Free chapter · Read without an account

15

by Nana Disoo · ƘADDARAR RAMLAH

ƘADDARAR RAMLAH

SHAFI NA GOMA SHA BIYAR



As’ad yana kwance a kan babbar gadonsa mai faɗi, an shimfiɗa zanen siliki mai launin zinariya, yana nannauyan bacci. Gidan sarautar sarki ne, inda kowane abu yake cike da ɗaukaka da ƙima. Bangaren As’ad na cikin kyalli, an lulluɓe ƙofofin da labulen alfarma.

Cikin tsakar gadon, Haneefa ta yi ninkaya a gefen gadon, tana kallo cikin tsananin son ganin yadda yake. Ta raba bargon da aka lullube shi da shi, ta shiga jikinshi da salo mai cike da izza. Ta sanya hannunta bisa kirjinsa cikin taushi, tana murza sumar kansa a hankali.

"Katashi mana... My Kankan..." ta rada masa a kunne da murya mai laushi kamar na mace mai tsananin salo.

As’ad ya motsa a hankali, yana jin yadda jikinsa ya fara zafi da nauyi. Bai riga ya buɗe idanu ba, amma yana jin yadda hannayenta suke yawo a jikinsa. "Haneefa... me kike yi?" ya furta a hankali, murya cike da natsuwa.

Ta kwanta a jikinsa tana narke masa, tana lasar wuyansa da salo mai cike da jaraba. "Nasan matarka ba ta yi maka irin wannan ba, ko?"
As’ad ya buɗe idanuwa, yana kallonta cikin rudani. "Ba haka bane... Haneefa..."
Ta yi masa shiii, ta sanya yatsanta a laɓɓansa. "Salona ba irin na kowacce mace ba ne. salona salon karuwai ne. Na san yadda zan sa ka manta da duniya."
As’ad ya ji zuciyarsa ta karye kamar an danna mishi wani irin abu. Bai iya musantawa ba. Jikinsa ya zafafa, zuciyarsa tana tafarfasa kamar wuta.

Ta yi dariya mai sauti tana jin yadda ya karaya. "Ba zan bar ka ba har sai ka furta cewa ni ce wacce ka fi so."
"Ni... Ni dai..." ya furta cikin rauni.
Ta latsa wuyansa tana cewa, "Katashi in tsotseka, my Kankan. Katashi in lasheka.”

Ya motsa cikin rashin natsuwa, yana kokarin fita daga karkashinta, amma kamar wani nauyi ya danne shi. Zuciyarsa tana masa tsananin radadi, amma kuma yana jin kamar yana buƙatar kasancewa da ita.
"Haneefa... Ni dai ina son in gaida Hajja. Tun jiya ban je ba..." ya furta cikin sanyin murya.

Haneefa ta turo baki tana wani murmushi mai cike da kishi. "Ita Hajja bata san cewa kana da amarya yanzu ba? Yanzu kake tunanin tsohuwa a lokacin da nake nan?"
As’ad ya dan daure fuska cikin rauni. "Kiyi haƙuri... Bazan daɗe ba."
Ta janye jikinta daga nasa a hankali. "To tashi muje tare.

Fadar Hajja tana cikin babban ɓangaren gidan sarauta, shimfidarta na musamman, cike da labule masu launin zinariya da kujerun alfarma. Fitilun falon suna ba da haske mai laushi da natsuwa, yayin da iska ke ɗauke da ƙamshin turaren Misira.

As’ad ya shiga falon cikin nutsuwa, yana sanye da riga mai launin rawaya da alkyabba mai ruwan gwal. A bayansa, Haneefa ce cikin doguwar riga mai launin ja, kanta a duƙe, tana biye da shi a hankali.

Hajja, matar sarki kuma uwar gida, tana zaune bisa kujerar alfarma, tana duba wani littafi na addu’a. Tana ganin su sun shigo, sai ta saki murmushi mai cike da kulawa.
"As’ad ɗana, kun shigo lafiya."
As’ad ya rusuna da ladabi. "Hajja, ina kwana?"
Haneefa ta duƙa a gefensa cikin ladabi. "Ina yini Hajja."
Hajja ta gyada kai cikin murmushi. "Lafiya kalau, ku zauna."

As’ad ya zauna a kujerar kusa da Hajja, yayin da Haneefa ta tsaya a gefensa, tana daidaita mayafinta da natsuwa.
Hajja ta dubi Haneefa cikin kulawa. "Haneefa, ya gida?”
Haneefa ta sunkuyar da kai. "Alhamdulillah, Hajja. muka yanke shawarar zuwa gaishe ki."
Hajja ta yi murmushi. "Nagode da girmamawa. Allah ya albarkace ku."
"As’ad, bakada lafiya ne” Hajja ta tambaya, tana kallonsa cikin kulawa.

As’ad ya gyada kai a hankali, amma idanunsa suna kallon Haneefa kamar mai bin umarni. Haneefa ta dan kalli As’ad ta gefen ido, ta saki murmushi kadan.

Hajja ta daidaita zamanta, tana kallon yadda As’ad ke zaune tamkar wanda aka ja da igiya. Idanunsa sun lumshe kadan, kamar mai cikin bacci, amma duk lokacin da Haneefa ta motsa, sai ya bita da kallo.

"Ya As’ad, lafiya kuwa?" Hajja ta tambaya cikin damuwa.
Ya ɗan gyara zama. "Lafiya, Hajja."
Haneefa ta katse shi da sauri cikin murmushi. "Eh, Hajja. As’ad yana gajiya ne."
Hajja ta kalle su duka biyu, tana jin tamkar akwai wani abu da ba dai-dai ba. Amma saboda nutsuwar Haneefa da ladabin da ta nuna, sai ta dan rage zargin da take yi.

Bayan sun gaisa, Haneefa ta ɗan matso kusa da As’ad, ta dafa kafadarsa da natsuwa. "My Kankan, tashi mu tafi ko? Ka san dai Hajja na bukatar hutu."
As’ad ya mike kamar wanda aka umarta, yana kallonta da murmushi mai rauni. "To, Haneefa."
Hajja ta yi murmushi mai cike da damuwa. "Kuna tafiya kenan?"
Haneefa ta gyada kai. "Eh, Hajja. Sai mun sake dawowa daga baya. Allah ya kara lafiya."
"As’ad, kada ka manta ka dawo kusa dani idan ka samu lokaci."
As’ad ya sunkuyar da kai. "Zan dawo, Hajja."

Yayin da suke fita daga fadar, Hajja ta tsaya kallon su har suka bace daga gani. Ta sauke numfashi mai nauyi, tana jin wani abu yana damunta.

"Ya Allah, ka tsare ɗana daga sharrin komai," ta furta a hankali.

******

A cikin ɗaki mai faɗi na fadar sarauta, wanda aka kawata da kyandirori masu ƙamshi da zanen zinariya, Fulany Maryam tana zaune bisa wata shimfiɗa mai launin ja. A gefenta, matar da ke taimaka mata tana durƙushe, tana haɗa wani magani a cikin ƙwarya mai faɗi.

Fulany Maryam ta gyara zamanta cikin izza, tana mai dariya mai ɗauke da tsana. "Daga nan za a tabbatar da cewa Hajja ba za ta sake jin daɗi a rayuwa ba. Na sa aka yi wannan aure ne domin na wulakanta ta da ɗanta gaba ɗaya."

Matar ta ɗago kai cikin alamar damuwa. "Amma Fulany Maryam, idan har maganin nan ya yi tasiri ya hana shi aiki gaba ɗaya, Haneefa fa zata iya guje shi. Kinsan dai Haneefa da son maza."

Fulany Maryam ta kyalkyale da dariya mai cike da izza. "Ke dai ba kya gane wayon mugunta! Da haka nake so! Idan As’ad ya zama marar amfani gaba ɗaya, Haneefa za ta fara tsanar shi. Kuma idan har ta guje shi, hakan zai zama babbar tozarci ga Hajja."

Matar ta ƙara dubanta cikin tsoro. "Amma Fulany Maryam, kin san cewa yanzu Haneefa ta nutsu sosai. Da alama Allah ya taimake ki, ta daina yawon banza. Amma idan maganin nan ya hana As’ad aiki gaba ɗaya, ba kya ganin hakan zai iya haifar da matsala?"

Fulany Maryam ta harare ta, tana nuna rashin jin daɗi. "Ke kuwa ba kya gane komai! A cikin cikar burina, har ɗiyata ba zan bar ta ba. Na sa aka yi wannan auren ne don ganin Hajja ta rasa dukkan farin cikinta. Kuma idan hakan ya faru, zan tabbatar da cewa As’ad ya zama kamar cikakkiyar mace.

Matar ta yi shiru na ɗan lokaci kafin ta ce, "Amma idan hakan ya faru, ko Haneefa ta guje shi, ya kike ganin za a fahimci hakan? Sarki fa zai iya gano cewa akwai wata mugunta a baya."

Fulany Maryam ta ɗaga kai cikin izza, tana dariya mai sauti. "Ai shi ne burina! Na tabbatar cewa da zarar Haneefa ta rasa jin daɗin zama da shi, zata yi kuka ta fice daga gidan. Hajja za ta rasa ƙaunar ɗanta kuma sarki da kansa zai nisanta kansa da shi. Kuma idan hakan ya faru, zan tabbatar da cewa As’ad ya zama tamkar wata cikakkiyar mace, marar amfani, wacce babu mace da zata iya zama da shi."

Matar ta ɗan ja baya cikin tsoro. "Amma Fulany Maryam, idan har hakan ya sa As’ad ya haukace, hakan zai iya zubar da mutuncin gidan sarauta."

Fulany Maryam ta yi dariya mai tsanani. "Ba ruwana da mutuncin gidan sarauta. Ni dai burina shi ne in ga Hajja da ɗanta sun wulakanta, sun rasa farin cikinsu. Zuciyata ba za ta huta ba sai na tabbatar da cewa As’ad ya zama marar amfani. Idan hakan ya faru, zan tabbatar da cewa ko wata mace ba za ta iya zama da shi ba."

Matar ta dubi Fulany Maryam cikin mamaki. "Me yasa kika tsani Hajja haka Fulany Maryam? Ai da alama ba ta yi miki komai ba."

Fulany Maryam ta tsuke fuska tana jan numfashi. "Ke dai ba kya gane wayon zuciya. Tun farko Hajja ba 'yar sarauta bace. Ba ta fito daga gidan masu mulki ba. Soyayyar sarki ce kawai ta kawo ta fada. Ta kwace min duk wata kulawa da girma da na kamata in samu. Ai ni ce ya kamata in zama mai juya duk matan sarkin amma ita Banda ita!"

Matar ta saki baki tana jin mamakin yadda mugunta ta ratsa zuciyar Fulany Maryam. "Amma Fulany Maryam, idan aka gano wannan makircin, faɗar sarauta za ta girgiza."

Fulany Maryam ta yi tsaki. "Ai duk wanda ya gano, na riga na shirya yadda zan rufe bakin sa. Babu wanda zai iya kawo ƙarshen wannan makirci nawa!"

****

Gidan sarauta ne mai cikakken tsari da alfarma. Masallacin fada yana kusa da babban zauren taro, shimfidarsa tana cike da jajayen kafet masu tsari na alfarma. Fitilu masu walƙiya suna haska harabar masallacin, yayin da ƙamshin turaren Misira ke tashi a ko’ina.

As’ad ya kammala alwala cikin nutsuwa, ya shiga masallaci don yin sallar Isha’i. Bayan ya gama salla, ya ɗauki alƙur’ani don yin karatu. Amma da ya bude shi, sai ya ji wani irin nauyi yana ratsa jikinsa.

Ya yi kokarin karanta Suratul Fatiha, amma bakinsa ya kasa furta komai. Yana jin kamar wani abu ya ɗaure masa harshe. Ya lumshe ido, yana neman kwanciyar hankali, amma ya gagara. Me yake damuna haka? ya tambayi kansa.

Daga karshe, ya rufe alƙur’anin cikin sanyin jiki, ya jingina da bango. Zuciyarsa na bugawa da sauri, ya tsinci kansa cikin tunanin Haneefa. Da alama zuciyarsa ba ta kwantar da hankalinsa ba. Ya yi addu’a da ƙyar, sannan ya fita daga masallaci yana jin tamkar an masa wani nauyi a jiki.

Da ya shiga cikin zauren gidan sarauta, sai ya ga bayin fada suna ta zirga-zirga suna shirye-shiryen biki na gaba. Ya nufi bangarensa, yana shirin hutawa kafin dare ya tsala.

Da ya tura ƙofar ɗakinsa, sai wani ƙamshi mai taushi ya doki hancinsa. A hankali ya shiga, ya rufe ƙofa da baya, ya tsaya yana kallon cikin ɗakin. Sai ya ga Haneefa a tsaye a tsakiyar daki, tana sanye da doguwar riga mai launin ja, amma cikin siririyar top da ta bayyana cikinta.

Gashinta ya barbazu har bisa kafaɗa, fuskarta ta yi matukar kyau, tana murmushi mai cike da salon jan hankali. As’ad ya tsaya a bakin kofa yana kallonta kamar wanda aka tsayar da lokaci.
"Marhaban da Sarkin zuciyata..." ta furta cikin wata murya mai rauni.

Ya yi ƙoƙarin magana, amma ya gagara. Zuciyarsa tana tsalle kamar tana neman fadi. "Haneefa... me kike yi haka?"
Ta matso da siririyar tafiya, ta kama hannunsa a hankali. "Na ga kanada gajiya, sai na ce bari na shirya maka wanka mai dadi."
Ya girgiza kai kamar wanda aka rikita. "Uhmm... na yi salla yanzu... amma..."
Ta sanya yatsanta a labbansa. "Shii... bana son surutu."

Ta dora kansa a kafaɗarsa, tana lasar wuyansa da harshenta mai laushi. "My Kankan... ka barni in sa ka ji daɗi."
Ya saki numfashi mai nauyi, jikinsa yana saki kamar ba nasa ba. Zuciyarsa na tsalle-tsalle, yana jin wani abu yana cike masa kai.

Haneefa ta ja hannunsa har bakin gado, ta sanya shi ya zauna a kan shimfiɗar alfarma mai launin ruwan gwal. Ta fara cire masa rigarsa a hankali, tana zuba masa idanuwa masu cike da kwarjini.
"Na lura kana gajiya... Bari na taimaka maka."
Ta kwance masa alkyabbarsa, tana shafa bayansa cikin salo mai rikitarwa.

Da suka gama wanka, ta shafa masa mai mai ƙamshi, tana murza wuyansa da ƙirjinsa a hankali. "My Kankan... ba ka san yadda nake sonka ba."
Ya rufe ido, yana jin tamkar numfashinsa yana neman tsayawa. "Haneefa..."
Ta yi murmushi tana shafa sumar kansa. "Ka san dai na fi kowa iya sanyaya maka rai. Kada ka damu da komai."

A wannan lokacin sai wayarsa ta yi ƙara. Ya ɗauka, sai ya ga sunan Aysha a jikin screen. Haneefa ta kama wayar da hannu guda, ta kashe ta a hankali.
"Ba zai ɗauka ba," ta furta cikin murya mai kwantar da hankali.
Ya yi shiru yana kallonta, kamar wanda aka rufe masa baki. "Amma... Aysha ce..."
Ta daura kanta a kirjinsa. "Bana son wani ya katse lokacinmu."

Bayan sun kwanta, Haneefa tana shafa sumar kansa. "My Kankan... gaskiya na gaji da zama a nan. Gobe mu koma Abuja."
Ya juyo cikin mamaki. "Abuja kuma da sai qfter 2weeks?"
Ta gyara kwanciyarta a jikinsa. "Ni gobe nakeso.”
Ya yi shiru na dan lokaci, yana kallonta cikin damuwa. Amma kafin ya ce wani abu, ta sumbaci goshinsa tana cewa, "Ka sani cewa kai ne kadai namiji a zuciyata."
Ya sauke numfashi. "To... zamu tafi gobe."

Ta saki dariya tana shafa fuskarsa. "Na san cewa ba zaka ƙi ba."
Ta sake kwanciya bisa jikinsa, tana lasar wuyansa cikin soyayya. "Bari in sa ka manta da komai..."
As’ad ya rufe ido, zuciyarsa tana bugawa da sauri, yana jin tamkar ya narke a jikinta. Bai san me yasa yake jin haka ba, amma ya san cewa yanzu ba zai iya cewa a’a ga Haneefa ba.






Nana hadiza
***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.