Free chapter 路 Read without an account
Chapter 12
IMARA 馃拫 馃拫
Mikiya writers asso...
Chapter 12
Wani irin abu ne ya tokarewa Imara a 茩irjinta, batasan sanda ta saki takardar hannunta ba, gaba-daya jikinta rawa yake, runtse idanu tayi wasu zafafan hawaye suka fara sintiri kan fuskarta. Batasan sanda ta silalo daga kan gadon ba ta yi zaman dirshan a 茩asa, wani zazza蓳i ne ya rufeta wanda yakeda nasaba da abinda idanunta ya gani, dafe 茩irjinta tayi jin yadda zuciyarta ke wani irin bugu daya zarce misali, 茩o茩arin take tayi kuka amma bakinta ya gagara, hawayen ma ya 茩afe daga idanunta, sai bin 蓷akin take da kallo tamkar wata zararriya.
"Mamah wai..."
Turus ya yi ganin wata kyakkyawar budurwa zaune ta zubawa kofar idanu, bai san da zuwan Imara gidan ba hakan yasa shi yayi mamakin ganin fuskar da bai sani ba a 蓷akin Mamah. 茦arasawa ya yi yana kallonta ya ce"Hyy, where is Mamah?" jin tayi shiru yasa ya 蓷an ha蓷e rai yana zare idanu ya ce"kee..baki jina ne?" Shirin da yaji ta sake yi masa ya sanya ya 茩arasa dab da ita ya ta蓳a ta, ga mamakinsa sai yaga ta tafi luu ta fa蓷i 茩asa sumammiya. Saurin ja da baya Khalil ya yi ya shiga girgiza kansa daidai nan Mamah ta bu蓷e kofar 蓷akin ta shigo da mamaki take kallonsa sai kuma ta kalli Imara wacce ke kwance 茩asa tamkar tana bacci, cikin hanzari ta 茩arasa gabanta ta shiga jijjigata amma shiru babu alamar tana jin abin da take cewa. Tashi Mamah tayi ta fice daga 蓷akin ba tare da ta sake bi ta kan Khalil ba, tana fita ya koma inda Imara ke kwance ya tsugana ya zuba mata idanu
"Woww Beautiful"
Khalil ya samu kansa da furta hakan yana sakin wani yalwataccen murmushi, ya saba ganin kyawawan 拼an mata amma bai ta蓳a ganin mai kyau irin Imara ba. Yana cikin wannan tunanin ta bu蓷e kofar ta shigo ta dawo inda take, not too long shima ya shigo 蓷akin yana sanye da wata jallabiya ash colour, gaba-daya gashin kansa ya rufe fuskarsa da alama daga wanka ya fito dan babu alamar gyara a kan nasa. Tafiya yake a hankali kamar ba wanda aka yiwa reporting ciwo ba
"Abaan mene haka?, bakaga halin da take ciki bane?"
Bai ce komai ba sai hannunsa daya sanya ya 蓷an hargitsa gashin kansa kafin ya tsugana daidai inda take, hannunsa ya kai ya ta蓳a wuyanta, ya yi kamar zai mike tsaye sai kuma ya sunkuya ya 蓷auketa tamkar Baby ya yi waje da ita.
45, Zaria road Kaduna
***Zaune take gefen gadon ta zubawa kanta idanu, wayarta ce ta shiga ringing ta kalli wayar ta ta蓳e baki ta cigaba da kallon fuskanta, saida akayi 4missed calls kafin ta 蓷auki wayar ta sanyata a flymode ta yi cilli da ita kan gadon. Turo kofar 蓷akin akayi wanda ya sanya ta juya dan ganin wanda ya shigo mata 蓷aki, murmushi ta sakar mata tana 茩arasowa ta ce"har yanzu shirin ne baki gama ba?, Kin fison sai babanki yazo yana jiranki ko?" mikewa tsaye tayi tana gyara zaman veil din jikinta ta ce"nafa gama Mom" numfasawa tayi ta ce"yanzu sai yaushe?" langwa蓳ar da kanta tayi ta ce"ke da kika koreni, wlh saina da蓷e ban zo Kd ba" murmushi Mom tayi ta ce"Allah ya huci zuciyar Mamana, ba korarki nake ba, halin mahaifinki nasani banason ya yi miki fa蓷a ko ya yiwa mahaifiyarki shiyasa amma ke kinsan I'm gonna to miss you alot" rungume small Mom 蓷in tata ta yi tana turo baki ta ce"me too Mom" shafa bayanta tayi ta ce"muje kar kuyi missing flight.
Tsaye suke a farfajiyar gidan, "A'isha! A'isha" juyowa tayi ta kalleta ta ce" lafiya dai?" Murmushi tayi tana kallon yar uwar tata ta ce"yau Aunty Jidda zata koma Kano fa" wani tsalle A'isha tayi ta rungumeta tana dariya ta ce"kai amma naji da蓷i, alhamdulillah, mun rabu da jaraba in Sha Allah ba zata sake dawowa gidan nan ba" bu蓷e baki tayi zata yi magana taga ta fito tana jan troley dinta, sanye take da wata doguwar rigar Egyft Abaya coffee colour ta sanya wani sun glasses a idanunta hannunta 蓷aya ri茩e da hand bag 蓷inta sai taunar cew gum take. Ta gabansu ta zo zata shige suka kalleta ba tare da sun ce mata ko a dawo lafiya ba suka shige cikin gidan, yanda basu nuna sun ganta ba haka itama bata nuna ta gansu ba kanta tsaye ta shige bayan mota driver ya jata zuwa Airport.
Kano state
Murmushi Mamah tana kallon Jadda bata ce komai ba. Ri茩e ha蓳a Jadda tayi tana 茩an茩ance idanu ta ce"au sallamammiya kika mayar dani ko me?, Ina fa蓷a miki abin da matar nan tayi min amma kina min dariya? Eh lallai! bari shi wanda na isa dashi 蓷in ya dawo, wlh sai na saka ya saketa idan batayi wasa ba". Girgiza kai Mamah tayi cikin cool voice 蓷in ta kamar koda yaushe ta ce"ki dai yi hakuri Jadda, maybe gajiyar tafiya yasa bata zo ta gaisheki ba"
"Babu wani gajiya rashin arziki ne irin nata, kuma zata san dani take zancen ba dai 蓷ana take aure ba!" Jadda ta fa蓷a cikin fa蓷a, Ita dai Mamah bata sake cewa komai ba gudun kada itama tayi wani laifin.
A hankali ta shiga bu蓷e idanunta wanda suka yi mata nauyi, 蓷akin da take ta 茩arewa kallo kafin ta fara yun茩urin tashi zaune, kallon hannunta tayi taga an saka mata drip a hankali memeries 蓷in abin da ya faru ya fara dawo mata, wani irin raunataccen kukane ya kwace mata ta shiga rareshi kamar 茩aramar yarinya, saida tayi mai isarta sannan ta tashi da niyyar fita daga 蓷akin daidai nan ya bu蓷e wata 茩ofa ya shigo, kallo 蓷aya ya yi mata ya 蓷auke kai ya nufi gaban gadon, drip din hannunta ya cire sannan ya 蓷ago yana kallonta, saurin 蓷auke kanta tayi wasu hawayen na biyo fuskarta. Ta蓳e baki Abaan ya yi bai sake bi ta kanta ba ya juya ya fice daga 蓷akin gaba蓷aya. Da idanu Imara ta bishi sai Kuma ta sake fashewa da wani sabon kukan tana bubbuga 茩afa.
***Da gudu ta tawo ta rungume mahaifiyar tata tana murmushi ta ce"Mom nayi missing naki" murmushi itama tayi ta ce"nima haka Jidda, ya hanya?" Bata ba ta amsa ba sai kallon 茩ofar 蓷aya apartment 蓷in da take, ganin abun take kamar a mafarki hakan yasa ta kasa 茩arasawa gurinsa ta juyo ta kalli Mom tata bakinta na rawa ta ce"Momm...Mom ya Abaan ya dawo?" wani kallo Mom ta watsa mata kafin ta ce"yadawo mana, mene ha蓷inki da dawowarsa?, ko har yanzu akwai wani abu a zuciyarki ne?, karki fara cewa zaki yi abin da zai sakani a bakin duniya Jidda, ki fita harkarsa a daina yi mana kallon wa蓷anda basu kai ba idan kuma ba haka ba..." Sakar baki Mom tayi ganin Jidda tayi hanyar Apartment din Babu ma alamar tana sauraren abin da take fa蓷a.
"Jidda! Jidda!"
Tamkar ba ita da ita take magana ba dan ko juyowa bata yi ba ta shige apartment 蓷in, tsabar takaici kasa motsi Mom tayi ta dinga kallon 茩ofar ko zata ga Jidda ta fito amma shiru babu labarinta
"Mom lafiya?, ina Jiddah?"
