Free chapter · Read without an account

Chapter

by Jamila · SAKACINA KO HALIN MAZA

*SAKACINA KO HALIN MAZA?*    



  *RUBUTAWA:-*
 *JAMILA LAWAL ZANGO*


                   *SADAUKARWA GA:-*

 *SUMMY M NA'IGE*
              _(Aminiya)_             

      
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO....*

                          *Page 33*

BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHEEM

"Hamdiya na roƙe ki kibar maganar nan don Allah,domin babu abin da zai saka ni sai tarin baƙin ciki.A halin yanzu wannan ba shi ne a gabana ba,ina son na koma gurin Mama ina jin ban kyauta ma ta ba,duba ga irin wahalar da na ke sha,wallahi ji na ke komai na duniyar ya yi mini zafi.

Sai ta saki kuka sosai tare da miƙewa tsaye, da nufin ta fice da da falon,amma wani irin jiri ne ya ibe ta,wanda ya saka ta koma da sauri ta zauna,tare da rintse idanunta.

" Haka ne ba ki yi mata adalci ba,amma ki gode ma Allah da iyayen A.m su ka karɓe ki,in da ace kin haihu ne ya karɓi ɗan sa,da wane irin ido za ki kalli Mama?"

"Duk da haka ban yi mata adalci ba alhalin yanzu,iya tsananin wahalar da na ke ciki,ya kamata na gane kuskuren da na aikata."

Sai ta ƙara sakin kuka." Ki yafe mini Mama ina nan dawowa gareki na nemi yafiyar ki."

"Ya kamata ko da za ki koma gurin Mama,ki nemi mutuncin kan ki a gurin Ya A.m,saboda abin da ya yi a gaban iyayenmu ya ƙona mini rai sasai,yana tare da ke amma ya dubi tsabar idanun ki ya ce baya sonki a gaban kowa."

Juwairiya ta kalle ta da kamar ba za ta ce ko komai ba,amma kuma ganin yadda ta mai da hankalinta da damuwarta gareta, amatsayin ta na yar'uwar sa,sai ta ce.

" Haka ne amma ni ban ga abin damuwa ba,tun kafin mu yi aure yake gaya mini ba ya sona,yana da matar so ni kuwa auren wucin gadi muka yi da shi,duk da ada ina masifar son sa, amma haka ya din ga wulaƙanta ni yana kirana da matar shige,a yanzu na yadda ni matar shige ce,kuma na ƙosa mu rabu na huta da warin da nake ji a jikin sa."

Hamdiya ta kwashe da dariya tana kallon ta." Yanzu babban Yaya ɗan gayu mai ji da ƙwalisa kike cewa yana wari?"
" Wallahi wari yake yi mini mai haɗe da ƙarni sam ba na so na ji muryar shi,sai na ji warin ya fara tunkaro ni."

Ta faɗa tana zuciyarta na tashi saboda maganarsa da ta yi.
" To Anty Juwai ba kya tunanin wannan wata dama ce da za ki yi,amfani da shi ki ƙwato ƴancinki a gurin sa?Kamar yadda yake nuna miki baya son ki ki nuna kin tsane shi fiye da wanda yake miki,ko da kuwa ba gaskiya ba ne a zuciyarki,sabada wani lokacin in ka nuna tsanar mutum ƙarara ko da shi ba ya ƙaunar ka,hakan ya kan sa ka ya ji abin ya dame shi matuƙa,sai ki ga da ga baya ƙauna ta zarge a tsakani"

Ta ce tana kallon ta amma ganin ba ta ce komai ba,sai ta ci gaba da magana tana cewa.
" Allah ki nuna mi shi sam ba kya son ganin sa,saboda cikin da ke jikinki a yanzu zai so ya din ga zama kusa dake yana ririta cikin,ke kuma sai ki yi amfani da damarki ki wahalar da shi,domin duk faɗin da yake ba ya son ki ni ina ganin yana yaudarar kan sa ne,saboda in da ba ya sonki,ba zai aure ki ba koda kuwa na kwana ɗaya ne,duba ga matsayin sa da na iyayen sa."

