Free chapter · Read without an account

Chapter 31

by Jamila · SAKACINA KO HALIN MAZA

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*    



  *RUBUTAWA:-*
 *JAMILA LAWAL ZANGO*


                   *SADAUKARWA GA:-*

 *SUMMY M NA'IGE*
              _(Aminiya)_             

      
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

                          *Page 31*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM


" Momi da gaske ne duk abin da na gaya miki na aikata,tabbas na sha maganin hana haihuwa don kar na haihu in tsufa A.m ya guje ni.Amma duk abin da na yi saboda shi ne ina..."

Wani irin gigitaccen mari Momi ta kwasa mata sai da ta wuntsila.
" Zainab are you stupid! Kin san abin da kika aikata kuwa kin san irin tashin hankalin da kika saka kan ki? Inna lillahi na shiga uku! Mai ya sa kika ɓoye min ina matsayin mahaifiyarki? Da duk haka ba ta faru ba."

Zainab da ta ji saukar marin Momi sai da ta yi suman wucin gadi,ta dafe ƙuncinta cikin tashin hankali,saboda tun da take Momi ba ta taɓa kai koda ɗan yatsarta jikinta ba.

" Momi marina fa kika yi?Bayan ba ki taɓa ko yin ihu mai ƙarfi gare ni ba,balle ki ɗora hannunki a jikina."

Momi da take cikin tashin hankali saboda abin da ta aikata,kallonta ta yi ji take kamar ta rufe ta da duka.

" Wallahi Zainab ji nake kamar na rufe ki da duka! Kin yi kuskure sosai in har kika yi wasa sai zaman duniya ya gundure ki,saboda girmar laifin da kika aikata.
Maihaifinki na matuƙar son ya ga kin haihu haka nima, dangin A.m suna nan suna tsananin damuwar su akan rashin haihuwa da ba ku yi,ina kallon sa a matsayin azzalumi baya haihuwa ya kuma ƙi rabuwa da ke,ashe tawa ƴar ne ba ta haihuwa."

Ta faɗa cikin kuka sosai wanda ya ɗaga hankalinta sosai.

Hannunta ta riƙe tare da fashewa da kuka ta ce." Idan har za ki yi irin kukan nan, ya kamata ni na yi hawayen jini Momi,amma har yanzu ban ji tashin hankali ba sosai don ba na haihuwa,asalima ni yara sam ba su dame ni ba saboda wahala kawai suke baka, kuma kin san Momi na tsani ƙazanta sam ba na son na wahalar da rayuwa."

Momi ta fisge hannunta ta juya mata baya,ta na kallon windo cikin wata irin murya,mai nuna tsantsar damuwa ga mamallakin muryar ya shiga.

" Har yanzu ke yarinya ce ba ki gane komai ba,amma na tabbata za ki yi nadama in har ba ki ɗauki mataki ba,na rantse miki duk ranar da ki ka yi sake A.m ya haihu,daga ranar za ki fara son yaran duniya ba ki ɗaya."

Ta juyo da ita suna fuskantar juna cikin murya mai sanyi ta ce."Duk da cewa Allah ya mallaka mini ke,amma mahaifinki har yau yana kukan rashin ɗa,ba za ki gane mai nake nufi ba sai ranar da kika yi hankali gurin tunanin wa zai gaji dukiyarki.Ki duba irin dukiyar da kike da shi in kika mutu wa za ki bar mawa?Ko so kike duniya suci.
A.m yana da kuɗi da ahalin sa mene nufin ki akan dukiyar babu rabon ki a ciki?"

" Haba Momi mai zan yi da wata dukiya iya abin da Allah ya mallaka mini ya ishe ni, ba sai na nemi agajin kowa ba,ga kuma dukiyar mahaifina, da ni ce kaɗai mallakin sa."

Ta ce da Momi cikin jin ƙosawar maganar ta, don ita ba ta yi tunanin za ta ɗauko mata wannan shirmen ba,saboda damuwarta ta fi gaban wannan.Abu ne na zuciya da Allah ya ke halittar so a ciki,sam ba za ta yadda wata ta ƙwace mata shi ba.

" Ba za ki gane ba ne Zainab dole ki ɗauki mataki na san mai kike nufi,kuma magana ta tana kan hanyar damuwarki,kin ga in kika yi gigin barin abin da kike faɗi ya faru,wallahi sai kin raina kan ki."

