Free chapter · Read without an account
Four.
by Hijjart Abdoul · SAIFUDDEEN
*****Kwanciya kawai ya yi yana mai buɗe bedside drawern shi ya ciro hotunan ta album guda yana ta kalla yana murmushi yana shafawa a hankali. Duk wani memories na sanda aka yi hotan yana dawo masa sabo fil akan sa. Be taɓa manta koda hoto ɗaya ba. Har date da time yake sawa a jikin hoton. Musamman ya siya camera mai fito da hoto a take dan kawai saboda ita. Sanda cameran ya lalace ne kuma hotan na su ya tsagaita. Be taɓa tunani haka so yake da zafi ba, ga wani irin kasala da yake ji a cikin jikin sa..dukkan wani kuzari na sa ya tafi, yana nan a kwance yana cigaba da kallan hotunan ya ji wayar sa na ƙara a aljihunsa. Hannu yasa yana mai ɗaukowa ganin Mubeena ce yasa shi sakin murmushi kawai yana zubewa sunan da ya yi saving da ita ido. Ko da ya goge numbernta, numbern ta na zaune daram a cikin kan sa. Shin zai iya mantawa da numbern ta? Ko kuwa de?
A hankali ya sake sauke ajiyar zuciya yana mai ɗan tashi zaune ya jingina da jikin gadon yana cigaba da kallan kiran ta da yake ta shigowa, kafin ya ajje ta a gefe har kiran ya katse kafin ya kashe wayar tasa gaba ɗayan ta ma. Sai kuma ya rufe album ɗin ya na mai rufe idan sa ya yi lamo da shi a wuri ɗaya ya kulle idan sa, ya yi shiru kawai kamar wani mai bacci. Yana ji Abbi ya shigo ya duba shi ya fita haka yana jin zuwa Mommy ta yi masa addu'a ta fita haka ma Sufaina sai can ya ji shigowar wani ƙanin nasa Yayan Sufaina Safwan shima ya taɓa shi cike da kulawa kafin ya mayar masa da album ɗin sa cikin drawer ya fita.
A hankali ya sake bude idan sa yaga duhu alamar an kashe masa haske kenan, sai kuma ya sake ƙudundunewa a wurin ɗaya abin har abin tausayi ma. Ko baka san mutum dole ka ji wani iri, balle shi da suka haɗu shekara da shekara, be taɓa tunanin cire ta a ran sa ba, be kuma taɓa tunanin akwai ranar da zata zo ace Mubeena ta yi masa haka. Taya ma hakan zata kasance? Ba kuma da wani ba, a'a da wanin da zai ke ganin ta, idan be ganta yau ba, zai gan ta gobe, ko ace baya gidan dole watarana zai ganta. Amma shin laifin waye ne? Laifin Mubeenan ne ko kuwa laifin Sufyan ne? Waye ya fi laifi a tsakaninsu biyun duka? Bama aje ga Mubeena ba, iyayen Mubeenan fa?.
Yana kwance anan wurin wannan yana ta tunani, jin bacci zai ɗauke shi yasa shi tashi ya je ya yi alwala ya zo ya yi Isha'i sannan ya sake komawa ya kwanta bayan ya sha maganisa duk da be ci wani abinci ba amma haka ya sha maganin ya kwanta. Jikin jikin sa yake gaba ɗaya wani irin kamar ba shi ba. Kamar de an zare masa wani daga jikin sa, yana matuƙar jin something is missing. Ya rasa gane kan sa da abinda ke faruwa da shi....
*********Kowa na tsakar gidan a zaune banda Mubeena dake cikin ɗaki. Tana jiyo su, duka ɗakin guda uku ne a gidan, ga yara ƴan mata biyu har Hafsah ta uku, sai kuma ɗan samari da ba za su wuce biyu ba suna tsaye su kuma, Baban su a zaune haka ma Umman su. Hafsah ce da uniform tun jiya tana rusa kukan abinda aka yiwa Saif.
