwikwiye shi sannan ta ɗora da cewa." A.m yar aikina fa kake nema!Na shiga uku Juwairiya ƴar matsiyata mai take da shi wanda ba ni dashi?"
Girgiza hannunta yake yi akan ta sake shi,ya fara magana da muryar sa da yake sace mata zuciya,amma sai ta ɗaga mishi hannu dare da daka mishi tsawa,kamar wani ƙaramin yaro tana masa wani mugun kallo.
"Sake ni na ce ka bani takadda ta kuma na rantse maka,sai na maida Juwairiya kalar da duk wani ɗa namiji ya ganta ba zai yi sha'awar ta ba.Ai ni ka gama tsara ni da kalamanka na yaudara matsiyaci kawai."
Ƙwace jikin shi ya yi yana hararar ta ji yake kamar ya kai mata bugu,ganin ta ƙara masa tashin hankali.
" Ki san maganar da za ki gaya mini mijinki ne, ni in har kika ƙara zagina zan miki hukunci,yanzu jikinki zai gaya miki ba tare da na yi nadama ba."
Ƙara cakumo shi ta yi ta kama gaban rigar sa ido cikin ido ta ce."Na faɗa kuma abin da ya fi haka zan faɗa banza mai zan yi dakai sake ni na ƙara faɗi mazinaci ƙazami!"
Mari ya kai mata amma sai ta goce da sauri tare da fisgo rigar shi,ganin ya na son ya fita a ɗakin ta kama ta sai da dire ta har ƙasa.
Duka ya kawo ma hannunta da ƙarfi ta saki jikin shi tare da sakin ƙara,amma kuma sai ta yi kukan kura ta kama shi da dambe.
A.m da yake jin zuciyar shi a wuya ba tare da tunani ba,ya shiga jibgar ta kamar ya samu jaka don iya ƙarfin sa yake dukan ta.
Da fari ta biye mishi tana kokuwa da shi,amma da ta ji kasheta zai yi,da gudu ta ruga ɗaki ta ɗauko gyale sai gida.
A.m ya durƙushe a gurin cikin nadama tare da kai ma bango naushi." Tabbas na gasganta cewa ke ɗin ba alkhairi ba ne a rayuwata!Juwairiya na tsane ki kuma wallahi sai kin yi nadama sosai,don sai na illata rayuwar ki yadda kika sa na doki matata mafi soyuwa a gare ni."
Juwairiya da take jin rashin ƙarfin a jikinta,amma haka take gudu don ta tseratar da rayuwar ta,saboda yau ta ƙara gasgantawa A.m ba shi da imani kashe ta zai yi.
Hawaye yana zuba a fuskarta da ta tuna irin tashin hankalin da A.m ya shiga,saboda jin ta zubda ciki nan take tsananin nadama ya shige ta sosai.
Tsayawa ta yi cikin tashin hankali ta rasa in da za je,gidan Hauwa ya faɗo mata a rai sai ta tari ɗan mashin.
Tana shiga ta rungume Hauwa da ta fito daga cikin ɗaki jin muryarta tana kuka.
" Juwairiya lafiya mai ya faru?"Ta tambaye ta cikin tashin hankali.
" A.m ya yi fushi da ni na shiga uku! Wallahi ya tsane ni baya sona!"Ta ce tare da sakin wani irin kuka.
" Don Allah ki daina kuka ki yi mini bayani mai ya faru."
Ganin ta kasa magana sai kuka take na fitar hankali.
Zaunar da ita ta yi sannan ta ba ta ruwa tasha sosai ta kama hannunta ta riƙe." Don Allah ki gaya min mai ya faru."
Zubbur ta miƙe tare da ɗaukar hijabinta.Hauwa ta riƙe mata hannu ta ce." Wai mai ke faruwa ina A.m ki sanar da ni."
" Gurin A.m za ni ya yi fushi da ni ya gane na zubda ciki,don Allah ki zo mu je mu bashi haƙuri,wallahi ba zan iya rabuwa babu shi ba,don ina son sa."
Da takaici ya ishi Hauwa tsaki ta yi ta kamata tare da zaunar da ita akan kujera." Ba na son shashanci kin san ba kya son ki rabu da shi,kika zubda cikin da yake so?Babu yadda ban yi da ke ba,amma da yake kunnin ƙashi ne dake kika ji ƙi.Na rasa yadda zan yi ba kya jin magana haba ya kamata ki fahimci mai kike yi."
