Free chapter · Read without an account
40
💞💞💞💞💞💞💞💞
AMATURRAHAMAN
*By*
OUM FATIMA
*(Hakimar D. A. W. A)*
💞💞💞💞💞💞💞💞
*DASHEN🌲ALLAH*
*WRITER'S📚ASSOCIATION*
*TEAM*
*JAJIRTATTUN💪🏻DASHEN🌲ALLAH*
BOOK 1
PAGE 40
*بسم الله الر حمن الر حيم*
"Wannan abubuwan da suka faru ne su suka ɗauke min hankali ban samu komawa ba, ga kuma case ɗin da nake yi a Kotu shi yasa ban koma naga halin da take ciki ba. Sannan kuma Akhi mutanen nan basu da kirki ko kaɗan, don kar kaga rashin kyautawar da sukayi mana don Ammah tace mu taho da ita a kaita taga ƙwararren likita." Muzaffar ya ƙare faɗa yana jin haushin abinda Kawu Isa da Sule sukayi musu wan can lokacin.
Baice komai ba ya gyaɗa kai kawai sai dai tunanin halin da halin da yarinyar take ciki yaƙi barin zuciyarsa ta huta. Suna haka Ammah ta fito ita da Haneen suka ci gaba da maida abinda ya faru da halin da Amaturrahaman ɗin take ciki amma suka murje ido suka hana a taimaketa bayan su ɗin ba taimakon nata zasu yi ba, Haneen sarkin karaya har hawaye sun cika mata ido. Tunda suka dawo tunanin halin da ƙawar tata ke ciki bai bar zuciyarta ba har dai komai ya lafa a gidan nasu aka fara shagalin bikin Anisa tana ranta, dama so take a gama bikin ta roƙi Yaya Muzaffar ya kaita ta ganota.
*Ƙasar Turkiyya, birnin* Istanbul.....
Duk da irin sanyin da ake yi a garin kasancewar yankin da ake sanyin ne sosai amma haka take tsaye a bayan gidan nasu da ya kasance wurin shakatawa ne da aka ƙawata shi da kujeru da tables don hutawar masu gidan, a inda take tsayen dusar ƙanƙara ce ke saukowa saman kanta amma bata damu ba hasali ma tayi nisa sosai a cikin tunanin da ya aureta ya zama bata da abinda ya fishi mahimmanci yanzu a rayuwarta. Musanman a waɗannan kwanakin abin ya ta'azzara ta yanda kullum ta kwanta sai tayi mafarkin ɗan'uwanta da Iyalinsa suna cikin matsanancin hali.
Haka zata saka mijinta gaba tana masa kuka akan ita dai gida zata koma taga halin da ɗan'uwanta yake ciki, sosai Alhaji Kabir Ahmad Datti yake damuwa da halin da matar tasa take ciki na tsawon shekarun da sukayi a Istanbul ɗin. Don haka kullum yake rarrashinta da kwantar mata da hankali, da kuma yi mata alƙawarin komawarsu nan kusa da zarar ya kammala abinda ya kawo shi.
Yauma kamar kullum ya dawo daga wurin aikin bayan ya biya ya ɗauko yaransu daga Makarantar ya duba ko ina bai ganta a cikin gidan ba, kai tsaye ya nufi inda yake da tabbacin samunta. Kamar yanda ya tsammata kuwa tana can tana aikin data saba, takawa yayi zuwa inda take tsayen ta ƙurawa wuri ɗaya ido alamar tunaninta yayi nisa da wannan duniyar. Ƙatuwar rigar sanyin dake jikinsa ya cire ya rufa mata yana rungumeta a cikin jikinsa, ajiyar zuciya suka sauke a tare kafin tace.
"Har ka dawo Dadyn Barru?." Ta ƙare maganar a sanyaye. Maimakon bata amsa sai cewa yayi.
"Sai yaushe zaki kwantar da hankalinki ki cire wannan damuwar a ranki ne Maman yara, bayan na tabbatar maki cewar nan da ƴan kwanaki zan gama tattara komai mu wuce gidan gaba ɗaya. Haba Halimtu, kefa ba ƙaramar yarinya bace yanzu." Ya ƙare maganar cikin tausasawa.
"Ba zaka gane bane Abban Barru shekara kusan takwas fa ban san halin da ɗan'uwana yake ciki ba, kuma duk duniyar nan shi kaɗai gareni shima ni kaɗai gare shi saboda sauran ba ƙaunar mu suke ba. Shi kuma ga halin ɗaya jefa kansa a ciki, Allah kaɗai yasan halin da Aunty Asiya take ciki ita da yaranta gidan can namu. Gashi kwanakin nan kullum sai nayi mafarki mara daɗi a kansu!". Ta ƙare maganar hawayen da suka cika idonta suna saukowa saman fuskarta.
"Ya isa haka ki kyautata zatonki, kairan in sha Allah, kiyi musu fatan alkairi in sha Allah zan yi ƙoƙarin kammala komai a cikin satin nan mu wuce."
"Da gaske kake yi Dadyn Barru?". Ta tambaye shi cike da farin ciki.
"Ƙwarai kuwa." ya bata amsa cike da son kwantar mata da hankali. Da haka yaja hannunta suka wuce cikin gidan inda yaransu ke jiran Mamansu tazo ta canza musu kaya ta basu abinci.
Irin rayuwar da Aunty Halima ke gudanarwa ita da Iyalinta kenan a Istanbul, tunda suka zo ƙasar da aiki ya kawo mijinta suke zamansu cikin farin ciki da walwala. Yana kulawa da ita sosai bata da wata damuwa sai ta ɗan'uwanta data baro a yanayin rayuwar da yake wacce kwata-kwata ba mai daɗi bace, ga ƴan'uba waɗanda da basa ƙaunar su buɗe ido su gansu.
Wannan damuwar ita kaɗai ke rage mata farin ciki a zaman da tayi, a haka har ta haifi Yaranta uku, babbar Mace ce mai suna Barru sai Namiji Asad sai ƙaramar Sanam. A kwanakin nan sosai ta ɗagawa Mijinta hankali akan son komawa gida saboda mafarkin ɗan'uwanta da Iyalinsa da take yi cikin yanayi mara kyau. To da yake dama shima Alhaji Kabiru Ahmad Dattin so yake ya koma gidan gaba ɗaya yaci gaba da gudanar da Kasuwancinsa a can sai ya roƙeta a kan ta bari ya gama tattara komai sai su koma baki ɗaya.
Wannan kenan.
__________ ★
A can gida Nigeria kuwa a Matazu Yau Amaturrahaman ta dawo gida cike da murnar kammala jarabawarta da tayi a yau ɗin. Don haka ta haɗa musu shagali ita da mutanenta su Labor ta sakar musu kuɗi suka ci daɗi suka saki kiɗa a gidan wanda ya ƙonawa su Kawu Isa rai har ya kasa haƙuri yayi ta masifa suka manna masa hauka.
Ɗansa Sule ya kirawo ya faɗa masa abinda tayi musu yau a gidan ya kuma ce idan har Sule ya haifu a cikinsa to ya tabbatar yayiwa Amaturrahaman abinda ko ance tayi rashin mutunci zata gudu da ƙafafuna. Cikin kurari da da nuna Mazantaka Sule yayiwa Babansa alƙawarin koyawa Amaturrahaman ɗin hankali.
Albarka ya saka masa ya tafi yana raya mugun abu a ransa a kan ƙaramar yarinyar da take matsayin ƴa a gare sa. Bayan sun gama shagalin ta sallami su Labor kuma sai ta zauna tana kuka sosai na tunawa da ƴar'uwata da Ummansu, da ace suna raye yanzu da suna nan zagaye da ita suna farin cikin a tare. Sai dai babu ko ɗaya a cikinsu ita kaɗai ta rage tana gararanba babu matallafi, kuka tayi sosai ta share hawayenta sannan ta buɗe lokarta ta ciro hotunansu ita da Ya Nafi da Ummansu har da Abbansu tun suna Yara ta shiga dubawa.
Ɗaya bayan ɗaya take kallon hotunan hawaye na sauko mata har ta kammala ta mayar ta adana, ATM ɗin da Ya Nafi tabbata wanda tace kuɗin karatuna ne ta saka mata a ciki ta ɗauko ta juj-juya ta mayar cike da tunanin ta inda zata fara. M card ɗin nan ta ɗauko shima ta juya ta juya ta mayar tana jan ƙwaffa da ɗaukar alwashi a ranta. Da haka bacci ya ɗauke ta wurin cike da mafarkai barkatai. Bata farka ba sai da aka kira sallar la'asar sannan ne ta tashi da wata irin yunwa saboda tun karin safe da tayi ta tafi Makaranta bata ci komai ba, ko shagalin da suka yi ita ƙin cin komai tayi.
Wanka ta fara yi tayi sallah kafin ta kira Labor a waya ta saka shi yayo mata take away, ba'a jima da kiran nasa ba sai gashi ɗauke da laidar abincin daya sayo mata. A babban zauren gidan suka ci karo shida Salaha ta dawo daga tallar abincin da take sayarwa, cike da shaƙiyanci Labor yace "A'a tsakuwata daga ina haka da yamman nan?."
"Daga inda ka aike ni ɗan rainin wayo." Salaha ta faɗa cike da fitsara "Kiyi komai, ba komai ƴanmata kin sace zuciyar Labor shi yasa ba zaki amshi hukuncin rashin kunyar da kika yiba." Tsoki Salaha ta saki tana faɗar.
"Allah ya kyauta in ƙare a ɗan'iska irinka bawan Mace, Macen ma ƙaramar yarinya." Ƙoƙarin riƙota yayi saboda ba'a taɓa masa Madam ɗinsa a zauna lafiya, da gudu Salaha ta rufta cikin gida saboda ta san tsaf zai mata akiyanci.
"Zamu haɗe ne yarinya." Ya faɗa yana ƙarasawa ɓangaren uwar ɗakin tasa ya kai mata saƙon bai zauna ba ya ƙara gaba aiken data masa. Tashi tayi tace abincin ta ƙoshi kafin ta fice a gidan don shan iska, inda ta saba zama can bayan layinsu wani wuri da ba yawaitar mutane take zuwa tayi karatu ko ta huta. Wayarta ta ciro ta shiga duba Makarantu tana son ganin wacce ta dace da ita, A.B.U Zariya ta tsaya a kai don haka ta shiga binkice a kanta sosai wanda ya ɗauketa dogon lokaci har aka kira magriba kafin ta koma gida.
***** Da dare bayan ta gama duk wasu uzurorinta ta kulle ɗakin tayi kwanciyarta kamar yanda ta saba ita kadai take kwana ba tare da fargabar komai ba. Cikin barci taji kamar ana taɓata, ji take tamkar mafarki take don haka ta ɗan saurara, amma sai taji abin na ƙara yawa. Hannu ta saka ta riƙe hannun dake taɓatan wanda taji hannun gardi ne irin wanda wahala ta kassra shi.
Wata irin faɗuwar gaba ce ta ziyarceta mamakin ta yanda aka shigo mata ɗaki na kamata saboda ta san ita dai sai da ta rufe ɗakin kafin ta kwanta. Ƙarfin halin buɗe baki tayi tace "Waye a nan?". Saboda kashe fitila takeyi idan zata kwanta hakan yasa ta kasa ganin ko waye saboda duhu daya mamaye ko ina a ɗakin.
Ƙoƙarin toshe mata baki ake yi ga wani azababben warin jiki dana hammata dake shige mata hanci yana ƙoƙarin sakata amai har numfashinta na ƙoƙarin ɗaukewa. Ƙin bada damar hakan tayi suka shiga kokawa ita da wanda ke ƙoƙarin wulaƙanta mata rayuwa, duka, mari babu abinda baya kai mata don ganin ya cimma mummunan ƙudirinsa a kanta, amma ta jure taci gaba da kare kanta saboda alƙawarin da tayiwa Ya Nafi akan ko zata rasa rayuwarta tayi ƙoƙarin kare kanta kar ta bari aci galaba a kanta.
Jin yana ƙoƙarin dole sai ya kai hannunsa inda ba zata taɓa bari hakan ta faru ba yasa zuciyarta yunƙurowa ta fusata ta shiga lalube da ɗayan hannunta, ɗayan kuma tana ƙare harin da ake kawo mata. Cikin sa'a ta lalubo kwalbar da tasha lemu a lokacin da taci abinci, ai kuwa bata tsaya jiran komai ba ta ɗaga ta bugawa mutumin kwalbar ba tare da sanin a ina ta doka masa ba.
Azabar data ratsa shine ta saka shi ƙwalla ihu wanda ya janyo hankalin sauran abokan tafiyar nasa masu masa gadi a ƙofar ɗaki, ya kuma tada wasu daga cikin mutanen gidan. Da gudu suka shigo ɗakin suna kunna fitila idanunsu a kan abokinsu Sule dake kwance a ƙasa kwalbar data doka masa ta fashe ta shige cikinsa jini na malala.
Idanu Amaturrahaman ta zaro ganin ashe Sule ne ya shigo mata ɗaki da kuma abinda tayi masan gashi baya numfashi.
Kansa suka nufa da gudu suna kiran sunansa wasu kuma suka nufi Amah da nufin dukanta. Ganin abinda suke shirin yi yasa ta rarumi wata kwalbar ta shiga nuna su da ita, basu fasa nufota ba ai kuwa suna zuwa ta shiga Dukansu da kwalbar kafin ɗaya a cikinsu ya shammaceta ya soketa da wuƙar daya cire a gefen cikinta wanda nan take ta ƙwalla ƙara ta zube a kuma dai-dai lokacin mutanen gidan suka shigo ɗakin har wasu daga cikin maƙota sun fara shigowa don ihun farko dana biyun babu inda bai kai ba a nan kur kusa.
Ihu Kawu Isa da Babar Salaha suka saka lokacin da sukaga Sule a kwance cikin jini, kansa suka nufa suna kururuwa da ihu an kashe musu ɗa babu wanda yabi ta kan Amaturrahaman dake kwancen itama cikin jinin.
Aunty Rakiya da isowarta kenan ita ta nufeta tana ƙwala kiran sunanta, abokan Sule da sukaga mutane sun fara taruwa zame wa suka fara yi zasu gudu. Sai dai suna zuwa zauren gidan zasu fice suka ji jiniyar motar ƴan sanda, Kawu Isma'il da shine ya kira police ɗin yaga zai haura katanga ya basu umarnin shigowa suka kamasu gaba ɗayansu aka zuba a motar ƴan sandan.
Shiga cikin gidan aka fito da Amaturrahaman da Sule da basa numfashi aka nufi asibiti dasu. Lokaci ɗaya unguwar ta ruɗe da abinda ya faru sai kace ba dare ba, zuwa asuba labari ya gama baza ko ina cewar wai Amaturrahaman ta kashe Sule tunda haka su Kawu Isa suka yayata sai Aunty Rakiya ce mai fadar gaskiya akan ba'a san ainahin abinda ya faru ba domin itama Amaturrahaman ɗin an soketa da wuƙa suna asibitin duka.
★ Washe gari zancen ya gama baza ko ina don haka su Labor da suka ƙaraso su suka kulle ɗakin Amaturrahaman suka rufe gidan suka nufi asibiti don jin halin da take ciki.
A can asibiti kuwa kuwa bayan an tabbatar gaba ɗaya su biyun an basu kulawar data dace ta hanyar basu taimakon gaggawa, sai dai basu farka ba har yanzu bare a san halin da suke ciki. Amma dai lokacin sunyi iya ƙoƙarinsu, wasu aka bari daga cikin police ɗin domin kula dasu inda wasu suka koma gidan domin fara gudanar da binciken ainahin abinda ya faru ta hanyar tambayar mutanen gidan kafin a koma kan yaran Sule dake tsare a police station. An fara da binciken ɗakin Amaturrahaman da aka amshi key an hannun su Labor kafin suka koma tambayar su waye su miye alaƙarsu da juna inda Kawu Isa da Babar Salaha suka faɗi son ransu sai Kawu Isma'il ne da Matarsa Aunty Rakiya suka faɗi gaskiyar abinda suka sani inda Kawu Isa yaji tamkar ya tsiresu saboda baya so a san ainahin abinda ya kai Sule ɗakin nata har hakan ta faru.
Kawu Isma'il kuwa da gayya ya faɗi gaskiya saboda yana jin haushin abinda Kawu Isa keyi masa na handama da baba kere akan komai suka samu da kuma abinda ya masa lokacin da Doctor Farhan yake neman auren Amaturrahaman, don haka yabi wannan hanyar don ya baƙantawa ɗan'uwansa kamar yanda ya masa wanda hakan yayi wa Aunty Rakiya daɗi ta samu hanyar da zata shiga al'amarin yarinyar da take matuƙar tausaya mata.
Ana cikin wannan ruguntsumin ne kuma Motocin Marshal Zayyad tare da rakiyar Sojojinsa sai kuma ƙannensa Muzaffar da Haneen suka tsaya a ƙofar gidansu Amaturrahaman dake can asibiti bata san inda kanta yake ba.......
Alhamdulillah a nan na kawo ƙarshen Amaturrahaman book 1 sai mun haɗu a book 2 wanda zai ci gaba da zuwa ba tare da ɓata lokaci ba.
Amaturrahaman book 2 paid ne wanda a cikinsa ne ainahin cakwakiyar take da kuma warwarewarta, ga mai buƙatar ci gaba da karantawa sai ya tuntuɓeni a lambar da zan aje a ƙasa domin biyan nasa ya shiga jerin waɗanda zamu ci gaba da tafiya da su.
Ku hanzarta biya domin sanin shin Amaturrahaman zata tashi ko kuwa? Shin Sule zai tashi ko ya mutu sakamakon kwalbar da Amaturrahaman ta caka masa? Shin za'a tuhumi Amaturrahaman da laifin kashe Sule? Shin Amaturrahaman zata cika burinta dana Ya Nafi na ganin tayi karatu ta tsaya da ƙafafunta? Wai mene ne a cikin memory card ɗin da Ya Nafi ta ɗauka a wurin Alhaji Tanimu wanda yayi sanadiyar rayuwarta? Wace tsiyarce Alhaji Tanimu da muƙarrabansa ke shukawa wanda suke salwantar da rayuka domin binne ɓarnar tasu? Me zai faru tsakanin Marshal Zayyad, Muzaffar da Amaturrahaman? Shin Hajiya Ruƙayya zata samu abinda take so kuwa na ganin bayan Ammah da Yaranta musamman Zayyad? Wai ina labarin dangin Mahaifin Umman su Amaturrahaman dake Niger? Aunty Halima fa, ya zataji idan ta dawo ta samu babu ɗan'uwanta da Iyalinsa sai Amaturrahaman kawai wacce itama rayuwarta take cikin hatsari? Wane irin ƙakubale Amaturrahaman zata fuskanta kafin ta taka matsayin da take son takawa domin cika alkawarinta ga ƴar'uwarta? Yaya Amarya Anisa zata kasance a gidan Abdulmajid, burinta zai cika na kashe auren domin mallakar Zayyad mai ɗinbin masoyan dake sonsa a gida da waje? Hajjaju Zaheera da kuma Samra, ya zata kasance tsakaninsu idan Zaheera ta gane abinda ke zuciyar ƙawarta a kan wanda take tsananin so?.
Duka amsar waɗannan tambayoyin dama duk wasu tambayoyi dake ƙunshe cikin labarin zaku same su a book 2 da yardar Allah. Abinda zaku yi kawai ku tuntuɓi a wannan lambar don biyan naku kusha labari, ***.
Sai mun haɗe taku Oum Fatima