Free chapter · Read without an account

Chapter 10

by JamilaUmarJanafty · TURKEN GIDA.

TURKEN GIDA.

Wattpad:Jamilaumar315

Arewabooks:Jamilaumarjanafty

SSADAUKARWA GA BARRISTER SALAMATU DOMA(MOMMY)

🅿️10

Tun da na tashi da safe na fara tunanin wani abinci zan dafa na kai ma Alhajinmu. Gashi kayan abincin mu duk sun ƙare kuma Yallaɓai har yanzu bai ce mini komai ba. Da safe ma Tea muka sha shima kayan tea ɗin saboda ya na yawan siyan shi ne ba sai ya ƙare ba shi ya sa shi ya kan zama na ƙarshen ƙarewa.

  Na daɗe ina tunanin abin da zan yi. Kafin na tsaida shawara yin tuwon shinkafa miyar agushi tunda shinkafar tuwon kaɗai gare ni. Sannan ina da kayan miya nikaƙƙe a frizer sauran kayan cefanen ba zai gagara ba. Tun safe na kira wayar Ya Auwal mun yi mgana ya ce sun je ma asibitin sun duba Alhaji da safe jikin sa da sauƙi ya na ta barci sun ɗan dawo gida su karya ne sannan su koma  ni ma na ce in na gama abin da na ke yi zamu zo asibiti tare da Yallaɓai in sha Allahu.

Yana falon farko ya na aiki na je na same shi na faɗa masa ina so zan yi ma Alhajinmu girki in za mu je mu tafin mai dashi.

"Me za ki dafa masa?

Ya faɗa ya na ture takardan gabansa lokaci ɗaya yana kallona.

Kai na rausaya kafin na ce" Tuwo zan yi masa miyar agushi. ".

Kai ya jinjina mini kafin ya ce" Kina buƙatar wani abu ne?

Kai na gyaɗa kafin na ce"E. Ina son Nama da ganda. Sai ganyen Ogun ina da sauran stock fish da agushi ɗin."

   Sai ya gyaɗa min kai kafin ya ce" Shike nan. Zan yi ma Musbahu waya sai ya siyo ya taho dashi."

Duƙawa na yi na sumbaci bakinsa kafin na miƙe ina faɗin" A huta lafiya Yallaɓai na."

Kai ya jinjina min yana ɗan mirmishi fita na yi daga falon bayan na rufe masa ƙofar saboda zane ya ke yi ba ya son hayaniya ɗakin su jidda na shiga ba hasken sai da na kunna dukkansu suna kwance suna barci ga darduman da suka yi salla nan da azkar din su ko kwashewa Jidda ba su yi ba ban tashe su ganin yau asabar kuma suna hutun Tahfeez ya kamata su huta tattara kayan na yi na maida shi a muhallin shi sannan na gyara ma Baby kwanciya ita kuma Jidda na zare mata Hijabin jikinta ganin da shi ta kwanta. Sake kashe musu hasken ɗakin na yi bayan na rage musu iskar fankar a hankali na rufe ƙofar kar ƙara ya tashe su.

  Tuwon na kunna gas na fara ɗorawa. Saboda ina so mu fita da wuri duk da za mu fara biyawa ta Gwammaja mu kai su Jidda sannan mu wuce asibitin. Ɗaki na koma ina gyarawa saboda Yallaɓai ya ce na haɗa kayanmu waje ɗaya mai wanki zai zo ya ɗauka sai na firfito da kayan ina haɗawa. Ni kaya ba su da yawa atamfofi ne da lesuna ƙananun kayana ni na ke wanke su da kaina in na samu lokaci tare da unders ɗin Yallaɓai na na yara kuma ba su taru ba ko sati biyu ba a yi da kawo musu wanki ba.

Bayan na gama haɗa kayan na saka su cikin ghana must go ɗin da daman saboda kai wanki ne in kuma za a dawo dasu a ciki ne a goge. Gyara ɗakin na fara saboda ya ɗan yi ƙura, sai na fara tunanin unders ɗin Yallaɓai duk sun yi datti ya kamata na wanke masa. Amman sai na duba ya na da sauran wankakku zan bari in Alhajinmu ya koma gida ya samu natsuwa sai na yi mana wankin. Allah ya sa ma ya na da su da yawa tun da in na samu kuɗi ina siyan masa da turaruruka in yi masa kyauta a matsayinsa na mijina.

   Ban ma gama gyaran ɗakin ba na koma kitchen na wanke shinkafar na saka kafin ma ya tafasa saboda in ya jiƙu ya fi danƙo. Ƙara komawa ɗakin na yi na gama gyaran na ɗauko abin shara na share sannan na ɗauko towel ɗin goge na gege madubi da jikin wardrope ɗina tunda ya na da glass. Sai kawai na ji yau gwara na yi aikin gidan tunda ba ma nan kar na ba ma Saude wahala tuna haka ya sa na ɗau waya na kira Sauden tun da ni na siya mata wayar saboda matsala irin haka bayan mun gaisa na ce yau ta yi zamanta ba sai ta zo ba sai ta ce mini toh.

  Ina tuwona ina aikina. Ban share falon farko ba saboda Yallaɓai na aiki amman gabaɗaya na share gidan na yi mopping sannan na turare gidan da turaren wuta na kajiji a burner.

Kitchen kuma ma bari sai na gama girki gabaɗaya. Sai da na tuƙa tuwon sannan Jidda ta taso ta na murza ido ta ganni ina fito da sabbin kolilina in da zan saka abincin.

"Ina kwana Umma."

Na waiwayo ina faɗin" Lafiya lau jidda. Ina Baby ba ta tashi ba ne?

Ta na murza ido ta ce" Ta na wajen Abba"

Sai na gyaɗa kai ina faɗin" Akwai ruwan zafi a flasks a saman dining ni da Abbanku mun ƙarya. "

Ta na kallona ta ce" Umma ba ki tashe mu ba to?

Ina kai kololin wajen sink ina faɗin" Na ga yau weekend sai na barku ku huta. In kun gama karyawan ki yi ma Baby wanka tare za mu fita. Gwammaja za mu kai ku ku zauna har dare."

"Umma ya jikin Alhaji?

Na ce mata da sauƙi ina ƙokarin fara wanke kololin sai ta ce in kawo kallonta na yi ina faɗin" Ki je ku karya. In gama aikin sai ki wanke sauran ki gyara mini kitchen ɗin" sai ta amsa da toh sannan ta wuce. Ni kuma bayan na wanke su na saka Towel na goge su tas sannan na kwashe tuwon a leda na ƙulla. Wajen guda goma na saka a kula sauran kuma guda huɗu na bar mana a gida in mun dawo mu ci ban ɗora miyan ba tunda har lokacin musabahu bai zo ba.

  Ban ko kai ga barin kitchen ɗin ba sai ga Jidda da leda ta kawo min ina karɓa na kalle ta ina faɗin" Uncle Musbahu ya zo ne?

Sai ta gyaɗa min kai. Ijiye ledan na yi na koma ɗaki na sako hijabin na fito falo in da suke da Yallaɓai muka gaisa.

"Anty Sadiya ya jikin Alhaji? Yallabai ke faɗa min bai ji daɗi ba?

Sai na amsa masa shi kuma sai ya yi masa fatan samun sauƙi na amsa da Amin Amin nan falon na bar su na koma ciki Ina ce ma Jidda in sun gama karyawan ta gyara ɗakin su kafin ta yi ma Baby wanka.

   Da ya ke miyar ba ta da yawa sosai ba ta ɗau lokaci ba tunda agushin ma soya shi kawai na yi. Naman kuma na rago ne akwai ƙashi ƙashi a jiki sai da na tafasa sannan na yi amfani dashi kafin ka ce me gida ya ɗau kamshi miya. Na gama ɗiban ma Alhajinmu miya na saka a kula har na haɗa shi cikin kwandon da za mu tafi dashi sai ga Yallaɓai ya shigo kitchen ɗin.

"Ni fa an gama cika mini ciki da ƙamshi. Me muka samu ne?

Ya faɗa ya na tsaye a ƙofar kitchen ɗin. Kallonsa na yi kafin na juya ina goge jikin gas ɗin da miya ya ɗan ɓata.  Mirmishi na yi kafin na ce"Sai anjuma za ka ci na ka fa Yallaɓai."

Koƙarin shigowa ya ke yi na wurgar da abin hannuna na nufe shi ina turashi waje lokaci ɗaya ina faɗin" Mu je ka yi wanka lokaci na tafiya."

  Ba shi da mafita haka na riƙa tura shi har cikin bedroom ɗin mu. Takardun hannunsa na karɓe ina faɗin" Mai wankin bai zo ba?

Ya na saɓule dogon wandom jikinsa ya ce"Sakarai ne. Na fa kira shi ya riƙa ce mini yana hanya amman sama da awa ɗaya bai zo ba"

Ina dariya na ce"Kai da Sabitu ba" saboda suna shan dirama shi Sabitu karya da saɓa alƙwari shi kuma Yallaɓai ba ya son mutum mai ƙarya da saɓa alƙwari. Su yi ta samun matsala kuma ko ya ce ba zai ƙara bashi wanki ba sai Sabitu ya yi ta magiya domin ya na samun alheri a wajen Yallaɓai.

Cikin side drower na ijiye masa takardunsa ina juyowa muka ci karo da Yallaɓai fuska na kwabe kafin in yi mgana ya rumgumeni ni kuma ina ture sa na ce"Ban yi wanka ba Yallaɓai."

  "Nima ai ban yi ba. Kawai yau mu bar ta ranar tsami na duniya ne."

  Ina dariya na rumgume shi ta baya ina ɗan dukan bayan shi mun daɗe a haka kafin mu saki juna hammatar shi na ɗaga tunda bashi da riga ina rufe baki kafin na ce"Yallaɓai na na bukatar shaving gaskiya."

  Hannuwansa ya ijiye saman kafaɗata yana faɗin" Sadiya ta sangarta Yallaɓanta. Ki zo kawai ki yi aikin ki Madame.'"

Dafa kafaɗansa na yi shima ya dafani muka fara tafiya ina faɗin" Muje Tiolet na gyara mijina."

Kallona ya yi ƙasa ƙasa kafin ya ce"To wai da na ce ko ni na fara gyara ki anan ne a ciki kuma ke sai ki gyara ni?

Ina jin haka na sake shi na yi gaba ina faɗin" bar shi kawai. Na gode Cafinter"

  Sai ya biyo ni yana dariya har ya na cewa" Wai kada mu yi ta asaran ruwa. Gwara mu haɗa aikin."

Ko juyawa ban yi ba na buɗe kofar tiolet na shiga bayan na yi addu'a shima sai ya biyo bayana zai shigo na ce" Yallaɓai addu'ar fa"

Sai ya koma da sauri ya yi sannan ya shigo ya maida ƙofa ya rufe zai yi mgana na masa alama da bakina na ja zif alamun ya yi shuru sai shima ya yi haka alamun ya kama bakin shi mirmishi na yi masa kawai Towel na zaro daga hanger dake sama na mika masa sai ya karɓa ya juya yazare gajeren wandon da ke jikinsa ya ɗaura towel ni kuma sai na ciro veet din a saman wajen ɗan dirowan ajiye su kayan wanka a cikin sink na ce ya shiga ya zauna kamar dai yadda muka saba.

  Ni na shafa masa a ƙasan sa da hammatarsa sannan bayan minti biyar ya yi na kwashe na goge wajen sannan na wanke masa. Tare muka yi wanka ranar bayan na chuɗasa nima sai ya chuɗani muna yi muna ɗan wasannin mu da muka saba cike da so da ƙauna muka fito dukkanmu ɗaure towel shi a kugunsa ni kuma asaman ƙirjina.

  Yallaɓai na fara tayawa ya shirya cikin shadda mai ruwan ƙasa domin ya ce min suna da ɗaure aure na wani abokinsu da suka yi secondary tare zai ƙara aure.

Ina saka masa link ina faɗin" Har da Uncle Abba zai zo daurin auran?

"E. Har da ma Tariq. Muhammad Bello ai ajin su ɗaya ma da Tariq lokacin muna makaranta."

  Sai na jinjina kai kafin na ce"Abokan ku sun fara biyu kuma kuna hanya kenan"

Ya na yar dariya ya ce"Wasu ma ko ɗayan ba su ijiye ba. Irin su kawu ba. Da wani Salihu bala wallahi sun zame mana tazuran kawai. Yau ina ga yau sai sun sha caccaka tun da kaf mate ɗin mu za su zo wajen ɗaurin auran nan "

Ina dariya na ce"Kar a taɓa min kawunaa. Ina nan ina nema masa mata."

Yallaɓai na kallona ya ce"Allah ya sa kar kawun naki ya baki kunya. Tun da kika har Nene ta ƙyale Abba da mganar aure kin san lamarin ya fi karfin kowa"

"Bai fi ƙarfin Allah ba. Muna addu'a in sha Allahu in lokaci ya yi zai yi."

Sai ya amsa min da cewa" Allah ya sa muna da rabon gani." Agogo na ɗauko masa wani ɓaki na fatar damisa na saka masa.

Turare na fesa masa sannan ya ce na zaba masa takalmin da zai saka. Wani baƙin takalmi na zaɓar masa ni na siya masa kwanki lokacin ina da ɗan kuɗina na ga wata mate ɗina a BUK na tallarsu suka yi mini kyau na ce ina so 18k na siye shi Yallaɓai na son takalmin nan fiye da sauran takalmansa duk da ya na ma cikin masu saukin kuɗi amman saboda ni ce na yi masa kyautarsa ya sa ya ke ji da shi.

Sai da na gama shirya shi tsaɓ sannan nima na ce ya ta ya ni zaɓan kayan da zan saka. Mun daɗe gaban wardrop duk wanda na nuna sai ya ce a'a. Daga karshe dai ya tsaya kan wata super shi ya siya mini ita mai kalan green na ciro ta ina faɗin" Amman Yallaɓai mayafi zan saka ko?

Hararata ya yi kafin ya ce" Asibiti gidan biki ne?

Na marairaice ina faɗin" Don Allah fa. Atamfar nan ba ta kyau da Hijabi."

  Jan gefen hannun rigansa na ke yi sai ya kalleni sai na marairaice ina faɗin" Haba My Yallaɓai na. "

Wani kallo ya yi mini kafin ya duƙa ya na faɗin" In kin yarda mu sabunta wanka."

Da sauri na ce" Bar shi na saka Hijabin."

Na faɗa ina tura baki shi kuma yana mini dariya.

Haɗe rai na yi ina faɗin" Ni ko? Ni ko ai shike nan."

Sai ya ce to na saka mayafin amman sai na yi alƙwarin amjuna akwai ɓarnan ruwa ya na iya sai na ce na yarda sannan ya bari na ɗauko mayafin kayan takalmi ma shi ya zaɓa min wani flat mai ruwan ƙasa irin kayan shi ya na da jaka sai na ɗauki jakar ina jin Yallaɓai na faɗin" Wai ko dai ba Alhaji za ki je gaisarwa ba. Biki za ki je?

  Ina dariya na ce" Kai Yallaɓai na. Wani biki kuma! Jinya zan je."

"To ma su jinya."

Share shi kawai na yi domin na san yanzu in na yi magana sai ya iya ɓata mini shiri shi ya sa na yi shuru ina bin sa da mirmishi.

Muna nan sai ga Sabitu ya kira ya ce ya na waje sai ya ɗau kayan ya fita dashi ni kuma fita zuwa ɗakin su Jidda na ga sun shirya dogayen riguna suka saka na Abaya saboda halin Yallaɓai na ce su cire mayafan su saka Hijabi yanzu nan zai ce yara ma ƙanana ina koya musu saka mayafi. Yallaɓai ba wai yana da tsanani ba ne amman fa ya na da saka ido kan iyalansa. Wani lokaci zai yi mini tsanani wani lokacin kuma sauƙin kanshi har ya na yi mini yawa.

  Jidda na ce ta ɗau kwandon abinci zuwa mota ni kuma na koma ciki ina fesa turare. Har na ɗan fesa kaɗan sai na tuna da Yallaɓai yanzu raina zai ɓaci. Da sauri na ijiye na koma ina shinshina kaina in ƙamshin ya fito na shiga uku da faɗan Yallaɓai.

Hon kawai ya yi ta mini daga haraba ni kuma sai da na kashe duka wutar gidan sannan na fito na kulle ƙofar falo.

Su Jidda na gidan baya ya na hira da su ina buɗe gaban mota na shiga ya juya ya na kallona kafin ya ce" Alhaji ki ka fesa ma turare ko likitocin ?

Ya faɗa cikin haɗe rai. Da sauri na ce" A'a. Turaren kayan ne ina ga."

Ƙura mini ido ya yi da sauri na ce" Da gaske ban fesa turare ba."

Bai ce mini komai ba ya yi ma motar key sai na koma na jingina da kujeren mota ina maida numfashi. Mun ɗau hanya na ji ya na faɗin" Mu fara zuwa asibiti in na duba Alhaji sai na kai su gwammaja ɗin"

Ni dai na amsa masa domin na ga ya wani haɗe rai ne.

Mun isa asibitin wajen sha ɗaya saura ne. Amman na iske har Ma'u ta zo ni da Rahila ne kawai ba mu iso ba amman har su Yaya Auwal da matansu da Amina ma ta iso daga kaduna. Mun gaggaisa da su har da Yaya Murja Baaba ta na nan ita da Gwaggo suma na gaishe su Baaba a dakune ta amsa ban damu ba. Yallaɓai kuma ya fara musabaha da mazan matan ma suka gaisa ga duka har ƙasa ya gaida Gwaggo da Baaba.

Ma'u har da cewa" Yallaɓai barka da safiya.'

Ya juya suna gaisawa su Jidda ma suka bi kowa ɗaya ɗaya suka gaishe su. Suna waje Alhaji na ciki ya na barci Yallaɓai ne ya shiga tare da su Jidda. Ba daɗewa ya fito ya ce za su tafi ni na raka shi har bakin mota muka rabu akan cewa sai anjuma za su zo tare da su kawu ina ɗaga musu hannu suka bar haraban asibitin Baby sarkin rigima jin wajen Nene za a kaita sai ta fara murna.

Abincin da na zo da shi Gwaggo na ba ta karɓa ta na ta saka albarka.

"Ba wacce ta zo hannu rabbana. Yadda kuke jin ƙan mu kuma Allah ya jiƙan ku wata rana."

Aka amsa da Amin Amin Baaba ta na ta wani taɓe ba ki ni ko ba ta isheni kallo ba

Mun gaisa da Ma'u da tambaya ya jiki daga nan na karisa saman darduman da Amina ke zaune ita da Laila da Khaleesat suna hira.  Sai bayan na natsa ne na tambayi Baba Aminu aka ce ya koma tun safe Baba Sani kuma ya koma gida ya huta sai anjuma zai dawo.

Na kira wayar Rahila ta ce min ga su nan a kan hanya ba daɗewa ta iso itama da kwandon abincin ta.

Kowa da wanda ya saba dashi ya zauna su Yaya Murja yan wajen Ma'u suna zaune waje ɗaya har da Zaitunan Yaya Abubakar. Yaya Aina ce ma ta ɗan zauna a wajen Rahila kuma daman kowa ya san kaf gidanmu na fi shaƙuwa da ita shi ya sa ko an gamu tare muna hira ba wanda zai bi ta kai.

 

  Muna nan har bayan azahar Laila Yaya Auwal ya ɗauke ta zuwa gidan su. Alhaji ya farka wajajen biyu duk mun shiga mun gaishe shi da jiki ya ce ya ji sauƙi yau ma ya ce likita ya sallame shi.

  Yaya Hamza ya ce ya bari ko zuwa gobe in ya ƙara jin sauƙi.

Baaba na gefe ta ce"Gaskiyar Hamza ka ƙara kwana ka samu hutu sosai Yaya Sule."

Shi dai Alhaji an fi ƙarfinsa kawai ne kawai shi ya sa ya yi shuru. Sai ya koma ya kishigiɗa bayan Gwaggo ta kara mai filo

"Yara nan fa duk sun taho maka da abinci me za ka ci?

Gwaggo ta faɗa ta na kallon shi.

"Allah ya saka muku da alheri. Allah ya yi musu albarka na gode."

Dukkanmu muka amsa da Amin Amin

Abincin ya ce sai anjuma amma ya sha ruwa. Ni ya kallah kafin ya ce"Dubu yau ke kaɗai kika zo? Ina kika baro min uwargidana Hauwa'u?

Ina dariya na ce"Ta zo ka na barci Alhajinmu. Yallaɓai ma ya zo amma anjuma zai dawo in sha Allahu."

Sai ya jinjina kai kafin ya kalli Ma'u ya na faɗin" Asma'u ki yi ma megidanki godiya maimuna ta faɗa mini bai bar yaran nan sun kashe komai ba. Allah ya ƙara ma arziƙin sa albarka Amin."

Ma'u ta amsa da Amin Baaba har ta amsawa da Amin Amin da karfi na kalle ta lokaci ɗaya ina taɓe baki. Ba mu daɗe a dakin ba muka fita waje saboda dokar likita. Muna asibitin nan har la'asar sai ga kiran Hauwa ta na ce min ga su a asibitin ita da Mutaƙƙa ina ne barayin ɗakin da aka kwantar da Alhajin? Ina jin haka ni na fita haraban asibitin na taho da su.

   Shi ya sa na ke son Hauwa in dai abu ya same ni ita ke fara zuwa ta yi mini jaje ko murna ita da mijinta. Mutaƙƙa ya shiga ya gaida Alhaji duk da ba lokacin dubiya ba ne na faɗa ma Alhaji ƙanin mijina ne ya na ta saka albarka. Mutaƙƙa ya zo da kayan marmari Hauwa kuma har abinci ta zo dashi kuma nan ya bar min ita karfe shidda ya ce ta koma gida. Na ji daɗi matuka ko da ganin sauran yan'uwana dangin mazajensu na ta zuwa gaida Alhaji. Ma'u har uwargidanta Hajiya Zainab ta zo da sauran ƙanensa.

  Hauwa ta zo ba daɗewa sai ga Anty Bahijja ni na yi mamakin ganinta har a cikin zuciyata na san ba domin ni ta zo ba illai Ma'u ce ta je ta taro ta. Hauwa ta saki baki ta na kallon su har da rumgume juna muna ji ta na faɗa ma Baaba matar Yayan mahaifiyar Alhaji Mustspha ne. Sai ta ɗago ta ga ina kallonta sannan ta ce"Kuma Yayar mijin Sadiya ne.".

  Gwaggo na ta saka albarka da godiya ina ji Ma'u ta nuna Baaba ta na faɗin ga mahaifiyarta. Anty Bahijja har ƙasa ta duka suna gaisawa Rahila na in da muke Khaleesat ta shiga cikin gari gidan ƙanwarta Anty Aina ma ta koma gida Amina ma ta je gida ta huta. Yaya Murja ma dazu ta koma mu da Yaya Balki ne kawai mu ke asibitin.

Daga zaunen da na ke na gaisar da Anty Bahijja sai lokacin ta kallemu ni da Hauwa.

"To su Hauwa ashe a nan nan?

Cikin rawan jiki ta ce" E. Ban daɗe da zuwa ba. Tare da Baban Sahla mu ke ya kawo ni sai ya wuce."

Sai kawai ta wuce tana faɗin" Hakan na da kyau."

Shiga ciki ta yi Ma'u na gefenta domin ta duba Alhaji.

Sai da ta shige ne sannan Hauwa ta kalleni nima sai na kalleta amman ba mu yi mgana ba muna nan zaune ta fito har ta na ba ma Gwaggo 10k. Wai sai ga Ma'u ta juyo ta na ce min" Sadiya kalli Anty  Bahijja da ɗawaniya."

  Mirmishi na yi kafin na ce" Allah ya ba da lada."

Ma'u ce za ta rakata ni dai ko kafata ban ɗaga daga daga na ke zaune ba.

Sai ta juya ta na kallon Hauwa kafin ta ce" Yanzu za ki tafi gida na yi miki lift?

Da sauri na ce"Mutaƙƙa karfe shidda ya ce ta koma gidan"

Sai ta wani kalleni kafin ta ce" Ya yi. Allah ya ƙara lafiya."

Na amsa mata da Amin Amin har da Baaba a masu rako. Sai da suka bar wajen Rahila ta kalleni kafin ta ce" Ku ba ku yi rakon ba Sadiya"

Kai tsaye na ce" Saboda mene! Ai ni ba na neman suna. Wacce ta zo domin ta ba ki ga har da uwarta arakon ba?

Sai Rahila ta kasa mgana. Saboda ta san halina ta na ƙara mgana zan saki wata mgana kuma ga Hauwa a wajen sai ta tashi tsam da goyon yarta ta wuce wajen Gwaggo itama na rakata da harara.

  Hauwa ce ta kalleni cikin mamaki kafin ta ce" Wai ya kuke da Ma'un nan ne Anty Sadiya?.

Kai tsaye na ce" Ina wanan tsohuwar da kika ga sun fita tare? Sai ta ɗaga mini kai. Kau tsaye na ce" Ita ce mamanta. Ita ɗin Baabar mu ce ƙanwar Alhajinmu ce da suka haɗa uwa ɗaya uba ɗaya."

  Sai ta jinjina kai ni kuma sai na ƙara mata da cewa" Baban Ma'u ya rasu tun tana ƙarama sai da Baaba ta yi wani auran Alhajinmu ya ɗauketa shi ya sa ta tashi a gidanmu."

Hauwa ta yi sakate kafin ta ce" Ikon Allah."

Sai na kalli Hauwa domin na san akwai mgana a bakinta.

Cikin sauri na ce"Me kika gani hala! Ko na ce kin ji wani abu ne a kaina daga bakin ta?

Shuru ta yi ni kuma da sauri na ce" Don Allah ki faɗa mini Hauwa. Ba lalle kin san ba shiri tsakanina da Ma'u ba kina gani da idon ki yadda take shigema Anty Bahijja kuma dalilina ne tunda ai ba Musbahu ta ke aure ba. Balle kusan ta yi musu yawa haka."

  Ƙasa ƙasa Hauwa ta ce" Ranar sunan Halima na ji suna mganarki."

Sai na yi kwafa kafin na ce" Ai ba za ta sauya ba. Munafuka ce makira."

Sai Hauwa ta riƙe min hannu tana faɗin" Ta so mu je ki ji wata mgana"

Barayin muka bari gabaɗaya mun haɗu da su Ma'u a hanya za su dawo. Har ta na ce mini Hauwa za ta tafi ne na ce mata a'a da gayya na ce mata za mu yi mgana ne ina gani ta yi tsam daga ita har uwarta ni ko na ja Hauwa muka wuce abin mu.

  Can haraba muka fita a babban falo muka samu kujeru muka zauna ina mai kallon Hauwa na ce"Me kika ji munafukar ta ce akaina?

Hauwa ta ce" Ni fa ina ta mamaki na san ƴar uwanki ce amman me ya sa za ta biye ma su Anty Bahijja suna kushe ki?

  Raina har ya fara ɓaci da sauri na ce"Me ta ce wai?

Hauwa tasauke numfashi kafin ta ce" ita da Anty Bahijja da wata ban san ta ba tare da Ma'un suka zo."

Kai tsaye na ce" Shema' u ce ƙawarta ce."

Hauwa ta cigaba da faɗin" da Anty Maimuna ma awajen ana mganar haihuwa Anty Bahijja na ta faɗan wai kamar Tafida zai ƙare rayuwa da ƴaƴa biyu. "Buɗe bakinta sai cewa ta yi" wai daman tun farko ke ba ki da burin tara ƴa'ƴa da yawa. "

  Ido na har wani ƙyalli bala'i ya haska a fusace na ce" Ita Ma'un ta ce haka don ubanta?

Da sauri Hauwa ta ce" Ni fa ba na faɗa miki saboda na haɗa faɗa ba ne. Na gaya miki ne saboda ki sani ne"

  Ina sassauta fushina kafin na ce" Ba zan yi ba Hauwa."

Kallona ta yi kafin ta ce" Kin tabbatar? Sai na gyaɗa mata kai sai ita kuma ta gyara zama ta cigaba da faɗin" Ita fa Ma'un ta ce haka aiko Anty Maimuna ta ce ba ki isa ba kin auri ɗan dangi saboda haka in ke baki son haihuwa za su aura masa wacce za ta zo ta cika masa gida da ƴa'ƴa."

Idanuwana har sun tara ƙwallah zuciyata na zafi. Na kalli Hauwa kafin na ce" Ban yi mamaki ba. Tun zuwan Ma'u gidanmu na san ita din ba alheri ba ce. Na kuna san watan wata rana sai ta zame mini matsala da damuwa. Amman ta je Allah ya fita ni dai ban taɓa bin ta da sharri ba in tana tunanin abin da ya faru na fasa auranta da Yaya Hamza take rike da ni a cikin ranta ta makara har gobe ban yi nadama ba. Da na bari ta auri Yaya Hamza da tuni ta haɗa mana yaƙi a cikin gidanmu."

  Cikin mamaki Hauwa ta ce"To daman da jiƙaƙƙiya a tsakaninku?

Kai tsaye na ɗaga kaina kafin na ce"Akwai kam. To sai aka yi yaya?

Hauwa ta cigaba da faɗin" Kawai sai wacce suka zo tare da kika ce ƙawarta ce ta na cewa shi ya sa kika yi tsarin iyali kenan ga shi ya ja za miki matsala kina son haihuwan kuma  ta ƙi samuwa. Nan take Anty Maimuna ta ce sai dai ke matsala ta ƙare a kan ki Tafida aure zai ƙara in sha Allahu."

  Mirmishi kawai na yi a cikin raina ina jin kamar in na ga Ma'u na shaƙe mata wuya. Sannan ido na idon shema'u wallahi tallahi sai ta raina kanta

Hauwa na faɗin wai na kwantar da hankalina ba su isa su saka Yaya Tafida ya yi aure ba.

Kallonta na yi kafin na ce" Sun isa mana tunda ƴan'uwan shi ne kuma suna gaba dashi. Ni bare ce ko yau ya sake ni gidanmu za ni su kuma ai ba shi da kamar su. Hauwa na rantse da Allah ba zan hana Yallaɓai ya ƙara aure ba, ya ƙara ta zo ta ci duk abinda suke tunanin ina ci ƴaƴa kuma ta tara masa duniya ni kuma biyun da Allah ya bani Allah ya raya min su."

Na faɗa ina ƙokarin maida kwallar da ta kawo min. Hauwa ta dafa kafaɗata ta na faɗin" Ki yi haƙuri. In sha Allahu ke ma za ki ƙara haihuwa. Ba kin je asibiti ya kuka yi da likitan?

Ina sauke numfashi na ce" Ta dawo da ni nan asibitin Aminu kano. Jibi zan fara zuwa in sha Allahu."

  Hauwa ta yi ta mini fatan dacewa na kalleta ina ƙaƙaro mirmishi.

"Na gode Hauwa."

Mun daɗe a wajen ta na ba ni baki na dai nuna mata bakomai ne amman ni kaɗai na san halin da zuciyata ta ke ciki. Amman na yi ƙoƙarin nuna ma Hauwa ba komai.

Saboda haka ne na kalle ta ina faɗin" Kin ji Yaya Usman zai ƙara aure?

  Sai ta gyaɗa min kai kafin ta ce" Na ji fa. Duk ranar sunan na ji ana tattaunawa. Shi kuma can bakin ƙannen shi na ji su Nasara suna ta zagin Anty Zabba wai so ta ke yi shi Yaya Usman ɗin ya zauna da ita kaɗai? Ko ya yi ma Ogan shi gaddama yaƙi karɓan auran. Sai zaginta suke yi suna faɗin kar Allah ya sa ta koma ɗin."

Cikin mamaki na ce"Ikon Allah. Mutane sai Allah yau kuma ita Anty Zabban suke zagi? To Maman farko ba ta yi mgana ba?

  Hauwa ta ce" Oh na ji dai kamar an ce ta kira shi a waya ta ce ya bar komai ya ke yi ya zo ta na son ganin shi " Sai na gyaɗa kai kafin na ce"Uhm. Allah dai ya kyauta.". Ta amsa da Amin ni na cigaba da faɗa mata yarda muka yi da Yallaɓai ya haƙinƙan ce. Ta na dariya ta ce" Ni ai ban yi ma Muttaƙa mgana ba. Kar ya ce ina son jin gulma amman na san shima bayan ɗan uwansa zai bi"

Dariya muka ɗan yi gabaɗayanmu. Muna wajen Munira ta kira waya ta. Ta na tambayata jikin Alhaji? Na ce da saúƙi a ina ta ji ta ce Nasir ya faɗa mata ya ce Tafida ya saka a group ɗin su na gida. Ta tambaye ni wani asibiti ne na faɗa mata sai ta ce min ƙila gobe ta shigo. Ina dariya na ce ma ai ga Hauwa ta zo tun ɗazu.

"Kai Hauwa sannu da ɗanwaken zagaye ko ki kirani mu taho tare."

A speaker na saka Hauwa ta maida mata da amsa da cewa" Ke ni fa mijina ya kawo ni. Goben ki saka mijin ki kema ya kawo ki."

Munira na dariya tace" Au gorin miji da kin ga Habibi ba ya gari? To na san hanya kin ji ta Yallaɓai gobe ina nan tafe." Na ce Allah ya kawo ta lafiya daga nan muka yi sallama.

Ganin shidda har ta gota yasa Hauwa ta ce bari ta je ta yi ma su Gwaggo sallama ta wuce gida. Muna zuwa na ga Shema'u ta zo har ga Allah na so na daure amman na ƙasa ta kalleni ta na mini mirmishin munafunci irin na ƙawarta amman ni ta ga irin kallon da na yi mata. Ba domin muna asibiti ba ne. Kuma da ba uba na ne ta zo dubawa ba wallahi sai Shema'u ta raina kanta baƙar munafuka.

Tana min magana na yi kamar ban ji ba sai da Ma'un ta ce" Sadiya ba ki ji Shema na mgana ba ne. Ba ta gari ne ɗazu ta dawo ta na zuwa, ke ta fara tambaya."

"Oh."

Haka kawai na ce na juyar da fuska ta domin na kasa iya ɓoye abin da ke zuciyata. Hauwa ta yi musu sallama kularta kuma aka juye abincin na riƙa mata har bakin asibiti ta samu adaidaita muka yi sallama.

Ba domin Yallaɓai ya kirani ya ce bayan mangariba suna tafe tare da su Uncle Abba  da har na gaji na ce tafiya ta gida zan yi. Rahila ma ta koma gida wai za ta yi abinci da ga ni sai Ma'u da kawarta Gwaggo ma Yaya Hamza ya maida ta gida kiri ƙiri Baaba taƙi bin ta wai ta je za ta zo. Can suka keɓe da yarta suna da ƙuskus ni ko dagani sai Yaya Balki itama mijinta take jira Zaituna kuma ta koma gida saboda yara a cikin raina ina fatan Allah ya sa a sallani Alhajinmu gobe na gaji da zaman asibitin nan

Waya ta na ɗauko na kunna Data na kwana biyu ban hau ba. Sai na ga an yi min mgana har da Yaya Maimuna ta na tambayan jikin Alhaji. Hindatu kuma ta ce ta kira waya ta ba ta samu ba.  Har da matar Muhammad kabir ma na ga maganarta. Kuma na ji daɗi na amsa su sama sama saboda an fara kiran sallar mangariba. Yaya Balki kawai na faɗa ma zan je sallah sai ta ce na tsaya mu tafi tare. Muna masallacin kafin mu fito Yallaɓai ya ce ga su sun iso asibitin.

A haraban wajen muka haɗu suka gaisa da Yaya Balki ta yi gaba ta bar mu ina gaisawa da Aminan mijina guda biyu. Uncle Abba da Tariq. Sun yi min ya mai jiki na ce da sauki muna gaba ni da Yallabai suna baya zuwa in da ɗakin da Alhaji ya ke ciki.

"Me ya faru na ga kamar ranki a ɓace?

Yamutsa fuska na yi kafin na ce" Na gaji ina son na koma gida."

Sai ya kalleni da saurin na ce" Zan bika yanzu ko za ku je wani waje ne?

Kai ya girgiza kafin ya ce" A'a Gwammaja muka yi. Sai mu wuce taren su ma daga can za su wuce."

  Tun da Gwaggo ba ta nan da Baaba suka gaisa sai su Ma'u sannan na raka su ciki suka duba Alhajinmu ya ma tashi Baba Sani ya ƙariso zai taimaka masa ya yi alwala ya yi sallah. Ya ji daɗi ya na ta saka musu albarka da godiya ba dadewa suka yi masa sallama dukkansu kuma sun aje masa kuɗi ya na ta saka albarka.

"Alhajinmu Allah ya ƙara lafiya zan bi Yallaɓai zuwa gida sai gobe."

Alhaji ya jinjina kai kafin ya ce" Shi kenan mu kwana lafiya Dubu! A gaida min da Hauwa kuluta."

Na amsa masa ina mirmishi,  sun rigani yin gaba ina fitowa na ce ma Yaya Balki zan bi Yallaɓai sai gobe ta ce ai ya kamata na je gida tun safe fa. Daƙyar na iya yi ma Baaba sallama ta amsa sama sama.

"Sadiya Gwammaja za ku je?

Na juya ina kallonta Shema' u ce. Kamar na ce a' a sai kuma na ce mata eh.

Sai kawai na ji Ma'u na faɗin" To ki je mana Shema. Sadiya itama Gwammaja za ta je gidan kawunta."

  Juyawa kawai na yi ban ko yi mgana ba ina ji ta na yi ma Baaba sallama. Ina zuwa na ce ma Yallaɓai za mu rage ma kawar Ma'u hanya. Ya ce to ba matsala Ma'un ce ta rakota abin mamaki tana ganin motar su Tariq dabam sai kawai Ma'u ta kalli Yallaɓai ta na faɗin" Yallabai bari ta bi wancan motar ko ba waje ɗaya za ku je ba?

"Can za mu je gabaɗaya. Ta je ta shiga."

"Tariq..."

Ya ƙwalama sa kira ya na waya ne tsaye a bakin mota Uncle Abba ya riga ya shiga bangaren direba tunda motarsa ce.

''Ga ƙari na samo muku itama Gwammaja za ta je"

Ya faɗa ya na nuna Shema'u dake tsaye ita da Ma'u.

Sai ya ɗan ɗaga masa hannu alamun toh sai ya ce ta je ta shiga. Ni dai tuni na shige gaban mota na zauna Ma'u ta leƙo ta na fadin sai da safe na ce mu kwana lafiya.

Muna tafe amman acikin raina ina tunanin me ya sa shema'u ta ke son bin motar su Uncle Abba? Tabbas da wani abu a ƙasa.

Kafin ma a kai gidan su Yallaɓai ta sauka domin suna bayanmu ne mu dai muka yi gaba. Har ma mun shiga mun gaisa da Nene ta na tambayata Tafida ya ce Alhajinmu ba lafiya ya jikinsa? Na ce da sauƙi ta yi masa fatan samun lafiya.

  Tariq ne na ji ya na yi ma Uncle Abba tsiya yau ko ya shafa kwalli ne ƴan mata sai kawo hari suke yi.

Shi kuma bai ce komai ba Nene ce ta ce"Me ya faru?

Tariq ya ce"Nene ɗazu fa a gidan su amaryan abokin mu yan mata shi kawai suke kawo ma hari. Yanzu ma da muka ɗauko wata yar uwan Sadiyan Tafida daga asibiti har lambar wayarsa sai da ta tambaya."

  Ya faɗa cikin dariya. Ina zaune a cikin raina na ce a biri ya yi kama da mutum daman kawu ta gani kenan ta ƙyasa. Mirmishi na yi na ce lalle za ta sha wahala wallahi ko  ya na sonta ba zan taɓa bari ya aure ta ba.

Ba wai ina dariya da daɗewan da ta yi ba ta yi aure ba ne. A 'a ba ta da hali mai kyau ne.

Sai kawai na shiga hirar da cewa" Ba ƴar'uwanmu ba ce ƙawar Ma'u ce kawai."

Nene ce ke faɗin" To Allah ya sa dai ya ga wacce ta yi masa a ciki?

Yallaɓai ne ya yi dariya kafin ya ce"Ai Nene wannan ƙanin naki sai dai in yana da rabon samun Hurul aini ma'ana in ya mutu ya samu rabauta a shiga aljannah."

Nene ta aika masa da dakuwa ta na faɗin" Kawun na ka ne ka ke yi ma mugun fata? To bakin Tafida ya sari ɗanyen kashi Abba"

Sai lokacin ya yi mgana ya na zaune kusa da yayarsa yana danna waya.

"Na ƙyale su Nene. In cikin su akwai wanda ya isa gobe ya ɗaura mini aure "

Nene ta yi saurin cewa"Ba su ma isa ba. Amman dai mu mun isa Abba ka fara furfura fa"

" Lokacin ta ne Nene ban tsufa ba da saura na. Aure kuma zan yi in sha Allahu."

Nene ta amsa da Allahu ya sha kafin ta ce"To yau duka ba ka ga wacce ta yi maka ba? Ko yar uwan Sadiya?

Gabana har ya na faɗi na ji me zai ce kawai sai ya ce"Duka fa ba su da kamun kai. Nene wacce mace ce ta gari ce mai kunya za ta yi shigar bayyana sura ta na nuna ma namiji alamun tana son shi? Ni ba irin matan da na ke son aura ba ne Nene ki bar mganar nan."

"To ita wacce kuka ɗauko daga asibiti fa? An ce ka ba ta lambarka?

Kai tsaye ya muskuta kafin ya ce" Ita ma ta na cikin jerin su. Ita ta fara mini mgana kin ga kenan itama kunyar ta yi ma ta ƙaranci sannan kuma ni ba lambata na ba ta na Tariq na saka mata."

Me za mu yi in ba dariya ba sai aka bar Tariq da buɗe baki sai yanzu ya tuna domin da ya saka mata lambar sai ya ce wayar ba ta tare da shi tana gida a kashe.

Sai ta ce ta hannun ka fa? Sai ya ce ta aiki  ne ashe shi ya gama ma aikin.

Ni da Yallaɓai muna ta dariya Nene ma sai da ta dara. Tariq dai ya ce zai rama ganin dare ya yi suka ce za su koma Nene ta ce su kwana Abba ya ce kamar wasu mata. Sanin halin su ya sa ta ce Abba ya gaida Innayi. Shi kuma Tariq ya gaida da Hajiya.

Tare muka fita har baby ta yi barci sai ɗaukan ta Babanta ya yi Jidda ce kawai idanuwanta biyu ta ga babaninta ta maƙale musu suna mata tambayoyin makaramta tana ba su amsa.

10k Kawu Abba ya ba ta shi kuma Tariq 5k ya ce ita da Baby su siya chaculate  sai ta ki karɓa ta na kallon Babanta.

  Uncle Abba ya kalli Yallaɓai kafin ya ce" Kai Tafida ko ba ka yi ma yar namu bayanin ko kana raye muna da iko a kanka da su gabaɗaya ba."

Yana dariya ya ce"Sai ku jira na mutu tukunna"

Ni dai ina jinsu ina ta dariya Sai da yace Jidda ta karɓa sannan ta karba ta wuto wajena ta ba ni na karba ina musu godiya.

Tariq ke faɗin" Abba mun kusa zama surukai fa. Ka ga Jidda da tsawon kafa."

Abba ya jinjina kai kafin ya ce"Zan fara neman aure ko domin kar azo neman aure tarihi ya zo uban jidda ya ji kunya." Daga Tariq har Yallaɓai na suka fashe da dariya nima na dara sanin halin su in sun haɗu. Na shige mota ina ce ma Tariq ya gaida Farida  ya ce za ta ji.

  Uncle Abba kuma ya ce" Ni kuma wa zan gaisar miki Sadiya?

Ina dariya na ce"Amarya mai jiran gado."

Yallaɓai ke faɗin" Su kawu Sa'adu ko matansu ba."

  Keyarsa ya tallaba ya na faɗin" Mara ɗa' a."

Tariq na gefe ya ce zai rama masa. Ni dai mun fi minti talatin a waje kafin su yi sallama su suka shiga mota suka ɗau hanyar Rano mu ma muka ɗau hanyar gida.

Muna hanya na kalli Yallaɓai ina faɗin" Dare bai yi ma su Kawu ba?"

Ya na tuƙi ya ce"To wallahi Abba har sha biyun dare ya kama hanyar rano."

Sai kawai na yi fatan Allah ya kai su lafiya.

Mun isa gida lafiya Yallaɓai ya dauki Baby zuwa ɗakin su na ce Jidda ta yi mata shirin kwanciya su sun ci abinci a gidan Nene, ni da Yallaɓai na zuba mana sauran tuwon da na yi muka ci muka ƙoshi. Sai da muka yi brush muka yi shirin kwanciya duk mun gaji sai barci sai da asuba ne Yallaɓai ya ja mu ka yi ta ɓarnan ruwa.

  Da safen daman ban yi niyyar zuwa asibiti da wuri ba sai ga ma wayar Amina ta ce an sallami Alhaji sai na ce shike nan sai zuwa anjuma zan leƙo gidan.

Zan tsaya saude ta zo ta kama ma Jidda ta wanke Unfiorm ɗin su nima Yallaɓai na gida ba zai fita ba ƙila sai zuwa anjuma.

Janafty

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.