Free chapter · Read without an account

38

by Kansa'u Bello · AMATURRAHAMAN

💞💞💞💞💞💞💞💞

AMATURRAHAMAN

*By*

OUM FATIMA

*(Hakimar D. A. W. A)*

💞💞💞💞💞💞💞💞

*DASHEN🌲ALLAH*

*WRITER'S📚ASSOCIATION*

*TEAM*

*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*

BOOK 1

PAGE 38

*بسم الله الر حمن الر حيم*

A ɓangaren Ango Abdulmajid da Iyayensa shirye-shiryen biki yayi nisa, domin kuwa sun shirya wa bikin kasancewar Abdulmajid shi zasu fara aurarwa a Familyn Abba gana.

Anisa kuwa ƙin shirya komai tayi saboda bata ƙaunar auren ko tunawa tayi a ranta wani da ban za'a aura mata ba wanda ta bawa duka zuciyarta ba sai taji baƙin ciki tamkar ta kashe kanta. Ƙwaƙw-ƙwaran kashedin da Dady yayi musu ne yasa Momynta ta saka mata ido ta hanata aikata ko wane irin kuskure.

Babu abinda ta shirya da kanta ko ankon ƙawaye su Haneen, Fatima, Najma da sauran ƴanmatan gidan sa'anninta sune suka fitar kuma suka tsara bridal shower iya na ƙawaye kuma suka yi rantsuwar zasu haɗata da Dady idan bata bada haɗin kai ba don ba zata saka suyi asarar shagali a bikin farko da za'a yi a sate ɗinsu ba. Haka dai aka fara gudanar da biki Amarya da Mahaifiyarta zuciyoyinsu ba daɗi ko kaɗan, don anfi ƙarfinsu ne kawai, Hajiya Sha'awanatu yaƙe kawai take yi a cikin mutane.

Ranar Laraba aka yi kunshin amare wanda amarya sai da Mammah tayi da gaske kafin ta fito aka yi mata, Alhamis kuwa ƴanmatan suka gudanar da bridal shower wanda yayi matuƙar ƙayatuwa. Ranar juma'a walima aka yi wacce duk ƴanmatan ne suka shirya.

A ranar juma'a da dare Zayyad ya sauka a gidan don sai da safe ma aka ganshi, Ammah kaɗai ya kira ya sanar da ita isowarsa don haka da kanta taje ta kai masa abinci. Da yake dama koda yaushe ana gyara ɓangaren nasa shi yasa babu wani gyara shiga kawai yayi, kasancewar baya son cin abu mai nauyi da dare shi yasa bai ci abincin ba ya zuba tea kawai ya haɗa da ƙananun cake guda biyu ya watsa ruwa ya kwanta.

★ Washe gari ƙarfe 8:00 na safe ya fito bayan yayi wanka ya saka ƙananan kaya ya nufi ɓangaren Ammah domin gaisheta. A can ya samu Muzaffar cikin shirin fita Office duk da kasancewar yau za'a ɗaura auren Anisa amma dole zai fita saboda suna da zama a Kotu a kan case ɗin da yake gudanarwa kuma dole ana buƙatar ya gabatar da gamsassun hujjoji wanda idan bai je ya kaisu ba za'a iya korar ƙarar tunda dama ɗan manya ne ya aikata ta'asar su kuma waɗanda aka zalunta talakawa ne.

Gaisawa suka yi cike da soyayyar da sukewa junansu a matsayinsu na ƴan'uwa jini ɗaya, suna ɗan taɓa hira Haneen na jere kayan break fast saboda zuwan Babban Yaya baya buƙatar masu aiki su taɓa abinda zai ci shi yasa Ammah da kanta take shiga kiching ita da Haneen suyi girkin ko baya nan ta saba da hakan. Masu aiki sai dai su taimaka musu da wasu abubuwan in sun kammala su gyara wurin sai kuma nasu da suke dafawa suda ma'aikatan ɓangaren Maza masu kula da harabar gidan shara, ban ruwan fulawa wanki da sauran aikace-aikacen gida.

Kasancewar Ammah keda Miji yau Dady a ɓangarenta zai yi break fast don haka suka yi mai yawa kala da ban da ban kowa yaci abinda yake buƙata. Sai da Haneen ta gama jere komai Ammah ta sauko cikin adonta taba baza ƙamshi, kun dai san Ammah ƴar gayu ce ta san martabar kula da kai da kuma mahimmancin ƙamshi. Don haka ko Haneen dake budurwa ita ke koyi da Ammah wurin ado da kwalliya, wannan na ɗaya daga cikin abinda ke ƙara danƙon ƙaunarta a zuciyar Mijinta ta zama ta musamman a garesa.

Da fara'a ta ƙaraso ta zauna tana kallon yaran nata cike da alfaharin kasancewarsu nata, gaisheta suka shiga yi cike da girmamawa tana amsa musu da sakewa tare da tambayarsu yanda suka kwana. Kallonta ta kai kan Zayyad da kansa ke ƙasa yana dannan wayar tasa ta fama da bata hutawa matuƙar yana zaune. Kanta ta ɗauke cike da kawaici irin wanda akewa ɗan fari tace. "Yaya gajiyar hanya?." Ajiye wayar yayi saman table ya ɗago yana kallon Mahaifiyarsa cike da ƙaunarta yace.

"Alhamdulillah Ammah, na same ku lafiya?."

"Lafiya lau Alhamdulillah." Ta faɗa. Daga haka hirar ta tsaya saboda babu sakewar yin doguwar magana a tsakaninsu saboda tun farko Ammah tana nuna masa kawaici a matsayin sa na ɗan fari, da yake dama shi ɗin ba mai yawan magana bane don in kaji yayi magana mai ɗan tsawo to da Hajiya Iya ne data san yanda zata saka shi ya magantu wasu lokutan ko kuma Baba Alhaji sai Uncle Maina musamman akan abinda ya shafi aikinsu.

"Kinga Auta ni dai ki sallame ni don na kusa makara." Muzaffar ya faɗa yana duban tsadajjen agogon hannunsa. Kallon zuwa ina Zayyad yayi masa yace. "Ina da zama a Kotu ne Akhi amma zanyi ƙoƙarin dawowa kafin ƙarfe 1 in sha Allah in halacci ɗaurin auren. Kai kawai ya gyaɗa masa ba tare daya yi magana ba.

Zuba masa Haneen ta fara yi Abba ya shigo palon da sallama idanunsa akan Zinariyarsa wacce yana sanyo kai haskenta ya fara gani. Tashi Ammah tayi fuskarta ɗauke da murmushi ta tare shi tare dayi masa sannu da zuwa kafin tayi masa jagora zuwa table. Cike da sha'awa yaransu ke binsu da kallo suna mamakin yanda soyayyar Iyayen nasu bata tsufa sannan kuma basa iya ɓoyeta ko a gaban waye wanda hakan ke ƙara haddasa ƙiyayyar Ammah a zuciyar abokiyar zamanta.

Gaba ɗaya suka haɗa baki wurin gaishe da Mahaifinsu ya amasa musu da fara'a yana tambayar Zayyad saukar yaushe. "Da dare na iso jiyan Abba." Ya bashi amsa cike da girmamawa, Ammah da kanta tayi serving ɗin Mijinta yana saka mata albarka, Haneen kuwa ta zubawa yayunta har da Ammah ɗin sannan ta zubawa kanta.

Abincinsu suka fara ci cike da natsuwa baka jin motsin komai sai ƙaran spoon da plate. Muzaffar shi ya fara kammalawa ya mike yana yi musu sallama ya wuce bayan ya sanar da Yayansa idan ya dawo za suyi magana. Kai kawai ya gyaɗa masa ya wuce.

Bayan sun kammala Zayyad ya fice domin gaishe da mutanen gidan, Haneen ma bayan ta gyara wurin da suka gama ficewa tayi zuwa inda ƴanmatan ke yini a ɓangaren Uncle Yusuf aka bar Ammah da Mijinta suna zantawa.

Kai tsaye ɓangarean Baba Alhaji inda yaci karo da Zaheera taci uban ado tana zaune a parlon Hajiya Iya ta kasa ta tsare saboda sanin da tayi cewar tabbas zai shigo. Tun da safe ta samu labarin dawowar tasa a bakin ƙanwarta Fatima wacce itama a wurin Haneen taji cewar ya dawo ɗin.

Don haka ta cancaɗa kwalliya sai zuba ƙamshi take ta nufin ɓangaren Hajiya Iya tana dakon shigowarsa, da itan kuwa ya fara cin karo lokacin daya shiga Palon. Kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kansa ya samu wuri ya zauna yana duba abu a wayarsa Hajiya Iya ta sauko. "Soja marmari daga nesa, yaushe a gari inji maƙi baƙo?." Hajiya Iya ta faɗa.

"Da dare na shigo." Ya faɗa cikin natsuwarsa kafin ya fara gaisheta, har da duƙawa ƙasa Zaheera tayi ta fara gaishe sa cike da iyayi tana son jan hankalnsa gareta. Ko kallon inda take bai yi ba ya ɗaga mata hannu kawai yaci gaba da abinda yake yi, wasu hawayen baƙin ciki ne suka ciko mata ido domin duk lokacin da ta ɓata wurin tsara kwalliya ya tashi a banza tunda bai ko kallaba bare ya gani. Sauko mata hawayen suka shiga yi lokacin da ta janye idonta daga hanyar daya gama haurawa zuwa ɗakin Baba Alhaji.

"Allah ya kyauta." Hajiya Iya da taga duk abinda tayi ta faɗa tana wucewa zuwa uzurin daya sauko da ita. Ƙin tafiya tayi tace har sai ya sauko ya kalleta kafin ta samu natsuwa. Tana nan zaune Mammah ta sauko daga saman itama a shirye tsaf don zuwa ɓangaren da ake bikin. "Ke kuma me kike a nan baki je wurin ƴanmatan ba?." Mammah ta faɗa tana kallon Zaheera.

"Wurinsu kuma Mammah, sai kace wasu sa'o'i na." Zaheera ta faɗa tana tura baki gaba.

"Ikon Allah!". Mammah ta faɗa tana riƙe baki. Suna a haka Zayyad ya sauko saboda ya samu Baba Alhajin ya koma bacci don haka ya bari zuwa jimawa sa gaisa. Kallonsa Mammah tayi ta kalli Zaheera dake ƙara gyara zaman rigarta, murmushi tayi tana gane dalilin zamanta a wurin don matuƙar ba Zayyad ɗin bane a gari to bata cika zuwa ɓangaren nasu ba, saboda basa Shiri da Hajiya Iya da bata ɗaukar iskancin Zaheerar, ita kuma bata son a faɗa mata gaskiya.

Zama yayi a kujerar dake kusa da Mammah ya shiga gaisheta cike da girmamawa domin kuwa akwai shaƙuwa a tsakaninsu saboda, da ita aka yi rainon sa a wurin Baba Alhaji. Zaheera dake kujerar dake fuskantar sa sai ta samu damar da take ƙare masa kallo son ranta. Sosai taga ya ƙara sauyawa ya ƙara zama babban mutum kwarjini da kamala na tattare dashi, sannan hutu, jin daɗi da kwanciyar hankali sun nuna sosai a jikinsa.

Kullum idan ta ganshi gani take yi tamkar ƙara masa kyau da cika ido ake yi, suna haka Hajiya Iya ta fito daga kiching riƙe da babban tire wanda ta shiryo break fast ɗin Baba Alhaji a kai. Tayin abincin ta yiwa Zayyad ɗin yace mata yayi break fast a wurin Ammah. Miƙewa yayi suka fice tare da Mammah zuwa ɓangaren Uncle Maina domin ganawa da shi.

A general parlor suka samu Hajiya Sha'awanatu da wasu daga cikin ƴan'uwanta sai Anisa dake kwance saman cinyarta suna faman rarrashin ta. Wani irin zillo zuciyar Anisa tayi daga ƙirjinta jin muryar Zayyad ɗin yayi sallama a palon, wani irin zabura tayi ta tashi zaune ta zuba masa ido hawaye masu zafi na zubo mata a saman fuskarta. Zayyad da bai san tana yiba zama yayi ya shiga gaishesu cikin natsuwa ba tare daya kalli kowa dake cikin palon ba.

Cike da yaƙe Momy take amsa wa domin itama zuciyar tata ba daɗi, bai wani jima ba yayi musu sallama ya nufi ɗakin Uncle Maina bayan ya yiwa Amarya kyautar manyan kuɗaɗen da suka gigita mutanen palon gaba ɗaya, kuka Anisa ta fashe da shi saboda tunanin ita ya kamata ta mallake shi shida abinda ya mallaka ɗin gaba ɗaya. Momy ma abinda ke zuciyarta kenan ganin irin asarar da Dadynsu ke ƙoƙarin janyo musu.

Shi dai wucewa yayi abinsa ya nufi ɗakin Uncle Maina ya gaishe shi shima ya bashi manyan kuɗi a matsayin gudunmawa bayan ya ɗauki nauyin duk abinda ake buƙata na kayan ɗaki. Sosai Dadyn yayi godiya ya saka masa albarka domin yaji daɗi sosai duk da shima yana da nasa arziƙin. Sallama yayi masa akan zai je ya huta kafin lokacin ɗaurin auren yayi.

Sauran sassan ya shiga ya gaishe su kafin ya dawo, a hanya suka haɗu da Sageer ɗan Uncle Yusuf da Muhsin ɗan wajen Barrister Kabir da suka dawo suma daga wurin aikinsu domin halartar ɗaurin auren. Tsayawa yayi suka gaisa cike da mutunta juna musamman Muhsin da tasu tazo ɗaya da Zayyad ɗin, shi dai a rayuwa Yaya Zayyad ɗin yana matuƙar burge shi, ɗabi'unsa da kuma yanayin mua'amalarsa harda life style ɗinsa da komai nasa yana burge sa don haka yake matuƙar girmama shi.

Ɓangarensa ya ƙarasa ya kwanta domin ya ɗan huta kafin lokacin ɗaurin auren yayi.......

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.