Free chapter · Read without an account
Chapter 30
*SAKACINA KO HALIN MAZA?*
*RUBUTAWA:-*
*JAMILA LAWAL ZANGO*
*SADAUKARWA GA:-*
*SUMMY M NA'IGE*
_(Aminiya)_
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*
*Page 30*
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM
Zainab ji ta yi ƙasa ba za ta iya ɗaukar ta ba,ta yi kukan kura sai ta faɗa kan Juwairiya ta ƙara shaƙe mata maƙogaro.
" Uban wa ya yi miki ciki da ma ke ƴar iska ce."
A.m da sauri ya yi kanta tare da ƙoƙarin ɗaga ta kanta ganin ta na son ta yi mishi illa."Ba ki da hankali ƴar mutane za ki kashe?"Ya ce lokacin da ya ɗaga ta daga jikinta.
" Barni da ita wallahi in a kwai abin da yafi kisa zan yi mata! Ta ya ya za ayi tayo ciki ta shigo mini da shi gida."
Sai kuma ta ce." A.m don Allah karka sa na haukace ahalin yanzu ji nake kamar numfashi na zai ɗauke!Ka da zargina ya zama gaskiya ka barni na koreta a gidan ta je can ta nemi uban cikinta."
" Zainab ki tsaya ki fahimce ni na yi miki bayan..."
"Wai mai za ka gaya mini?In dai ba ka na son ka faɗa mini yau ne ranar da fitan numfashina zai yi bankwana da gangar jikina"!To na roƙe ka don Allah ka ƙyale ni.Juwairiya ta fita daga gidan nan shine kawai zai saka na fitar da zargi a cikin zuciyata."Ta ce tana kuka sosai.
" Sam ba za ta bar gidan nan ba samun sauƙin ki shine ki fahimci abin da zan gaya miki,domin ba ni da nufin na cutar da ke duk abin da yake faruwa na yi ne don ke."
Ja da baya ta fara yi tana mishi wani irin kallo,sai ta kalli ta ta kuma ƙara kallon sa kawai sai ta shaƙe shi.
" Na shiga ukuna ni Zainab zuciyata ,za ta buga A.m zai kashe ni,ka da son yara da kake yi don kawai ba na haihuwa ya sa ka naimi Juwairiya ka haihu ta zina! Tur mai za ka yi da ɗan zina kuma ya fito ta jinin matsiyata."
Sai kuma ta sake shi ta nufi kanta tana faɗin."Wallahi saina kashe ku iyaye sun danƙaramin dukiya,shine za ku din ga zina akan gadona har ku samu ciki h."
" Ya ishe ki Zainab! Kar ki ƙara ai banta min yaro,kin san halina ba zan taɓa aikata zina."
Ya buɗe baki zai gaya mata matsayinta sai ya kasa ya sunkuyar da kan shi ƙasa,yayin da tsananin tausayi ya kamasa ganin yadda ta koma kalar tausayi tana kallonsa.
" Ki fahimce ni Zey ke san ba zan taɓa haɗa ki da..."
" Ba na son ji! Ba na son ji!! Mayaudari munafiki mai alƙawarin banza.Tur da na aureka na yi nadamar ranar da na ce ina sonka,kar ka matso kusa da ni in ba haka ba kashe ka zan yi!"
Ta faɗa tana girgiza kanta tare da toshe kunninta ganin ya nufi ta zai riƙe ta.
" Wannan dalilin ya sa na yi duk iyakan ƙoƙarina na fahimtar dake."
Ya ce da ƙarfi ya na kallonta sannan ya ci gaba da cewa." To tun da ba ki bani dama ba,bari na gaya miki gaskiya..."
Katse shi ta yi da ƙarfi tare da ƙara cakume shi ta ce." Mai za ku gaya mini mai kake son kace?Abu ɗaya na sani cewar mijina A.m ya na kwana tare da ƴar aikina,wallahi kaf duniya sai sun ji don a jarida zan buga,A.m ya yi ma ƴar aikina ciki za su haifi ɗan shege ɗan zin."
Wani irin shaƙa ya kaima wa da ya sa ta ji numfashinta zai ɗauke.
" Kar ki ƙara aibata min ciki ɗan dake cikinta halastacce ne kuma ta aure muka same shi,don ban san ta ba a matsayin ƴa mace ba,sai da aka karɓar min aurenta."