" To a yanzu mai kike so na yi?Bayan kin san ni ko kallon sa ba na son yi."Ta ce da ƙosawa saboda ita ambatar sunan sa da take yi,ya ishe ta sai tana jin kamar za ta yi amai.

" Ki wahalar da rayuwar shi sam kar ki nuna tausayi,kuma kar ki bari ya matso kusa dake."Ta faɗa ba tare da shakku ba.

" In dai wannan ne kar ki damu fiye da haka zan yi mi shi."Ta ba ta amsa tare da mai da kanta ta kwanta,saboda wani irin bacci da take ji.

Tun Momi na ɗari-ɗari da ita da mutanen,gidan har suka saki suna nuna mata wani irin ƙauna,da abin da ke cikinta.A.m gabaki ɗaya sai ya ji hankalin sa ya tashi,don ya so ace masoyiyarsa ake nuna wa ƙauna ba ita.

A.m ya ba ma Zainab lokaci zuciyarta ta huce sannan ya je gareta,saboda ya san cewa a halin yanzu babu abin da zai ce mata ta kula shi,Daddy ya gaya masa kutu mahaifinta yake so ya kai a ba ta takaddarta,in har A.m ya ƙi sakar mi shi ƴa,yayin da shi kuma ya dage don bai ga abin da zai saka ya rabu da ita ba.

Juwairiya na zaune akan ɗaya daga cikin kujerun falon Hajiya Binta,abokiyar zaman Umma,ita da Hamdiya da ba ta daɗe da dawowa daga makaranta ba.

Hajiya Binta ta fi kowa tarerayarta a cikin gidan,saboda ta ya ba da hankalinta sosai kuma mace ce mara damuwa da ɗora ma kai jiji da kai,ku san duk ta fi kowa sauƙin kai a gidan.

Fate ne ta yi mata da ga ɗan manja sai magi da gishiri,in ban da kwatira ta ciki babu abin da zai saka ta sha.

Hira suke yi sosai da Hamdiya sai Hajiya Binta da take saka musu baki jefi-jefi,yayin da hankalinta yake kan tibi tana kallon shirin daɗin kowa.

A.m ya yi sallama ya shigo cikin shadda kalar bula mai kyau.
Daga ɗakin mahaifiyarsa yake aka ce mi shi tana nan,ya taho da zumuɗinsa ya ganta saboda tafiya da ya yi,zuwa cairo har tsawon sati ɗaya.

Idanunsa akan cikin shi burinsa ya ga ya fara girma don har yanzu shakkun tana da ciki yake yi ya ƙosa ya ga cikin ya fito.


" A a lale barka da mutanen turai."Hajiya Binta ta faɗa tana kallonsa da ya yinsallama ya shigo.Gefenta ya zauna yana shafa kansa.

Bayan ya gaishe ta ya kalli Juwairiya da ta haɗe girar sama da ƙasa,ba tare da ta kalle shi ba ta kauda kanta gefe,tana shan faten duk da ta ji ya fitar mata a rai,saboda ƙamshinsa da ta shaƙa.

Hamdiya ta gaishe shi ta fita Hajiya Binta ta miƙe tana faɗin." Bari na kawo maka abinci Momi ba ta dawo daga gurin aiki ba."

Bai amsa ba ta shige kicin don haka ya ɗago kan sa ya watsa mata wani kallo da ƙyamar a faten da take ci.

" Matar shige ya babyna da fatan ki na kula min da shi?Ba ki bar shi ya yi kukan rashina ba."

Wata uwar harara ta sakin mata kullum a zaman su tana ƙara sanin A..m, baya ƙaunarata kamar yadda yake nuna mata,sam bai gaya mata ya yi tafiya ba.
Ganin taƙi tanka mishi sai ya tashi ya koma gefenta tare da rungumota gabaki ɗaya yan faɗin." Allah Sarki baby na yi missing ɗin ka bari na ji lafiyarka."