" Wannan dalilin ya sa na ce tuntuni mu watsa mata acid amma Momi kika ƙi,da yanzu matsalata ta kau yanzu gashi kin sakani a cikin matsala,don ko kaɗan ban yi tunanin tana cikin gidana ba."Ta ce da ita tana ganin kamar Momi ta ja mata duk abin da ya faru.

" Na hana ki ne saboda watsa mata ba shine mafita ba,in har yana sonta to zai yi komai don ya ceci rayuwarta.Na bari ki dawo hankalinki ya kwanta sai mu ɓullo ma abin ta ruwan sanyi,ba tare da ya yi tunanin da saka hannunmu a ciki."

" To yanzu Momi ya zan yi?Ba zan iya barin ma wata kucaka ƙazama yar talaka mijina ba,ina son sa shi kan sa ya san irin son da nake masa.Ki taimake ni mijina ya dawo gareni Juwairiya ta fita daga rayuwar sa,in har ba so kike ki rasa ni ba,don na yi rantsuwar ba zan taɓa barin wata ta raɓe shi ba,ko da ace ba ni tare da shi! In ko hakan ta kasance mutuwa zan yi,sai dai ku nemi wata ƴar."

Jijjiga ta da ƙarfi take yi ganin yadda ta fita hayyacinta tana watsi da kayan ɗakinta.

" Ya isa ki natsu ki gane wace ce mahaifiyarki sam ba zan bari hakan ta faru ba,ko da ace zan yi yawo tsirara ne! Kin san wace ce mahaifiyarki ya kamata ki zama jaruma.Irin zuciyata ya kamata ki ɗauka,ba in aka yi miki abu ki ce za ki rama ta kisa.Sab ba haka jarumi yake cin nasarar sa ba,dagewa za ki yi ki saka makamanki ki yaƙi duk wanda ya zama garnaƙaƙi a cikin rayuwarki."

Ta faɗa yayin da ta yi shiru tana kallonta don ba ta fahimci mai take cewa ba." Bari na baki labarina wanda baki taɓa sani ba Zainab.Mahaifin ki yaso wata mace kamar ransa yana jin zai iya mutuwa in bai same ta ba,ita kuma ƙawatace da muka haɗu a makaranta.
Mun shaƙu sosai muna shiri da ita,duk ƴan'uwanta na san su,don har zuwa nake na kwana a gidan su.Mahaifinta hamshaƙin mai kuɗi ne sosai suna da kuɗi,yayin da ni ina karatu a gidan kawuna shi ya ɗauko ni ya sani a makaranta iyayena talaka.

Tun da na fara mahaifinki na ɗauki son duniya na ɗora mishi sosai,sannan ina son na canza rayuwata daga ƙangin talauci.

Matar kawuna ta yi mini hanyar wani malami ya ta kaini gurin sa,don ya janye hankalin sa daga gareta,amma sai dai in na yadda da sauran ƙwayayen haihuwana za'a yi asirin,in da za'a bar ɗaya kawai wato ɗa ɗaya zan haifa a duniya.Ba tare da damuwa ba na amince.A lokacin har an saka ranar auren su biki ya rage kwanaki aka fasa auren,in da ya zo gidammu da fari iyayena sun ƙi,amma ganin zai haukace dole aka ɗaura aurenmu wanda dalilin haka ta aikata suicide. ta mutu.
Sai dai na fara nadama bayan aurenmu duk lokacin da hankalin sa ya dawo jikin sa,sai ya kasance ina yawan zuwa a juyar masa da hankali,a haka muka rayu har na haife ki bayan na haife ki sai Allah ya saka mi shi tsananin sonki,domin yana son yara sosai ya sha gaya min zan haifa masa yara da yawa."

Momi ta yi nisa tana kallon Zainab da ta yi zuru ta zuba mata ido tana kallonta cikin al'ajabin labarin da take gaya mata.

" Na yi matuƙar dana sani sosai da na yadda aka yi amfani da sauran ƙwaina,saboda dangin sa sun takura mi shi akan ya ƙara aure,sai dai na yi ruwa na yi tsaki har yau ya kasa ƙara auren.Don haka ki share hawayen ki A.m bai isa ya zauna da wata mace ba bayan ke,ke kaɗai ce za ki zauna da shi har abada,na yi miki wannan alƙawarin in...."

