Free chapter · Read without an account

35

by Kansa'u Bello · AMATURRAHAMAN

💞💞💞💞💞💞💞💞

AMATURRAHAMAN

*By*

OUM FATIMA

*(Hakimar D. A. W. A)*

💞💞💞💞💞💞💞💞

*DASHEN🌲ALLAH*

*WRITER'S📚ASSOCIATION*

*TEAM*

*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*

BOOK 1

PAGE 35

*بسم الله الر حمن الر حيم*

Lokacin da da su Muzaffar suka isa sosai jikin Baba Alhajin yayi tsanani saboda ana ma ƙoƙarin fitar dashi India domin ganin likitan daya saba duba shi, kai tsaye asibitin suka isa suka duba shi kafin su koma gida. Wannan rashin lafiyar ta Baba Alhaji ita ta ɗauke hankalin su Ammah daga kan Amaturrahaman gaba ɗaya, duk da cewar sai da Muzaffar ya gama abinda ya dace a can ɗin na kulawa da ita kafin ya wuce.

Abinka da manya masu ƙumbar susa cikin ƙanƙanin lokaci aka gama duk wani shirin daya dace aka wuce dashi ƙasar India, a can Zayyad ya same su domin ganin jikin nasa. Don da farko gidan zai dawo sai Abba ya sanar dashi cewa za'a fita da shi ne, shi yasa ya fasa ya taresu a can.

Alhamdulillah an bashi duk kulawar data dace kuma ana ganin ci gaba sosai don haka suka fara samun nutsuwa, ciwon suga (diabetes) yake damunsa sai kuma ciwon ƙafafu da yake fama wanda girma ke haifar wa. Duk sanda jikin nasa ya tashi kuwa ba ƙaramar wahala yake sha ba don ma yana samun kulawa sosai sannan ana kiyaye wa sosai akan abincinsa.

Rashin lafiyar Baba Alhaji ta yiwa Hajiya Sha'awanatu rana sosai domin kuwa ta dakatar da maganar auren Anisa da Abdulmajid wanda bai fi sati biyu ya rage ba, da wannan damar tayi amfani ta saka Anisa take yiwa Abdul ɗin rashin mutunci wanda kare ma ba zai cisa ba, wai duk don yayi zuciya ya janye maganar auren amma sai ya nuna musu cewar ya fisu rashin mutunci domin kuwa yaƙi janyewar kuma cikin ruwan sanyi yake gasa mata baƙaƙen magan-ganun da suke sakata kwana tana kuka.

Gaba ɗaya Anisa ta fita hayyacinta ta rasa mafita ta kuma yi nadamar hakan da tayi wanda ya janyo Dady zai aurar da ita ga wan can mara mutuncin da bata taɓa sanin haka halinsa yake ba. Lokacin da Baba Alhaji ya kwanta jinya hankalin kowa ya koma kansa aka manta da zancen auren ba ƙaramin daɗi suka jiba, don haka ta dage don ganin ta rusa alaƙar dake tsakaninta da Abdulmajid ɗin amma da yake maye ne ko gezau bai yi ba akan maganar sai ma sabon salon rashin mutunci da yake fito mata dasu.

A ɓangaren Zaheera kuwa sosai take farin ciki da hakan take kuma ganin cewar dama ce ta samu don haka ta dage da nacin kiran Zayyad ɗin kullum da tura masa text message da sunan kulawar ƴanuwantaka, bai taɓa mata reply ba haka baya ɗaukar kiran sai sanda yaga dama shima suna gaisawa zai tambayeta dalilin kiran sai ta fara kame-kame shi kuma ya kashe wayar sa saboda bashi da lokacin shiririta.

Matazu.......

Allah Sarki Amaturrahaman baiwar Allah, tunda su Kawu Isa suka tabbatar da cewa su Muzaffar sun bar garin Matazu suma sukayi tafiyarsu suka kama sha'anin gabansu suka manta da wata halitta a asibiti wanda su da kansu suka hana mutanen kirki tafiya da ita domin su bata kulawar da suka san cewa ba zasu bata ba.

