Free chapter · Read without an account

13

by Asmy b Aliyu · Dangin juna

DANGIN JUNA

Asmy b Aliyu

13

Y'an taron biki duk sun watse sai masu gida ,hajja itama takoma gidanta  dake acikin zoo road. Wanda take xaune itada ya'r kaninta mabarooka ,wacce  itama mijinta ya dde da rasuwa haka Allah bai bata haihuwa ba.

komai na more rayuwa akwai shi gidan hajja bbu abunda ba'a wadatata   dashi ba na xamani.

  

*

Amman  dai kinsan cewa baxai yuyu nakoma gobe ba."

Meyasa baki bi su mami kuka koma tare ba?"..

Shikenan naji tunda kayi aure wulakanci kala-kala nake gani a gurinka anya buddy akwae sauran sona a xuciyarka?"

Tayi masa tambayar ne gamida kafesa da idanunta.

    Shima kallonta yakeyi ,,inhar yace bayason raudha har yanxu to yyi karya "yana mata haka badan baya sonta bane ko ɗaya."

Yana mata hakane a matsayin daukar fansa "ko yanxu da xa'a amince masa akan ya aureta a guje xai bukata .

   dan yana cikin bukatar macce a wannan lokacin Dan shi namiji ne mai yawan bukata ,ko yanxu Allah kaɗai yasan irin dauriyar da yakeyi.

  idan watarana abun yafi karfinsa sai dai ya kora beer  gaya dai ammasa aure amma shi A Tunaninsa

Rufy baxata iya dauke bukatunsa ba. tayi kankanta da yawa dayawa haka ake daukar abun a kullum.

Clapping din hnnunta tayi duka biyu a gaf ,da fuskarsa.mekuma kake tunani ne?"

Am sorry bbu komai kawae inason nayi tunanin yadda xan bullowa Abba ne,da kuma ammah."

"Bana son tafiata da wannan yarinyar,nafison ta xauna a kano nasamar mata makaranta anan" sabida xamana da ita hadarine raudha "komai xai iya faruwa " kinfi kowa sanin wanene ni!

   ~~~~~~bana son kuma haka ya faru Dan raini xai iya Shiga a tsakanin mu" yatsunta  ta axa akan chest nasa  tana xagayesu a hankali murmushi dauke a fuskarta,kallonta kurum yakeyi.

   Baisan meyasa ba sai yafara jin ddin abunda take masa hka kuma yakasa hanata.

Jin yyi hankalinsa ya fara tashi jawota yyi sosai ajikinsa yana kallon cikin idanunta itama din kallonsa takeyi nan take taga idonsa sun kada xuwa kalar ja.

Dingil tayi duk da tana da tsawo amma Ab. Ya kereta sosae a tsawo xagaye kugunta yyi da hannayensa.

Lokaci ɗaya ta hade fuskarsu gamida fiddo harshenta tana wasa dashi akan face dinsa nan take ya rude saurin kama harshen yyi yana yimata wani irin kisses tareda shafa kowace gaba ta jikinta gamida sauke wani irin numfashi.

Tsayuwar ta gagara suka xube akan coach dukansu sun fara fita a hayacinsu.

#

Auhh lunch dinma tsoron kaimasa kikeyi?"amma fa kinsan bana da lfia assha?"

Tom.naji ai sai kixauna naga cingam dinsa ta tafi part dinsa kingama tsinanun kayan dake ajikinta?"

  "Bani lunch din nasa xan kaimasa  murmushi assha tayi yawwa my special sister ko kefa idan taganki ai dole tabaku wuri

keda turakar mijinki.

   Rufaidah bata maji mai assha ke fadaba tayi nisa cikin tunaninta taya xata raba Buddy da raudha take tunani..

Anan ashha ta fito dauke da karamin tray dauke da kulan abinci da kuma sauran kayan xuba abinci

muje na taka maki bakin part dinsa  tunda baki da lfia " Assha na gaba tana bayanta...

  ###

Suna shiga corridor da xai sada su da side dinsa Assha taja ta tsaya ta juyo tana kallon rufaida dauke da murmushi a fuskarta.

" yawwa my rufaidah karbi idan xaki shiga ki shiga da sallama first " abunda xaki fara yi kenan kinsan buddy bayaso a fada koina ne bbu sallama.

qarba kurum tayi ta juya ta shiga part din nasa, haka xuciyarta na wani irin bugawa wanda ta rasa dalilin haka.

 Falon farko tayi sallama

Wanda tayi mugun gani raudha na xaune a kafafun ab. Sai shagawaba take xubawa abunta.

   Ido hudu sukayi dashi baisan lokacin da ya tura raudha agefe ba.

Haka yyi saurin mikewa a tsorace da yake namijin dunia ne sai ya bata rai yana jefarta da mugun kallo saurin dauke kanta tayi kai tsaye Dinning area ta nufa ta aje tray din.

ganin xata juya abunta a fusace ya nupi gurinta ya fisgo hnnunta xuwa master bedroom dinsa.

  Ganin haka raudha tamike tana gyara rigar jikinta.

Kan gado ya wurgata yana binta da wani irin matsiyacin kallo a tsorace ta mike tsaye jikinta na kyarma.

 Wata uwar uban tsawa yyi mata nan take ta gigice tafita hayacinta

uban me ya kawo ki part dina

Na nemeki ne?"

Ko cemaki akayi ina bukatar ganin kine? "

Ya fada cike da zafin xuciya "why did yhu do dis to me ? Why?"

Plzzzzz tell me?

"Ya fada gamida rike right hand nata koshi mugun riko yyi masa, jin take kamar hannunta xai cire.

" mekike nema ne acikin rayuwata?"

Kin fara wuce iyakarki !" Idan kika kara shigowa part din nan xanyi mugun saba maki!"

"I don't need yhu in my life any more!!

Bcoz I don't like yhu!

Ya sakar mata hannun gamida turata gefe hawaye taji suna ambaliya a fuskarta ...da gudu ta fita.

A kofar fita part  dinsa taga raudha  tasha gabanta ,,baka ramin ddi raudha taji ba ganin hawaye a idonta.

  To masu miji ya akayi kuma naganki da hawaye?"

Ikon Allah!

"Ai wlhi tallahi kaɗan kika gani sai kinyi da na sanin auren Ahmad da kikayi acikin rayuwar ki a hakan ma ba'ayi komai ba somin tabi ne."

"Ki dubeki ke kanki kinsan ba kalan matan da ahamd basheer (Ab)" ke kulawa bane ,,Dan dai bayarda ya iyane."

Muje xuwa ta kashe mata ido daya.

Anan tabarta tafiya take batasan inda take taka kafafunta ba.

Cikin ikon Allah sai gata a part dinsu,

Assha taci karo daita ganinta haka yasa tasha jinin jikinta gefe tajata suka xauna.

"Rufaidah mekuma ya faru?"

Saurin guntun hawayenta ta goge shiru tayi bbu amsa karshema da ta dameta barmata falon tayi .

Zuwa bedroom din Ammah

kusan 4;30pm..ya'n komawa school sun gama shiri . driver ne xai maidasu Kaduna.

lokacin rufaidah jitake kamar tabisu tareda ita akayi masu rakkiya har xuwa bakin mota 'batama ga tafiyarsu ba ta koma cikin gida.

anan kan gadon ammah ta zube  tabuda babin sabon kuka...

Wandda ya jaza mata matsanacin ciwon kai yanxu shikenan itada queen amina!

  A haka ammah tasameta rarrashi ta hauyi da banbaki 'jikinta sosae ya dau zafi haka lokaci daya zazzabi mai xafin gaske ya rufeta ....

Ammah tayiwa moha wya akan yaxo ya dubata.

*

Kaida kawo ya shigayi taya xai fara tunkarar Abba nacewar a gobe xai koma Kaduna.

Kuma shi ɗaya batareda rufy ba."

Bayan sallar isha,,ya nupi part  din Abba xuciyarsa na harbawa...

Abba basheer tunda yaga Ab.yaxo a wannan lokacin yasan akwae mgana  sannu da hutawa Abba!! Yawwa Ahmad ya yau?

Alhmdullahi Abba."

"Masha allahu

shiru ab. Yyi haka xuciyar sa tacigaba da bugawa

dam     da-dama Abba gobe nakeso nakoma Kaduna" yyi maganar a tsorace kansa kuma a kasa.

Gyaran murya abba yyi bangane mekake nufiba?"

Ina nufin Abba gobe xan

Koma Kaduna ,,sabida company suna min Neman gaggawa akan wata kwangila daxamu samu."

Ohhh yanxu na fahimta

Sukuma kamfanin naka sabida basa da tunani basu San sabon aure ne akanka ba halaama?"

   "Ba haka bane Abba ,gobe xamuyi meeting akan kwangilar ,shikansa yana mmkin karyar da ya shiryawa abban nasa. Wanda tun tasowar sa baitaba yiwa iyayen nasa karyaba.

" naji amma kasan da xancen kafarka kafar matarka!

dan nasan baka da matsalar gida acan haka komai akwai cikin ido Ab. Kekallon abban nasa

Sai yaji baxai iya cigaba da kallonsa ba.

Dan wani kwarjini yyi masa.

Abba mexai hana ta zauna anan sai, a samar mata wata makarantar.

"Kaniyarka !kaniyarka nace Abba yashiga watsa masa dakkuwa a hasale ,,dan uwarka ban yardaba!

Kafarka kafar rufaidah " kaji na faɗa maka kuma nan da sati daya xaka Samar mata makaranta acan..dan banaso karatunta ya samu tangarda.

  Ab. Jin yake kamar ya fasa ihu da wannan faɗan na Abba kara ya rufesa da duka..

Afusace yabar part din Abba  a bakin kofa suka cikaro da aunty Wacce  tayi saurin matsa masa.

Ganin yadda Ab. Ya fito Dan itakan duk cikin ya'yan Abba tafi shakkarsa dan baya daga mata kafa ko kaɗan.

Kai tsaye part din Ammah ya nufa.kallo ya samu sunayi itada rufy a tashar zee world ,,sakin fuska yyi sosae gamida shigowa da sallama.

Gefen rufaidah ya zauna plate ne a hnnunta yana lekawa yaga hadaddiyar jelop din macroni.

     Kwace plate din yyi rufy bbu tayine?"

Ya faɗa murmushi dauke a fuskarsa,saurin dauke kanta tayi ..

Karbi abunki karki samin kuka ,takarbe abunta spoon tasaka ta debo macroni da nufin takai bakinta .

Caraf! Ya rike hannun ya saitosa xuwa bakinsa.lumshe idonsa yyi da alamr yaji ddin macronin ,sannan ya budesu akanta kallonsa kurum takeyi.

shagwabe fuska yyi plzzzz muci tare yyimin ddi .samomin wani spoon a kitchen nayi joining naki.

Ammah kallonsau kurum take ,cike da farin ciki akan ahmad yafara sakewa da rufaida.

Wani bangare tana mmkin rashin kunya irin nsa.

   Karbar spoon din hannunta yayi  anan ya shiga feeding dinta.

   Juyawar da tayi

taga wayam  bbu Ammah plate din ya axa mata kan cinyarta batareda yace komaiba.

Ya juya yabi bayan ammah.

*

Washe gari da ya dawo masallaci kai tsaye part din ammah ya nufa ,,kan sallaya yasameta tana azkar "yayinda gimbiyar tasa ,tana can mike a gado ta tattake cikin duvet.

Kai tsaye gurinta ya xauna gefen gado hannunsa yasa yaye duvet din ,fiddo manyan idonsa,yyi ganin rigar barcin dake ajikinta

saurin mayarwa yyi yana karema innocent face nata kallo.

  Anan yashiga tashinta Rufy ! Rufy!

Ya tsine fuska tayi idonta a rufe meya faru buddy?"

Plzzzz le't me sleep kara Jan duvet tayi ya fisgesa a Dan fusace malama ki tashi haka da wuri xamu kama hanya."