" No Momi don Allah kar ki saka wani abu daban a cikin aurena! Ina son A.m ina burin na rayu da shi har abada,kuma kin san ni ba na son waɗannan halayen da kike yi,don haka in ba za ki taimaka min ba,kawai ni zan watsa mata acid ko na ɗauketa a garin."Ta ce da Momi cikin shagwaɓa tana kallonta yayin da hawaye suke ƙara turereniya a fuskarata.

" Banza shashasha! Ita kin san abin da ta yi har A.m ya kula ta? Ki zauna garin kallon ruwa kwaɗo ya yi miki ƙafa,kuma Allah kin ji na rantse miki ko ke baki yadda da hakan ba,dole mu zamu ɗauki mataki."

"Haka ne Momi ki yi haƙuri amma gaskiya ba zan amince da abin da kike so ba,zan kira Anty Lubna na san za ta ba ni shawara."

Gabaki ɗaya kayan sawarta suka kwashe ita da Momi,bayan ta kira mahaifinta ta sanar masa take ya buga ma Daddy A.m waya saka yi kaca-kaca.

Jikin Daddy ya yi sanyi to fa asiri ya tonu ya san cewa a kwai daru saboda shi ya saka hannu aka ɗaura auren.
Jikin shi ya kama rawa saboda irin zagin da mahaifin Zainab ya din ga yi mi shi,ya san dole ya kira ainihin mahaifin shi ya gaya mi shi.

Wani irin zufa take tsefo masa don ya san Allah kawai zai fidda shi,sai yanzu yake ganin mugun wauta da ya yi har suka yi galaba ya amince da aure.

Wayar sa ya zaro ya don ya kira A.m cikin fushi.A ran sa yana baƙin cikin halin dukan mata da A.m ya ɗaukar wa kan sa.
**********
" Wai mene ne haka ne A m ka san mai kake yi kuwa a asibiti muke,kuma ka duba idanun mutane a kan ka suke sam ba ka da kunya."

A.k da ya yi wa Juwairiya rumfa da take kwance kan gado,ya kuma tura hannun sa a cikinta wai zai ji in da yaron yake.

Juwairiya da wani irin kasala ya rufe ta zuciyarta tashi take yi,kamar wani aman yake son ya zubo mata.


Da sauri ta ture hannun sa ji ta yi kamar an ɗora mata wuta a in da ya ɗora mata hannu a cikin.

Ita ji ta yi da ya matso ta kamar wani irin wari za ta ce ko ƙamshi mara daɗi yake mata.

Hannunta ta saka ta toshe hancinta da jin wani amai zai taso." Don Allah ka matsa kusa da ni sam ba na son jin ƙamshin ka kusa da ni."Ta faɗa da muryar kuka tana jin wani ƙunci a tare da ita.

A.m ya yi turus kamar zai saka kuka ya juya ya kalli A.k da ya zuba masa ido sosai cikin son dariya.

" To fa baban baby ka ce kai ma ka shiga daga ciki kenan."
Ya faɗa a ransa yana tunanin kamar Juwairiya tana daga cikin jinsin matan da Allah ya halitta,a lokacin da suka samu ciki sai Allah ya jarabce su da tsanar miji tsana mai tsanani,yayin da suke ƙaurace ma mazajen su wasu har suna cutar da kan su.

Don matar sa tana daga cikin irin masu wannan halittar,duk sanda ta samu ciki shikenan zaman lafiya ya yi ƙaura a gidan su har ta haihu.

" Humh ka na ji fa wannan yar rainin wayon take faɗin na matsa,ai ita ta san in da ba babyna da yake jikinta ba babu abin da zai saka na matso kusa da ita,bayan ta san babu macen da nake so irin matar so."Ya faɗa yana hararar ta sosai ganin ta hana shi jin motsin baby.

Ga mamakin sa sai ya ga ta mayar masa da hararan da ya yi mata,don ita har ga Allah ta ji wani irin tsanar shi a cikin ranta,ba wai don abin da ya faru ba,sai dai wani canji da ta ji a jikinta,saboda in ya matso wani irin wari take ji har da ƙarni-ƙarni a jikin sa,wanda yake tado mata da hararwa.