Baba yace, "Kin zo kin tasa ni a gaba kina min kuka, tun jiya kin ƙi ki ci komai kin ƙi sha komai, idan wani ciwo ya kamaki ke ki ka sani".
Daya yaron dake tsaye mai suna Jabir yace, "Yo Baba ba dole ta yi kuka ba, ai wallahi tallahi abinda ka yi mana Baba kawai de akwai Allah".
"Jabiruu? Jabiruu? Yanzu ni ka ke cewa akwai Allah?
Shima ɗayan mai suna Jafar yace, "Ai Baba gaskiya ce, yanzu gaba ɗaya a unguwar nan, kallan ƙaramin mutum ake yi maka, da mutuncin ka da kirkin ka, da kimar ka a wurin mutane, ai dole Baba a samu abin faɗa wallahi".
"Kuma dole ai ta yi kuka saboda ko gidan su Farooq...
Umman su tace, "Mahaifin na ku ku ke faɗawa wannan zancen?
Shiru suka yi suna haɗe fuskar su tamau irin na yara nan da sam basa ji amma kuma sun san abinda ya dace ai.
"Kawai ta ja mana abin faɗa da mutuncinmu, bawan Allahn nan yana yi mana hidima dai-dai gwargwado".
Jabir ya sake faɗa yana hura hanci.
"Ba za ka yi shirun ba kenan ko?
Shirun ya yi yana janyo hanky yana fatsewa abun sa.
Hafsah tace, "Dan Allah Baba a taimaka a bawa Ya Saif matar sa".
Umma tace, "Ki dena ɓata bakin ki, domin Baban ku ya yi nisan da ba zai taɓa ji ba. Be san da cewa kudi na wucin gadi ba ne ba. Amma mutumci da kima da kuma hakkin wani ya fi komai sawa mutum nadama a duniyar nan...
"Keeeee Samira, wallahi tallahi ki fita a idona. Gaba ɗaya kin sa yara sun renani sai abinda ki ka ce musu? To ita wannan na isa da ita ne shiyasa na yi abinda na yi ɗin".
Taɓe baki kawai ta yi tana janyo Hafsah. Mubeena ce ta fito, hannunta riƙe da bandir ɗin kuɗi ta ajjewa Baban gaida shi haka na Umman sai de bata amsa ba.
"Baba gashi, Umma na bawa bata karɓa ba".
"Tana maki baƙin ciki ta ina zata karɓa".
Murmushi ta yi tace, "Baƙin ciki? Ni nake yiwa Mubeena baƙin ciki? Wallahi ba de ni ba".
Ta faɗa tana ɗan murmusawan takaici.
Jabir yace, "Allah de ya isan Ya Saif wallahi".
Ya kuma fada yana haɗe fuskar sa tamau. Baban zai yi magana yayar su ta shigo da yaron ta a baya. Yaran ƴan mata suka je suka taro ta tana amsa yaron ta ƙara so ta gaida Baba sannan ta gaida Umma. Kafin ta ɗauka abincin Hafsah dake gaban ta wanda Umman ta yi mata tayi ta fara ci, tana kallan Mubeena.
"Menene ya faru?
Jabir yace, "Aww baki san abinda ya faru ba? To Mubeena ce zata auri Yayan Ya Saif. Kuma Baba ya ɗaure mata wurin zama, gashi nan za'a ɗaura auren. Tun yaushe ake wannan dabon, ƴan unguwa kowa ya sani, banda zagin mu ba abinda ake yi a gari".
"Labarib fa daman sai jiya ya bazu, daman haka zaki ji ana ɗan jita-jita. To jiya a ƙofar gidan nan, Mubeena ta same shi ta sanar da shi. Shine ya fita bakin titi mota ta bigeshi".
Cewar Jafar.