Share hawayenta ta yi ta ce." Zan je na ba shi haƙuri ba zan ƙara zubda cikin ba,in dai haka zai saka shi farin ciki,amma ki je ki ba shi haƙuri don Allah."
Hauwa ta yi shiru ta na jinjina lamarin domin sam bai yi mata daɗi ba,ta san da ma in dai A.m ya sani gakan zai faru,gara da ya sani ya ɗauki mataki.
" Hankalina ya tashi sosai baki ga irin fushin da ya yi ba ,na san cewa ba zai taɓa nema na ba,gashi garin neman gira na rasa rasa ido.Na san ayanzu ya tsane ni ba ya son ganin fuskata.
" Rashin ɗaukar shawara irin na ki shi ya ja miki,Juwairiya ya kamata ki gane gaskiya.Ni dai yanzu shawarata kar ki ce zaki koma gurin sa saboda ya yi fushi dake mai tsanani."
Ta ce tana kallonta da takaicin abin da ta jawo ma kanta,sannan ta ci gaba da cewa."Yanzu kin ga ba ki da lafiya ki ci abinci kisha magani,ni na san da zarar A.m ya huce zai neme ki don lamarin ku sai ku."
Ta faɗa tare da miƙewa ta nufi kicin bayan ta rufe ƙofarta da key,saboda a take-taken ta za ta iya fita ta je gurinsa.
A.m ya daɗe a ɗakin yana zaune tamkar mutum-mutumi,gaba ki ɗaya ran sa ya ɓace da abin da ya faru,duk sai ya ɗauki laifin komai ya ɗora akan Juwairiya.
Wayar sa ya fara dubawa don ba zai ce ga in da take ba.Sai dai ya gwammace dama faɗuwa ta yi kan yadda ya ga Zainab ta mai da wayar.Sai ya ɗauki key ɗin mota ya fice gidan A.k.
A.k na kwance a falonsa yana ya ɗora yaron sa a kan ruwan cikinsa yana mishi wasa.
A birkice ya shigo fuskar sa babu walwala ji yake kamar ya ɗora hannu aka ya yi ta ihu.
Zama ya yi ba tare da ya tanka ma Matar A.k da ke tsokanar shi ba,ganin haka sai ta ja bakinta ta tsuke.
A.k ya matso kusa da shi tare da dafa kafaɗun sa." Lafiya mai ya faru."Shiru ya yi zuciyarsa kamar za ta ƙone sai tafarfasa.
"Mu je cikin falonka ina cikin matsala A.k wallahi na rantse da zan ga Juwairiya ni ne a jalinta."Ya faɗa da ƙarfi cikin ɓacin rai.
Da sauri ya ja shi suka shige falonsa har da saka key.
A.k da ya yi shiru kamar ruwa ya cinye shi cikin tsananin mamaki yake kallon sa,domin lamarin ya girgiza shi.
" Yanzu kana nufin Juwairiya ba ta gidan,ina ta tafi na san dai ba za ta je gidan Baba Sani ba,sannan Zainab ta yi yaji yanzu lamari ya ɓace."
A.m ya yi ƙuta ya ce." Ina zan san in da take wallahi yarinyar nan ta ɓata min lissafi komai ya rikice,ban san wace hanya zan bi na shawo kan Zey,don ta yi fushi sosai,in da Allah ya taimake ni ba ta gane ta yi ɓari ba,saboda ba ta tuhume ni akan haka ba.Ina ji ina gani ta yi min asarar babyna abin da na daɗe ina nema."
Sai ga hawaye shar a fuskar sa ya na jin tsananin baƙin cikin asarar da tayi masa.
Wayar A.k ya fara ringing da sauri A.k ya kalle shi ya ce." Daddy ne yake kira kuma ina ga kai yake nema tun da kace Zainab ta fasa wayar ka."
Gaban A.m ya faɗi da ido ya nuna masa da ya ɗaga wayar.
A.k ya danna wurin amsawa tare da saka sifikar wayar.
" Ina abokin ka yake dama ya fara hauka ne?Ƴar mutane zai daka kamar ya samu jaka,maza ka taho da shi zaku gane baku da wayo tun da kai ba za ka iya ba shi shawara na gari ba."
Ɗif Daddy ya kashe wayar ba tare da ya ji mai A.k zai ce ba,don ya san suna tare da A.m.
Shiru suka yi kamar ruwa ya cinye su ko tari babu wanda ya iya yi.