Nurse Zuwaira itace taci gaba da kula da ita da yi mata duk abinda ya dace har ta fara dawowa hayyacinta, kasancewar manyan kuɗaɗen da Muzaffar ya bayar domin kula da ita ya kuma shaida musu cewa zai dawo yasa ake bata dukkanin kulawa tun daga kan doctor ɗin daya bawa amanar kulawa da ita zuwa Nurse Zuwaira mai yi mata dukkan hidimar data dace a yiwa mara lafiya. Tuni ta sauke girman kai take ririta Amaturrahaman ɗin saboda ba ƙaramin alkairi ta samu ba itama.

Lokacin da ta dawo hayyacinta ta tabbatar cewa ta rasa Ya Nafi itama domin an tabbatar mata da anyi mata sutura an kaita gidanta na gaskiya. Tun daga wannan lokacin babu wanda ya ƙara jin muryarta a asibitin ta zama tamkar kurma bata da aiki sai bin mutane da ido. Duk yanda aka so tayi magana ta ƙiya har abin ya fara bawa Nurse Zuwaira tsoro taje ta sanarwa da Doctor Zubairu aka yi mata wasu gwaje-gwaje don tabbatar da cewa ba abinda ya sameta wanda ya hanata yin maganar.

Sai da result ya fito sannan hankalinsu ya kwanta saboda ba abinda ya sameta mai alaƙa da hakan, kawai dai bata buƙatar yin maganar ne, duk da cewar dama can ɗabiarta ce amma yanzu abin ya lullunka na baya.

A binciken da aka yi mata an tabbatar da cewa zuciyarta na fuskantar barazana ta kamuwa da ciwo domin kuwa nauyin damuwowin dake damunta da yawan tunani da kuka da kuma rashin samun sauƙin zuciyar yasa kwata-kwata bata samun hutun da ake so ta samu, tana bugawa ne fiye da adadin da ake buƙata don haka dole ake sakata bacci sosai domin a samu ta huta.

A haka tayi sati biyu a asibitin a ƙarƙashin kulawar Doctor Zubairu da Nurse Zuwaira, ganin shiru Muzaffar bai dawo ba kuma ta fara samun sauƙi yasa aka bata sallama saboda takurawar da tayi akan a sallametan don sai a lokacin ne ta buɗe baki tayi magana tace gida zataje ta miƙe ta nufi ƙofa tun kafin a bata takardar sallamar, sai da Nurse Zuwaira ta dakatar da ita taje ta amso mata takardar sallamar wurin doctor ta bata ta kuma yi mata rakiya har bakin gate tana jin kewar yarinyar na kamata.

Ita kaɗanta kamar yanda ta gama tabbatarwa kanta cewa bata da sauran galihu bata da wani sauran gata a duniya daya rage mata tunda ta rasa Ya Nafinta, dole itace zata tashi tayi faɗa matuƙar tana son ci gaba da rayuwa ko don ta cika burin Ya Nafi da kuma Umma, wannan dalilin ne yasa ta matsa aka sallame ta ta tafi gida ita kaɗai zuciyarta a ƙeƙashe a kuma bushe ƙamas.

Tun daga yanda ta shigo gidan mutanen gidan suka sha jinin jikinsu da ita domin kuwa yaron Kawu Isa da yazo wucewa ya bangajeta kuma yake ƙoƙarin wucewa ba tare daya bata haƙuri ba. Ai kuwa tafasashshiyar zuciyarta ta yinƙuro saman ƙirjinta ta damƙi wuyan yaron ta ɗaga shi sama yana ƙaƙari.

A guje mutanen gidan suka yo kansu Babar yaron na ƙwala ihu tana faɗin "Zata kashe min yaro ku taimaka!". Sai da taga idanunsa sunyi jajawur suna ƙoƙarin juyewa sannan ta wurgar da yaron ƙasa don duk yanda aka so amsarsa zafin zuciyarta ya hana hakan. Murƙususu yaron ya rinƙa yi yana wani irin kukan azaba dake fitowa da ƙyar, Salaha ce ta yinƙuro da nufin taɓata ta ɗauketa da wani azababben marin daya sa taga wulgawar taurari a idonta sannan ta bita ta danne ta shiga kai mata mahaukacin duka sai da ƙyar aka ɗagata daga saman Salaha.