Tace, "Kawai jita-jita nake ji a unguwarmu. Har gidana aka zo min da labarin, kuma ƙanwata ake cewa wai".
Ta faɗa tana kallan Mubeeana. Mubeena tace, "Ba wai bane Anty haka nan gaskiyar zancen kenan".
Jabir ya kwashe tas labari ya sanar da ita game da cin amanar da suka yiwa Saif.
Mubeena tana zumɓura tace, "Ai gaskiya ce Anty, shikenan mu ƙare a wahala? Dube ki fa, kin fini kyau da komai. Amma kalle yarda ki ka koma. Abincinma sai da ki zo nan ki ka ci, gaskiya ba zan iya ba".
Ta faɗa tana turo ɗan kwali gaba irin na rashin mutuncin nan..
"Ko ba komai zan ke tunawa da ku, kuma ku ci arzƙi ai".
"A'a Mubeena ba zancen arziki ake maki ba. Zancene na mutunci ai".
"Baki san irin kirarin da ake yiwa mai kuɗi ba? Idan baki da labari to yanzu ki samu labari ki ji. Ba wani wanda zan yarda da shi kuma ni a yanzu".
Umman su tace, "Da ke da Baban ku, ku yi abinda ku ka ga ya fi maku, ba wani wanda zan sake cewa be kyauta ba, kowa ya yi nagari kan sa".
"Umma baƙin ciki kawai ki ke yi min".
Cewar Mubeena..
Baba yace, "Faɗi ki ƙara dan taga ba ita ta haife ki ba".
Hafsah tace, "Wacce irin magana ce wannan ɗin Yaya Mubeena?
Baba ya kusan bige mata magana ta yi saurin komawa jikin Umman na su.
"Idan ina magana kina yi sai na bige ki marar kunyar banza da wofi kawai. Saifun ubanki ne ko ƙanin uwarki ne?
Umma kawai girgiza kan ta ta yi tace, "Wallahi tallahi ba za'a ce ina yiwa Mubeena baƙin ciki ba kuwa".
Jabir yace, "To da riƙon da ki ka yi mata ko Babarmu bata yi mata ba. Balle ace kina baƙin ciki da ita. Da ace kina nuna banbanci ko baƙin ciki da ita da za'a kai wannan lokacin ne?
Baba tashi ya yi yana kallon Jabir..
Yace, "Ku kama hanya ku fice min daga gidana, kafin ran ku ya yi mummunan ɓaci".
Sum-sum suka fita suna buɗe ƙafa wai su baya su sun kai minzalin ƴan iska. Da kallo ya bi su kafin ya kalli yaran nasa mata ɗaya bayan ɗaya sannan ya yi ja musu kunne sosai. Shima ya fita batare da ya bi ta kan kuɗin da ta ajje masa domin yana da su da yawa a cikin ɗakin sa.
"Anty Bilki ga shi kya yi cefane".
Cewar Mubeena tana miƙa mata kuɗin. Sai ga Babar su Mubeenan ta shigo tana sallama. Ganin haka yasa Umman tashi tana cewa da Hafsah.
"Tashi ki cire kayan ki, ki yi wanka. Kar ki ce mun a'a kuma".
Ta faɗa mata babu alamar wasa. Hakan yasa ta tashi tana ɗan share hawayen ta da har yanzu be tsaya ba. Sosai abin ya soso mata rai . Bata sani ba ko dan yana matsayin abokin Farooq ne ta ji hakan ba. Yayin da Mubeenan ta tafi da gudu tana taryan Babar ta su.
"Baaba sannu da zuwa, zo ki zauna".
Ta faɗa mata tana kaita kan tarbar ta zaunar da ita, ganin haka yasa yaran ƴan mata tashi suka basu waje bayan sun gaida Baabar ta su.
"Ke faɗa min, abinda nake ji a gari wai shin gaske ne ?
Ɗan murmushi Mubeenan ta yi tace, "Haka ne Baaba wallahi".
