Free chapter · Read without an account

Chapter 12

by Sadiya Auwal · MUMINA KO AZZALUMA

⚫ *MUMINAH DA AZZALUMA*⚫



⚫ _SADISAKHNA_⚫




⚫ *BOOK 1*⚫



⚫ _PART 12_⚫



Kaman yanda ya faɗa basu daɗe suna takawa ba sai gasu a gidan,sallama yayi tareda shiga gidan itama tabi bayansa. Bashida girma sosai amma baza'a ƙirashi da karami ba.
Ana shigowa tsakar gidane sai kuma ɗakuna sun zakagayeshi kowanne da shirgi a ƙofar ɗakin alamar da mutanen da suke amfani dashi. 
Gidan shuru kamar babu kowa,sai kukan wani yaro dayake fitowa a ɗaya daga cikin ɗakunan gida,da kuma wata tukunya babba akan murhu tana turiri,alamar mai jaurar safece ta ɗora.
A karshen tsaƙar gidan wani ɗan lungune na hanyar wucewa,nan suka shiga inda wani ɗaki yake da dan farfajiyarsa da kuma banɗaki a gefe. Dukka gidajen gidan na ƙasane anyi masa shafen suminti,amma wani wajen flastar ta fara fita,alamun ginin yaji ruwan damina.
Ɗaga murya yayi yaƙara sallama,daga ciki wata ta amsa musu tareda faɗin tana zuwa.
Dattijuwa ce amma ba wai tayi tsufa tukuf ba,domin kana ganinta kasan da alamun ƙarfi tattare da ita.
"Lale maraba sannu,ahhh Baban Isa kaine tare kuma da baƙuwa,sannun ku da zuwa barina ɗauko tabarma"
Komawa ciki tayi ta dawo da tabarmar karauno ta shimfiɗa ɗaya ta gefen sa,ɗayar kuma ta shimfiɗa ta gefe tareda nuna mata itama ta zauna.
Bayan sun zauna gaisheda ita yayi cikin ladabi kafin ya ɗora dayin magana.
"Wato Abinda yakawo da sassafennan wata magana ce"
"To inajinka maike tafeda kai?"
Kwashe yanda sukayi da baiwar Allahn ɗazu Asuba yayi ya faɗa mata,bata katseshi ba har saida ya kai aya tukunna.
"To naji zancenka ɗaki dai gashi can amma jiya wasu ƴan ci rani shida matarsa sunzo sun dubashi,basu bada kuɗi badai bamu ƙarƙare magana ba.Domin tun ranar danaga baka maida hankali ba dana baka kasaka amfani gona na sakashi kasuwa. Amma tunda dai harkar taimako ne kayi niyya nima bazan ƙi tayaka ba mu samu ladan tare,shi mutum duk inda yake maganine. Dabba ma kana iya taimakonta tayi maka rana balle kuma Mutum.
Ga nan ɗaki sai taje ta share ta zauna,akwai sana'o'i da dama a garinnan shiyasa mukeda baƙi sosai,ta zabi daidai ƙarfinta ta dungayi tana yiwa kanta ƴan laluran da baza'a rasaba. Na yafe mata kuɗin hayar shekarar nan,amma wata shekarar idan tasamu abinda zata dogara da kanta to saita biya kuɗin hayar ta in Allah ya kaimu da rai in kuma ta tuna ita wacece ta tafi gurin danginta da mijinta to haka ake fata. In ma batada miji to wannan ita ya shafa taje ta ƙarita,amma dai kyakykyawan zato ake fata"
"Nagode addah,dama nasan idan har na zi wajenki ke bazaki koreta ba kamar Hansatu,ke kuma saikiyi mata godiya da taimakon da tayi miki,sannan ki zauna lafiya da mutan gidan ki kama kanki,karki bari wata matsala ta kunno ta sanadiyyarki"
"Nagode nagode inna Allah yasaka miki da alkhairi,kaman yanda kika taimakeni Allah ya hanani baki kunya,namiki alƙwarin inshaallah babu wata matsala dazata faru,zan iya ƙoƙarina naga in wata shekarar Allah ya kaimu da rai na biya kuɗin. Saidai kafin sannan ina roƙonki da ki nunamin yanayin zaman garin da kuma menene yafi dacewa wanda zan fara dashi?"
"Wannan ba wata matsala bace inshaallah,munada babban rafi daya kewayemu ta yamma maso kudu,anan ana noman Samurai sosai,shiyasa mutane daga cikin garuruwansu suke zuwa suyi noma. Yanzu lokacin damina ce nan gaba kaɗan za'a fara rainon iri,yanzu kuma lokacin yin kwanduna ne,bari inkikayi wanka kikaci abinci kika huta zan kaiki wajen wata aminiyata tana koyar da yin kwandon saiki koya ki dingayi ki tara. In lokacin nemansa yayi saiki siyar kiyi wasu buƙatun,sannan in kina zaune keda kanki zaki gane wasu dabarun sana'ar kifara inshaallah,garinnnan ƙaramine amma yanada albarkar samun kuɗi sosai idan mutum ya tashi ya nema."
"To addah ni zan wuce zan barki da ita,idan da wani abun daya kamata na sani saiki sanar min"
"To shikenan ka gaida su isa da wannan birkitacciyar matartaka,da bata iya komai ba sai kishin tsiya"
Ta ƙarisa maganar tana tabe baki ta buge gefen zaninta data tashi tana gyarawa.
"Ɗan murmushi yayi ya jijjiga kai tareda yimata sallama"
Da alamun Addan tanada kirki amma kuma sam babu shuru shuru da kuma haƙuri a lamarin ta,wayayyiyar matace maiyin komai kai tsaye.
"Salamu alaikum Addah barka da safiya naji motsinki ai nace to kin tashi"
"Ehyi na tashi ya akayi?"
"Ahhh baƙuwa kikayi ne da safennan itakuma daga ina take hala ba ƴar garinnan bace,naga ban saida Fuskarta ba"
"Ahh Zulai uwar surutu da gulma dama kowa kika sani a garinnnan da saikin santa?"
"Hhhhh ahah ba haka bane Addah amma kinsan yanda nasan garin Samurai ciki da bai kaman ɗakin uwata zayyi wuya bansan mutanen cikinta ba. Duk da ni baƴar garin bace amma daɗewar danayi da kuma sanin danayiwa garin ba ɗan kaɗan bane"
"To naji, ina ƙoƙon zuba koko kikazo karba da kuma kuɗin jiya? To gashi. Wannan kuma baƙuwace itama zuwanta garin kenan a ɗakin gefen Ramma zata zauna. In kin gama kokon ma kisaka Su umaru don Allah su share minshi"
"To shikenan ayyah ashe baƙuwa mukayi kuma abokiyar zama,sannunki da zuwa,ya sunan ki kuma,mijinnki yana wajene naga hadda yaron ciki gashinan yafara girma. Hala zamusha suna nan kusa kenan"
Duk wannan tambayoyin baiwar allahn take jerawa wacce ta tsaya kurum tana kallonta batareda ta motsa bakinta ba ballantana ta bata amsar ko guda ɗaya ne.
"Kuma gata kyakkyawa kaman jinin buzaye ga........."
"Haba haba Zulai wannan wanne irin tambayane na ya uwaka ta haifeka,don Allah kije ga ruwan kokonki kada ya tafaso ya zube,mutum yana girma amma yana cigaba dacin ƙasa haba"
Ganin Addah ta hauta da faɗane yasa ta amshi kwanon shan kokon ta tafi,amma a idonta cike take da zumuɗin son jin amsar tambayoyinnata.
"Wai hmmm ai kinga takanki aikine yakeso ya ganki,wanann gidan da kike gani da matan cikinsa saikinyi a hankali."
Ɗaga kai kawai tayi batareda tace komai ba.
"Sannan wannan tambayoyin datayimiki dole ki tanadi amsa daidai dasu. Kince bakisan sunanki ba,idan sun tambayeki kice sunanki Salaha sunan ƴata ne data rasu,inason sunan sosai dafatan zaki karbeshi kafin ki tuna naki. Sannan in sunce ina mijinki kice ya tafi rani sai ya barki anan."
"To inshaallah zan kiyaye,sunan yayi sosai nagode, Allah yasaka da alkhairi"
"Ameen barina yi ɗumame kafin ta kawo kokon idan ta zuba saiki sha"
Daga haka Addah da salaha suka ɗan fara taba hira sama sama,don ma addan tana yi a takaice don taga ita batada yawan surutu.


Amin magana ta wannan layin 
***
Sadi-sakhna ce.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.