Lokaci ɗaya gida ya ruɗe don sai da tayiwa yara da yawa duka wanda hakan ya haifar da tsoro da shakkarta a idanun yaran dama Matan gidan don ba wanda yayi tunanin tana da wannan ƙarfin zuciyar duk da dama can sun san tana da zafin zuciya. Duk wani abinda taci karo dashi a tsakar gidan ƙwallo take yi da shi tayi gaba abinta, a haka ne ta take bokitin tallar awarar Babar Salaha da aka dawo da bandaro.

Zaburowa ƙanwar Salaha tayi zata yi magana Babarsu ta janye ta tana cewa. "Dawo nan dan Ubanki, bakiga aljanu ta tada ba, so kike ta kashe ki a banza. Barta tayi na Allah ya isa." Ta ƙare maganar a hankali ta yanda Amaturrahaman ɗin ba zata ji ba.

Ƙofarsu ta tura ta shige ta maido ƙyauren da ƙarfi ta rufe wanda har sai da mutanen gidan suka zabura, ajiyar zuciya suka shiga saukewa lokacin da suka tabbatar ta shige sannan kowa ya samu bakin magana daga mai cewa ta haukace sai mai cewa aljanu ne suka shigeta.

Ɗakinsu ta buɗe ta shiga tana jin wani irin rauni na kamata, gani take tamkar zata ga Ya Nafinta zaune tana mata sannu da zuwa cike da murmushi. Kwanciya tayi saman katifa ta fashe da kuka mai ban tausayi kewar Ya Nafi data Ummansu na kamata, babu mai rarrashinta sai da tayi ta gaji sannan ta tashi ta shiga duba kayan Ya Nafi, lokar da take aje kuɗi ta buɗe taga kuɗin da suka rage a ciki suna da yawa. Mayarwa tayi ta rufe sannan ta buɗe wurin da take aje abubuwanta masu mahimmanci.

Ɗan boxs ɗin da Ya Nafi ta bata ajiya ta kuma ce ta adana shi ta fito dashi ta buɗe, memory card ne nannaɗe a takarda ta ciro shi ta shiga dubawa. Wayar Ya Nafi ta shiga nema a ɗakin ta rasata sama ko ƙasa don haka ta fita ta dafa ruwa tayi wanka ta shirya, tea kaɗai ta iya sha ta ɗebi kuɗi ta zuba a hand bag ɗinta ta fice bayan ta kulle ɗakin da ƙofar.

Wucewa tazo yi dai-dai majalisar su Labor wani yaro ne mara jin magana da ya haɗa kan yara irinsa suka addabi mutane da sace-sace a unguwa domin su sayo kayan shaye shayensu. A dai-dai wurin ne jakar hannunta ta faɗi kuɗin ciki suka zube. Duƙawa tayi ta shiga tattarewa akan idanun su Labor don haka suka zaro ido ɗaya daga cikin yarana Labor yace "Kai Oga kuɗine fa a hannun waccen tsakuwata!."

"Na gani cizo kawai mu take mata baya." Labor ya faɗa cikin mayen da yake, ai kuwa miƙewa suka yi suka shiga binta cikin dabara har suka je inda babu mutane sannan suka shiga gabanta Labor ya zaro wuƙa ya nuna mata yace "Kawo abinda ke hannunki." Tsaye kawai tayi tana ƙare musu kallo sun sha sunyi tatul ko tsayuwar kirki ma basa iya yi sai layi suke amma a haka wai zasu mata ƙwace.

Shammatar sa tayi ta daki ƙafarsa da ƙarfi ai kuwa ya lanƙwashe ya faɗi ƙasa wuƙar hannun masa na yin wani wurin. Binsa tayi ta take masa ƙafar da ƙafarta dake sanye cikin sneakers ta shiga murzawa cike da mugunta yayinda ya shiga ƙwalla ihu tamkar ba Namiji ba. Ƙoƙarin nufo ta su cizo suka yi ta wurga masu wani mugun kallo mai ɗauke da gargaɗi.