Juwairiya da ƙarfinta ture shi gefe tana toshe hancinta,yayin da ta fara kakarin amai.
" Don Allah ka rabu da ni kar ka ƙara matsowa kuda da ni! Ba na sonka kuma ba na son na ji ƙamshin turaren ka.Wallahi wani irin wari kake yi,wanda i don't want to say ga irin sa."

A.m ya zaburo cikin ɓacin rai ya kalle ta da ƙarfi ya ce." Ke kar ki raina mini wayo kin ce ba ƙya son ƙamshin turaren na canza kan dole, yanzu wannan daga Cairo na siyo shi,za ki raina mini wayo ki ce ina wari,bayan duk zuriyar ku babu ba wanda zai iya siyan turaren."Cikin ɗaga murya yake maganar,amma sai ta kalle shi ta saki ɗan ƙaramin tsaki,wanda ya ji ran sa ya ƙara ɓaci sosai.

" Ya akai yi Abdurrahman tana fama da kanta kake ɗaga mata murya?"Hajiya Binta ta faɗa lokacin da ta kawo masa abinci ta ije a gaban sa.

Hararar Juwairiya ya yi ganin tana mi shi
wani kallo sama-sama yana mamakin rashin kunyar da take so ta fara yi masa.
" Ya zan yi da ita gabaki ɗaya tun da ta samu ciki take yi mini gani-gani,duk turaren da na sa sai ta ce bai yi mata ba,tana son ta nisanta ni da babyna."Da shagwaɓa ya yi maganar da kuma murya mai alamun ɓacin rai.

" Sai ka yi haƙuri ka san sha'anin mata in suna da ciki,wataƙila ba ya yi mata daɗi ne saboda ana fuskantar haka."

Kasa cewa komai ya yi saboda takaici sai hararata yake yi,yayin da ita hankalinta ba shi garesa goruba take ta gwawiya.
" Cinyau kawai daga samun ciki komai kika samu kici,kuma ni takaicina cimar talakawa da kike yi."Ya yi tsaki ya ƙara cewa."Dama duk abin da ka haɗa da talaka sai ya ba ka haushi,yanzu fisabilillahi mai za ki ci da waɗannan cimar wahalar da  kike yi,to wallahi ba za ta saɓu ba dole ki canza ni zan tsara miki kalar abincin da za ki ci,kar yarona ya fito yana cin cimar talakawa."

Juwairiya da takaici ya ishe ta tun da yake gaya mata magana bai taɓa damunta kamar na yau ba,ta buɗe baki za ta mayar masa magana,amma idanun Hajiya Binta ya saka ta kasa,sai kawai ta shige ɗakin ta yi kwanciyarta.
" Dole fa sai ka jure dama haka mata suke yi in suna da ciki,in ka yi haƙuri laulayi ne yana fara girma za ta daina." Ta ce masa tana kallon sa da murmushin abin da ya ce." Haba ji fa don Allah wannan abin mai kama da icce take ciki,salon ya karce yarona."Ya faɗa bayan ya ɗauki goribar yana juyata a hannunsa.

Miƙewa ya yi lokacin da take dariyar abin da ya ce." Bari na gaisa da baby na dawo ko hutawa ban yi ba."Ya wuce ɗakin da ta shiga.

Juwairiya na kwance sai ji ta yi mutum ya kwanta gefenta tare da ɗora hannunsa a cikinta.

Kafin ya yi magana wani irin amai ya turnuƙo ta shiga kyara shi a jikin sa.Am hankalinsa ya tashi sosai ran sa kuma ya ɓace,ganin yadda ta ɓata mi shi jiki da amai.
" Wannan wane irin rainin wayo ne?Amai za ki yi mini a jiki."Ya faɗa yana wani yatsina fuska tamkar shi ma zai yi amai

Ɗaga idanunta ta kalle shi a wahalce ta tabbata A.m ba shi da tausayi a zuciyar sa.

