Free chapter · Read without an account

MAKIRIN IKO

by Aisha abbas Bidami · MAKIRIN IKO

☠️☠️ MAKIRIN IKO ☠️☠️

The hunted house 🩸

Jarumai writers association 📚📚📚🖋️🤩

MALLAKIN

MRS ISHAM

04

Layin shuru hakan yasa ya soma tafiya har bakin junction dakyar ya samu wani me motar ya masa lift ya faɗa masa sunan anguwar da ze kai sa.

Ko da isan sa gidan su me gadi da ya buɗe masa se kallon sa yake yana tunanin meyafaru direct dakin hajiyarsa ya nufa ya kwankwasa mata

“Waye ne?”

“Hajiya ni ne,Mahmoud ne hajiya”

Hajiya dake zaune kan sallaya da ta idar da nafila kallon kofar tayi cikin mamaki da al’ajabi jin muryar Mahmoud.

A ƙasan makoshi ta furta “Mahmoud de ?a irin wannan lokacin ?to ko de Siyama ta haihu ne ko wani abun ne ya faru Innalillahi “wayannan tunanin ne su suke ta yawo a zuciyar hajiya

“Bismillah shigo”

Shigowa yayi tana ganin sa da yanda yake a birkice ta miƙe tana

“Mahmoud me zan gani?menene abinda ya same ka?”

Zubewa yayi a gabanta yana me riƙe kafafunta ya fashe da kuka

“Hajiya na tuba,na bi Allah na bi manzonsa na bi ki,tabbas duk wanda be ji maganar mahaifiyarsa ba yana tare da shan wahala a rayuwa da ace na ɗauki maganar ki da bamu shiga cikin tashin hankalin nan ba”

Hankalin hajiya yayi kololuwa wajen tashi ɗagosa tayi tana duban fuskarsa

“Mahmoud me yake faruwa ne hankali na ya tashi ka sanar dani dan Allah “

“Hajiya muna cikin matsala dani da Siyama da ɗan mu. Hajiya ina tsoron kar su kashe min iyalina “

“Innalillahi wainnailaihi rajuun,su waye haka shin barayi ne suka shigo muku gida ?”

Cikin muryar kuka yace “gidan ne hajiya wannan gidan attajiri Tahir ne yake kokarin ganin bayan mu” sake sa hajiya tayi ta fara tafa hannu tana sallallami

“Na shiga uku ni Madinatu… Mahmoud kana nufin abinda aka faɗa akan wannan gidan gaskiya ne?”

Gyada mata kai yayi “fiye da abinda ake faɗa,se wanda yayi rayuwa cikinsa ze san da haka. Hajiya ku taimaka min sun shiga jikin Siyama har suka yi kokarin kashe ni yanzu haka tana can gidan ita kaɗai “

“Allahumma ajirni fi musibati “cewar hajiya tana zama yaraf akan gado jin abinda ya faɗa

“Yar mutane,ka sa rayuwar yar mutane a matsala Mahmoud. taurin kan ka be yi maka rana”

“Nasani hajiya!Nasani wallahi “

Wayarta ta jawo ta Kira babban yayan su Mahmoud ta sanar dashi abinda yake faruwa,sannan ta kira gidan su Siyama ta sanar dasu halin da ake ciki sosai hankalin su ya tashi.

Karfe shida dede yayyun Mahmoud da kuma maman Siyama da kuma baban ta da Fadila suka hallara a gidan hajiya Madina,a falo duk suka zauna kowa yayi jugum-jugum suka sa Mahmoud a tsakiya ya basu labarin duk abinda yake faruwa tundaga lokacin da Siyama ta soma sanar dashi akwai wasu bayan su a gidan har izuwa abinda ya faru jiya duk se da ya sanar musu. Salati kawai suke yi cikin damuwa da tashin hankali gaba daya sun shiga alhini. Basu yi wata-wata ba suka shiga motaci suka nufi hanyar gidan Mahmoud,koda suka isa gate din gidan a wangale suka same sa packing suka yi suna saukowa. ƙarewa gidan kallo suke yi babu kowa a compound din hakan yasa suka shige ciki kai tsaye falon was so neat and quiet babu kowa nan ma hakan yasa suka nufi bedroom din su dukkansu tsayawa suka yi daga bakin kofa suna me hangota tana zaune akan gado ta juya baya basu samu damar kallon fuskarta ba,gashin kanta yana nan a yanda yake a hargitse.