Wata guda ta cancanɗa ta dire. Umman su tace.
"Ai abin rabo ne wai kuturu ya kama tarwaɗa".
Ta faɗa tana yin gaba da roba a hannunta alamar abu ta ɗauko zata wanke. Hararanta Baabar sun ta yi tace.
"Samira bansan me nake tsare maki ba, Wallahi tallahi duk ranar da na tashi dawowa cikin gidan nan, abin ba zai taɓa yi maki kyau ba".
Umma tace, "Aww haba? To Allah ya baki haƙuri, kin san nace abin faɗa na mai baki ne".
Hararan ta Baaban ta yi ta yi ƙwafa. Sannan ta kalli Mubeena.
Bilki tace, "Allah ya bada zaman lafiya, shine kawai abinda zance. Amma zancen kyautawa kam ba'a kyauta ba".
"Kar a kyauta ɗin, ai kuɗi su ake so. Da su ne ake hutawa a duniyar nan. Daman wannan Saifun ɗin na ki baya da komai sai ɗan kyau da yake da shi. Ince de zai kai ne saudiya ko?
"Baaaba, daga zaran mun yi aure fa zamu tafi honeymoon can 7 wonders of the earth mu je mu zaga duniya mu dawo".
"Ke ki ka san su ni ga inda nake kwadayin zuwa nan. Yanzu nake so a bani jari, a buɗe min shago. Na ji na kama ƙasa nima".
Mubeenan tace, "Kin san me Baaba? Kin fi ƙarfin nan gidan nan na ji kina cewa zaki dawo. Sawa zan yi mijina ya gina maki gida sabo daall wallahi sai de Baba ya biki amma ba de ke ki dawo wannan gidan ba".
"Allah ko?
Jinjina kai ta yi cike da tabbatarwa tace, "Allah kuwa Baaaba, ke ma Anty bilki zan sa a baki jari ki ke ɗan juyawa tunda ke mijin ki baya gari, baya nan baya nan, kullum yana hanyar zarya tsakanin Lagos da Kano porthcourt".
Shiru ita de ta yi bata ce komai ba. Dan har ga Allah idan zancene na kyautawa kam ba'a kyauta ba.
"Allah yasa haka shi ya fi Alkhairi".
Cewar Bilki.
"Haba Yaya Balki Alkhairi ne ma ai".
Hafsah da ta fito daga ɗaki daga ita sai daurin ƙirji idan nan ya yi luhu luhu.
Tace, "Yaya Mubeena, ba wanda ya san gobe sai Allah, kin yaudare bawan Allah kawai, duk san da yake maki...
"Zan zo nan wurin na zane ki Hafsah, har yaushe ne reni ya fara shiga tsakanina da ke?
Haɗiye ruwan hawaye ta ta yi kawai tana ɗaukan bucket ta zuba ruwa tana jin su suna zaginta ta, daga ita har Saif ɗin sa Farooq. Yayin da Baaba ta ringa zuga Mubeena akan cewar ta yi dai-dai. Gwara su ɗanɗana cin jar miya. Har azahar suna fama kafin sauran yayun na ta su zo suma, wasu sun ce bata kyauta ba, inda wasu suka ce ta kyauta sabga ce ta kudi da jin daɗi gwara ta ji daɗi kafin ta mutu. Haka ta bi su ta raba musu kuɗi wai su yi hidimar biki da shi. Dake sam bata da rowa sam bata ji ƙyashin basu ba da ta yi....
**********Saif har yanzu ya kasa yadda sa cewar wai Mubeena ce ta yi masa haka. Bata tunanin ko jin cewar an taɓa yaudara mafi muni da zafi kamar yadda aka yi masa. Anya zai cigaba da zama a cikin inuwa ɗaya da Mubeena kuwa? Duk idan ya yi juyi ita yake gani, daƙyar ya samu ya yi bacci a daren jiya har wayewar asuba, ƙarfafa zuciyarsa kawai ya yi ya je ya yi sallahr asuba domin be san abinda Abbunsa zai ji babu daɗi.