Ya zaro idanun sa ganin ba ta fahimci abin da ya faɗa ba." A taƙaice Juwairiya matata ce ta sunna wanda Daddy ya karɓar min aurenta! Don haka karki ƙara aibanta min yaro don wallahi sai kin gane baki da wayo."
Kawai gani ya yi ta sulale a ƙasa ta faɗi sumammiya.Da sauri ya yi kanta ya na kiran sunan ta.
Gabaki ɗaya ya ruɗe ya rasa ta in da zai fara rungumeta ya yi cikin tashin hankali sunanta kawai yake kira.
Da gudu Juwairiya ta shiga kicin ta ibo ruwa ta watsa mata,amma sam ba ta farfaɗo ba jikinta ya yi ɗip kamar babu rai a jikin.
" Zainab don Allah kar ki mutu ki barni ba zan iya rayuwa ba,in har babu ke a cikin duniyar nan,ki tashi na yi miki bayanin na aure ta ne don ke,don Allah ki buɗe ido.
A.m yake faɗi ya na jijjigata cikin tashin hankali." Ya kamata a kaita asibiti fa kar ta mutu."
In ji Lantana da take kallon tashin hankali wanda ba' a saka mishi rana.
A.m ya miƙe daidai lokacin da Lantana ta ruga kiran direba,don ya kasa komai sai zare idanu da yake yi.
Zubbur ya ga ta miƙe tare da sakin wani irin ƙara wanda sai da gidan ta girgiza,kawai sai ta saki dariya kamar sabon kamu.
Wani ihun ta saki da ƙarfi ta yi kansa ta na faɗin." Ƙarya kake yi wallahi ni kaɗai na tashi a gidanmu na rayu ni kaɗai ban taɓa sharing ɗin wani abu ba,sai kai abin da nafi so fiye da komai a rayuwa.Ina hakan ba zai taɓa faruwa ba!"
Ta ƙara riƙe shi ƙam ta ci gaba da cewa.Ƙila mafarkinmu duniyar mahaukata ya kawo mu,don na lura kai kanka ba ka san mai kake faɗa ba,don wataƙila baka cikin hayyacin ka."
Mari ta kawo mishi cikin zafin nama ya kauce tare da riƙe hannunta,ya zare idanun sa ya ce."Tabbas bari na ƙara gaya miki ita ɗin matata ce,gaskiya kunninki yake gaya miki,kamar yadda igiyar aurena uku yake a kanki,haka ita ma amma ki tsaya ki sauraare ni,kin san ina sonki ba zan yi abin da zai cutar dake ba. na aureta ne don na..."
"Kai."
Ta daka mishi tsawa da idanunta da suka rine sukai jajur!Saboda tashin hankali.
" Karka gaya min maganar banza ka rabu da ni macuci haƙiƙa ka cuce ni,ka kuma yaudareni.Ka manta ka yi min alƙawarin ba za ka taɓa min kishiya ba,balle ka sanar da ni ce ba na haihuwa shi ne yau ka auri wata mace ban sani ba,kuma saboda cin mutunci ka kawo ta gidana ka na kwana da ita a gadon da iyayena suka siyar mini,wallahi mafi girmar kuskuren da ka yi ka kawo ta gidana,ka maida ni banza shashasha sauna! Ashe in bana nan sakewarka kake da ita?Har kana mini munafucin baka riƙe sunann ta ba.
Wayyo Allah na! A.m ya maida ni banza ya kawo matarsa gidana a matsayin mai aiki!Wace irin banza ne ni har na kasa gane tsakanin su?
Wallahi sai kun yi nadamar abin da kuka yi mini,zan nuna maka cewar da gaske ba a yi ma family ɗinmu kishiya,take yanzu zan kasheka in kashe kaina haka kuma in kasheta!Mutuwar kasko za mu yi daku,ban taɓa sharing ko da wani abu ba balle na haɗa jiki dakai ƙazami kawai."
Da gudu ta ruga kicin kafin ya farga har ta ɗauko wuƙa ta yi kansu ta na faɗin." A yanzu za ayi ta taƙare yanzu zamu yi mutuwar kasko,hisabi akan abin da kuka yi mini zan yi muku tun kafin aje lahira ku haɗu da ubangiji,munafuki mai karya alƙawari."
" Zainab ki ki natsu karki aikata dana sani! Look Zainab kar ki aikata abin da kike son yi,sheɗan ne yake so ya kaiki ya baro,don Allah ki natsu zan yi miki bayani,ina da dalilin da ya sa na ɓoye miki auran."
Kallon mahaukaci take mishi ta tsaita wuƙar daidai gurin Juwairiya tana matsawa kusa da ita.
" Saina nuna miki kuskuren da kika yi mijina za ki aura,kin yi babban kuskure ni kaɗai nake rayuwa a gidan mahaifina,haka dangimmu kaf babu wata mace da aka yi wa kishiya sai ni?Wallahi ba ku isa ba,sai na nuna muku kuskurenku."
Gadan-gadan ta yi kanta data tsorata ganin ta nufo ta da wuƙar,ɓoyewa ta yi a bayan A.m da hankalin sa ya tashi matuƙa,saboda yadda Zainab ta koma za ta iya yin komai.
" Zainab kar ki kashe musu ƴa za ki yi dana sani fa shari'a ba za ta ƙyale ki ba kema kashe ki za'a y."
"Don na kashe ƴar matsiyata uban wa zai taɓa ni na san ko an kulle ni Daddy zai fito dani."Ta bashi amsa idanunta a bushe.
" To ni in kika kashe min ɗa wallahi saina kulle duk yan gidanku ba ke ba,saboda ko ba komai zan ga ɗana a duniya na rungume shi iyayena su yi alfahari da hakan."Ya ce mata cikin zafi da ɗaga murya.
Kukan kura ta yi taho kan kanta da gudu jin abin da ya faɗa,yayin da idanunta suka rufe ba ta ji ba ta gani.
" Yadda ba na haihuwa kai ma ba za ka taɓa ganin ɗanka ba,saboda kai na lalata mahaifata,don na faranta maka shine za ka auri wata,wallahi baka isa ba."
Da sauri ya cakume ta ya riƙe ƙam iya ƙarfinsa ganin abin da take shirin yi.
Juwairiya ta sadaƙar mutuwa za ta yi lokacin da ta yi kanta da wuƙar.Ta rintse idanunta tana salati.
Fuɗuwa suka yi a ƙasa ita da shi ya fara kiciniyar karɓe wuƙar.
Sai kawai ta kai mishi wukar jikin shi Allah ya ba shi sa'a ya kauce,wuƙar ta yanki hannun sa sosai.
Ba Juwairiya kawai ba hatta wanda ta yi yankan sai da ta ɗan firgita ganin irin jini da ya fara tsartuwa a hannun sa.
A.m ya kira sunan Allah da ƙarfi ya ji wani irin raɗaɗin azaba yana ziyartar sa,jikin shi ne ya kama rawa ganin duk da yankar da ta yi masa,jini na zuba amma ba ta razana ba,sai ta nufi Juwairiya da ta yi kan sa ta kama hannun sa tana kuka,mai haɗe da salati matuƙar tsoro ya shige ta ganin abin da ta yi.
" Ai na gaya muku wallahi sai kun gane kuskuren ku na cuta ta da kuka yi!"Ta faɗa lokacin da ta yi kanta.
Da sauri A.m ya miƙe ya saka ƙafafun sa ya taɗiyeta ta faɗi yarab!Amma da ƙarfin hali duk da buguwar da ta yi,sai da ta ƙara nufo ta da wuƙar.
Ƙara hankaɗe ta ya yi za ta faɗi ya tare ta bayan wuƙar ya faɗi gefe.
Ta saki ihu tana zage-zage kamar wata mahaukaci.
Da ƙarfin tuwo ya riƙe ta tare da yin dubara ya sakata a cikin ɗaki,sannan ya jawo ƙofar ya kulle.
Wayar sa ya ɗauka ya kira Mominta don ita kaɗai yake tunanin za ta shawo kanta.
Zuciyar sa a fusace ya ja hannunta suka fita,a cikin mota ya saka ta sannan ya shiga ya ja.
A.m dake tuƙi gabaki ɗaya hankalin sa ya tashi ƙwarai,ko a mafarki bai taɓa tunanin abin da Zainab za ta yi mishi ba,duk da daman ya san zai sha fama da ita.
Ya juyo yana tuƙi da bai san in da za shi ba ya kalle ta,sai ya ga ta dunƙule jikinta hawaye yake turereniya a fuskarta,kamar rawar sanyi take yi ganin yadda ta takure lokaci guda.
Ya sani cewa ya tono ma kan musamman in iyayen sa suka ji abin da ke faruwa,don ya san Zainab sai ta fallasa komai.
Guri ya samu ya samu ya yi parking ba tare da sanin abin da zai yi ba,ya kwantar da kan sa a jikin sitiyarin ɗin.
Karo na farko yau ta ga karaya a fuskar shi tun iya rayuwar da suka yi ba ta taɓa ganin abu ya saka jikin shi ya yi sanyi ba,ko da kuwa Baba ne Sani da ta lura ya na matuƙar tsoron shi,amma yana ɓoyewa,sai ya ba ta tausayi sosai.
Ta kalli hannunsa da yake tuƙi jini duk ya ɓata in da ya riƙe kuma ya na ta zuba,kawai sai ta saka kuka tare da cire ɗaukwalin da ta ɗaura,ta kama hannun za ta ɗaure.
" Asirina ya tonu ko kaɗan ban taɓa tsammanin lamarin zai tafi ta haka ba,ina tsoron mahaifina in ya ji abin da na aikata,Daddy zai yi fushi sosai.Dama haka Zainab take da kishi kai mata basu da tunani wallahi!Duk abin da na yi don na faranta mata ne.
" Ina tsoron Daddy in ya jin wanan lamarin ban san abin da zai yi min ba,wataƙila ya tsame ni daga cikin yaran shi."
Kamota ya yi ya riƙe da hawaye a fuskar shi ya ce." Ki ba ni shawara na rasa yadda zan yi zuciyata za ta fashe."
Kawai sai ta fashe da kuka sosai tana tausayin kanta da shi,don ita kanta tana tsoron ranar da za ta koma gurin Mama.
Rungumeta ya yi ƙam yana jin kamar rungumar za ta yi masa maganin damuwar sa.
Wani irin hucin zafi ya ji a jikinta da sauri ya matsa gefe yana kallon ta,daidai lokacin da ƙamshin turaren sa ya ƙara taso mata da amai,ta buɗe motar a guje ta fara sheƙa shi.
A.m hankalin sa ya tashi sosai ya tsaya yana kallonta ya rasa wani tunani zai yi,gashi ko ruwa babu wanda za ta kuskure bakinta da shi.
Sannu yake ta jera mata ya riƙe ta sosai kamar zai mayar da ita jikin shi,sam bai damu da aman da take yi ba.
Da ta gama aman ta miƙe sai ta ji jiri ya kamata za ta zube a ƙasa,da sauri ya tare ta ta faɗa jikin shi,bai damu da jinin da ke zuba ba ya riƙe ta sosai da hannun.
Mota ya mai da ita sannan ya ja suka wuce asibiti.
" Doctor ka fara duba ta da gaske wani cikin ta ƙara samu?"
Ya ce da likitan bayan ya zaunar da ita akan kujera.
Likitan ya kalle shi ya ga irin jinin dake zuba a hannun sa,sannan ya juya ya kalle ta da ta yi sanyi sosai,ciki mai ilinbo gabaki ɗaya jin wani iri take a jikinta.
" Ya kamata na fara duba ka kalli bleading hannun ka yake yi.".
"Kar ka damu da ni doctor kawai ka duba ta ina son na sani da gaske na kusa zama uba"A ɗokan ce yake magana.Ya faɗa jin abin da likitan ya ce.
" Ok to shikenan bari na kira doctor Garkuwa ya duba ka kar ka fara ganin jiri."
" Congratulation ina farin cikin sanar dakai matarka na da ciki sati uku."
Sujjada kawai ya ga ya yi sai ya rungume shi yana murna." Ashe nima zan zama Baba! Allah na gode maka."
Gurin da take kwance ya nufa ba tare da ya ji kunyar doctor dake tsaye yana kallon sa yana dariya ba,ya bata hot kis bayan ya rungume ta.
" Da gaske za ki haifa min Baby?"
Dariya doctor ya sannan ya kalle shi ya ce."Aman da ta yi ya ɗan galabaitar da ita so yanzu za mu ba ta rest bed zuwa an jima sai ku tafi,na rubuta muku maganin da zai dakatar da aman."
" No doctor a ƙara mata ruwa kawai saboda jikinta ya yi weak ina son yarona ya samu kuzari,kasa ka mata drip kawai ba na son abin da zai cutar da shi,kaga in ba ta da ƙarfi ba zai samu damar ya juya yadda yake so ba."
Dariya ya yi sosai ya bugi bayan sa." To fa yau Allah ya haɗani da patient sabon shiga to Allah ya sa madam ta haifi ƴan biyu,amma jikinta ba sai an saka mata ruwa ba,ka ba ta maganin nan da zarar kun je gida.
Duk yadda doctor ya yi da shi amma ya kafe sai an yi mata ƙarin ruwa,don kar yaron sa ya wahala,dariya sosai yake masa ganin yaushe akai daren da har gari ya waye yaron da ko gudan jini bai zama.
A.m ya ruɗe duk da tashin hankalin da yake ciki amma in ya tuna zai sami baby,sai ya ji ya ɗan rage damuwar shi.
Wayar sa ya zaro ya kira A.m akan ya zo asibiti ya same shi.
*********
Zainab ta sa saki wani gigintaccen kuka lokacin da Momi ta shigo gidan tana sallama.
Ƙofa ta shiga bugawa tana faɗin." Momi ki buɗe ni ina ɗaki ya kulle ni."
Jikin Momi ya kama rawa sosai ganin jinin da ya zuba a hannun A.m face-face a falon.
" Mai ya saka ya kulle ki lafiya wai mai ke faruwa ne jinin waye a ƙasa?"
Ta jero mata tarin tambayoyi cikin tashin hankali.
" Faɗawa jikinta ta yi ta saka gigitaccen kuka.
" Momi tun da na taso na taɓa neman wani a bu na rasa?Kuma kin taɓa ganin na yi sharing ɗin wani a bu a gidammu,ko da mota ce?"
Da sauri ta girgiza mata kai alaman
" a'a."
To wai Momi A.m yake tare da Juwairiya mai aikina da Lantana ta ba ni labarin suna tare, kuma wai auren ta ya yi har tana da ciki,ya ije ta a gidana suna rayuwar aure."
Sai ta saki razanannen kuka tana girgiza kanta.
" Ni wallahi gani nake kamar mafarki nake yi! Komai ya canza cikin ƙanƙanin lokaci.Wayyo Allah na!Na shiga uku."
Da sauri ta miƙe a zabure." What impossible! Amma wasa kike mini ko?Haba ina ta ya ya za'ai A m ya aikata wannan ɗanyan aikin, bayan ya san ba'a yi wa family ɗinmu kishiya,sannan kika ce ta samu ciki wa ya yi mata,bayan shi baya haihuwa ku..."
" Momi ki tsaya ki fahimce ni na san na yi miki laifi ban taɓa gaya ma kowa ba,amma ki yi mini uziri don Allah!"
Ƙara miƙewa ta yi a zabure bayan ta gama gaya mata abin da ta ɓoye mata tsawon shekaru.
Zaro idanunta ta yi da ƙarfi ta furta." Innalillahi wa inna ilaihir raju'un! Zainab.
"Da gaske ne ke ce ba kya haihuwa ba A.m ba?"
TSANANIN FIRGITAR DA TA NUNA YA TADA HANKALINA NA IJE RUBUTUN DON NA SAMU NATSUWA.
KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.
BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI
SAKACINA KO HALIN MAZA
TAKU
JAMILA LAWAL ZANGO
JAMCY
Kar dai ku manta sunan labarin "SAKACINA KO HALIN MAZA" Ga masu buƙatar shiga cikin group ɗina na whatsapp ga numba ***_.
Kuma ƙofa a buɗe take na ƙorafi gyara ko ƙarin bayani ga zakakuran marubuta,har yanzu ni mai koyo ce.
Kar dai ku manta da wannan lintafin sadaukar wa ne ga zaƙauran marubuciya,kuma ƙawata (SUMAYYA NA'IGE) Allah ya ƙara fasaha ya sa ki fi haka,ina alfahari dake a cikin marubuta da irin taimakon da kike bani.
COMMENT,READ FOLLOW AND SH