Miƙewa ta yi za ta shige bayi ta ce." Na ce ba na son ganin ka balle na ji warin jikinka,ba ciki kake da buƙata ba?Meye na ka da sai ka addabi rayuwata,in na haihu sai ka yi yadda kake so da babyn, amma kar ka ƙara kusa toni,saboda babu wanda na tsana fiye dakai a duniya sa..."

" To tun da ba kya sona sai ki zo ki kashe ni!An gaya miki ni ɗin son ki nake yi,kawai saboda na ji ɗumin yarona nake matsowa garaki.Aikin banza kawai."Ya ce da ƙarfi saboda ya ji zafin tsanar shi da take faɗin tana yi,a tunanin sa ba wannan lokacin ya kamata ta nuna masa ba ta son ya matso gareta ba,saboda yanzu yana buƙatar ya din ga jin girman babynsa.

Ƙoƙarin cire rigar da ta ɓata ya yi ya ije mata a gefenta." Kin san Allah sai kin wanke rigar nan,kuma in mutuwa za ki din ga yi ba amai ba sai na din ga jin motsin babyna saboda babu uban da ya isa ya hanani kuɗi na biya."Ya fice cikin ɓacin rai.Tsaki ta yi ta gyara jikinta ta koma ta kwanta

Bacci ya soma ɗaukarta ta ji ƙarar waya da sauri ta miƙe ganin numbarsa ne ya sa ta datse kiran ta koma ta kwanta,sai dai yawan kiran da yake yi ya sa ta ɗauka ba tare da ta ce komai ba.

" Hello ki na ji na?"Ya tambayeta cikin ƙosawa.
                               " Umh."
Kawai ta ce mi shi ba tare da ta ƙara cewa komai ba." Na kasa tafiya gida ina falon momi don Allah ki zo ki gaya mini kalar turaren da kike so na din ga sawa,amma ki bar ni na din ga jin lafiyar babyna don Allah."

Ta yi shiru tana tunanin mai za ta ce mi shi sai ta ji ya ƙara cewa." In dai a kwai kalar ƙamshin da ya yi miki,ki faɗa mini zan siye shi ko nawa ne."

" Ni babu ƙamshin da nake so sai humrar da Hamdiya take shafawa."Ta ce da shi.

Kamar tana ganin sa ya ware idanun sa da ƙarfi ya ce." Amma ba ki da hankali ni ne zan shafa turaren humra mata fa suke sawa."A ƙufule kuma cikin muryar tsawa ya gaya mata duk da ya san A.k ya gaya mi shi,ba a yi ma mai ciki tsawa,amma abin da ta ɗauko na rainin da ta ɗauko ba zai ɗauka ba.

" In ba za ka shafa ba dole ne dama ban ce dole sai ka shafa ba,na san ta mata ce, ita take birgeni kuma nake son ƙamshinta,don haka ka sha zaman ka,ba dole sai ka zo in da nake ba ko ka taɓa jikina,don yanzu kamar yadda ka tsane ni baka son wallahi na fi ka tsanar ka."

Ɗif ta kashe wayar har wani huci take ita kanta ta san ta koyi tsiwa,wanda ta rasa gane dalilin haka kowa ma haushin sa take ji.

A.m da ya yi sagalo da waya a hannunsa tsananin mamakinsa ya kamata,tunaninsa yaushe ta canza.

Hamdiya ya ƙwala ma kira sai ga ta ta fito da sauri." Don Allah sis turaren da na shafa ba shi da daɗi?"Dariya tambayar ta ba ta don ta san kanun,amma sai ta ƙunshe dariyar ta kalle sa yadda ya ci magani ran sa a ɓace ta ce."A a yana da daɗi Ya A.m duk turaren a kwai daɗi da fatan ka yi mana tsarabar sa?"