Bude idonta tayi akansa yana cikin bakar jallabiya sai taga yyi mata kyau batasan lokacin da ta sakar masa murmushi ba.

Bata rai yyi lfia kike kallona ?"..

Kaxo ka takurata ba dole ta tsareka da idoba."

Cewar ammah dake a tsaye tana linke sallaya.

Ina kwana ammah!

Lpia qlau ."

Tafiar safe zamuyi ne ammah shiyasa juyawar da xaiyi akan rufaidah wayam har tashige toilet.

Ammah tashiga kitchen da kanta ta hada masu hadadden break fast....

qarfe 9 sun gama shiryawa lokaci daya jikin rufaidah yyi sanyi ganin harda raudha xa'a tafi sai wani rawar kai takeyi ..sukuma iyayyen nasu basu kawo komai aransu ba.

"shima moha da safe yaxo sukayi sallama da Dan uwan nasa, da kuma rufaidah ,,sai kara tuna masa yake akan ya kula da rufaidah,hakama Amma,Abba.

Daga gefe Taga su hanan sun kebe suna tattaunawa itada raudha sai kyalkyalar daria suke abinsu.

   Yah moha ne ya budewa rufaidah gaban motar sai da tashiga ya rufe a fusace raudha ta bude back seat   ta shiga , Kowa yana daga masu hannu har suka fita daga get din gidan.

   Ab. Yana lura tunda suka fito yaga raudha ta hade rai

parking yyi gefen titi. Ya kalli rufaidah fuska a tamke

ke!

Koma baya

ke kuma raudha dawo gaba."

Raudha tayi saurin fitowa wacce dama kamar jira take

A sanyaye rufaidah ta koma baya.

Kai tsaye tashar mota suka nufa

Buddy mexa muyi a kuma tashar mato.

Wannan yarinyar xan samarwa mota yana gama fadar haka yyi parking ya fito motar kai tsaye gurin driver's ya nufa.

Cikin minti

biyar yagama mata komai  hnnunsa yasa

ya buɗe mata motar jiki sanyaye ta fito tana kallonsa.

"Jeki kishiga mota

Wace motar dai kake nufi?"

Bana son iskanci wacce mota kika San ana shiga anan?"

Folding din hnnunta tayi akan qirjinta ta turo masa bakinta. ni gaskiyya baxan shiga waccan motar ba."

Sai dai na koma gida!

Yarda tayi maganar tabasa daria  dama yarinyar nan na magana.

    "Rufy banason rashin hnkali kina bata min lokaci kije kishiga mota kafin na sassaba maki."

Yyi mganar cikin fushi.

   Juyawa tayi tafara tafia maimakon yaga ta nufi gurin motar sai yaga ta nufi hanyar fita ,,cikin tashar .

A hanxarce ya sha gabanta!

Ina wasa dake ne?"

Nifa Allah buddy baxan shiga waccan motar ba."

"Plzzzz Buddy kabarta kar tashiga motar mana." Kaxo mutafi.

  Lokaci daya rufaidha ta galla mata harara,aikece ya kamata kishiga motar haya."

Bani ba dake da miji a hnnu.

In har kuka matsamin na shiga motar haya,xan koma gida na fadawa Abba!

Nan ta juya takoma motar Ab. Tashiga gaban motar baki wangalau Ab.ya saki yana kallonta  dama hka yarinyar nan take?"

Ba kaji mai take faɗaba,ka saki baki kana kallonta" da nice nayi maka hka da yanxu ka rufeni da masifa''

Jiyarda karamar yarinya ke gasa maka mgana".

Enough!!

"Raudha shin baki majin mai take fadaba  xataje fa ta fadawa Abba,

Duk baraxa nace bbu abunda xata iya!!

  " Aimun saba ganin haka to ni kuma wlhi da nashiga mota ɗaya, daita har xuwa Kaduna gara kabarni kawae kuyi tafian Ku kawae.

"Rike kansa yyi  da hannayensa duka biyu afusace ya nufi motar ya fisgota daga cikin motar haka ya bude mata manyan idanunsa ,,yana nunata da yatsa.barikiji na faɗamaki dole ki shiga motar haya,saboda raudha tace baxata shiga mota ɗaya da keba."

"Wuce mutafi hka yaja hnnunta xuwa cikin motar dama ita kawae ake jira hawaye taji sun ciko idonta.shiga motar tayi ganin idon mutane na akansu.

Raudha na gefe tana murmushin mugunta.

saida yaga tashinsu ya dawo mota.

"Buddy sauri fa xakayi

jirgin 12:*** xuwa Ghana " mugun kallo ya juya yana mata.

  Yah haɗe rai sosae na fadamaki kidaina bani umurni ko yanxu bakiyi lattiba.

Xaki iya canja moto ,,yyi maganar a fusace,Ya tsani yadda Raudha ke basa umurni kamar wata uwarsa...

Idan anjini shiru ina wani uzurin dan Allah.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol