Free chapter · Read without an account
5.
by Hijjart Abdoul · SAIFUDDEEN
*******Saif yana shigowa parlour ya gan su dukan su suna zaune sa yanzu za su yi dinner. Amma Safwan na zaune a parlour yana shan lemu mai sanyi sosai gefen sa kuma alawace da chocolate yana aiki a system. Be bi ta kan shi ba ya je wurin Abbi ya gaida shi, da Mommy sannan Sufaina ta gaida shi, shi kuma ya gaidar da Sufyan..
"Hope ka dena jin komai ko?
Cewar Abbi ya faɗa cike da kulawa. Ɗan murmushi ya yi mai kyau yana ɗan kallan Sufyan..
"Ah bakomai Abbina".
Murmushi ya yi masa Abbin yana ɗan shafa fuskarsa. Tare da jinjina masa kai..
"Ka yi haƙuri...
"I'm not comfortable with it please Daaad".
"I'm satisfied thank you so Much Love".
Ya faɗa cike da ɓoye abinda ke ran sa yana mai zagayo da hannunsa ta wuyan Abbin na sa. Shina Abbin cike da nuna nasa shikenan zai yi yarda yace ɗin ya ɗan kama hannunsa tare da bashi kyakkyawan peck a kunci yana sa masa albarka. Da sauri Sufaina itama ta zo ta yi yarda ya yi ta gefen Abbin.
"Sarkin kishi, Sufaina kin shiga uku".
"Ni baka min peck ɗin Dadd".
Ta faɗa cike da taɓara, peck ɗin ya yi mata yana sa mata albarka.
Sakin sa Saif ya yi yana cewa.
"Su lollipop har yanzu ana nan ba'a sauya hali ba".
Dariya ta yi mai kyau tana komawa wurin zamanta.
"Ai bakai ne auta ba, kuma Abbi ai an fi so na".
Safwan dake wurin zaman sa yace, "Daɗin abin muma ana san mu, ba'a bola aka tsinto mu ba".
Dariya duk suka yi banda Sufyan, Mommy na sa musu baki. Saif wurin zaman Safwan ya je ya zauna yana kallan abinda yake ci, kafin ya kwashe daga gabansa.
"Ban san sai yaushe ne zaka sauya ba daga wannan shan zaƙin ba kwata-kwata".
"Please...
Hararan da ya zuba masa ne yasa shi yin kalar tausayi irin ya da haka ɗin nan?
"Ba zan baka ba, wallahi ya kamata ya ka dena shan wannan abun, amma ka cigaba lokacin da zai tambaye ka ƙilan ma ni bana duniyar".
Dariya Safwan ya kwashe da shi yace, "Baka duniyar? Wai dan Allah Lili kana abu sai ka ce wani wanda ka bani irin ages ɗin nan da yawa, duka duka nawa ka bani".
"Shekara biyu ce na ka, kai fa yaro ne har yanzun, kawai saurin girma ka yi aka yi maka jumping ka yi saurin gama makaranta. At your of 23 ace wai kana aiki".
"Lalle Ya Saif, kai yaushe ka gama makarantar?
Shiru ya yi yana muzurai alamar ai na manta da nawa age ɗin nake faɗar na wani. Sosai abin ya bawa Safwan dariya.
Yana dariya yace, "Na ji, shikenan, ba wannan ba, yi min wannan design ɗin dan Allah, so nake na fitar da wani irin special design da babu kamar sa, special aka kawo aka ce na yi, ni kuma bansan taya zan yi design ɗin atamphar ba".
"Excuse me? Kai ma ba abinda na karanta ka karanta ba kenan?
"Ya ilahi! Haba Lilina".
"Ba zan yi ba, ka je ka yi abinka".
"Kaga kar mu yi haka da kai mana, ni ne fa".
"Na ji, sai de na gwada maka yadda zaka yi, amma gaskiya ba zan yi maka ba".
"Hakan ma i really appreciate and love it at the same time Kuma thank you".
Ya faɗa yana dariya irin hakan nan ɗin ma na gode, sai ya harare shi sannan ya janyo system ɗin kusa da shi ya dawo tsakiyar su ya fara koya masa daki-daki komai. Har sai da kowa ya baje ya je ya kwanta suna nan suna aiki. Sai wurin sha ɗaya na dare sannan Safwan ya fara hamma, hakan yasa Saif cewa.
"Ubangiji Allah ya shirya min kai, ka sani a gaba ina maka abu, kuma ka zo ka ce zaka min bacci, and ƙilan you promise them cewar gobe suke so ko?
"Dan Allah ka yi min....
Hararan da ya zuba masa ne yasa shi saurin cewa, "Sorry".
"Daman de ka dawo aiki a office ɗin mu".
Ya faɗa masa ƙasa-ƙasa dan ba yau ba ya sha yi masa tambayar meye yasa be aiki a tare da su. Tun sanda ya fara aikin yake bibiyar shi akan ya dawo shima. Yanzun ma be tanka masa ba ya tashi..
"Idan Allah ya kaimu da asuba za mu ƙarasa, yanzu ka je ka kwanta uhm? Nima bacci zan yi".
"Sure Lili".
Ya faɗa yana tattare papers ɗin da ya baza duk akan koyon abun. Papers ɗin Saif ya ƙwace ya faka masa a fuskar sa.
"Na sake ji ka ce min wannan Lili ɗin".
Yana dariya ya ƙwace abin sa yace.
"Liliiiii".
Ya sa gudu, da sauri Saif ya bishi zai kamo shi suka fara zagaye parlourn na su suna gudu idan ya yi nan sai ya yi nan. Ga system ɗin sa a hannu da takardu be so ya kama shi ya ƙwace ya ce a bakacin aikin sa.
Fitowar Sufyan da Abbi ce yasa Abbi kallan ɗan na sa cike da wani shauƙin ƙauna daga shi har Safwan ɗin. Zaka ce ba abinda yake damun sa a yarda yake wannan dariya, amma deep inside sabon al'amari ne gami da wani irin sauyin baƙon yanayin dake a danƙare a ƙasan zuciyarsa. To me zai ce game da hakan?
A hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya kalle su.
"Meye hakan ku ke ji a cikin dare? Kun san time kuwa?
Hakan yasa su yin shiru.
Safwan yace, "Dad Lili ne".
Saif ma yace, "Dad Lili ne".
Suka faɗa a tare. Tsaki Abbi ya ja yana zuwa yana cewa.
"Zo nan Safwan ina san magana da kai".
Sai da gabansa ya faɗa tunowa da abinda suka yi da Sufyan ɗazu tashin hankali kenan. Amma he's ready da duk abinda za'a yi sai de ayi.
Saif wucewa ya yi shikam be wani tsaya ba, to daman me zai jira ya yi? Aikin su ne na office shi ba yi yake ba. Yana zuwa kwanciyar sa ya yi bayan ya gama tunanin Mubeena, kawai gani yake kamar zata dawo gare shi. Kafin ya tashi ya je ya yi alwala ya zo ya yi wutri ya kwanta dan ita ce Sallahr sa na ƙarshe da yake yi sai ya kwanta abinsa.
A parlour kuwa a ƙasa dukan su Abbi ya zaunar da su, sai ga Mommy ta fito itama ta zauna a kusa da Abbi.
"Sufyan maimaita abinda kace Safwan ya yi maka".
Abinda ya fara faɗa kenan ya haɗe fuskar nan sosai. Tiryan tiryan ya kwashe komai ya sanar da shi batare da ya cire ko ya rage ba har faɗan da suka yi".
"Safwan anyi haka".
Kan sa gaban sa na mugun faɗuwa sosai yace.
"Ehh Abbi".
Ya faɗa a hankali batare da ya ɗago ba.
"Reni ne hakan ka yi masa ko meye?
"Abinda ya yiwa Saif be kyauta ba, shine nake jin haushinsa".
Ya faɗa kan sa tsaye batare da ya ɓoye ainahin haushinsa da yake ji ba.
"Sai kuma aka yi me?
"Sai kuma zancen contract, ni ba baƙin ciki nake yi masa ba kawai ya dena haɗa shirginsa da nawa".
Ya faɗa yana kumbura baki cike da sabuwar rashin kunya.
"What next?
"Ba komai".
Ya faɗa a hankali har yanzu ya kasa ɗago da kan sa.
"Me ka ke so?
Abbi ya faɗa yana kallan Sufyan.
"Ya fita harkata Abbi...
Mommy tace, "Zancen fita harka be ta so ba...
Kallan da Abbi ya yi mata ne yasa ta yin shiru.
"Daga yau, na raba wurin a biyu. Kowa ya yi aikin sa, ba ruwan kowa da kowa".
A tare suka ɗago suka kalle shi. Sufyan yace, "Abbi? Taya za'a yi ace ka yi wannan ɗanyen aikin?
"Kai ne uban ko ni?
Sunkuyar da kan sa ƙasa ya yi be ce komai ba.
"Idan ba zaku yi aiki tare ba, hakan na nufin cewa ko bayan na mutu ba ku wannan haɗin kan na yin aikin tare, ba zan ce kar ku haɗa kan ku ba. Ku cigaba da yin faɗa a tsakaninku. Ku ne a wahale ba ni ba. Kune rayuwar za ta yiwa ƙunci ba ni ba. Ruwan ku ku haɗa kan ku, ruwan ku ne kuma ku raba kawun nan ku daga nan har ƙarshen mutuwar ku".
Ya faɗa yana miƙa musu takardun dake nuna cewar mallakin su ne.
"Safwan jira".
Sufyan tashi ya yi ya bashi waje.
"And kai kuma....
Ya faɗa yana kallan Safwan, Safwan na jin haka ya ja da baya a hankali. Aikuwa be je ga gama ja da bayan ba Abbi ya sakar masa wani shegen mari.
"Yayan ka zaka yi faɗa da shi ko?
Ya faɗa yana sake kai masa wani marin.
"Ni zaka lalatawa tarbiyya ko? Rena na gaba da kai ko?
Girgiza kan sa yake yi sosai yana so ya ce ayi haƙuri amma ba zai taɓa yin haƙurin ba. Sai da ya zane shi tas sannan ya ce ya tashi ya bashi waje. Kafin ya shiga ɗakin Sufyan ya tarar da shi yana waya da Mubeena. Ganin Abbi yasa shi kashewa yana sinne kai. Uffan Abbi be ce da shi ba, ya balbale shi d faɗan biyewa Safwan da ya yi shima sosai ya yi masa faɗan da ya gwammace shima dukan sa aka yi ɗin. Domin ɓacin ran Abbi suna mugun tsoron sa sosai.
Ajiyar zuciya ya sauke bayan fitar sa kafin ya na tunanin taya za'a yi ace yana riƙe da abun nan tun kafin zuwan Safwan sannan ace za'a raba shi gida biyu? Like seriously shiyasa da za su fito suka ga kayan aiki kenan, ya tambaya aka ce masa Yallaɓai ne yasa a kawo, kenan raba shi za'a yi? Shine wanda za'a bawa wannan wurin gaba ɗaya, shine ya cancanci wurin domin shine ya ƙarasa gina shi ya jawo mutane da dama cikin wannan harkar, amma sama ta ka azo a raba shi? Ajiyar zuciya ya sake saukewa kafin a hankali ya kwanta ya rufe idansa.
****Gadan-gadan aka shiga bikin, har ake neman yau ne za'a ɗaura auren, tunda aka fara kuma bikin Saif be sake zuwa gidan ba daga shi har Safwan, kusan za'a ce Safwan ma ya fi Saif jin haushin abinda ya faru Sufaina itama bikin ba wani nan take yi da shi ba, hasalima ko sabon kaya bata yi ba dan ba su da telan da zai ɗinka mata a cikin kwana ba daya ba, sai kawai dan bata san bikin. Da suka haɗu da ƴan uwan su ne ma abin ya zo da sauƙi ta sake sosai a cikin mutane tana yake domin basa san fitar da sirrin gidan su. Mommy har ta yi faɗan ta gaji ta zuba musu ido kawai, to shima ba'a zaune ba yake, suna ta hidimar bikin Farooq wanda za'a yi a rana ɗaya kuma a wuri ɗaya. Sai de fa iyayen su Farooq da Hafsah gaba ɗaya bama sa magana da juna. Amma wai a haka za'a yi bikin. Shide Baban Hafsah yana nan akan batun sa cewar ba ruwan sa haka ƴan uwan sa maza da suma ba su bi goyan bayan yardar sa auren Mubeena ba. Suka goyi bayan auren Hafsah haka yasa shi ƙara cika ya batse tare da cewar duk baƙi ciki suke yi masa, ba sa so ya fi su arziki, hakan yasa su jan bakin su suka yi shiru da wannan lamarin.
A babban masallaci mai suna Saif Masjid anan za'a ɗaura auren, wanda ya kasance Abbi ne ya gina da sunan Saif. Sanda za'a ginin kuri'a ya yi a tsakanin yaran cewar duk wanda Mommy ta zaɓa sunansa shine wanda za'a gina da sunansa, ita ta rubuta sunan ita kuma ta zaɓa sunan. Tun suna yara ba su girma. Hakan yasa suke mutuwar san masallaci. Da duk wata shekara sai an sake modernizing ɗin sa. Zaka iya cewa ba'a ƙasar yake ba, kama daga cikin harabar masallacin da kuma shi kan sa masallacin. Wurin mata daban, haka ma na maza......
Suna zaune a harabar da aka sa kujerar wurin parking, ya yi shiru kawai yana jin yadda aka kira sunan Mubeena da Sufyan. Bema ji sanda aka ɗaura auren Farooq tsabar yarda ya lula duniyar tunanin Mubeena. Kenan haka Allah yake ikonsa. Wallahi ko da wasa be taɓa tunani ko kawo a ran sa cewar Mubeenr sa watarana zata yi auri wani bashi ba. Wanin ma da ta tashi aura sai ya kasance ta auri Yayansa. Shin an taɓa yin haka daman? Ko kuwa akan sa aka fara? Sai a yanzu ya sake gaskatawa da kuma sallamawa cewar shikenan ba matar shi ba ce ba. A yanzu ta zama matar wani ba shi ba. A hankali ya Kulle idansa da suka yi ɗan Kada suka yi jaa yana jin bugun zuciyar sa na sauyawa sosai. Dafa shin da aka yi ne yasa shi kallan Saleem da abokan su gaba ɗayan su sun zagaya shi wasu sai yanzu suke jin labari. Sai ga Safwan.
"Sai da ka zo?
Saleem yace, "Ba yarda ba'a yi da shi ba akai bikin wani wajen ba nan ba, ko a sauya lokacin amma yace ba haka ba".
Saif yace, "Ya nagan ka haka?
Ya faɗa yana kallan kayan jikin sa, sai a lokacin mutanen wurin suka bi jikin da kallo. Ƙanana kayane a jikin sa, fuskar nan ta yi burɗi-burɗi da ita alamar daga bacci yake ɗan ga kayan bacci nan a jikin sa.
"Just to check on you to make sure you are fine shine kawai".
Girgiza kan sa Saif ya yi yace, "To sai ka tafi bana buƙata indai a haka zaka zo wurina".
Sake turo bakin ya yi yana kallan Sufyan dake can nesa da su suna ta ɗauka hotuna. Juyawa ya yi kawai ya shige motar sa yana barin wajen. Sai a lokacin abokansa suka jajanta masa suna jin wani irin a jikin sa. Duk zumuɗin bikin na fitar musu a rai. Daƙyar de ya samu ya ja hankalin su suka tafi aka kai su inda za su zauna su ci abinci. Ganin kiran Mommy ya sa shi barin wajen yana yin gaba wurin parking ɗin sosai can nesa yana amsa wayar. Yana juyawa ya sake ganin kiran Sufaina yasa ba wani abu ne serious da zata faɗa sai de ya zo ana ta tambayar sa a gida. Hakan yasa shi ya ke kallan kiran tare da contemplating akan ya ɗaga ne ko kar ya ɗaga.
Hankalinsa na ga wayarsa sam be lura ba kawai ya ji ya yi karo da mutum, wayar da key ɗin da suka faɗi ya bi da kallo, kafin ya maida kallansa ga kan kyakkyawar fuskar ta da ta sha kyau sosai bakin nan ya sha red velvet lipstick ya yi kyau sosai. Ta taje girarta ta sa mascara a idan ta sai idan ya fito ya yi zara-zara da shi abin gwanin ban kyau. Da ɗaurinta da ta sha sosai ya zauna mata kai, ta yafa ƙaramin veil ɗin ta a jikin ta akan riga da skirt ɗin ta.
"Rowdy?
Ta faɗa cike da mamakim sake ganin sa a karo na biyu. Shi wallahi sam be gane ta ba ma, ganin irin kyan da ta yi.
"Me yasa baka ganin gaban ka ne wai? Kana tafe kana shegen iyayi ba? Dan ka burge mata ne hakan ko kuwa me?
"Shi yasa naga ka zo wurin parking ka kana karewa mutane kallo ko?
"Ko zaka samu wata irin Mubeena ba?
"Ohh Sorry....
Ta faɗa cike da renin wayo tana masa wani kallan uku saura kwata, Shima sake kallanta da mamakin uban me ya sake haɗa shi da wannan matar kuma? Da fa yana niyyan faɗa mata sorry ne. Amma ganin yar renin wayon nan ce yasa shi tamke fuskar sa.
"Ko auren ka za'a yi? Nagan ka a haka kamar wani ango, ina Mubeenar?
"Keeee bana san munafurci wallahi. Ki fita daga ido na na rufe, munafuka kai".
"And kuma ki sa wa zaki kira da ya burge mata. Meye abin burge ku? Mayaudara kawai".
Sakar baki ta yi kawai tana kallansa. Daga tambaya?
"Kai wai meyasa ka ke da girman kai ne a rayuwar ka....
"Har yaushe ki ka sanni da zaki ce ina da girman kai? Ji munafuka".
"Kai ne munafiki amma bani ba....
Bata yi ba kawai ya zabga mata mari.
"Ni ba sa'an wasan ki ba ne, banzar yarinya kawai".
Ya faɗa yana wucewa ta gefenta ya wuce ya barta da hannu a dafe, ga zafi da hannunsa ke da shi, who hell is he da zai ke taɓa ta haka? Kawai ƙwalla ce ta fara zubo mata tsabar takaici da mamaki. Ganin fa zai ci bulus yasa ta saurin janyo shi da sauri tana dawo da shi baya.
"Baka isa ba wallahi, ka min laifi kuma ka zo ka mareni".
"Kai ne ka buge ni, dan haka ka bani haƙurin buge ni da ka yi da kuma na marin da ka min".
"Ke shiyasa naga kina kallan gaban na ki ai, dalla malama sake ni kafin na ƙara zabga maki wani mari wallahi.....
"Saifff....
Abbi ya faɗa a bayan sa, da sauri ta sake shi tana kallan Abbi, kallan yarinyar ya yi dakyau kafin ya sake kallanta yana sakar masa lallausan murmushin da be san daga ina ba ya fito masa zuwa kan fuskarsa. Ta gaida shi da ladabi.
"Me ya faru?
"Abbi marina ya yi, kuma ya fadar min da kayana, be bani haƙuri ba".
Ta faɗa cike da tsantsan Shagwaɓa. Tana turo baki, shima kumbura baki ya yi yana mis-mis da baki yana hararanta.
"Mari?
Ya faɗa yana kallan Saif.
"Abbi baka san yarinyar nan ba ne, munafuka ce ta ajin ƙarshen nan ga shegen surutu da san a sani".
Ya faɗa yana hararanta. Abbi ya yace.
"Rama marin ki".
"What?
Ya faɗa yana yatsine fuskarsa. Gadan gadan ta zo zata mare shi ya yi saurin cewa.
"Dan Allah ki yi haƙuri Cheeky".
Ya ƙarashe yana durƙusawa. Ta dari ido tace.
"What?
"Abbi he called me Cheeky na yi kama da stubborn lady ne?
Tashi ya tsaye yana karkaɗe kayan shi ganin Abbi ya juya alamar baƙinsa na san magana da shi yasa shi ce mata.
"Kinga saboda Babana na baki haƙuri, idan kinga dama ki haƙura idan baki gani ba kuma kar ki haƙura banza kawai uwar shishigi da shiga al'amarin mutane“.
Ya faɗa yana ɗan yarfe mayafin da ya kusa zamewa daga jikin ta. Takaici da baƙin ciki ne suka cika mata suka yi mata yawa. Wasu mutanen sam ba su da ɗaga da iya magana mai daɗi. Fatan ta kar Allah ya sake haɗa su balle har ya faɗa mata magana. Ga wani irin abu da take ji game da shi tun farkon haɗuwarsu da ta yi. Tausayin yaudarar da aka yi masa ne? Ko kuwa wani abunne na daban da bata san daga ina yake ba?
Daga inda take tana kallan shi yana ta dariya a cikin jama'a. Ga mamakin ta sai ta ji she's happy and pray for him Allah ya bashi wacce ta fi Mubeena.
"Me nake yi haka?
Ta faɗa tana tambayar kanta, kafin ta saki murmushi kuma tana ɗan share fuskar ta ta ciro powder a jakarta ta sake gyara fuskar na dakyau sannan ta gyara mayafin ta, ta kwashi kayan dake yashe a ƙasa ta yi hanyar masallacin mata wanda za'a gudanar da walima ta wani bikin. Har suka tashi daga taron walimar lokacin Saif sun zo tafiya da wasu abokan na su da suka yi lattin zuwa ɗaurin aure. Ya hangota sun fito da kayan biki s kyakkyawan jaka, kowa tashi a hannun sa, sai dariya itama take yi da'alama tana jin daɗin yarda ake bata labarin. Da sauri ya wani kau da kan sa gefe. Sam bata lura da shi ba dan ya juya baya ta wuce ta gaban sa ta zagaya ta wurin motar ta. Zata shiga ya ji ance da ita.
"Ke Ma'u dalla bani key ɗin motar nan, ki shiga wata motar".
"Anty gida zaki je? Ki hau sai mu tafi".
"Ba zaki bani ba ko me ye ne?
"Ina so na shiga asibiti daga nan zan wuce gida...
Jin saukar kyakkyawan mari a kan fuskarta yasa Saif saurin juyowa ya zuba mata ido. Ƙwalla sosai ta cika mata ido har hawaye na zubowa tace.
"Amma fa motatace me yasa baki ɗauko ta ki ba...
"Zaki bani ne ko sai na sake zuba maki wani marin, tunda ke musu shine aikin ko? Jaka yarinya kawai".
Jiki a sanyaye ta miƙa mata key ɗin ta shiga ita da kewayenta suka tafi. Gashi ƙawarta Aliya ta tafi. Share hawayenta ta yi ta duba jakarta ta ga ba kuɗi kawai tarkacen alawa ce da kayan kwalliya. Dafe kan ta ta yi kawai tana sake jin hawaye na zubo mata kafin a hankali ta fara tafiya ana share hawaye akai-akai. Ga hill ɗin takalmi ne a ƙafarta, kusan faɗuwar da ta yi ne yasa ya sa Saif yi kamar zai tarota sai kuma yaga ba faɗuwa ba ce. Gaba ɗaya ji ya yi wani irin tausayinta ya rufe shi, wato idan kowa akwai abinda yake damun sa kenan ko? Shi yasa take da san jin labarin mutane ko Allah zai sa ta ji wanda ya yi iri ɗaya da nata ne ko kuwa ba haka? Amma ta kirata da Anty? Sannan dole akwai wani abun a cikin labarinta, but she's happy da yadda take yi.
'Who is she?
Ya faɗa a hankali yana cigaba da kallanta ko rabin harabar masallacin bata fita ba tsabar yarda yake da girma.
"Mu je ko?
Cewar Saleem tare da abokan na su.
"Da ina ku ka tsaya".
"Sallah na tarar su suna yi".
"Ohk".
Motar su, suka shiga suma ganin akwai extra mota yasa Saif cewar.
"Dan Allah mu je mu ɗauka wannan yarinyar".
"Zata yarda?
Cewar wani abokin nasa.
"Zata yarda mana, bari na zauna a baya idan ya so sai ta shiga gaba, amma kar ka nuna tare muke".
Jinjina masa kai ya yi. Daƙyar ya shawo kan ta ta yarda suka hau suka tafi.
"Suna fa?
Ɗan kallan sa ta yi tace, "Asma'u".
Ta faɗa ran ta duk a jagule.
"Gari fa? Nan? Idan nan wacce unguwar?
"Bansani ba".
"Allah ya baki haƙuri".
"A'a as in bansan sunan unguwar ba, mantawa nake, bamu jima da dawowa ba".
"Ohh, da wanne gari ku ke".
"Sokoto".
"Ahhh wonders, nima acan nake, wanne wurina Sokoto".
"Wamako".
A hankali ya shiga yi mata tambaya tana bashi amsa har unguwar da take da inda take da komai cike da mamaki yace.
"Ke ƙanwar Abdul ce?
"Ehh".
Sai kuma ya sake kallanta yace, "Ki ka ce Asma'u?
Tace, "Ehh".
"Kar ki ce min Ma'u majina ce".
Turɓune fuskarta yi tace, "Meye hakan ?
Yana dariya sosai yace, "A'a yi haƙuri".
Bata sake kula shi bata juyar da kan ta,sai de shi zai juyo akai-akai yana kallonta, idan ya kalleta sai ya saki murmushi ya sauke ta a asibiti.
Zata fita yace, "Ki ce AB yana gaida Abdul".
"Ba zai ji ba".
Ta faɗa tana banka masa murfin motar. Tana zuba masa harara.
"Me ya yi zafi?
Saif ne ya dawo gaba yace, "Ka santa a ashe".
"Ehh ba".
"To ya naji bata hausar Sokoton?
"To aka ce maka kowa ne ke yi?
"A'a Wallahi naturally kowa na Sokoto yana yin maganar ku".
"Nima ai bana yi ko?
"Kai kuma ba ka yi boarding school ba a Azare?
Har suka zo be kuma tambaye shi komai akan ta ba, shima AB ɗin be ce masa komai ba akan ta. Sun samu fun sosai da ƴan Course mates na su, an yi raha an yi wasa da dariya sosai kafin aka yi la'asar aka wanda bana gari ba suka kama hanyar tafiyar, na gari kuma kuma suka hau shirin kai amarya.
A bangare Mubeena kuwa dare na yi aka haɗa party mai shegen haɗuwa da tsari. Wanda ta yi kyau sosai abin ba'a cewa komai, komai kuma ya tafi cikin kyau da tsari yarda suka tsara abin su. Kowa sai yaba Amaryar yake dan yarda take da kyau ɗin nan ga fara'a da take yi. Gashi sun dace sosai da juna. Haka aka yi komai suna komawa gida aka je aka ɗauko ta aka kaita gidan su Saif wanda yake gidan mijinta za'a ce. Akwai ƙofar hawa a beninsu daga waje ta wurin ƙofar kitchen ta baya. Haka ma zaka shiga ta cikin gida idan kana son ka yi sauri. Part ɗin na ta kam ya hadu iya haɗuwa kowa yaba irin kayan da aka zuba mata yake yi, dan duk kushewarka baka isa ka kushe tsaruwar da wajen ya yi ba. Mommy ce ta karɓe cikin mutunci da mutuntawa gami da karamci. Ba su wani jima ba ƴan kawo amaryar suka tafi. Yayin da ta zauna a wurin Mommy har Sufyan ya dawo ta haɗa su sosai ta yi musu nasiha kafin ta je su je su huta.....