Free chapter · Read without an account

Chapter 4

by AMEENATOU MUHAMMAD ALHASSAN · YAR HANNU A LAGOS

tace To bata nan zaman me zamu yi?

promise tace tana cikin dakin hutawar ta fa,

kai ta jinjina kudi yayi a rayuwa ta raya a zuciyarta, ɗakin suka shiga tana kwance, tashi tayi ganinsu tace "aa my beautiful lady zo ki zauna....,

zama sukayi ta rungumota tare da shafa kanta tace "me ya saka har yanzu baku tafi ba....?,

haleemo tace baki bamu albashi ba, kuma yau ce ranar biya,

madam trisha tace da kinxo tun ɗazu kin karɓa ai, ta faɗa tana kallon nonuwanta

tace ai tun dazu muna jiranki, saboda munga kin yi baƙi shiyasa

hakane my beautiful lady ta kara shafa kanta, kuɗin ta ta kirga ta bata tasa aljihun skirt ɗin ta, taba promise nata itama

My beautiful baby ta faɗa tana sake kallon kirjinta, bata ankara ba taji hannun madam Trisha a cikin rigarta, da sauri ta riƙe hannunta sai dai madam trisha irin babbar macen nan ce, dan haka bata iya kwace mata, ɗaga mata riga sama tayi tuni taci karo da albarkatun kirjinta, tamkar za sufa sa kirjin'ta su fito saboda tsabar cikar su

Allah ne ya bata iko ta tureta, ta miƙe a guje ta fita jikin ta na rawa har ta isa gida, ko sallama batayi ba ta shiga dakin ummanta ta cire hijabin, umma cikin tashin hankali tace "yanzu nan nake shirin zuwa na nemoki, yau me kika tsaya yi har kika dade.....?,

rungume ta tayi ta rushe da kuka, kafin ta dena zuwa makaranta saboda rashin kudin makaranta har ƙoƙarin fyaɗe akai mata, yanzu kuma yan neman mata na bibiyarta, cikin kuka tace "umma madam yar iska ce, nan ta bata labarin abin da ya faru....,

gaban umma ne ya faɗi tace"innalillahi wa'innailaihir raji'un, ina nan zaune za'a lalatamin rayuwarki? shi yasaka naji hankalina ya kasa kwanciya....,

zama tayi a baƙin ƙaramin gadonsu tace "umma dan Allah mu koma garin mu....,

hawaye ne ya fara zuba a idon umma ta fara kuka har da shashshe, rarrafowa gurin ta haleemo tayi jikinta na rawa tace "dan Allah umma kiyi hakuri na dena tambayar ki....,

rungumeta tayi tace" wallahi ba tambayar da kika mun bace ta sani kuka ba, a'a tuno rayuwar da nayi a baya nayi......,

ba me rarrashin wani haka suka haɗu suna kuka har sukai me isar su, kwanciya umma tayi ta faɗa duniyar tunani....

Shekara goma sha takwas baya...............

Garin adamawa ƙauyen mayo belwa

HALEEMATOU YAR LAGOS

EPISODE 14-15

Shatu shatu

da sauri ta fito daga cikin bukkarsu ta ɗorƙusa tace "baffa gani...,

Shatu ga nonan nan maza ki ɗauka kafin innai ta dawo ta buge ki,

ɗurƙusawa tayi ta ɗauki kwaryar nononan da botikin, jamin kunne yayi yace "saura ki tsaya wasa, kuma karki sake ki dawo ba tare da kin siyar ba....,

kai ta gyada mai jikinta har rawa yake godun kar ya maka mata sanda, tafiya take hawaye na bin kuncinta, inda sabo ya kamata ta saba, bata tashi ta buɗe ido taga mahaifanta ba duk sun mutu, kawu da innai kawai ta sani sai ɗansu ɗaya Usman, sai adda Binta itama tayi aure tana kano, kullum cikin azabtar da ita suke,

shi kuwa dama ya Usman yana cikin garin Adamawa yana karatu, banda makarantar allo da take zuwa ba bokon da aka sata, share hawayenta tayi ganin ta fara shiga cikin mutane, bakin titi ta fita ta zauna a bakin wata bishiya, shatu! da sauri ta juyo tace faɗima kin taho kenan,

harararta yi tace "wallahi shatu baki da kirki, kika ki zuwa mu tafi tare...,

dafa ta tayi tace yi hakuri, wallahi bana so baffa ko innai su yi mun faɗa ne

Fadima tace Allah ya kyauta, in har zaki ci gaba da tsoran su to wallahi kina tare da wahala, mutane kin mai dasu tamkar wasu mala'iku Saboda tsoransu da kike,

ajiyar zuciya ta sauke jikinta yayi sanyi, amma ba yanda zatayi, fadima ta dan kara matsowa kusa da ita tace, ke ƙawata jiya naje cikin gari na haɗu da yayanki Usman

tace Dan Allah fa, a cikin makarantar su?