Tsaki ya saki." A a wancan ƴar rainin wayon ta ce wari nake turaren bai da ƙamshi,tun da ba ta son turaren zan kawo miki sai na canza wani,yauwa ta ce turaren da kike shafawa take so humra ina son ki ba ni."Ya faɗa ba don yana so ba ran sa na suya saboda ta ce yana wari,kamar shi duk wanka da gayu da yake yi.

Duk yadda ta so ta ɓoye dariyar sai da ta dara ganin yadda ya yi." Mai za ka yi da humra ta mata ne f.."
" Ya kike so na yi kwata-kwata ta hanani in ji ɗumin babyna ni kuma ba zan iya zama ba tare da jin ɗumin shi ba."Ya faɗa ba tare da ya ji kunyar ta ba.

Ganin yadda ya yi maganar ba wasa sai ta shige ɗaki tana dariya ta kawo masa.

" Bari na shafa sai na je."


Ya faɗa yana sinsinar kwalbar turaren amma bai ji wani daɗin da take da shi ba.

" Da ka yi haƙuri sai ka canza kaya ka shafa ka dawo kar ta ƙara wani amai,tun da a kwai ƙamshin wancan turaren da ba ta so a jikinka."Ta ce da shi.

Ficewa ya yi ya nufi motarsa ba tare da ya tanka mata ba,shi a ganin sa Juwairiya raina mi shi wayo ta yi,shi ya sa take faɗin yana wari.

Bai zo gidan ba sai washegari gabaki ɗaya kunya ta kama shinda ya fara shafa humrar sai ya ji sam ƙamshinta ba ta yi masa ba,amma kan dole ya shafa ya ɗauki wayarsa da ya gama tura ma Zainab tsaƙon text na ban haƙuri da gaya mata dalilin da ya saka ya aure ta,ya sauko ƙasa.

A.k ya gani zaune a falon wanda tun ranar da bin ya faru bai ƙara ganin shi ba,har ya yi tafiya ya dawo sai yau.

Kamar yaro ya duƙa lamun yana ba shi haƙuri tare da ƙama kunninsa duka.

A.m da ke saukowa yana ganin sa ya ɗaure ya kauda kan sa don ya ba shi matuƙar haushi,wato da kashe shi za a yi sai dai a kashe shi kenan,shi ya gudu don haka ko kallon in da yake bai yi ba ya kama hanyar fita 

Da gudu A.k ya ruga ya kama hannunsa yana roƙonsa tare da yi masa dariyar ƙeta.

Da  takaici ya ishe shi bin shi ya yi da gudu suka kama tsere-tsere kamar wasu yara,har A.m ya riƙe hannunsa tare da ɗaukar filon kujera,ya din ga maka masa a jiki shi kuma yana dariya.


Da ya gaji sai ya faɗa jikinsa suna haki can kuma suka saki dariya suka tafa.
" Wato ka gudu ka barni duk abin da zai faru ya faru ko?Wallahi ban san ba ka da mutunci ba sai a lokacin sam ba ka cika aboki ba."

Dariya ya yi." Ah to ya kake son na yi kaga laifina haka kawai yadda Abba ya harzuƙa so kake na ja ma kaina?Ai tsunttsun da ya ja ruwa...."

" Aiko na sha mari sosai kumatuna har sai da suka yi."Ya faɗa masa jin abin da ya ce.

Dariya suka ƙara yi sannan A.m ya miƙe." Well zan je na ga babyna ka san mun shiga da ga ciki,yanzu ina da wanda zan kula da shi so yanzu lokacin sa ne."

" To sabon shiga ofis nake son na je saboda tsoron kar mu haɗe na fara zuwa gidan ka sabon shiga."

" Ni fa ƙamjin turaren humra nake ji na mata ko Zainab ta dawo ne?"A.k ya ce yana wani shinshine-shinshine.
Bugu ya kai masa a baya." Gulma babu kyau ban sani ba."Dariya ya yi ." Allah da gaske nake yi kamar irin na Maman Najwa da take shafawa,na sani ko lallaɓo abin ka ta dawo."Ya ce da shi lokacin da ya buɗe mota zai shiga.