A.k da ya yi tsuru yana kallon abin al'ajabi ganin yadda suka ɗauki fushi,bai taɓa tsammanin Juwairiya tana da tsiwa ba.

" Ikon Allah yau kuma irin murnar da za ku nuna kenan,bayan yau Allah ya kusan cika muku burin ku.Kai zaka samu magaji,ita kuma za ta koma gurin Mama kamata ya yi ku nuna ma Allah godiyar ku."

A tare suka harari junan su sai ta ji wani irin kewar Mama da son ganin ta ya kamata.

Hawaye ta soma zubarwa wanda ya ɗaga hankalin A.m,cikin ɗaga murya ya daka mata tsawa.

" Ki yi ma mutane shiru so kike ɗana ya gado shegen kukan ki na rashin dalili."

A.k da yake kallon dirama dafa kafaɗan sa ya yi ganin yadda ya daka mata tsawa.
" Haba A.m be a man. Baka ka san ba'a ɗaga ma mata masu ciki murya,irin shi ne suke haihuwar ɗa motsi kaɗan sai ya birkice."

Da sauri ya kalli A.k cikin razana ya kama hannun sa ya riƙe sosai." Da gaske kake?Ina ga zan duba duba google akan yadda zan kula da cikin saboda kar a samu matsala, ina son yarona ya fi ɗan kowa a duniya,kuma ba na son ya yi kama da waccan abar mai emotionally fence."Ya ce yana nuna ta da bakin sa tare da galla mata harara.

Tura bakinta ta yi ba ta ce masa komai ba,don ita yanzu haushin sa take ji na rashin dalili

A.m ya ƙara hassala don ya tsani raini, karfa don ta ga ta samu ciki tace za ta yi mi shi rashin kunya,da kuma ya tuna abin da A.m ya gaya masa sai ya duƙa kusa da ita.
" Kin san fa yanzu bake kaɗai ba ce,don haka duk kulawar da zan ba ki babyna nake ma wa,ki kwantar da hankalin ki yarona ya sakata ya wahala ya yi ƙatoto."

Ya ƙara sausauta muryar da ba ta taɓa sanin yana da shi ba." Baby mai kake son ci?Ka faɗi duk abin da kake so zan kawo maka shi."
Ture hannun sa ta yi ganin ya ƙara kawo wa "Don Allah ka ƙyale ni ba na son cin komai."

" Ba ke na tambata ba babyna nake magana da shi don na san dole yana buƙatar abinci."
Ya faɗa a kausashe don shi jin yake anya zai iya ɗaukar raini daga gare ta.
" Ka dai kula da abin da na ce maka, in ka din ga daka mata tsawa ta haifi yaron matsoraci, kai ka sani ka san dai wannan shikenan babu ƙari."A.k ya ce da shi.

Sosa kan shi ya yi." Na ji kuma zan kiyaye in sha Allah.Dole na samu babban likita wanda zai dinga ɗorani a kan yadda ake rainon ciki."

Juwairiya ta miƙe ta tana wani yatsina irin na masu ciki gabaki ɗaya ta ji wani canji a jikinta.Dambu da kalallaɓa ta ji kawai tana son ta ci,amma ta san ko ta faɗa masa ƙila ba zai nemo mata ba.

Amma kuma da ta ji son cin abincin zai saka mata amai,in dai ba ta ci ba kallon sa ta yi ta ce." Ni fa dambu zan ci da kalallaɓa kuma yanzu nake so."
A.m ya zare ido ya ce." To yar rainin wayo gara dambu na san shi matar A.k tana yi,amma kuma mene ne kalallaɓa?Ni fa kar ki raina mini wayo ƙila ba baby ba ne zai ci."
" Ko ma waye zai ci dole ka nemo ai wallahi tausayinka nake ji,don yanzu ka shiga hannu dole ka zama ɗan siyayya."A.k ya ce mishi yana kallon doctor da ya turo ƙofa ya shigo.

" Yauwa doctor yau she zan dawo ka ba ni shawarar yadda zan kula da babyna."
Dariya ya yi suka tafa da A.k." Abinka da sabon shiga."Hararar A.k ya yi jin abin da ya faɗa.

