Free chapter · Read without an account
2
ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA BIYU
Yau kam wallahi na gaji sosai a makaranta. Test ɗin da muka yi ban tsammanin zan ci ko rabi, domin kuwa ko kaɗan ban samu na yi karatun ba saboda ayyukan gida da suka jibge min jiya. Makarantar da nake zuwa ba ƙarama ba ce, makaranta ce ta 'ya ƴan masu kuɗi da yara masu ji da ji da kansu da fahimtar zamani. A cikin ajinmu ma, zan iya ce muku ni kaɗai ce mai sauƙin kai da rashin damuwa.
Yanzu haka ma ina tsaye a gefen kujerun da muke zama bayan an tashi daga makaranta, ina jiran Malam Idi, direban gidanmu, ya zo ya ɗauke ni. Kawayena suna gefe suna hira suna dariya, ɗaya daga cikinsu mai suna Fatima ta matso kusa da ni tana bani labarin saurayinta. Ban ce mata komai ba, na dai yi murmushi kawai ina jin mamakin yadda ita Fatima ke ta ɓata bakinta a banza akan saurayi tun yanzu.
Can sai ga Malam Idi ya iso cikin harabar makarantar, ya shigo ciki yana faɗin,
"Auta, nazo fa, muje gida."
Sai na yi sallama da su Fatima na shiga mota, muka kama hanyar gida. Yayin da muka hau hanya ne tunanina ya tafi wajen kakata, mahaifiyar mahaifiyata.
Da can idan aka tashi daga makaranta kakata tana zuwa ta ganni, amma yanzu bata zuwa. Shin, na ba ku labari kuwa? To, bari ku ji.
Tun bayan haihuwata, kakata ta roƙi mahaifina ya bata ni ta raineni a wurinta, amma sam-sam ya ƙi. Ya ce bazai iya rabuwa da ni ba. Wannan batu har ya jawo rigima mai zafi tsakanin kakata da Mumy. Mumy dai ta tsaya kai da fata cewa ni diyarta ce ita zata riƙe ni. Abba kuwa ya ce idan kakata tana son ganin jikarta, to a kawo ni wajenta, amma ba za ta zo gidanmu ba. Wannan abu ya taɓa zuciyar kakata sosai.
Amma saboda ni kaɗai ce jikarta daga mahaifiyata, sai ya sanya ta yi ƙoƙarin bibiyar karatuna da rayuwata ta kowace hanya. Tun ina jin kunyarta har muka zama aminai. Yanzu ina matuƙar ƙaunar kakata, kuma duk lokacin da na tuna wannan lamarin, sai na ji zuciyata ta yi rauni.
Mun kusa isa gida, zuciyata cike da tunani daban-daban. Wannan rayuwa dai, duk yadda mutum ya so ta, ba dole ne ta so shi ba.
Muna karasowa gida, na sauka daga mota, sannan na yi wa Malam Idi godiya tare da yi masa sallama cikin girmamawa.
Ina shiga babbar harabar gidanmu, na tsaya na kalli kicin ɗinmu. Abin takaici sai na ga duk an yi kaca-kaca da shi. Kawai sai na ji zuciyata ta baɗe. Na tuna dai da safe na bar ko'ina tsaf, amma yanzu kamar ba gidan da na bar ba ne. Sai kuma na juya na duba falonmu, nan ma abin sai dai ku gani da idanunku, kamar an yi fadan duniya. Wannan ba aikin wani bane sai aikin Mumy, gimbiyar Abba. Ai dama gimbiyoyi ba sa aikin wahala!
Wannan gimbiya ta gidanmu kuwa akwai mulki da izzah. In dai ba don Abba ba ya cin abincin 'yan aiki ba, da sai dai a ɗauko mata masu aiki su yi mana girki. Amma duk wannan mulki da izzar tata, ita ce kawai take girkin Abba, kuma bata barin kowa ya yi masa abinci.
Mumy kyakkyawar mace ce, mai kyau sosai, gata fara tas! Allah ya albarkace ta da cikar jiki da kyan fuska. Amma fa, bata da wani tsayi sosai. Wani lokacin ma idan tana magana, sai na ji kamar muryarta ce kawai ke isa mutum, saboda tsarinta da iya zance. Abin burgewa da shi a wurinta shi ne, ban taɓa ganin tayi faɗa da Abba ba, ko da kuwa shi ne yayi mata laifi. Idan ma faɗa take mana , to tana hadawa addu'a , musamman ni. Wani lokaci idan ba ka san halinta ba, sai ka ɗauka cewa matan Aljannah ce gaba ɗaya!
Amma bari dai na yi shiru kawai, domin idan kuka ga abin da na gani yanzu, sai kun tausayamun. Yanzu da na shiga cikin kicin ɗin nan, wallahi babu wani abincin da aka shirya. Da alama dama tana jira ne har na dawo daga makaranta sai na zo na yi girki!
Sai na girgiza kai kawai, na buɗe fridge, na ɗauko fura da nonon da na dama tun jiya, na ɗauki biscuits, na saka a cikin jakata a hankali, don kada Mumy ta ji motsina.
Sannan na shiga ɗakina na shirya cikin kayana na islamiya. Na san tana can sama kwance, tana ta juye-juye da dannawa waya kawai. Dama ta kore mai aikinta, wai yanzu Na isa aiki!
Ina fitowa da jakar islamiya ta, lokacin har ƙarfe biyu saura kaɗan. Na yi sallar azahar, sannan na ce da Malam Idi
"Mu je kawai malam Idi, makaranta zamu koma."
Na san dai cewa idan na dawo gida daga makarantar islamiya, dole akwai wani sabon shirin Mumy yana jira na. Amma dai yanzu bari in yi tafiya ta. Na dai san tabbas, Amma yanzu dai na fita da dariya kawai muka wuce makaranta.
Tun lokacin da Mumy ta sauko ƙasa wajen ƙarfe huɗu na yamma take ta kwalamin kira, har ta gaji. Ta yi tunanin ko na dawo daga islamiya, ina ɗakina ina hutu, ko kuma na ɓoye ne saboda aiki ya ishe ni. Ta jira na yi mata sannu da gida kamar yadda na saba, amma shiru kake ji, babu amo babu labari.
Ganin ban fito ba ne yasa ta tashi cikin ɗan hanzari ta shiga ɗakina don ta duba. Sai dai tana shiga taga ɗakin babu kowa, wayam! Nan take zuciyarta ta ɗan tsinke, hankalinta ya tashi kaɗan, domin ko kadan bata saba ganina bana nan ba lokacin da take bukata ta.
Da sauri ta ɗauki wayarta, ta kira Malam Idi direba.
"Malam Idi, ina Ramlah take? Ko akwai inda kuka tsaya ne bayan kun dawo daga makaranta?" Ta tambaye shi cikin ɗan ɓacin rai.
"A'a Hajiya, ai Ramlah tana islamiya yanzu. Tun ƙarfe biyu na kai ta makarantar islamiya," Malam Idi ya amsa mata cikin girmamawa.
Mumy ta ji zuciyarta ta tashi, har tana shirin yi masa faɗa akan me zai kai ni makaranta ba tare da ta sani ba. Amma sai ta danne zuciyarta, ta ja numfashi cikin natsuwa tace
"Allah ya tsare min ita, Malam Idi. Ya dawo min da ita lafiya."
Malam Idi ya amsa mata da amin, ta kashe wayar, zuciyarta cike da takaici. A zuciyarta tace, "Yau kam Ramlah kin wuce gona da iri. Dole akwai maganar da zan yi dake idan kin dawo."
Ta dube agogo, sai ta ji yunwa tana neman cin cikinta. Ga kuma takaicin babu abinci a gida. Dole ta mike cikin nutsuwa ta shiga kicin da kanta, ta ɗora ruwa akan gas cikin fushi amma babu yadda za tayi. Duk tana masifa a zuciyarta amma tana ƙara tabbatar wa kanta cewa ni kaɗai ne 'yar aikinta da babu na biyu.
Cikin lokaci kaɗan ta gama girkin jallof din shinkafa mai daɗi, ta haɗa shi da coslaw mai kyau. Ta zuba cikin flask ɗin abinci ta shirya akan dining, dai-dai adadin mutanen gidan. Bayan ta gama komai, ta yi sama kawai cikin yanayi na sarauta irin nata, zuciyarta kuma tana cike da tunanin yadda zata nuna min cewa tayi fushi da abinda na yi.
Ni dai a wannan lokacin, ina can ina koyon karatu a makarantar islamiya, ban san abin da ke jirana ba a gida.
Ƙarfe biyar na yamma daidai, Abba ya shigo gida yana cike da gajiya bayan dawowa daga wurin aikinsa. Bai ƙarasa shiga cikin falon gidan ba, ya tsaya daga bakin ƙofa yana kallon ko'ina da mamaki. Gidan nan fa kamar ba gidanmu ba, ko'ina kaca-kaca! Kicin, falo, komai ya hargitse babu alamun cewa akwai wani mai aikin tsafta a nan gidan.
"Subhanallah! Me yake faruwa a gidan nan yau ne? Ina mutanen gidan suke haka?" Abba ya tambaya cikin ɗaga murya, fuskarsa cike da ɓacin rai.
Mumy ta ji muryarsa daga sama, sai ta fito a hankali tana ɗan dafe kanta kamar mai ciwon gaske.
"Abban Ramlah, sannu da zuwa," tace cikin murya ƙasa-ƙasa kamar ba ta da lafiya.
"Meke faruwa ne a gidan nan Zainab? Ina Ramlah take da gidan nan yake haka?" Abba ya tambayeta da damuwa.
"Ai wallahi Abban Ramlah, ni kaina ciwo yake min sosai tun safe. Ga shi kuma Ramlah tace min ita fa ta gaji da aikin gidan nan, bazata iya ba. Shine fa gidan nan ya zama haka. Ni kuma ka ga ban da lafiya sosai," Mumy ta faɗi hakan da muryar tausayi, tana nuna kamar tana kare ni.
Abba ya fusata sosai jin wannan magana. "Ramlah tace maka ta gaji da aiki? Wannan wani irin shiririta ne haka? Yarinya ƙarama da ba ta da wani aiki sai karatu da kula da gida, amma yanzu zata ce ta gaji? Ai wallahi ba zan ɗauki wannan halin ba!"
Mumy ta matso kusa da shi da sauri, cikin hikimar kissa tace masa:
"Abban Ramlah, ka yi hakuri da ita, yarinya ce fa. Ko da yake ni ban ji daɗin maganarta ba, amma kasan dole mu riƙa yi mata haƙuri. Amma da ka bari idan ta dawo sai ka yi mata nasiha a hankali, kada zuciyarka ta ɓaci sosai, ni kaina na san ba halinta ba ne."
Abba ya ja tsaki yana girgiza kai cikin takaici, zuciyarsa cike da ɓacin rai. "Zan nuna mata wannan halin ba zai yiwu ba a gidana. Ina ƙoƙarin ganin komai yana tafiya daidai, amma ita kuma sai ta ce ba zata iya aikin ba. Wani irin abu ne wannan?"
Mumy tana tsaye tana murmushi a zuciyarta, ta san cewa wannan labarin da ta kirkira zai ɗora min aiki da yawa da kuma faɗa. Amma daga waje ta cigaba da nuna kamar tana tausaya mini tana kare min martaba.
Ni kuwa ina can a makaranta ban san cewa akwai wani babban matsala da ke jirana a gida ba.
Na dawo daga makaranta cike da farin ciki, babu abin da ke raina sai in je gida in huta. Ban san cewa wani babban abin mamaki ne yake jirana ba a gidan yau.
Ina shigowa cikin gidan na tarar da Abba tsaye a falon gidanmu, fuskar nan tasa babu walwala ko kaɗan. Nan take gabana ya faɗi, zuciyata kuma ta fara bugawa da sauri.
"Sannu da gida Abba," na faɗa cikin sanyin murya, amma kafin in gama gaisuwar ya ɗaga min hannu cikin ɓacin rai ya ce,
"Ramlah, wannan wani irin halin banza kika ɗauko ne wai? Yaushe kika girma har zaki ce kin gaji da aikin gida? Shi aikin gidan nan wani nauyi ne a gare ki har ba zaki iya ba?"
Na ji numfashina ya ɗauke, kalmomin nan sun shige ni sosai. Na dubi gefena sai na ga Mumy tsaye tana nuna kamar tana tausayina, har tana riƙe da kafadata.
"Abban Ramlah, ka yi hakuri mana, yarinyar nan fa ƙarama ce. Ba zata iya komai ita kaɗai ba," Mumy tace cikin murya mai sanyi kamar mai tausayawa.
"Ban yarda ba! Ai wannan raini ne da rashin tarbiyya. Wani aikin ne ma Ramlah take da shi sai karatu da aikin gidan nan? To, wallahi ki gyara halinki. Ba zan lamunci wannan halin ba a cikin gidana!" Abba ya sake faɗa cikin muryar faɗa.
Hawaye suka fara zubowa daga idona, na kasa magana. Ina ji a raina cewa Mumy ce ta tsara wannan ƙarya domin ta ɗora min aiki da yawa.
A wannan lokacin ne sai ga babban yayana, Abbas ya shigo gidan yana sallama.
"Assalamu alaikum! Me ke faruwa ne, Abba?" Abbas ya tambaya cikin damuwa ganin yadda Abba ya fusata, ni kuma ina kuka.
"Abbas, duba wannan yarinyar taka! Wai tace ta gaji da aikin gida, ba zata iya ba," Abba ya sake maimaita maganar cikin ɓacin rai.
Abbas ya matso kusa da ni cikin tausayawa, ya ɗaura hannunsa akan kafadata yana cewa,
"Abba ka yi hakuri. Ai Ramlah ƙarama ce sosai, wannan aikin gidan gaskiya yayi mata yawa. Mumy, ki nema mata wata mai aiki mana, ina auta ina wannan aikin mai yawa haka?"
Nan take Mumy ta girgiza kai cikin ƙissa tace,
"Ai wallahi Abbas na bada cigiyar mai aiki sosai, amma har yanzu ba a samu ba. Kuma Baba Zuwaira ba ta da lafiya ne shiyasa ta daina zuwa yanzu."
Abbas ya dubi Abba cikin nutsuwa yace,
"Abba ka yi hakuri da ita. Ka daina yi mata faɗa haka. Ni da kaina zan taimaka a nema wata mai aiki daga yanzu. Ki yi hakuri Ramlah, kin ji?"
Ya ɗan bubbuga kafadata cikin rarrashi, nan take naji zuciyata ta ɗan yi sanyi kaɗan. Na ji kamar na samu wanda zai kare ni a wannan lokacin da babu mai jin ƙorafina.
Na share hawayena a hankali, ina godewa Allah da ya bani yaya mai tausayi kamar Abbas.
Ina tsaye, hawaye na bin fuskata a hankali, zuciyata cike da baƙin ciki da takaici. Sai kawai naji Abba ya yi min wata irin tsawa mai tsoratarwa da girgiza zuciyata.
"Ke Ramlah! Ki hanzarta ki cire uniform ɗinki yanzu ki gyara gidan nan tass! Idan da mahaifiyarki ce da rai ai nasan ba za ta taɓa barin gidanta haka ba!"
Wannan kalma ta shiga cikin zuciyata har ta ƙona ni. Numfashina ya ɗauke na tsaya cak kamar an dasa ni a wurin. Amma kafin in ce komai, Yaya Abbas ya yi sauri ya tare shi yana cewa,
"Haba Abba! Wannan magana tayi tsauri. Ka yi mata faɗa, amma ba haka ba."
Mumy ta yi saurin katse zancen da ta ga yana neman rikicewa tace,
"Tsakani da Allah, Abban Ramlah, menene ma dalilin wannan magana? Ai Ramlah cikakkiyar 'yata ce. Kowa ya san haka, kuma tana ƙoƙarin iyawarta."
Ni dai ban iya cewa komai ba. Cikin sanyin jiki na juya na fita zuwa ɗakina, na cire uniform ɗina na sanya wata tsohuwar riga. Sai na ɗauki bokiti da abin goge-goge na fara aikin share gidan.
Wallahi idan kuka ga yadda kicin ɗinmu ya koma sai kun tausayamin. Amma haka na dage ina sharewa, ina wankewa, har na tabbatar ko'ina yayi fes kamar yadda nake so kullum. Na yi wannan aikin cikin gajiya da damuwa.
Ina gamawa wata irin yunwa ce ta bugi cikina. Na nufi wajen dining, amma da na isa sai na tarar babu abinci kwata-kwata. Nan da nan zuciyata ta sake cika da takaici. Na koma sama wajen Mumy domin na yi mata sannu da hutawa.
"Mumy, sannu da hutawa. Don Allah ina abincina?" Na tambayeta cikin sanyin murya.
Tace min, "Ban duba dining ba ne? Ai na aje abincin can."
Na ce mata, "Babu komai a dining, Mumy."
Sai tayi murmushi kadan tace, "Oh, Abbas kenan! Ashe ya kwashe duk abincin nan, ban sani ba wallahi."
A cikin ranta kuwa daman ta san cewa babu abin da ta bar min, kuma ta riga ta yanke shawarar cewa ba zan ci ba.
Sai kawai ta sake ce min, "Amma bari na dafa miki indomie ko taliyar da kike so."
Abba wanda ke gefe yana sauraronmu, sai ya dubi Mumy da faɗa yace, "Ita ba za ta dafa ba sai ke uwarta?
Ina jin wannan kalma daga bakin Abba, zuciyata ta ƙara cika da baƙin ciki. Na koma kicin a hankali, amma da na shiga ciki sai kawai na fashe da kuka mai tsanani. Kuka na takaici, kuka na rashin uwa, kuka na rashin gata.
Nana hadiza
***