" Ba ita ba ne wancan ƴar rainin wayon ce,wai ba ta son ko wane irin turare sai wannan turaren,har yanzu cewa take ina wari ka san Allah bacin cikina da ke jikinta da sai ta gane ba ta da wayo da take faɗin ina wari."

Dariya sosai ya yi." Ikon Allah sai haƙuri haka yawancin masu ciki suke yi,amma mafi yawancin mazaje ba sa ganewa sai suna ganin kamar ƙarya suke yi,bayan da gaske iya gaskiyar su suke faɗa.".
Rufe motar ya yi." Ok bari na je mu gaisa sai na shigo."Ya ta da motar sannan A.k ya wuce gurin motarsa.

A.m ya yi sallama a cikin falon mahaifiyarsa wacce ya tabbata tana gurin aiki a wannan lokacin,kamar yadda ya yi tunani haka ne kuwa don babu kowa sai yan aiki da suke ta hidimar su.

Kai tsaye ɗakin da ya san take ya nufa a ƙofa suka kusan karo, da Hamdiya ta ta fito da gudu da kofin tea a hannunta tana kurɓa.

Matsawa ya yi gefe ganin yadda take sauri kamar za ta tashi sama." Barka da zuwa Ya A.m na yi latti sosai so by."

Ta fice ba tare da ta bari ya amsa gaisuwan ba."Shirmanmun yara kawai mutum ya san yana da lecture amma ya tsaya yana ɓata lokacin sa."Ya ce tare da tura ƙofar ɗakin.

A.m da ya yi turus a tsaye gani  tana bacci ya yi kamar ya juya,saboda abin da Hamdiya ta rubuto masa har da ba a tashin mai ciki da ga bacci.

Sai kuma ya fasa ya yanke shawarar ya gaisa da shi kawai  a hakan.

Hannunsa ya saka ya ɗaga rigarta ya ɗora hannunsa a lafaffen cikinta da bai nuna alamun tana da ciki ba.Tsaki ya yi don shi ya matsu ya ga cikin ya fito.

Juwairiya da take bacci ta ji kamar an taɓa ta kafin ta buɗe ido sai ta ji ƙamshin A.m da ta tsana.

Da sauri ta buɗe ido ta yi ido biyu da shi da yake tsaye yana taɓa cikinta.

Ture shi ta yi tare da miƙewa da gudu ta ruga bayi.Tsabar takaici ya sa A.m tsayuwa kamar an dasa shi har ta gana amai, ta fito ta tsaya can nesa da shi yayin da miyau ya taru a bakinta.

" Na lura iskanci da rashin mutunci yake saka ki kike mini wulaƙanci,kin mai da ƙamshin jikina sai kace warin kashi da na matso kusa dake ki fara amai,to ki sani wallahi ko kayan cikinki za ki mayar sai na din ga gaisawa da babyna,don na lura so kike kawai ya shaƙu dake ke kaɗai saboda in na raba ku,ya ne me ki,don ki sani ba zan zauna dake ba kamar yadda iyayena suka faɗa mini."

Tsaki ta yi ta tofar da miyau sannan ta yi mishi kallon banza ta ce." Na lura ba turaren da ka shafa ba ne na tsana,kaine na tsana kake mini warin da ya fi na kashi ɗoyi,don haka kai ya dama in ka rabu da ni,saboda in zan din ga jin irin wannan warin  da nake ji a jikinka,to zan yi fatan Allah ya nisanta ni da kai har ƙarshen rayuwata."

Cikin mamaki ya tsaya yana kallonta a ran sa tunani yake to ko dama yaudarar sa take da take cewa tana son sa,jin irin kalaman da take mi shi,wai yaushe ta zama haka duba ga da ko kallon sa cikin ido ba ta yi,sai hawayen banza da take mi shi,lallai ya yi sake ta raina shi.