Wayar sa da take da can gefen Juwairiya ta ɗauki ruri sosai.Gaban sa ne ya faɗi don ya san kiran bai wuce daga gidan su.

" Please A.k ɗaga wayar ba zan iya ba na san bai wuce Daddy."Ya faɗa yayin da fara'ar shi ta kau.

Shi kan sa A.m a tsorace yake ya san ayau Allah kawai zai raba su da shi.
Da ya ɗaga wayar sai ya saka ta a hands pree.
" Kaicona Abdurrahman! Yau na yi dana sani da na ɗora yaƙinina akan ka.Abin da ka aikata kenan?A she baka da hankali wallahi ban taɓa sanin mahaukaci ba ne kai sai yau.Maza ka taho gida ina neman ka duk in da kake, da kuma yarinyar da Zainab ta ce ka dake ta saboda ita,don ni bazan ce matar ka ba ce sai dai kuma in ka canza iyaye bayan ni da Daddy ɗinka.Minti biyar na baka."

Mahaifin A.m ya faɗa yana huci ya kashe wayar,yana kallon Daddy da ya yi tsuru-tsuru.

A.m jikin sa ya yi sanyi ya kalle ta duk tana jin abin da ke faruwa,amma ba ta nuna komai a ranta ba.

"Mahaifina ya na son ganina dotor ka sallame mu."
Ya faɗa jikin sa a sanyaye saboda ya san a yau duk wanda yake da ƙima a idanun su, ƙimar shi za ta zube,ya san mahaifiyar sa ba ta da wasa mace ce da ba ta ɗaukar raini,hankalin sa ya ƙara tashi da ya tuna ƙannin sa ko ya za su kalle shi.

" Ka san Allah babu in da za ni, sai da na gargaɗe ka amma ka yi mini rashin mutunci,yau sai ka ƙwaci kan ka da Daddy,amma babu in da za ni na san Daddy ya yi fushi sosa."A.k ya ce da ya ga yana kallon sa.

" Juwairiya tashi mu tafi sai ki jure duk abin da za ki gani,sauƙinta ma siyen ki na yi da kuɗina balle ki ce na kai ki in da za'a wulaƙan ta ki."

Hankalinta ya tashi gabaki ta fita hayyacinta ji take kamar ta ga ta ɓace.

" Na shiga yau zan ga ahalin A.m wani irin tarba za su yi mini?Yau na san zan sha wulaƙanci wataƙila dukana za su yi."

Ta faɗa cikin tashin hankali ganin yadda shi kan shi ya ruɗe,sai ta raya a ranta babu in da za ta don ba za ta je su kashe ta ba.

Kamar ya san mai ta raya a zuciyarta ya ja hannunta,da ƙarfi ya nufi mota yayin da gabansa yake dukan tara-tara.

A.k kuwa daga asibitin gida ya koma ko aiki ya ƙi zuwa,tunanin shi Daddy zai iya bin shi gurin aiki,bayan ya shiga gida ya sanar da maigadin gidan sa duk wanda ya zo ace ba ya nan,ya rantse ba zai ƙara zuwa aiki ba sai ranar da aka gama wannan rikici.

A lokacin da ya gaya ma matar sa ta yi shiru,ta zuba mishi ido tana jin tatsuniyar da yake mata,zuciyarta na matuƙar mamakin sa,tsawon shekara biyu suka shirya hakan,amma ko wanka mai kama da jirwaye bai taɓa yi mata ba,sai abin ya ƙara ba ta matuƙar mamaki ta din ga kallon sa tana son ta yi magana amma ta kasa.

Kofin gilas ɗin da ke hannunta ta saki tare da zare ido da ta ji ya ce." A yanzu Juwairiya na da ciki kuma Zainab ta gane,Daddy ya yi kiran sa tsoro ya sani na ƙi zuwa don babu irin abin da ban faɗa masa ba,amma ya yi kunnin uwar shegu da ni sann..."

" Na shiga uku wayyo Allah na! Oh Zainab mai ya kai ki aikata wannan kuskuren lallai kin yi sake."Ta ce da tsananin mamaki sai abin ya ba ta tsoro hararar A.k ta yi ta ƙara cewa.
" Amma wallahi kun munafunce mu gaskiya ba ku yi mana adalci ba,haba Baban Najwa yanzu watarana in za ka ƙara aure haka za ku munafunce ni."