Kallonta tayi bata ce komai ba, ta juya ta bar wajen, da idanu Suhaila ta bita sai kuma ta 蓷aga kafa蓷arta irin bai dameta 蓷in nan ba tayi waje tana ri茩e da car key 蓷inta. Kai tsaye Jidda sama ta haye dan babu kowa a parlon kasancewar lokacin duk suna gurin aiki, 茩ofar dakinsa ta bu蓷e ta shiga bakinta 蓷auke da sallama, shiru taji da alama ma baya ciki, dan ha蓷e fuska tayi s shagwa蓳e ta ce"ina kuma yaje to?" Juyawa tayi zata fita taji an bu蓷e 茩ofar bedroom 蓷in an fito, da sauri ta juyo bakinta 蓷auke da murmushi saidai abinda ta gani yasa ta yi saurin ha蓷e fuska kamar ba ita ba, kallonta Imara tayi da idanunta wanda suka kumbura saboda kukan data sha bata ce mata komai ba ta zo zata shige ta gefenta. Kasa jurewa Jiddah tayi ta jawo rigarta tana watsa mata wani banzan kallo ta ce
"Hyy, what brought you here?, Ina mai 蓷akin yake?" Kallonta kawai Imara ta yi badan batasan abin da ta ce ba, yin shirun nata ya sake 蓳atawa Jiddah rai cikin masifa ta ce"keeee! Wane ubanki a garin nan da har ina yi miki magana kina jina?, me kike ta茩ama dashi?" Numfasawa Imara ta yi ta sake yun茩urin fita a karo na biyu, a fusace Jidda ta jawota kafin tayi aune ta sauke mata wani lafiyayyen mari daidai nan Abaan ya bu蓷e 茩ofar 蓷akin ya shigo, da idanu ya shiga bin su Jidda tayi saurin 茩arasawa inda yake tana murmushi ta ce"Yaya daman ka dawo?" kallonta ya yi bai ce mata komai ba, tasan me yake nufi hakan yasa ta ha蓷e ranta tana kallon Imara wacce ke tsaye hannunta 蓷aya bisa kuncinta ta ce"wai ina yi mata magana tanaji tayi min banza, kasan ni kuma bana 蓷aukan raini" ta 茩arashe maganar tana ha蓷e hannayenta a 茩irji. Kallon Imara kawai ya yi sannan ya kalli Jiddah cikin cool voice ya ce"get out" kallonsa Jidda ta yi nan da nan hawaye ya kawo idanunta ba ta ce komai ba ta juya ta fice daga 蓷akin tana banko 茩ofar, girgiza kansa ya yi kawai sannan ya 茩araso gabanta, wuyanta ya ta蓳a yaji sanyi klao da alamar zazza蓳in ya sauka,
"Je ki wajen Mamah ta baki abinci"
Abin da kawai ya fa蓷a kenan ya shige bedroom 蓷insa, da idanu Imara ta bishi kafin ta juya ta fice daga 蓷akin har sannan hawaye bai bar zuba daga idanunta ba.
Mamah na zaune kan kujera idanunta ma茩ale cikin glasses tana kallon show 蓷in da ake haskawa a TV Jiddah ta sakko daga saman, da idanu ta bita har ta 茩araso gabanta ta tsuguna
"Mamah ina yini"
"Saukar yaushe Hauwa'u?"
茒an murmushi Jiddah ta yi ta ce"zuwana kenan, shine naga motar Ya Abaan na biyo shi" jinjina kai Mamah ta yi ta ce"toh sannu da hanya yasu Jamilan?" "Suna nan klao Alhamdulillah, Ina Jadda?" Murmushi Mamah ta yi ta ce"tana ciki, tunda ta dawo taki komawa apartment 蓷inta" dariya Jidda ta yi ta ce" Jadda rigima, let me take shower sai nazo na gaisheta" okay Mamah ta ce Jidda ta tashi ta fita. Abbiey ne ya sakko daga cikin shigarsa ta manyan kaya kamar koda yaushe, kallonsa Mamah ta yi ta ce"yau ka makara yalla蓳ai" rollex 蓷in hannunsa ya kalla ya 蓷an yi tsaki ya ce" ban san time ya tafi haka ba, ina Abaan yake?" tashi Mamah ta yi ta ce"yana ciki, kasan halinsa dai, maybe jira yake hutun daya 蓷auka ya 茩are ya koma bakin aiki" girgiza kai Abbiey ya yi ya ce"no munyi magana dashi ai, ya ce yanason a gama komai na asibitin ne kafin ya koma Abuja so kinga dole a sake bashi lokaci" numfasawa Mamah ta yi ta ce"Jadda na nemanka tun 蓷azu" dafe kansa ya yi ya ce "ya rabb, har zan manta na fita" "ai kuwa da ka dawo yanzu" ta fa蓷a tana murmushi, girgiza kansa ya yi shima yana murmushin ya yi hanyar part 蓷in da take.
Yana barin wajen Imara ta sakko tana tafe a hankali, kallonta Mamah ta yi ta ce "daughter kin tashi?" jinjina mata kai tayi dan bakinta yayi nauyi, kama hannunta tayi tana kallon fuskarta ta ce"lafiya?, me ya sami fuskarki?, who slapped you?" girgiza kai Imara tayi tana aro dauriya gudun kada tayi kuka ta ce "babu kowa, bigewa nayi" shiru Mamah ta yi ba dan ta yarda da abin da ta ce ba, sai dan batasan 茩ureta,
"Muje kiyi breakfast"
Girgiza kai tayi ta ce"na 茩oshi yanzu" ha蓷e rai Mamah ta yi ta ce" da kika ci me?" sunkuyar da kanta 茩asa tayi tana wasada fingers 蓷inta, tallafo habarta Mamah ta yi ta ce"ki daina 蓳oyemin komai, muje ciki Inason magana dake" kallonta Imara tayi hawaye na taruwa a cikin idanunta ta ce"Tom Mamah".
***Zaune ya sameta tana jan cazbaha saida ya bari ta idar sannan ya gaisheta,
"Jadda lafiya kike nemana?" Girgiza kai Jadda ta shiga yi tana kallonsa ta ce"wai kamarni! Kamarni za'a yiwa irin haka ko?, kana sane da matarka bata zo ta gaisheni ba tunda na dawo daga asibiti?, yau ko zaman kafurci muke da ita ai ya ci tazo ta dubani ko?, amma wlh matar nan shiru bata zo ba, ina jin sanda suka dawo daga bikin amma ta kasa shigowa ta cemin sannu ya jiki, haka ake rayuwa Fadeel?, an kyauta min kenan?, haka taga Fatima nayi?, kullum cikin 蓷awainiya take dani yarinyar nan bata ta蓳a gazawa ba, shine ita zata dinga wula茩antani?, me nayi mata?, me na mata Eh?!..." Ta 茩arashe maganar tana goge hawaye da hijab 蓷in jikinta. Shiru Abbiey ya yi na wasu sakkani, gaba蓷aya ransa ya gama 蓳aci koda wasa bai yi tunani bata zo ta duba mahaifiyarsa ba, duk da tasan abin da ya sameta, a hankali ya kamo hannunta cikin son kwantar mata da hankali ya ce "dan Allah Jadda kiyi ha茩uri, zan yi mata magana, kuma in sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba, zan sanda yanda zanyi da wannan matsalar, amma kar ki damu kanki wani ciwon ya sake kamaki kamar da, kiyi mani wannan alfarmar" jinjina masa kai tayi ta ce "babu komai, ni kawai fa蓷a maka nayi, amma ban ri茩e kowa a zuciyata ba" ajiyar zuciya ya sauke ya ce"Nagode Jadda, bari naje" "Allah ya tsare ka, ya yi maka albarka, ya kula dakai da yaranka" murmushin jin da蓷i ya yi ya ce"Ameen ya rabbi Jadda".
***A fusace ta bu蓷e 茩ofar parlon tana zuwa ta fa蓷a kan mahaifiyar tata tana fashewa da kuka, girgiza kai Mom tayi cikin 蓳acin rai ta ce"dana garga蓷eki ai baki ji ba Jiddah, kinyi tunanin ko ya sauya ne?, da dai Abaan ya so ki amma tuni aka shiga tsakaninku, saboda haka tun wuri na fa蓷a miki ki fita hanyarsa!, ki daina zuwa in da ma yake kada ke ma ayi miki wani mugun abun" cikin shasshe茩ar kuka ta ce"wlh Mommy ina son Abaan kuma ni shi xan aura, wlh shi nakeso, shine wanda zuciyata ta za蓳a mini kuma za蓳inta zan bi, ki taimakeni Mommy, ki taimaka!" Ta 茩arashe maganar tana sake rushewa da wani sabon kukan, shiru Mommy tayi dan abun nema yake yafi 茩arfinta, tsayin lokaci tana neman yanda zata raba wannan al'amari amma abu ya茩i yiwuwa, tana cikin wannan tunanin ya bu蓷e 茩ofar ya shigo, da sauri Jiddah ta tashi ta shiga goge hawayen fuskarta ta tsuguna kanta a 茩asa ta ce "ina yini Abbiey" saida ya 茩are mata kallo sannan ya ce"lafiya klao" daga haka ta tashi ta shige ciki.
"Yanzu abinda kika aikata daidai kenan?, mahaifiyata ita ce abar rainawarki?, daga ke har yayanki babu wanda ya iya zuwa ya gaisheta?, kunsan kuma batada lafiya daga jin ya ta dawo, to bari kiji idan har kina son zama cikin gidan nan 茩ar茩ashina to dole sai kin girmama mahaifiyata, idan kuma ba haka ba wlh zan 蓷auki mummunan mataki akan ki, zaki san dani kike!" Yana gama fa蓷ar haka ya juya ya fice daga 蓷akin kamar zai tashi sama, da idanu Mommy ta bishi sai kuma ta ta蓳e baki
"Allah na tuba matar da ba son ganina take ba me zan je yi mata?" Ta fa蓷a a fili tana danna wayarta.
***Kallonta Mamah tayi ganin yanda jikinta ke rawa ta ce"nutsu Imara, fa蓷amin me yake faruwa, me kika yi masa ya sake ki?" Batasan sanda ta fa蓷a jikin Mamah ta fashe da wani raunataccen kuka mai ta蓳a zuciya ba, kuka take irin mai fitowa tun daga 茩asan zuciya, kukane wanda ke nuna zallar damuwar da take ciki, kuka ne irin wannan ke nuna komai ya 茩are min a rayuwa, yanda take jan numfashinta yasa Mamah tayi saurin rungumeta tana shafa kanta
"Ma...Mamah...ya sakeni,. Maheer ya sakeni, baya sona, meyasa Mamah?, me nayi masa?, ya yimin laifi kala-kala amma na ha茩ura, meyasa shi ba zai iya ha茩ura ba idan nayi masa laifi?, ni kawai son sa nake Mamah, amma shi kuma ya fa蓷a min baya sona, meyasa!, meyasa Mamah!!, wlh bani na kashe Ameer ba!, ban kashe shi ba Mamah!, meyasa zan kashe Ameer bayan shine wanda ya 茩aunaceni a lokacin da kowa ya juyamin baya?, meyasa zan kashe mutumin da al'umma ke maraba da samunsa a cikinsu?, bazan iya kashe koda 茩waro ba ballantana mutum kamar Ameer, bani ba ce! Wlh ban aikata ba Mamah!, ban kashe Ameer ba!, nima inason Ameer!, IMARA nason Ameer, amma ya mutu, ya mutu ya barni a wannan duniyar me cike da ru蓷ani da tashin hankali, wlh bazan iya ba, so nake na mutu Mamah!, mutuwa nakeso, kowa ya mutu ya barni, na rasa Mama, na rasa granny, narasa Dodona, na rasa Maheer, na rasa Ameer, banida kowa! Banida kowa Mamah!..."
Wasu zafafan hawayene suka shiga sintiri kan fuskar Mamah, duk da batasan labarin Imara ba amma tayi matu茩ar tausaya mata, shekarunta sun yi ka蓷an wajen 蓷aukar wa蓷annan matsalolin, rayuwarta abar tausayawa ce, wa ta kashe?, wani irin tashin hankali ne ya saukarwa Mamah, ta 蓷ago fuskarta tana goge mata hawayen ta ce" tell the truth Imara, wace ke?, me ya sami rayuwarki?, bani labari!" Lumshe idanunta tayi wasu hawayen suka sakko mata 蓷an 茩aramin bakinta wanda ya yi jajur dashi duk ya ji茩e ta shiga bu蓷ewa cikin wani irin yanayi ta ce" zan baki labarina Mamah, zan sanar dake abin da ya sameni da kuma irin tawa 茩addarar".
# Bestnovel
# Heart touching 馃挃
# IMARA 馃拫
# Nanameera
# 2025.
***.