Free chapter · Read without an account
6
ƘADDARAR RAMLAH
SHAFI NA SHIDA
Ayayin da ya daga narƙakkun idanunsa ya zubasu cikin fuskarta, idanuwansa sun ɗauki launin dusar rana kamar yadda zuciyarsa ta ɗauki zafi mai nauyi. Bacin rai ya bayyana a kowane kwarjinin fuskarsa.
Aishatu ta ɗago kai cike da jin nauyin laifinta, tana jiran hukuncin zuciyarsa kamar wacce ta kusa fuskantar sarƙaƙƙen zargi a gaban alƙalin kotu.
"Aishatu..." ya ambaci sunanta da sautin da ya sa zuciyarta ta tsinke.
"Na fa gaya miki sau nawa ki daina saka abu a gabanki?"
Cikin raɗa mai cike da hawaye tace,
"Dan Allah kayi hakuri Habibie... wallahi ba don komai nake sakawa ba, shekaruna sun ja ne, ina buƙatar gyara... kuma abun yana ƙara ni’ima ne..."
Yana daɗa huci , ya ce da ita
"Ni na taɓa ce miki ina son ki saka wani abu a jikinki? Gabanki ba bola bane Aishatu... kuma ban gaya miki sau ɗaya ba!"
Yana ficewa daga gado ya ɗauki tawul, yana gyara rigarsa cikin fushi. Aishatu kuma ta durƙusa cikin ƙasa tana kuka da neman yafiya.
"Habibie please... banson fushinka. I just want to make you happy... kuma... ni naji bushewa sosai..."
Yayi mata wani kallo na ƙarshe kallon da ya haɗa tausayi da yanke hukunci. Ya shiga bandaki, addu’a na fita daga bakinsa, ya kunna ruwan zafi yana shigewa ƙarƙashin ruwa kamar yana wanke zuciyarsa daga rudanin da take ciki.
A yayin da ruwan ke zuba a jikinsa, zuciyarsa na sake jaddada masa abu guda: "Ina buƙatar aure."
Sanin halinsa da idan ya fito masa bazai saurareta ba, yasa Aishatu miƙewa cikin nutsuwa, ta shige ɗayan bandakin dake cikin tafkeken ɗakin barcin da ke cikin katafaren gidan gidan da ke ɗauke da tarkacen alfarma da kamshin kuɗi a ko'ina.
Bayan ta gama wanka da ruwan zafi, ta tsane jikinta, sannan ta zura rigar wanka mai launin fari, ta fito. Tana fitowa, ta tarar da shi zaune a gefen gadon royal, yana danne-dannen system ɗinsa, agogon Cartier a hannunsa na leƙowa daga rigar barcinsa. Ko kallon gefenta bai yi ba.
Cike da natsuwa da salo, ta karaso ta zauna kusa dashi, zuciyarta cike da fargabar kada laifinta ya cusa hazo a tsakanin su.
Bai kalleta ba, amma cikin sanyi da izza ya ce, “Kiyi kwanciyarki. Gobe flight ɗinku da rana ne. I already booked everything.”
Ta narke murya da sassauci, kamar mai kokarin tunzura zuciyarsa da tausayi, "I’m very sorry Habibie... na yarda nayi kuskure, bazan sake ba wallahi."
Shiru ya ɗauki ɗakin, sautin Ac ɗin dakinsu na tsintuwa kamar yana karanta yanayin zuciyar ma’auratan.
Daga bisani ya dago, idanunsa suka haɗu da nata, cike da bacin rai da takaici, yace, “But sau nawa zan gayamiki Aysha? Duk abinda kike buƙata kisha, ki shafa, na barki. Amma wannan saka abu a gabanki da sunan yana ƙara ni’ima? Kinsan dame ake yin waɗannan abubuwan? Kinsan irin cutar da zai iya janyo miki? Kinsan ciwon da zai iya ɓoye a ciki har sai lokacin da babu magani? Cancer is real fa.”
Tana ƙasa da murya cikin kaskantar da kai ta ce, “Please Habibie… bazan ƙara ba. Kayi hakuri.”
Ya lumshe idanu, ya dafe goshinsa kamar mai tunani mai nauyi, amma bai ce uffan ba.
A haka ya juyo gefe, ya kwanta. Ita kuma ta na cikin rigar wankanta, ta na kallo kamar karamar yarinya da aka yi wa gargaɗi. Tana ba shi haƙuri har baccin dare ya ɗauketa a gefen gadon, cikin dakin da yake dauke da kamshin turaren Oud Royal da murɗaɗɗen labulen siliki.
Zuciyarsa na faman bugawa da juyayi. Kodayake fushi ne ya mamaye sa tun farko, amma yanzu zuciyarsa na karkarwa da tausayi da buƙata. Ba wai buƙatar jiki kadai ba, a’a buƙatar kusanci, tausayinta, da ƙaunar da ke neman dusashewa a tsakanin su.
Ya juya a hankali ya kalleta, tana kwance cikin barci mai nauyi, numfashinta na fita a hankali kamar sautun waƙar dare. Fuskar ta ta haske a ƙarƙashin fitilar bango, idonta rufe cikin natsuwa, leɓenta na ɗan motsi kamar tana ƙoƙarin faɗin wani abu.
A hankali ya matsa kusa da ita. Bai faɗa mata komai ba. Amma zuciyarsa ta cika da salwanta.
Ya ɗora hannunsa a saman kugunta, ya janyo ta a hankali kamar jaririya. Ya rungumota kamar yana ƙoƙarin haɗa zuciyarsa da nata. Jikinsa ya buga da nata, zafin ƙauna ya daki lafiyarsa. Numfashinsa ya fara canzawa, jikinsa ya fara rawar buƙata, amma zuciyarsa ta hana shi bin buƙatar jiki sai dai ya yi shiru yana jin dumin jikinta.
Sai da ta ɗan motsa a barci, sannan ya matseta sosai a ƙirjinsa. Leɓensa ya ɗan sauka a gashinta, sannan a saman goshinta, yana sauke numfashi mai nauyi.
"Aysha... Ina jin ki fiye da yanda zan iya bayyana... Amma me yasa kike cutar da kanki har kin manta da irin wacce kike?"
Ya dora fuskarsa a ƙugunta, yana jin hawaye na taruwa a idanunsa, amma ya hana su zubowa. A wannan lokacin, ba miji da mata suka kwanta ba zuciyoyi biyu ne da ke neman mafita a cikin dakin da ya cika da shiru, da motsin ƙauna, da tambayoyin da babu amsa.
Rana na ɗan kaiwa ƙarfe takwas da rabi na safe lokacin da Aishatu ta sauko daga saman bene cikin shigar da ta haɗa ladabi da salo. Riga ce mai launin ruwan kwai, mai ɗauke da ɗan kamshi na turaren Maison Francis Kurkdjian, wanda ko iska na busa daga gabanta, sai ya bar ƙamshi a ko’ina.
A cikin babban falon gidan dake ratsawa da gilasai masu sheƙi da fitilun kristal, ta shinfida kayan karin kumallo a teburin girma croissant, omelette, lemo na orange sabo, da shayi mai madara. Komai cikin kayan fure masu kwantar da zuciya.
Yana saukowa daga sama cikin shigar white linen da agogon Rolex a hannu, ta tarbe shi da murmushi.
"Good morning Habibie… breakfast is ready."
Bai ce komai ba, amma ya zauna yana kallon girman kwazon da ta yi. Duk da jiya sun yi rigima, yau ta taso cikin salo da nuna kulawa irin wadda bata buƙatar magana.
Yana ci, ita kuma tana zaune kusa da shi, tana jiran ya gama. Bayan ya kammala, ya ɗan share bakinsa da tissue.
Bayan ya gama karin kumallo, Alhaji As’ad ya nufi gidan yayarsa, Mamy, domin da yamma zai tafi garinsu don wata muhimmiyar ganawa da Mai Martaba. Da ya isa, ya tarar da ita tana zaune a falo, abinci kala-kala a kan tebur ba sai an gaya maka ba, za ka gane gidan attajirai ne.
Fiddausi, wacce ke gefe tana zaune kamar tana jiransa, ce ta fara gaidasa da murya a sanyaye. Sai dai bai ma amsa ba, ya karkata ya gaida Mamy da girmamawa. Duk da cewa yayarsa ce, ba ita yake binta ba, amma akwai tarin girmamawa da mutunta juna a tsakaninsu.
Mamy ta kalleshi cike da kulawa, tace "As’ad, dan Allah kayi hakuri da halin Fiddausi. Kasan yarinya ce, tana cikin damuwa da matsalolin aurenta. Ko da ta gayamin matsalarta a waya, ni ce na bata shawarar taje ta same ka."
As’ad ya gyara zama, ya dan yi shiru na ɗan lokaci sannan yace da tsantsar takaici a muryarsa "Fiddausi ce yarinya? Mamy kema zaki biyewa Hajja kuna barin fitsararriya tana aikata abin da taga dama? Bari na gaya miki ko kallon banza kika yi wa matata, wallahi sai na dauki matakin da ba zai birgeki ba. Wannan mugun hali kike ɗauka kamar burgewa ne? Yar sarki ce? Mai kudi? To sai ki sani, kasa ce ƙarshenmu– babu daraja a hakan.
Maganar mijinta kuma, da kin san irin abubuwan da take masa, da kun tofa baki tuni. Ta hada kai da kawayen banza tana tozarta mijinta. Fiddausi ba ta da komai sai raini da wulakanci. Ba ta girmama mijinta, ba ta mutunta shi, balle ta sauke nauyin aure da ke kanta.
Ina gaya muku, mace idan ba ta bin mijinta ba wallahi sallarta da azuminta da hijjabinta, duka wuta ne a gaban Allah. Nagartar mace sharadinta shi ne ta bi mijinta.
Kuma Mamy wai har zagin iyayensa take yi? Wallahi Mamy, wannan ba daidai ba ne. Fiddausi, idan kina ganin abin da kike yi shine daidai, to bismillah ki fice daga gidan. Amma idan kina ganin zaki zauna kina kuntata masa, wanda yake ƙaunarki da gaske, to sai na gaya miki, duniya za ta juyo miki.”
Nana hadiza
***