Dariya ya yi ganin ta birkice kishi ƙarara a fuskarta." Baki fahimce ni ba A.m ya kashe maƙudan kuɗi ya auri Juwairiya akan za ta ba shi baby in ta haihu su rabu ya bawa Zainab,wannan dalilin ya ije ta a gidan sa don tana haihuwa za su rabu,sakacin Zainab ya kusanta Juwairiya da shi,don tana da hankali ga kula da tsafta da iya girki ni kaina in na ci abincinta ina yabawa."

Ya numfasa sannan ya ɗora da cewa."kuma kin san A.m da son kula shi ya sa nake kallon Zainab a matsayin wawiyar mace,saboda mijinta irin mazan nan ne masu son mace ta mai da su yaro,a yadda na kula da A.m zai iya barin mace ta yi masa komai na kulawa,wanda ita ta gaza hakan da haka Juwairiya ta samu ta saka shaƙuwa a tsakanin su,duk da har yanzu yana kan bakan shi na rabuwa da ita,ni dai lamarin yana ɗaure min kai sosai ina tunanin yadda za ta haihu ta ba wa wata mace ɗanta.Sannan ba lallai ba ne Zainab ta riƙe."

" Humh wannan lamari a kwai rikitarwa har yanzu zuciyata ta kasa yadda da kai,don kun yi matuƙar ba ni mamaki,ashe duk ƙus-ƙus da kuke yi maganar auren ne,in na yi maka magana ka ce kuna maganar kampani,ai ga shi nan kun ibo ruwan dafa kan ku,sannan ba ka kyauta ba da ba ka je ba."

" Wa ni wallahi babu in da zani tsuntsun da ya ja ruwa."
Bugun ƙofa ya ji da sauri ya shige cikin ɗaki bayan ya ce " Don Allah ko wane ne ki ce ba na nan,kar na zo na fito Daddy ya zo."

Dariya ya ta saki a ranta tana mamakin wannan girman lamari da ya faru da ita.
" Ikon Allah duk cika da isar Zainab taƙama da kuɗi! Yau ita ce da kishiya kishiyar ma talaka da take wulaƙantawa."

Sai kuma ta nisa ta kuma cewa." Allah sarki Juwairiya kin yi wauta ina tausaya ma rayuwar ki ko ya ya iyayen A.m za su karɓe ki waɗannan ƴan nuna isa da raina talaka."Wayarta ta ɗauka ta shige ɗakinta.

A.m da yake jin bai taɓa jin matsananciyar kunya irin ta yau ba,da ya yi hon maigadin gidan su ya buɗe masa get.

Sai ya ji kamar ya koma lokacin da ya yi parking ya fito.

                     " Ki biyo ni."

Kawai ya ce hankalinsa a tashe ya nufi cikin gidan yayin da take taku cikin tsoro,ganin irin daular duniyar da ya kawo ta sai ta raina kanta.

Juawairiya ta tsaya cikin tashin hankali tana kallon mahaifin A.m da ko ba'a gaya maka ba,za ka nuna sa ka ce shine saboda sun yi matuƙar kama kamar har ta ɓace.

Ta kuma kallon sauran mutanen da ke falon sun taru da yawa sun zuba mata ido.

Kyawawa da su masu zubin larabawa kamar A.m da su ta yi yawa.Sai tsananin kunya ta kamata ba ta taɓa jin ta muzanta irin na yau ba.

" Inna lillahi wa inna ilaihir raju'un! A she da gaske ne ba ƙarya ba A.m ya zama uban kan sa ya yi aure?Ko kuma karuwa ce ya ije a gidan sa?"

Mahaifin A.m ya faɗa ganin Juwairiya ta ɓoye a bayan sa,sannan sam Zainab ba ta gaya musu ba ta haihuwa da kuma maganar ciki ba.

Gani suka yi Daddy ya yanke jiki ya faɗi sharab! Gabaki ɗaya suka saka kuka suka yi kan shi.


TO FA MASU KARATU GA DAI JUWAIRIYA TA BAYYANA CIKIN FAMILY ƊIN A.M SHIN ZA TA ƘARƁU KO YA YA?



KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

   BARI NA TUNA MUKU DA SUNAN SHI

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.