Sai da ta tabbatar da cewa ya gama galabaita sannan ta ɗaga masa ƙafar ta duƙa kusa dashi tace. "Koda wasa kar kayi tunanin ƙara aikata min irin wannan, idan kuma ba haka ba hmmm." Ta ƙare maganar tana jan ƙwaffa. Har ta juya ta fara tafiya ta dawo ta buɗe jakarta ta ciro kuɗi masu yawa ta jefa masa tace.

"Idan na koma gida ku same ni ina da aikin da zan baku." Tana gama faɗa ta juya tayi tafiyarta. Da sauri cizo yazo zai ɗauki kuɗin Labor ya maka masa wata ƙatuwar ashar ya rarrafa ya kwashe kuɗin yana faɗin "Sakarkarun banza marasa amfani, shine kuna tsaye kuna kallo waccan tsakuwar tayi min duka. Ko dan ba matsala tunda ta biya ta kuma ce zata bada aiki kaga za'a samu alkairi." Ya ƙare maganar yana ƙoƙarin tashi amma ya kasa.

"Dalla can kuzo ku ɗaga ni!". Ya daka musu tsawa, zuwa suka yi suka kama shi suka wuce.

********* Amaturrahaman kuwa kai tsaye babban shagon sayar da woyoyi taje ta sayo waya babba ta koma gida ta shiga ɗaki ta kulle sannan ta hada wayar ta saka M card ɗin nan don ganin meye a cikinsa da yayi sanadiyar salwantar da rayuwar ƴar'uwarta gatanta. Abinda ta gani a cikin ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba don haka nan take ta cire shi ta mayar yanda yake ta ɓoye wani tunani na ɗarsuwa a ranta.

Ranar Amaturrahaman tayi kuka irin wanda ke ƙarar da karfin mutum har a daina jin sautinsa ya koma na zuciya.

★ Washe gari su Labor suka zo har gida kamar yanda ta buƙata kawu Isa ya fito zai fara banbamin a kan me zata kawo musu ƴan daba gida, sawa tayi Labor ya sakar masa ƙaton karensa mai kama da zaki aiko sai da ya hargitsa kowa a gidan tana zaune saman kujera ƙafa ɗaya kan ɗaya tana ƙare musu kallo. Kawu Isa har fitsari yayi a wando zagi kuwa da tsinuwa ba wacce bai mata ba ko a jikinta.

Sai da tabbatar duka gidan sun gama jigata saboda bala'in haushinsu take ji sannan tasa Labor ya kama karensa. "Ina fata wannan zai zama gargaɗi a gareku duk uban daya ƙara shiga harkata a gidan nan hukuncin sa kenan." Tana gama faɗa ta miƙe suka fice su Labor na take mata baya suna mata kirari.

Tun daga ranar su Labor suka zama ƙarƙashin Amaturrahaman duk abinda ta saka su suke bin umarninta yayin da ita kuma take kyautata musu sosai tana basu ci sha har sutura, sannan tana bakin ƙoƙarinta wurin gani ta hana su shan kayan maye duk da sai a hankali zasu daina. Sabon gidansu wanda Ya Nafi ta saya musu shi ta buɗewa su Labor suke zama a cikinsa.

Yanzu Amaturrahaman ta zama boss rashin mutunci take tsulawa son ranta babu wanda ya isa takata, kana mata iskanci zata sa Labor ya koya maka hankali. Domin kuwa mahaukacin karensa zai sakarwa mutu ya masa fata-fata.

Har yanzu a cikin gidan Iyayenta take zaune bata koma wancan gidan ba don tace matuƙar tana garin to a gadon Iyayenta zata zauna ba wanda ya isa shigarsa. Duk sanda Amaturrahaman ke gidan jinin mutanen gidan a farce yake don kuskure kaɗan zata sa aci mata uban mutum.

Akwai lokacin da Sule yazo zai dake ta wai shi Namiji, ai kuwa ranar ya gane kuskurensa don sai da karen Labor ya masa fata-fata da suturar jikinsa. Haka Amaturrahaman ta gagari kowa ya zamana bata tausayin kowa duk wanda ya taɓata sai ta rama. A haka ta zana Jamb ɗinta sannan kuma suka fara jarabawar fita daga makaranta da burin suna ganawa zata jona Karatunta......

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.