a'a a wani shago nakai nono, baki ga yadda ya koma ba dan birni dashi

tace Allah sarki, yayi miki magana?

fadima tace tab, Ni zai ma magana kamar baki san halin girman kansa ba? ko ke naga ba magana yake miki ba

Murmishi tayi tace hakane kuma wallahi, suna nan zaune shiru shiru ko wacce mota na wucewa ba wanda ya tsaya ya siya, sai wani daya siya na faɗima da yake nata me kyau ne, na shatu innai na hada shi da waken suya, kallon ta tayi tace "ko za mu tafi cikin gari ko Allah zai sa a siya...?,

fadima tace gaskiya bani da kuɗin mashin.

ƙasa shatu tayi da kai ta jawo dan yalolan mayafina tace "nima bani da shi gwara ke an siya ma....,

fatima tace to muje yar kasuwa mana,

batayi mata musu ba suka tafi, ga yunwa saboda tun safe ba abinda taci, kafin su isa yar kasuwa tuni na faɗima ya kusa karewa saura kaɗan, isa sukai ta zauna gabanta sai dukan uku yake, lah shatu ga yayanki shi da wasu, ɗago kai tayi karaf muka haɗa ido da shi...

Cikin dari dari ta buɗe baki zata mai magana taga ya haɗe rai, ai kuwa taja bakinta ta tsuke

ta mai da idanuwanta wani gurin daban, jin muryar wani tayi yace "sannu yan mata nawa ne nono ƙwarya ɗaya....?,

ɗagowa tayi ashe wanda suke tare da ya Usman ne tare, nace " dubu daya da dari biyar...,

buɗewa yayi ya duba sannan ya rufe, ya kalli faɗima yace "ke nawa ne naki....?,

Duk kuɗi ɗaya ne ta bashi amsa, ciro kudin yayi ya bata ta zuba mai a leda me zane zane, kallan Usman yayi yace "haidar zaka rakani na hau mota ko daga nan gida za ka tafi....?,

yace muje na raka ka sai na tafi nima

tashi faɗima tayi tace " shatu sai mun haɗu a dandali...,

Tace to sai anjima.

Ta tafi suma suka tafi aka barta nan sai raba idanu take, ganin sai zama take ko anzo an taya ba'a saye yasa taji kamar tasa kuka, duk wanda yasan nono me kyau to bai iya siyen nata, ga kuma rana tazo inda take, tashi tayi ta dauki kwaryar nonon da botikin ta koma inuwa ta zauna, tana zaune sai zabga hamma take ya Usman ya dawo, da sauri ta dauke kanta dan kadama su hada ido, har karfe shida tana nan zaune ba wanda ya siya.....

lokacin ta galaɓaita da yunwa sosai, wata mata ce tazo tace ta bata na dari bakwai, ta karbi kudin hannunta na rawa na bata ta tafi, kai har magariba tana kasuwar nan, ganin ana ƙoƙarin rufe kasuwar ne ta tashi, tafiya take tamkar zata faɗi, hanjin cikinta har curewa suke gu ɗaya saboda tsabar yunwa, dakyar ta ƙarasa gida ga ciyayi ga duhu, tayi sallama innai tayi banza da ita kuma ba wanda ya amsa, ashe adda Binta tazo ta ganta zaune da ɗanta, ta ajiye kwaryar nonon tace adda Binta dama zaki zo yau?

toshe hancinta tayi tace "da hallacan matsa sai warin rana kike....,

jikin shatu yayi sanyi ta miƙe, sai taji ance kee....

gabanta ne ya faɗi tace innai ga kudin,

amsar kuɗin tayi ta soma kirgawa, sannan ta buɗe kwaryar ta duba sai kuwa ta ɗauki sanda ta fara bugun shatu da ita, sosai take kuka tana neman dauki amma ko a jikin adda Binta, sai ma danna waya da take abunta ga danta gefe, ganin ba me cetonta yasa ta shige bukkar ya Usman da kullum sai ta gyara mishi, duk kuwa da baya nan, a gigice ta faɗawa kansa ashe yana nan, ya ja da baya cikin faɗa yace "ke wacce mara hankali ce zaki faɗo kai na...?,

tayi ƙasa da kanta tace kayi hakuri dan Allah hawaye nabin kuncinta......