Mama ce a hankali ta furta “Siyama “ shuru babu amsa sannan bata juyo ba, hakan yasa a karo na biyu ta kuma furta “Siyama na,kin ga mamarkice “

Still no response hakan yasa mama ta yi kokarin shiga da sauri Mahmoud ya ce “ah ah mama kar ki shiga,ni zan shiga”

Shiga yayi zuciyarsa na bugu a hankali ya kai hannu kan kafadarta yana “Siyam”

A fusace ta juyo da fuskanta da ya koma abin tsoro, fuskan yaƙara tsayi,idanunta sun zama manya baki wuluk,ga kuma bakin ta da yayı tsayi kamar an tsaga shi.

Ja baya duk suka yi domin sun yi mugun firgita da tsorata a irin yanayin da suka ganta,faɗowa kasa tayi tana bangarewa hannunta ya murɗe ya koma baya haka kafafunta suma suka lankwashe suka koma baya.

“Kun yi kuskure” ta faɗa da wani irin murya me kauri tamkar muryar ƙaton namiji.

Fashe wa da kuka mama ta yi ganin halin da ƴarta take ciki rungumeta Fadila tayi itama tana hawaye,girgiza kai Baba yai sannan ya shiga dakin yana soma karatu yana tofa mata a fusace ta dubesa da firgitattun idanunta,a lankwashe ta fara tunkarosa tana gurnani haɗe da huci,duk da baba a tsorace yake domin tunda yake be taɓa ganin al’amari irin wannan ba amma yayi karfin halin ci gaba da karatunsa yana jawo ayoyi,tana zuwa kusa dashi ta sa hannu zata shake sa ya tofa mata karatu a fuska lumshe idanunta tayi ta sulale zata faɗi yayi saurin riƙota ta faɗo jikinsa. Da sauri Mahmoud yazo ya karɓeta a hannun baba ya kaita gado ya kwantar da ita.

Zama duk suka yi Baba yace “yanzu ta suma bamu san da me zata farka ba” ya faɗa yana duban fuskar ƴar ta sa cike da tausayi tana nan a yanayin da take na ban tsoro jikinta gaba daya ya yamutse ya koma kamar jikin tsohuwa ga fuskarta me ban tsoro gashin kanta ya kara tsayi yayi fari kamar kan tsohuwa cikin jikinta yayı ƙasa sosai ta koma kamar ba ita ba kamaninta gaba daya ya sauya.

“Ya Allah ka kawo mana ɗauki,bazan iya jure ganin Siyamata a wannan hali ba,ta koma tamkar ba ita ba. Babansu Yakamata a Kira malamai su zo a cire su a jikinta ina tsoro kar su cutar da ita da abinda ke cikinta.”

Tabbas abinda mama ta faɗa gaskiya ne saboda yanzu basu san wani lokaci zata ɗauka kafin ta farfaɗo ba.

“Hmmm malamai zasu iya cire abinda ke jikin my siyam kuwa?ni na san abinda na gani. karfine da ita tamkar doki. Ina gani a fina-finai pastors ne suke cire fatalwa a jikin mutum “

Cike da takaici hajiya take kallon Mahmoud ji take kamar ta buge masa baki cikin tsawa tace “ dallah rufe ma mutane baki,duk waye ya janyo abin yakawo har haka in ba kai ba?da ace tun farko baka siya gidan nan ba da duk haka be faru ba,da ace ka yarda da abinda yarinyar nan ta ke gaya maka tana gani a gidan nan da duk baa zo nan ba,sannan yanzu kana faɗawa mutane maganar banza…shashasha kawai. Saboda kai ga ka ka je turai shine zaka kwasowa mutane banzan dabi’arsu muna musulmai me ya haɗa mu da zancen pastors”

Hajiya ta gama magana cikin faɗa-faɗa jikin sa ne yayı sanyi jin yanda hajiya take masa faɗa kamar zata tashi ta dake sa.

“Kiyi hakuri hajiya duk wannan faɗar ba shi ne mafita ba a yanzu kamata yayi mu nemo malamai masu cire aljanu”cewar baba.

Ya Ibrahim ya ce “hakane baba na Kira Bilal na faɗa masa abinda yake faruwa nasan yanzu haka yana zuwa dame cire shedanu”

Suna zaune kuwa suka ji horn din motar Bilal mikewa Mahmoud da yan uwansa suka yi suka fito compound din gidan suna jiran fitowarsu.

Kafar sa daya ya sanya ya fito waje tundaga kafarsa zaka fahimci shigarsa da yayi na yan tsubbone yan bori,fitowa yayi babban mutum ne Kayan jikinsa kayane masu yawa da nauyi ga wasu jakukkuna a rataye a hamatar sa kansa na sanye da hula irin na wanzamai baki ne yana da tsayi matsagaici fuskarsa na da gashi sosai sun fara fitar da furfura idanunsa sun sha tozali (kwalli) radau. Ga guru da layoyi da suke daure ta ko ina a jikin kayansa. Wayanda basu san yan bori ba in suka gansa zasu yi tunanin mahaukaci ne,tsayawa yayi bayan ya fito ya ɗaga kai yana ƙarewa gidan kallo. fitowa mataimakinsa da ya kasance matashi yayı shima yana sanye da kayan yan bori se de shi Kayan jikinsa basu da tarkace sosai.

Miƙa musu hannu suka yi suka gaisa sannan suka musu jagora suka shiga ciki a falo kuwa ya zauna kallon mamaki hajiya,mama da baba suke bin mutumin da kuma Bilal da ya kawo sa suke yi. Bilal da ya san maanar kallon ne yasa ya ce “hajiya,mama da baba mu ɗan yi magana mana” miƙewa suka yi suka kebe ta hanyar kitchen

Hajiya ce ta soma fadin “Bilal kai da zaka kawo mana malaman sunnah shine zaka ɗauko mana wannan yan tsubbun?”

“Hajiya nasan dama duk abinda ke cikin ran ku kenan,amma wannan mutanen da ki ke gani sun kware sosai wajen fitar da aljanu da shedanu duk taurin kansu kuwa. Kaf kaduna babu wanda be san su ba. Kawai ku sa kyakyawar niya akan abinda zasu yi.”

“Shikenan Bilal nide fatana Allah ya sa a dace “cewar mama duk suka ce “Ameen” daga nan duk suka koma falon suka zauna.

Ya Ibrahim yace“Barka da isowa yallabai dama abinda yake faruwa shine..” ɗaga masa hannu da mai cire shedanu yayi ne yasa ya dagata batare da ya karasa abinda yake son cewa ba

“Bilal ya faɗa min komai sannan kuma tunda na taka kafata a cikin wannan gida na sake fahimtar komai tabbas akwai jiga-jigan shedanu a cikin gidan nan amma sun haɗu dani karshen su yanzu “

Jinjina kai suka yi domin sun ji dama-dama na damuwar da suke ciki,jin abinda ya faɗa hakan ya tabbatar musu da ya kware wajen aikin sa.

“Tana ina ne ita yarinyar?” Ya tambaya yana mikewa tsaye

“Tana daki a kwance” hajiya ta basa amsa tana yin gaba duk suka bi bayanta. Shiga cikin dakin suka zo yi ya ce bazeyu su shiga ba sede su dakata daga bakin kofar dakin. haka aka yi a yayinda me cire shedanu da mataimakinsa suka shiga. Sosai yake kallon Siyama dake kwance jikinta a sansandare kamar gawa ta koma abin tsoro.

Fito da wata kwalba yayi a jakansa ya buɗe kwalbar ya zuba turaren dake cikin kwalbar a hannunsa ya soma bin kusurwan dakin yana watsa turaren duk wani lungu da sako seda ya bi ya watsa turaren. Sannan ya dawo gaban gadon ya tsaya yana kuma buɗe jakan a karo na biyu ya fito da kaca (chain) me kauri da girma ya ajiye akan gadon kusa da kafanta yana fito da wani farar calbi a jakar sa ƙato yasa a wuyansa ya dube yaron sa gyada kai yaron yayi saboda yasan abinda me gidan nasa yake nufi. Fito da wasu gari yayi fari ya fara zane a ƙasan dakin drawing yayi na triangle sannan ya kuma zana circle a cikin triangle din. Ya ɗauko candle guda bakwai ya zageye wannan zanen da yayi ya kunnasu ya karkade hannunsa ya dubi me gidan nasa yana

“Nagama shugabana “

Gyada mai kai yayi sannan ya dubesu gaba daya suna tsaye a bakin kofa sun yi curko-curko suna kallon abinda ake yi a ciki.

“Kai ne mijin ta?”ya faɗa yana kallon Mahmoud gyada masa kai yayi.

“To ka shigo “

Shigowa Mahmoud yayi ya tsaya yana jiran abinda ze ce masa

“Ka ɗauki wannan kacan ka ɗaure hannayenta da kafafunta a jikin gadon nan da kyau “a sukwane suka kallesa Mahmoud yace

“Ban gane in ɗaure ta a jikin gado ba?ba fa haukacewa ta yi ba. Gaskiya ni bazan iya ɗaure matata ba".

Batare da ya kallesa ba yace”dole hakan zaka yi baka da wani zaɓi hakan shine ze bamu damar yin aikin mu ba tare da an samu mishkila ba.”

Girgiza kai yayi yana komawa baya “noooo ko me zaka faɗa bazan taɓa yarda a ɗaure min mata kamar mahaukaciya ba”

“Nikam Mahmoud kana da hankali kuwa? Idan bazaka iya ba fito ka bawa mutane guri”cewar hajiya cikin faɗa

“Amma hajiya......"

“Ka fito na ce ko,ibrahim je ka taimaka dan Allah” ta faɗa tana mai da kallon ta kan ya ibrahim,yana ji yana gani ya fito a dakin. yayinda ya ibrahim ya shiga ya ɗauki kacan ya ɗaure hannunta na dama sannan ya koma hannunta na hagu shima ya ɗaure. sannan ya koma kan kafafunta suma ya ɗaure su gam. Duk abinda ake yi Siyama ko motsawa sau daya bata yi ba tana nan kwance lifeless.

Zama me cire shedanu yayi a cikin wannan zanen sannan ya tankwasa kafarsa yai zaman me ɗaukan karatu ya rufe idanunsa ya fara wasu irin maganganu a hankali wanda babu wanda yasan me yake cewa saboda basu san wani irin yare bane.

Yakai mintuna goma yana wayannan sambatun. Waral ta ware manyan idanunta da yanzu suka koma ja kamar gaushi tana kokarin fisge jikinta daga ɗaurin da aka mata tana yi tana wani irin gurnani me ban tsoro. Yanda take jijjiga alamu ya nuna sambatun da yake yi kamar yana azabtar da ruhin da suke jikinta domin hatta gadon da take kwance akai shima girgiza yake kamar ze ɓalle. Juyar da kanta tayi izuwa bakin kofar da suke tsaye sun yi jugum cike da tausayinta. Sauke idanunta tayi a cikin na Mahmoud

“Ya Mahmoud ka kwaceni a hannun su ina jin zafi zasu kashe ni,ya Mahmoud babyn mu ya Mahmoud “ta faɗa tana hawaye batare da yayi tunanin komai ba cike da tausayin matarsa ya shigo dakin yana hawaye ya nufi kafarta ze kwance kacan da aka ɗaure ta dashi,me cire shedanu ya buɗe idanun sa yana faɗin

“Tarko ne,ba matar ka bace fatalwan da suke jikinta ne suke son ɗana maka tarko “

Ƙin yarda da abinda ya faɗa yayı yana sa hannunsa ze kwancenta mataimakin me cire shedanu ne ya ja sa baya yana sake jaddada masa abinda mai gidan sa ya fada.

Dariya ta fashe dashi me ƙara gadon da take kwance akai ya tashi sama ya soma juyawa a saman dakin sun matukar tsorata da ganin abinda yake faruwa. gadon in banda juyawa babu abinda yake yi ga ƙaran dariyar da take yi se ƙaruwa yake yi wanda suke jinsa har tsakiyar kwanyarsu yana tayar musu da tsikar jiki. Mama kam ta kasa jurewa kuka kawai take yi tana addua.

Kifa gadon tayi up side down tana kallon ƙasa shi kuma gadon shine a sama dubansu duka tayi

“Kuna tunanin kun kawo mutanan nan akwai abinda zasu iya yi mana ne?,babu Wanda ya isa ya hanamu ɗaukan ruhinsu “

“Dole se kun bar jikinta ko kuma in kona ku dan haka Ina muku gargadi kuyi gaggawan barin jikinta tun kafin raina ya baci”

“Lalalallalalalalalalalalalahhhh gagaggagagagagagagaggag “ wayannan kalmomin take fada a yayinda take datse harshenta jini na zuba a ƙasa tana murmushi

Cikin tsawa yace “ku dena cutar da ita kuna ji mata ciwo ko kuma...! “

Muryanta ne ya soma fita bibbiyu “ko kuma me..!menene zaka yiiiiiiiiiii gagagagaggagagagagagag” ta yi maganar tana ci gaba da furta kalaman da basu san me take cewa ba.

“Ku mazan ku zo amma banda kai “ ya faɗa yana nuna baba,shigowa Bilal da ya ibrahim suka yi Mahmoud dama already yana ciki.

Fito da wasu tattasai danye kore shar yayi ya miƙa musu Bilal ya karɓa

“Duk abinda zaku gani duk abinda ze faru ku tabbatar da kun je can cikin gida in da ya tara ciyawa ku binne wannan koren tattasan sannan ku dawo”

Gyada kai suka yi suka fito a dakin,kallon Kwan wutan dakin tayi nan take wutan dakin da na gidan suka ɗauke ko ina ya zama babu wuta a hankali duhu ya fara mamaye gidan tamkar ba safiya ba.juyawa gadon yayi sannan ya faɗo ƙasa mazauninsa da karfi ta fara fisge-fisge da ihun da kowa seda yasa hannu ya toshe kunnuwansa amma banda me cire shedanu da yaronsa.

Da fitan su suka ga wutar gidan ya ɗauke sannan ko ina ya zama duhu dakyar suke iya ganin gabansu hakan yasa suka fahimci akwai abinda ze faru tafiya suke yi yaƙi ci yaƙi cinyewa amma sun gagara isowa stairs se sun yi tafiya me yawa se su gansu a inda suka fito. waka suka ji ana rerawa a bayan su ko da suka juya babu kowa hakan yasa suka ci gaba da tafiya inda har Allah ya basu sa'a suka sauko down stair kara suka ji a kitchen ana watsa kwanuka a kasa suna fashewa ga duhu basa iya ganin komai wani iska me sanyi ne suka ji ya shafesu ya wuce. Juyowa suka yi nan ma basu ga kowa ba.

“Duk abinda ze faru mu kasance guri daya kar wanda ya yi wani gurin”

Cewar ya ibrahim

Kofar fita a main falo suka isa amma babu kofa a gurin wajen a shafe yake kamar bango,ko ina sun duba a falon amma babu kofa.

“Me ku ke nema?” Suka ji muryar Siyama a bayansu a tare suka juya suka ganta tsaye garau a gabansu hannunta rike da candle ya haskaka kyakyawar fuskarta tana sakar musu murmushi

“Siyama?” Suka fada a tare

“Naam! Me ku ke nema a nan” mamaki ne yakama su ganin ta tsaye gabansu cikin koshin lafiya

“Siyama dagaske ke ce ko kuma gizo ne?”

“Ya ibrahim wallahi nice malam ya gama min magani shine na sauko kasa motsa jiki”

“Alhamdulillah Allah na gode maka da ka warkarmun da Siyama na” cewar Mahmoud fuskansa dauke da murmushin farin ciki. Shima ya ibrahim murmushi yayi saboda ya ji dadin ganin ta a good condition shi de Bilal jikinsa be gama yarda da cewa ita ce ba.

“Ya Bilal me ku ke nema haka?” Yana kureta da ido yace “muna so mu fita ne amma ba mu ga kofa ba”

“Tofah! Ina kofar falon ta ya koma”

Ta fada tana isa gurin kofar itama ta fara duddubawa amma bata gani ba.

Haka ya gama neme-nementa amma bata gani ba.

“Rike min candle din nan ya Bila “ta mika masa karba yayi da dayan hannun dayan kuma yana rike da tattasan da akace su binne.

Cigaba da duba wa suka yi a inda Bilal kuma yana haska musu da candle hannunsa.

“Ya Mahmoud me ku ke yi a nan ?” Suka jiyo muryar Siyama a hankali a bayansu. Wani irin shock ne ya kamasu da yasa suka daskare suka gagara juyawa baya,a hankali suka kai kallon su kan Siyaman da suke neman kofan falo da ita suka ga basamuden namiji sanye da fararen Kaya a gabansu fatarsa baki kiran gashi me tsayi ya rufe masa fuska. Wani irin lugude kawai kirjinsu yake yi kamar ze faɗo,dakyar suka juya baya suka kalli Siyama tana tsaye hannunta da candle gashin kanta yayi buzu-buzu ya rufo mata gefen fuskanta ta dayan gefen suke iya hango mugun kallon da take jifansu dashi.

A tare suka sanya ihu suna mannuwa a jikin junansu,candle din da ta bawa Bilal ne ya zama maciji yana ganin maciji ne yayı wani tsalle yana watsar da tattasan da kuma macijin a ƙasa.

Su hajiya da suke tsaye a bakin kofa ne suka jiyo ihun su Mahmoud a downstairs hakan yasa suka sake mannuwa guri daya cike da tsoro.

Duk su ukun a tare aka kwashesu aka watsar a tsakiyar falon sannan kujeru da duk wani abubuwan falon suka dinga tashi sama suna faɗowa kansu.

“Bazan taɓa barın wani abu ya same ki ba my siyam ko me zan fuskanta” Mahmoud ya faɗa yana laluba inda Bilal yake yana zuwa yace

“Ka bani tattasan ni zanje in binne”

Murya na rawa Bilal ya ce “na yar da su tare da macijin”

Rarrafawa yayi ya bar inda suke yana rarrafe a ƙasa yana lalube ko Allah zesa ya ji tattsan.

Hangosu yayi a ƙasan wani table suna sheki dasauri ya rarrafa har kasan table din ya zura hannunsa kasan yana taɓa tattsan ya saki ajiyar zuciya ya fara kokarin ɗauko sa, amma yaji tattasai yaki matsawa daga inda yake hakan yasa ya sunkuyar da kansa yana leka kasan table din wata jaririyar yarinya ya gani tana wasa da tattasan kara ya sanya yana fincike tattsan da karfi a hannunta sannan ya mike da gudu ya nufi hanyar barin falon koda yaje yaga kofar har yanzu babu wani tunani ne ya zo masa aikuwa yaje da gudu ya daki jikin ginin kawai ya gansa a compound din gidan. ko waigawa bayansa be yi ba ya nufi backyard da gudu yana zuwa ya ɗauki shovel ya soma tona rami nan take iska me karfi ya soma tashi duk da haka be karaya ya bari ba yana gama tonawa ya sanya tattasan a ciki ya binne ya sa kafa ya tattaka gurin da ya mayar da kasa ya rufe,yana gama binnewa kuwa haske ya gauraye gidan sannan wuta ya dawo iskan ya tsaya.

A ciki kuwa ihu kawai take yi tana banbankarewa kwalba me cire shedanu ya fito dashi ya zo inda take ya ɗaura hannunsa a goshinta ya soma sambatunsa irin na dazun se de wanda yake yanzu da karfi ne. Ya buɗe kwalban ya motso dashi daf da bakinta.

“Bazamu taɓa rabuwa da su ba, saboda an sadaukar mana da ruhinsu”

“Karya ku ke yi bazaku iya komai ba” ya fada yana sa yaron sa ya wasa mata wani jan garin magani a kanta.

Ɗaga kanta sama tayi ta fasa wani ƙara da gidan se da ya fara girgiza jijiyoyin kanta da na wuyanta suka fito ɓaro-ɓaro kamar zasu fito waje damkar gashin kanta yayi ya sunkuyar da kanta da karfi seda yayi ƙara,hayaki ne suka fara fitowa ta bakinta da hancinta yana shiga cikin kwalban har suka gama fitowa ya sa murfi ya rufe yana miƙawa yaron sa kwalban a yayinda Siyama kuma ta faɗa kan gadon a sume suffan jikinta yana koma daidai yanda take da cikin kankanin lokaci.

Shigowa Mahmoud yayi ya tsuguna a gadon da take kwance yana me ɗaura kansa a goshinta yana hawayen danasani.

“Sun bar jikinta daga yau. Yanzu suna cikin wannan kwalbar zan tafi dashi zan tabbatar da na tarwatsa ruhinsu. Ita kuma bayan kwana biyu zata farfaɗo. Bayan kwana biyun in ta farka zan turo da yarona ya kawo muku wasu magungunan da zaa mata amfani dasu muna mata fatan samun lafiya.”yana fadar haka ya sa kai ya fita yaron sa ya bi sa tare da su Bilal suka bi bayansa.

“Alhamdulillah Allah mun gode maka Allah ya bata lafiya ya sa iya masifar kenan” cewar hajiya da ta shiga ciki ta zauna. Kowa amsawa yayi da ameen kafin suka samu guri suka zauna.

Nasiha baba ya musu sosai na zaman rayuwa da kuma yarda da juna da goyawa juna baya da sauransu sannan ya musu sallama ya tafi.

Bayan sun yi sallah azahar ne hajiya ta soma magana “ Siyama tana yanayin da bata san a inda take ba dole ana bukatar a samu wanda ze zauna da ita saboda Mahmoud baze iya Lura da ita shi kadai ba kuma yana zuwa aiki. Dan haka İbrahim ka Kira matarka Hajara da Walida su zo su zauna da ita su yi maza su zo kafin mu tafi.”

Sosai sun yarda da hakan kuma hakan yayı wa mama dadi ganin yanda suka damu da ƴarta domin kuwa ita tunaninta zata dauki Siyama ne su koma gıda a yi mata magani a Can amma tunda yanzu ga abinda hajiya ta fada shikenan.

“Mama ni ma zan zauna anan in tayasu lura da anty Siyama “ cewar Fadila

“To shikenan Fadila yanzu de ni kadai zan koma gıda “ murmushi kowa yai

Hajiya tace “aikam tunda ita ta zabi ta zauna da yar uwar ta”

Mahmoud da tunda ya zauna be sake magana ba tunani kawai yake yi yana tuna rayuwar da suka yi na jin dadi da Siyamarsa cikin lokaci kalilan komai ya lalace.amma yanzu tunda an fitar da su daga gidan komai ya zo karshe.

A gidan suka wuni abincin rana kuma Anty Hajara ne da walida driver ya kawo su suka zo dashi,se yamma lis kowa ya tafi suna me yi mata addua samun sauki aka bar Mahmoud,Fadila,anty Hajara,se walida.Mahmoud yana can bedroom din su kusa da Siyam. su kuma suna falo Fadila da komai ya faru a gabanta tana ta basu labarin komai daki-daki.

Sosai suka girgiza jin abinda ya faru su sun dauka abin ba wani serious bane ashe al’amari ne babba.

Your comments means a lot to me,in bakwa comment zan yi tunanin bakwa jin dadin book din ne

Don’t forget to share,comment and like 👍

Se mun haɗu Gobe in Allah yakaimu da rai da lafiya❤️

Kamar yanda ku ka sani bana posting on weekends in aka yi Friday se kuma Monday 🥰

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.