Free chapter · Read without an account
1
Da sauri ta sunkuya tana mai dafe tarin takardun dasuka watse zuwa ƙasa wanda hakan yayi dai dai da shima sanda yakai nashi hannun zuwa ƙasan cikin rashin sa'a kuma hannunsu ya sarƙe dana juna atake anan taji wani baƙon yanayi ajikinta mai wuyar ta fassara shi.
Saɓanin shi dayay saurin ɗauke hannunsa daga saman nata gefe guda kuma yana jefa mata kallon raini da ƙasƙanci.
Sam bata lura da hakan ba face ƙarasa tattare mai takaddun nashi datai tana sakin wani irin lallausan murmushi.
Hannunta har yanzu rawa yake sakama kon baƙon lamarin daya faru agareta yanzu.
Seda ta kammala tattara mai sannan ta ɗago fuskarta cike da murmushi mai ƙayatarwa ta dube shi da matsakaitan idanunta.
Wanda kallo guda tayi masa takasa cigaba da kallon nashi murya na rawa kamar zatai kuka ta furta!
"Afuwan yallaɓai ban kula ba"
Tafaɗa tana mai janyo maganar da kyar tsintar kanta tayi dajin wata irin wawiyar faɗuwar gaba marar misali acikin kirjinta zuciyarta kuma kamar zata fasa kirjinta ta faɗo dan tsabar rawan data keyi.
Bai amshi takaddun ba kuma bai dena kallonta ta ƙasan idanunshi ba yarinyace wadda batafi shekaru goma sha takwas ba sanye take cikin ɗamammun kaya waɗanda suka bayyana baiwar kyan surar da Allah ya bata gawani dogon gashi data zubo dashi har gaba da dokin wuyanta kallo ɗaya yayi mata yagane ainihin itan wacece.
Tayi mai kama da karuwa marar aji kokuma tantiriyar ƴar iska marar aji! Abin da ya faɗi kenan aranshi yana mai lumshe kyawawan idanunshi.
Totaly batafi sa'ar ƴar ƙaramar ƙanwarshi ba to mai yasa zata ɓata rayuwarta ta nakasa kanta.
"Yallaɓai ka amsa hannuna"
Taja maganar cikin ƙosawa.
Tana mai tsareshi da nata idanun wannan lokacin ta ɗan ƙare mai kallo kaɗan.
Ataƙaice Shiɗin dogon namijine ƙaƙƙarfa baƙi mai ɗauke da manyan idanu da yalwatacciyar gira kallo ɗaya zaka masa kasan yana cikin jerin maza masu aji tare da izza da taƙama uwa uba kuma hutu gayu da ƴaƴan banki sun sami muhalli atare dashi.
Har yanzu hannunshi na naɗe a saman kirjinshi idanunshi lumshe wanda shi kallonta yake batare data farga da hakan ba.
"A'a ya subuhanallahi A'A yana ga baka ƙarasa ciki ba"
Maganar wani magidancin farin namiji daya karaso wajansu yanzu wanda hakan yasanya yarinyar zube mai takaddun ajikinsa ta ƙara gaba cikin sauri tabar wajan.
Cikin sauri yarinyar take sauka ƙasa har tana haɗawa da ɗan gudu kafin ta fita compound na hotel ɗin wata baƙar mota ta buɗe da sauri ta shiga taja murfin tana maida numfashi.
"Ke Ummul lafiya naga duk babu nutsuwa atare dake kodai...?"
Bata bar wadda ke mazaunin drivern tai magana ba tai saurin tarar numfashinta.
"Ameera ja mota mutafi yau nai gamo da ƙaddarata"
Wadda ta kira da ameerah itake mazaunin driver wadda daga gani zata girmewa ummul da sauri tai revars haɗi da nufar gate ta fita a hotel ɗin baki ɗaya.
Titi tahau tare da kunna redion motar.
Seda suka bar arean sannan Ameera dai ta kuma juyowa ta dubi ummul ɗin haɗi da ce mata.