A hankali ya tashi zaune daga kan gadon da yake yana fama tunanin jin buga ƙofar da ake yi masa. Wanda yake da tabbacin Sufaina ce dan bata shigo masa ɗaki kai tsaye jiyan ma dan tasan baya da lafiya ne yasa ta shigowa. Rigarsa ya zura yana bata izinin shigowa. Fuskar sa ƙawace da kyakkyawan murmushi.
"Ya Saif ina kwana".
Wani murmushi ya sake mata yana amsawa.
"Ya jikin naka? Da sauƙi?
Ta faɗa tana zama kusa da shi tare da taba jikin sa.
"To waye yace maki banda lafiya wai?
"Jiya mana aka kai ka asibiti harda su ƙarin ruwa".
"Kawai suma na yi, shine waccen bagidajiyar likitar dalibar ta sa min ruwa ta haɗa magani, tsabar ta rena min hankali. Daga suma kawai shegiya mai kan kwakwa".
Yarda ya yi ɗin dole ya baka dariya. Hakan yasa Sufaina dariya sosai tace.
"Saboda ka ji ƙarfin jikin ka mana, idan mutum ya suma yana rasa ƙarfin sa, balle kai kuma da tsantsan anxiety ne ya sa ka suman ba komai ba".
Ɗan murmushi ya yi yana kallanta, ta riƙe hannunsa cike da kulawa tace.
"Ka dena damuwa, kana samu a cikin damuwa. You know kai ne best happiness ɗin mu a cikin gidan nan".
Sosai best happiness ɗin da tace yasa shi sake sakin wata dariyar.
Tace, "Ehh man, baka barin mu mu shiga wani hali, akan me mu zamu bari ka shiga wani hali saboda wata can mace? Duk san da nake mata sai na ji I hate her more then Ya Sufi, dan idan yana da laifi to nata ya fi yawa ita da ta yarda ɗin".
Riƙe hannunta ya yi dake cikin nasa yana kallonta yace, "Kar ki kuskura ki sake furta You hate them. Yayar ki zata zama soon, idan baki so ta ba, be kamata ki tsane ta ba".
Ya faɗa mata a hankali. Jinjina masa kai ta yi tace.
"Am sorry ban sake faɗa".
"Thank you lollipo".
Murmushi ta sakar masa tana cewa.
"Bari na je na yi wanka".
Jinjina mata kai ya yi alamar toh. Kafin a hankali ya zame ya kwanta. Safwan ya shigo duba shi.
"Lili".
Ya faɗa masa a hankali yana zama a kusa da shi.
"Ya jikin?
"Alhamdulillah".
"Be wuce ka yi haƙuri ba, shine kawai abinda zan ce da kai. Dan Allah".
Safwan ya faɗa masa a hankali cikin Muryar lallashi sosai. Jinjina masa kai kawai ya yi yana cigaba da sakin kyakkyawan murmushin sa, kawai Safwan ya sa shi a gaba yana ta kallan sa batare da yace komai ba. Shi kan sa a wannan lokacin ba zai iya cewa ga abinda yake tunani ba. Amma kam tunanine yake yi wanda ya yi zurfi a cikin sa. Sai da Saif ya taɓa shi kafin ya saki ajiyar zuciya.
"Kawai na tunani a gaba kana kallo, kama na sauya ne?
Murmushi ya yi yana girgiza masa kai, kafin ya tashi ya fita. Kawai murmushi Saif ya saki yana saukowa daga kan gadon, ya kalli maganin sa.
"Wannan yarinyar banzar likita ce, kawai ni ba zazzaɓi ba a haɗani da magani, irin su ne masu kashe mutane".