YAR LAGOS

Episode 16-17

Yace Dalla Zo ki fita kin wani tsaya kin tsare mutane da ido, kuma fa ba kallonshi take ba,

hannuwanta ta haɗa waje daya tare da ɗurƙusawa tace "Dan Allah ka temake ni, wallahi ina fita dukana zata ci gaba da yi....,

be ce mata komai ba ya koma ya kwanta, adda Binta ce ta shigo hannunta riƙe da yaronta tace "dan uwarki zo ki fita, banda uban gantali ba abinda kika aje, gidan ubanwa kika tsaya har kikakai dare a waje? kin tsaya rabawa yan tasha gindi ko?...,

Jikinta na rawa ta tashi ta soma bin bango, a lokacin shekarunta 15 bata ma san me take nufi ba, bata da wayewar da zata fahimci ina zancen ta ya dosa, ganin ta kasa fita tace "Usman rikemun yaron nan yau sai naci uban yarinyar nan, sai ta jawo mana abin magana da alama...,

yayi tsaki ya amshe shi yana fadin shegiyar ba, ganin tayo kanta ta ɗurƙusa ai kuwa ta shiga dukanta ta ko ina har ta gaji, komawa tayi ta takure jikin bango ta kasa fita, ɗaukan yaronta adda Binta tayi ta fita ranta a ɓace, ganin ta fita ta koma gefe ta haɗa kai da gwuiwa tana kuka, batasan lokacin da bacci yayi awan gaba da ita ba.

azaɓa ce ta farkar da ita ya Usman ne taji yana daure mata hannuwa ta baya, sannan ya sa mata wani tsumma a baki ya toshe ta yanda kar aji ihunta, ya daga rigarta ya kurawa yan kananan nonuwanta ido, shafarsu ya fara yi gashi ko wani fitowar kirki basuyi ba, ba kunya ba tsoran Allah be dubi yarintar ta ba balle maraicinta ya fara tsotsarsu tamkar ba gobe, sai zogi suke mata shi kuma ba ruwanshi, bata ƙara shiga wani tashin hankalin ba sai da ya cire mata kayan jikinta, a karshe dai sai daya rabata da mutuncinta, tayi kuka sosai har hawayen sun bushe a fuskarta, yace "saura inji kin fadawa wani, wallahi saina ɓatar dake.....,

ta daga kai da kyar alamar bazata fada ba, domin ba ƙaramar a zaba nate ji ba ta ko ina, ya cire mata tsumman daya tusa mata a baki sannan ya kwanceta, ya wurgo mata kayanta ta sa da kyar, be mata Magana ba ya nuna mata hanyar fita ba shiri ta fita jikinta na rawa, bukkarta ta shiga ta kwanta akan tabarmar kaba, ta buɗe kafarta saboda data hade cinyoyinta azaba takeji, har asuba tayi tana cikin wannan hali, gari ya waye innai ce ta shiga kwaɗa mata kira, da kyar ta iya fitowa ta ɗurƙusa cikin dashashshiyar murya tace "gani....,

dan ubanki yau wani salon iskanci kika fito dashi...?, gari ya waye ba ruwan da za'a dora abin kari amma kin kwanta gaki yar hutu ko?

ƙasa tayi da kanta dake tsananin sara mata murya na rawa tace 'innai yau bani da lafiya...,

au ta haka kika biyo? to jeki, Usman Binta ku fito suka fito suna mamakin kiran innai, tace "ku zame min sheda tun da bata ɗebo ruwan da za'ayi amfani dashi a gida nan ba, to wallahi daga safiya har dare bazan bata abinci ba....,

okay kawai ya usaman yace ya koma, ta fita tayi kofar gida da kyar take tafiya, kallo adda Binta ta bita dashi ta ankara da jinin daya bushe a kafarta, ga kuma wani na gangarowa, dariya ta sheƙe da ita tace "innai yarinyar nan ta girma ba mashin shine...,?

kamar ta yanzu wasu ana shirin aurar dasu wasu kuma har da ya'ya

ita dai batace ƙala ba tacigaba da tafiya har ta isa bukkarta, ta kwanta jikinta na mata matsanancin ciwo musamman ma kirjinta da gabanta, a haka har baccin wahala ya ɗauke ta, jin maganar baffa suna hira dasu adda Binta tasan karfe uku tayi, dakyar ta tashi farin ciki ya kamata jin sallamar faɗima, baffa ya amsa tace "innai shatu na nan...,

Eh kawai tace mata, wucewa tayi ta shiga bukkarta da sauri taso tace "faɗima a galabaice

Cikin mamaki fadima take kallonta tace "shatu me ke damun ki? baki da lafiya ne? wannan jinin fa daya ɓata miki kaya da kafa...?,

da kyar ta tashi ta zauna tace eh wallahi bani da lafiya fadima, bakona ne yazo kuma ba ruwan da zan wanke jikina

cikin tausayawa tace "to Bara na ɗauki tulu na ɗebo miki ruwa...,

kamo hannunta tayi tace harda abinci fadima ina buƙata dan Allah, banci komai ba tun jiya

riƙe hannunta tayi gam tace" karki damu kawata, zan damo miki kindirmo amma bamu da siga,

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.