"Ina mukai can ko nan?"
Lumshe idanu ummul tayi tare da cewa.
"muje rufaida ki mana order babu wani target yau kam mu tara gobe insha Allahu"
Tafaɗa har yanzu kirjinta bai dena rawa ba wanda tun haɗuwarta da A'A kamar yadda taji ɗayan ya faɗi ta tsinci kanta tare da hakan.
Gangara motar ameera tayi zuwa Rufaida fita tayi zuwa cikin wajan ta siyo musu ta dawo har lokacin idanun ummul suna lumshe haka ameera taja motar tare da ɗaukar hanyarsu kai tsaye hotoro ta nufa da motar tafe da ƙwarewa.
"Ameera yau naso shiga cikin gari amman hakan baze samu ba"
Tafaɗa tana mai cije lips ɗinta ameera batai magana ba sabida wayarta datai ringing ɗauka tai tana magana cike da barikanci still idanunta yana bisa kwalta.
Hotoro tsamiyar boka dai dai rakat ameera tasha kwana layi na uku ta shiga wanda yake tsit babu alamun jama'a awajan.
Abakin wani dogon gate ta tsaya tare da kashe motar ta ɗauki ledar data siyo musu rufaidan tayi waje itama ummul cike da sanyi ta balle nata murfin ta fita.
Gate ɗin suka karasa ameera taja kofar ta shiga itama ummul taja ta shiga ciki wanda tundaga farkon gidan har zuwa ciki matane zaune wasu na lido wasu na karta wasu tabar sigarice agabansu wasu kuma shisha gefe ɗaya kuma dogayen ɗakuna ne masu layi layi kallo ɗaya zakama gidan kasan gidane na karuwai amman na haya.
Kowani ɗaki akwai number ajikinsa hakan yasa ameera nufar ɗaki mai lamba ta hamsin ta buɗe da key suka shiga ita da ummul.
Ɗakine madaidaici domin babu tarkacen komai aciki daga gado se wadrobe na kaya se gas karami da frij babu toilet sabida gaba ɗaya bayi yana can waje kowa da kowa shiga yake.
Ameera ta aje ledar tare da faɗawa gado tana furta.
"washh kawata yaufa naci ubana babu karya komai na jikina ciwo yake lallai Alhaji motar daya bani ba abanza ba"
Murmushi ummul tai kafin tayi magana wata mace kakkaura baƙa ta shigo ɗakin nasu.
"Yau akwai gayu zasu zo da daddare acikinku idan da wadda bata da M point sedai magana domin babbar fita ce"
Ummul batai magana ba sema tashin datai zuwa gaban wadrobe tana kokarin ɗaukar zani ta ɗaura Ameera ce ta kada baki tace.
"nikam yau na gaji sedai ummul"
Tafaɗa tana mai kallon ummul dake tube kaya tare da zira hijab akan zanin data daura.
"Nima bana jin fita yau bana jin daɗi sam"
Murmushi matar tayi tare da cewa.
"Haba keko ina hasko alkairi atare da fitar nan taki gaskiya kiɗan daure sabida sunfi son irinku ƴan yara sekinfi kawo light"
Tafaɗa tana mai kashe idanu irin na ƴan duniya.
Rabeta ummul tai haɗi da ɗaukar boket tabar ɗakin.
Da kallo ameera da matar suka bita.
"Rabu da ita Anty ladi lafiya lau muka fita amman duk tai wani iri kamar wadda akama sukuwa"
Ameera ta faɗa tana dariyar iskanci.
Taɓe baki anty ladi tai tare da cewa.
"Ki shawo kanta ami sabida wannan fitar mai lasisi ce ok sena jiki yadda kukai"
Tafaɗa haɗi da ficewa daga ɗakin gaba ɗaya.
Da sanyi jiki ta ƙarasa gaban famfo ruwa ta tara haɗi da nufar toilet ɗinsu dake tsakiyar gidan..........