Ya faɗa yana fara cire kayan sa ya shiga wanka . Yana shiga Abbi na zuwa duba shi ganin yana wanka yasa shi fita daga waje. Haka ma Mommy itama ta shigo taga be fito ba. Sai da ya shirya tsaf abinsa cikin ƙananan kayan da sam ba su da wata tsada dan a gwanjo ya nemi abinsa. Amma sun yi masa kyau sosai. Dukan su suna kan dining suna cin abinci gently ya je ya gaida su yana kallan Farooq dake zaune a cikin su yana cin abinci da'alama zuwa ya yi, Abbi kuma ya ce yana wanka ya kuma matsa masa da ya zauna su ci abincin.
Gaba ɗayan su ya haɗa ya gaida su har Sufyan. Sosai kowa ke sake yi masa ya jiki. A ran sa kuwa cewa yake kamar wani wanda ya kwanta ciwo.
Sufyan yace, "Ya jikin na ka?
Wani murmushi ya yi mai kama da harda kai a masu tambaya na? Kafin ya amsa masa kawai yana girgiza kan sa. Zai wuce.
Abbi yace, "Ga Kosan ka Farooq ya kawo maka, ka zauna ka ci a cikin mu mana".
Ya faɗa masa cike da kulawa.
Sufaina tace, "Please Ya Saif".
Safwan yace, "when last ka ci a cikin mu?
Mommy da kan ta ta tashi ta janyo masa kujera tana zaunar da shi. Tare da ta haɗa masa tea wanda take da tabbacin ba zai sha ba. Aikuwa be sha ba ɗin kawai ƙosan na sa ya ci. Haka suka cigaba da ci batare da kowannen su ya yi magana ba har suka gama. Kafin Saif ya ce wa da Farooq ya tashi su tafi, yayin da Abbi ya bishi da kallo kawai yana jin wani abu mai girma na ta so masa game da ɗan na sa. Sai kuma ya dawo da kallansa wurin Sufyan kafin ya kalli Safwan da Sufaina, kawai ya tashi shima yana mai goge bakin sa. Kamar jira Safwan yake ya fita ya kalli Sufyan yace.
"Dole ne ace abinda ka yi baka kyauta ba. Bar ganin kana sama da mu, dole mu yi maka magana....
Ya faɗa cike da rashin kunya. Yayin da Mommy ta tare shi da cewa.
"Yayan naka ka ke faɗawa wannan maganar?
Sufyan yace, "Mom ai daman ke ce ki ke rabuwa da shi yana yin abinda yake so a cikin gidan nan. Gashi nan yaro ƙarami yana kallar tsabar ido na ya na faɗa min magana".
Tashi ya yi tsaye cike da hargowa har yana ture plate ɗin dake wurin Sufyan ɗin yace.
"An faɗa maka ɗin, ka yi abinda zaka yi sai me?
Tashi ya yi ya wanka masa mari, yana ɗagowa shima Safwan ɗin ya wanke shi da mari, ya ƙara da cewa.
"Bana ganin girma da mutuncin mutumin da ya ci amana. Ya kuma yi yaudara. Cin amana mafi muni da ƙasƙanci. Ƙanin ka fa? Ƙanin ka ne fa, for God sake". Me ya tare maka a rayuwa? Ko kunyar kan ka baka ji ba?
Abinda baka taɓa tsammata ba idan ya faru, dole ne ya baka mamaki da al'ajabi, ko da ace Saif ne idan ya mare shi baya jin zai iya ɗaga hannu ya rama balle kuma Safwan ɗin da yake ƙani da Saif wanda daga shi har Saif ɗin sune ƙasa da shi shine yau ya ɗaga hannu ya mare shi?
"Safwaaan?
Mommy ta faɗa cike da tsantsan mamaki tana kallansa. Hararan Sufyan yake kawai yana huci. Sufyan kuwa mamakin da yake ciki ya kasa barin kwanyarsa da ƙwaƙwalwar sa.....