A.k ya kalle sa da takaici yana gani duk shi ya janyo komai,haba ka auri mace ka ije wa matar ka,amatsayin ƴar aiki abin ya yi muni kuma babu tausayi a ciki.
" Lamarin mata haƙuri ake yi sai haƙur in ka ce dukan mace zaka din ga yi,to ya zaka yi duk ranar da ka haɗa mata uku ko huɗu?"
" Allah ya kyauta ya kuma tsare ni da tara mata uku,ko ita Juwairiya rabuwa da ita zan yi,zuciyata ba ta son wata ƴa mace sai Zainab."Dariya A.m ya yi suka fice.
Daddy ya yi faɗa kamar zai ari baki yana ta huci ji yake kamar ya rufe shi da duka.
"Saboda baka da hankali sai ka kama mace da duka goto-goto da kai.To wallahi maza ka je ka dawo da Zainab in ba haka ba za ka fuskanci fushina mai tsanani.Kuma duk ranar da ka ƙara dukan musu ƴar mutane wallahi sai na ɓata maka rai."
A.m ya yi shiru yanzu yake tsananin dana sani da ya duke ta.
Ko da ya shiga shashin mahaifiyar sa ranta ya ɓace matuƙa ta yi mishi tatas!Akan ya je ya dawo da Zainab.A.k yake ta bada haƙuri.
Daddy ya yi mishi faɗa sosai ya ƙara masa da hadisan monzon Allah da nasiha,sannan ya ba shi umurnin ya je ya dawo da ita.
Miƙewa suka yi kai tsaye gidan su Zainab suka nufa.A.m gabansa na ta faɗuwa don ya san ba za su kwashe ta daidai ba.
Jefi-jefi yana kallon hanya yana jin matsanancin ɓacin rai,in ya tuna da Juwairiya sai ya ja tsaki da ƙarfi ya kauda kan sa,daga ƙarshe ya ɗauki laifin komai ya ɗora akan Zainab don ita ta bada ƙofa har ta shigo rayuwar su.
Maigadi ya wangale ƙofa da alamun wani zai fita daga cikin gidan don ko hon ba su yi ba,Daddy Zainab ya fito da shiri makullin mota riƙe a hannun sa zai fita,ganin su ya sa ya tsaya yana musu wani irin wulaƙantaccen kallo.
Ya rantse da ace A.m ba ɗan amininsa ba ne yau kotu za ta raba su da shi,tun da har ya iya dukan masa ƴa guda tsoka ɗaya a miya.
" Mara mutunci uban mai ya kawo ka gidana ko ka zo ka ƙara dukanta a gabana ne? Ashe dama ba ka da mutunci na ɗauki abu mafi soyuwa na ba ka?"
Masifa yake musu bai bari sun shiga daga ciki ba ya shiga zagin su har da A.k da ya yi rakiyan,sai da ya samu na shi kason saboda mahaifin Zainab ya yi fushi,bakinsa har kumfa yake saboda an bugi shalele.
A.k haƙuri yake badawa har da duƙawa ya kuma janyo hannun A.m,don ya duƙa da ya yi ƙikam ya na tsaye,zuciyar sa na tafarfasa jin rashin mutuncin da yake musu,a gaban ƴan aikin gidan.
Da ƙyar ya basu izinin shiga cikin falon baƙi suka zauna kusan awa babu wanda ya bi ta kan su.
Tsalam mahaifiyar Zainab ta shigo cikin falon tana kallon A.m a wulaƙance.
" Sannu isashshe da za ka kama min ƴata da duka,an ce maka jaka na aura maka? Na rantse Zainab ba za ta dawo gidan ka ba,tun da ba ka da mutunci.
Mai take amfana da shi da auren ka sai tsiya da haƙuri na rashin haihuwa da ba ka yi,shine saboda kai mara mutunci ne za ka kama min ita da duka akan wata banza ƴar aiki,to wallahi ba ka isa ba don ba za ta dawo gidan ka ba.
Shekarar ku nawa da aure ko ɓatan wata ba ta taɓa yi ba,dole ka sakin mini ƴata ko kutu ta raba mu."Ta faɗi tana harare-harare.
Duk irin rarrashin da A.k ya yi musu amma sun kafe kan ba za ta koma gidan sa ba,sai nanata maganar haƙurin da take yi saboda rashi haihuwar da baya yi.
Cikin fushi A.m ya miƙe yayin da idanun sa suka kaɗa suka yi jajur.
Ya buɗe baki zai yi magana da sauri A.m ya kama shi suka fice waje.Hannun sa ya ja zuwa mota ba tare da ya ce komai ba,ya shiga motar suka fara tafiya.Ganin yadda yake huci sai ya kunna ƙira'ar alkur'ani.
Suna tafe babu wanda ya yi magana sai zuwa can A.k ya kalli A.m ya ci gaba da tuƙi.Jingina kan shi da kujera tare da lumshe idanun sa.
A lokacin da A.k ya shigo cikin falon A.m riƙe baki ya yi cikin tashin hankali yana kallon yadda falon ya hargitse babu mamora a falon
" Taɓ sai ka tanadar mata wasu ka ije saboda duk ranar da ta san da igiyar auren ka da Juwairiya,wallahi in babu kayan da za ta fasa sai dai wani Abdurrahman ba kai ba,lallai Zainab na da zafin kishi."Ya faɗa cikin tsigar mamaki da tsokana.
A.m da ran sa a ɓace ya kalle sa da takaici ya ce." Fata ma kake min ko so kake na rasa wani shashin na jikina,ni kaina yau na ƙara tsorata da lamarin ta,dole na ɗauki mataki kafin ta san da wannan zancan in dai ba so kake na koma tafiya da ƙafa ɗaya ba."
Dariya A.k ya yi sosai ya ce." Wannan ya rage naka ni dai babu ruwana tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka,kuma wanda bai ji bari ba ai ya ji hoho."
A.m ya matsa kusa da shi ya gallah masa harara."Ni ba wannan ba yanzu ya zamu yi da waɗannan marasa mutuncin gaskiya bazan iya zama ni kaɗai a cikin gidan nan ba,ni da nake da zuƙa zuƙan ƴan mata biyu yanzu na koma babu ko ɗaya.Gashi yaunwa make ji wunin yau ko ruwa ban saka a bakina,saboda matsalar da damuwata ta saka ni."
" Ya rage naka sai ka san in da zaka je kaci abinci amma ba'a gidana ba,don matata ba kukun ka ba ne,ko da ka ga ada ina baka abinci saboda babu wanda zai baka ne,amma yanzu tun da a kwai Juwairiya sai ka je ka yi biko."Tsaki ya saki take fuskar sa ta canza.
" Na rantse har yanzu ina kan bakana sai na hukunta ta za ta san da wane irin namiji take zama,da na je na kirata gara na kwana banci abinci ba."Ya ce da A.k da ya ɗauki makullin motar sa.
" Ok fine ya rage naka da na yi tunanin za ka yi bikon matar wucin gadi,ka huta kafin matar so ta dawo,saboda iyayenta sun yi fushi sosai kuma dole sai ka danne zuciyar ka akan duk abin da iyayenta za su yi maka,ƴar su kake aure kuma kai ka dakar musu ƴa."
" Na ji don Alkah ka tafi babu abin da kake yi sai ƙara tafarfasa min zuciya,da na so na gaya ma mahaifiyarta magana amma kuma na gode da ka hana ni da na yi katoɓara."
" Ok bari na tafi tun da ba za ka dawo da matar wucin gadi ba,sai ka ci gaba da cin abincin Lantana,sannan kar ka yi gigin zuwan min gida mai mata biyu ya zama gwauro."
Ya ce yayin da A.m ya fito don ya raka shi ba tare da ya bashi amsar shaƙiyancin da yake mishi ba.
Ya shiga cikin mota ya zauna tare da riƙe sitiyarin ya kalli A.m da yake riƙe da murfin motar yana jiran ya shiga,ya rufe mishi ƙofar motan.
" Ya kamata ka yi tunani A.m lokaci yana wucewa lamura canzawa,suke yi ka sanar da iyayen Zainab komai ka bayyana Juwairiya a matsayin matar k,tun kafin lamura su kwaɓe maka.Na tabbata da kai ne ba ka haihuwa Zainab ba za ta zauna da kai ba."
Rufe mishi motar ya yi ganin ya shigar da ƙafafunsa ciki,saboda fahimta da ya yi maganar da yake masa ba ta tasiri a zuciyar sa.
" Na riga na yi wa Zainab alƙawari ina sonta ba zan iya haɗata da wata ƴa mace ba.Na san cewa Juwairiya na sona sai dai ba ta san irin namijin da ya kamata ta so ba,duba ga ni ba ajin aurenta ba ne kuma babban goro ai sai magogin ƙarfe!Don haka ina kan baka na."
A.k ya ja motar sa ya fice ba tare da ya ƙara ce masa komai ba.
Zainab zaune a ɗaki ita da ƙawarta Nabila suna hira,wacce ta yi takakkiya ta taho Zariya tun daga Abuja,saboda kiranta da ta yi tana kuka ta gaya mata abin da ya faru.
Nabila da ta gaji ta ɗauko gajiyar hanya tana zaune akan gadon Zainab abinci take ci.
Wayar Zainab ta yi ƙara kusan sau goma na kiran ta,amma sai taƙi ɗaga wayar daga ƙarshe kashe wayar ta yi ta wurgata can gefe a fili ta furta.
" Maye kawai mazinaci."
Ko da ba ta gaya mata ba ta san wanda yake kiranta.
" Yanzu kin tabbata abin da na ke gaya miki ko kin yadda namiji buhun ƙaya ne? Wai ki gaya min ta ya akai kika gane suna cin amanarki?"
Zainab ta saki tsaki ta kalle ta da ɓacin rai ta ce." Ni ba wannan ba ina acid ɗin da nace ki taho min da shi?"
" Karki damu tsaƙon ki yana ije a jakata amma don Allah ki gaya mini,ya akai kika gane bayan duk kin ɗana musu tarko sun tsallake?"
"Wani magani na tsinta a cikin drower ta A.m ya na sha na ɗaukar ciki da wuri."
Ta ce cikin damuwa yayin da idanunta suka kawo ruwa.
" In yana shan maganin haihuwa to meye hujjarki ko kina tunanin,A.m zai so ya haifi ɗansa ta zina bayan ga matar sa ta sunna?Sannan ni ban ga abin da kika faɗa a matsayin shedar suna cin amanar ki ba."
Ta faɗa da tana kallon Zainab da ta yi tsuru-tsuru ta manta cewar,ba ta taɓa gaya ma kowa ba cewar ita ce ba ta haihuwa,sai ta shiga in da in da daga ƙarshe hannunta ta kama tare da fashewa da kuka cikin kuka ta ce
" Yau zan gaya miki wani sirri amma don Allah ko sauran ƙawayen, ba na son ki gaya musu cewar na gaya miki ni ce bana haihuwa ba A.m ba,domin ya yi min alƙawarin ba zai faɗa wa kowa ba kuma ba zai ƙara aure ba."
Gwalalo idanu ta yi cikin mamaki jin abin da ta faɗi da gaske ita ce ba ta haihuwa ba A.m ba.
Sai tsananin mamaki ya kamata ta shiga kaɗa kai kamar wata ƙadangaruwa zuwa can ta nisa ta ce." Har yanzu wannan ba hujja ba ce Zainab saboda wataƙila A.m ya na shan ƙwayoyin ne don yana tunanin ƙila ƙwayoyin Zai taimaka miki."
"Haba akan me za ki ce haka bayan na gaya miki cewar mahaifata aka yi min aiki aka cire.Kuma idan haka ne mai yasa ka bai gaya min ba"Ta faɗa cikin ƙosawa jin bin da ta ce.
" Wannan ma ba hujja ba ce har yanzu ba ki da hujja Zainab.Kina abu kamar ba likita ba bayan kin manta mahaifa takan tiƙo a jikin mace ko da an cire ta,mata nawa ne suka haihu bayan a n cire musu mahaifa?.Musamman ke da baki taɓa haihuwa ba."
" Wayyo Allah kin sani a ruɗu in kin ce duk wannan ba hujja ba ce,to numbar A.m da na gani a wayarta shi kuma mene ne?"Ta ce da ita tana kuka sosai.
" Ba zan ɓata bakina gurin faɗa miki irin son da nake masa ba.Na roƙe ki kamar yadda kika yi min alƙawarin za ki watsa mata acid ki taimake ni ki yi yadda muka shirya,ga bayanin in da take gidan kawunta wanda na samu labarin mahaifiyarta ta ɓata."
"Ok tun da haka kike so zan yi amma na so a ce mun ɗan ƙara lokaci,mu samu ƙwararan sheda, yau ɗin nan zan cika aikin ki na koma Abuja bari na gama cin abincin.Niƙabi zan saka na watsa ma shegiya ki huta.
BARI NA YI NAN DON YAU BANI DA TACE WA LAMARIN YAFI ƘARFINA.
KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.
BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI
SAKACINA KO HALIN MAZA
TAKU
JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY
Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba ***_.
Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.
COMMENT,READ FOLLOW AND SHARE.