" Tun da mun tsani junanmu na ji daɗi sosai kin ga rabuwarmu za ta zo cikin sauƙi,amma wallahi ba ki isa ki hana ni jin ɗumin babyna ba."

Da sauri ya matso tare da ƙanƙame ta kamar zai mai da ta cikinsa.

Juwairiya ta saka kuka da ƙarfi ji take da ya rungume ta kamar ana soka mata allurai,yayin da wani amai ya ƙara ta so mata.

Momi da ta dawo sakamakom mantuwar da ta yi ta ji kukan Juwairiya da ƙarfi,duk da ta ga motar A.m a gidan,amma kukan da ta saka da ƙarfi ba na lafiya ba ne.

Turus! Ta yi tana kallon sa yayin da kunya ya kama dukannin su.

Shafa kan sa ya yi." Momi rashin mutunci take mini wai wari nake yi duk iya gayuna,shi ya sa na murɗe mata baki don ni ba na ɗaukar raini."

A kunya ce ya faɗa ganin ta gan shi rungume da ita." Ba na son iskanci maza ka tattara ku tafi gidan ku,don ta ce kana wari shi ne za ka mata irin wannan matsar ina falo fa na ke jin ƙarar ta,kaman ta abin da yake cikinta."

" Na sani raina ni ta yi da yawa don kawai ta samu ciki,to ta sani ba zan ɗauki raini da ga gareta ba.Kuma Momi ta zauna a nan kawai har ta haihu "Ya ce da ita saboda sam baya son ta ƙara komawa gidansa,shi burinsa ya san yadda zai yi ya dawo da Zainab.


" Ka san Allah gobe zan tura masu aiki su gayara muku gidanku ku je can ku ƙarata in kun so ku kashe kan ku."Ta juya ta shige ɗakinta don ta ɗauko abin da ta manta.

A.m ya juya ya kalle ta tare da banka mata uwar harara." Kin san Allah ki gaya musu anan za ki zauna in kika bari aka tilasta mini yaga-yaga zan yi da naman jikinki,don kullum ina jikinki ina jin ɗumin babyna ina ya so duk abin da zai faru dake ya faru.Bayan nan matar so za ta dawo in ba so kike ta yi miki dukan mutuwa ba."

Kwatankwacin hararar da ya ke masa ta mayar masa ko in ce fiye da haka ta ce." Allah ya ba ka sa a in ka so ka shige cikin jikina ka zauna ba ka raɓe ni ba,amma ina gaya maka wallahi in ka takurani zubar da cikin nan zan yi sai na ga ƙaryar raɓar jikina tun da na gaya maka ba na son ka na tsane ka tsana mai tsanani,sannan matarka ta dake ni ta daɗe kai za ta yi ma illah,kuma wallahi in har ka yadda na koma gidanka sai na hana ka ko shan ruwa a gidan kai da matarka?..."

Da sauri ya kawo mata shaƙa yayin da idanunsa suka yi jajir jin tace za ta zubar da ciki.

Juwiriya ta takura ta tsandara ƙarar saboda hankalinta ya tashi ƙwarai ganin yadda ya canza kammanni,ƙarar ya saka Umma ta yarda abin da ta ɗauka ta rugo ɗakin da gudu,har da ma aikatana gida.

ƘARAR YA SA NI MA NA RUGA A GUJE GANIN A.M ZAI SHAƘE TA BAI JI ABIN DA A.K YA FAƊA MI SHI BA.







TO MASU KARATU KU DAI BIYO NI KU JI YADDA ZA TA KAYA A TSAKANIN SU YAU BAN YI TYPIND DA YAWA BA,SABODA BA NA JIN DAƊI KU YI HAƘURI DA WANNAN ANA TARE.


KU CI GABA DA BIBIYAR LINTAFIN DON JIN YADDA ZA TA KAYA  A CIKIN LINTAFIN NAN MAI FARIN JINI.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol