Free chapter · Read without an account

MAKIRIN IKO

by Aisha abbas Bidami · MAKIRIN IKO

☠️☠️ MAKIRIN IKO ☠️☠️

The hunted house 🩸

Jarumai writers association 📚📚📚🖋️🤩

MALLAKIN

MRS ISHAM

05

Walida da Fadila ne suka shiga kitchen suka musu abincin dare da za suci. anty Hajara kuma na falo fitowarta Kenan daga dakin da Fadila take sauka ta idar da sallah mangriba.

“Na san ya Mahmoud kam baze ci nasa a falo ba,kawai ki saka masa se akai masa dakin su”cewar walida yanda ta faɗa haka Fadila tayi sannan ta bata ta kai masa.

Gyara kitchen din tayi ta kai musu nasu abincin falo anan suka ci suka ɗan taɓa hira har karfe goma saura sannan suka shiga dakin Siyama suka tadda ita kwance har yanzu bata farfaɗo ba, shi kuma Mahmoud yana toilet alaman wanka ya shiga domin suna jiyo ƙaran saukan ruwa,gyara mata Kwanciya anty Hajara tayi saboda dazun ta sauya mata kayan jikinta izuwa doguwar riga mara nauyi sannan ta goge mata jikinta da tsumma da ruwan dumi tayi tsaff-tsaff sannan ta fesa mata turare hakan yasa yanzu iya Kwanciya ta gyara mata saboda ta ga kamar wuyanta ya karkace. Ba su fita a dakin ba suna tsaye ya fito sanye da jallabiya

“Sannu da kokari anty Hajara “ ya faɗa yana zama

“Yawwa Mahmoud...mu bari mu je mu kwanta dare yayi,dama mun zo dubata ne da kuma yi maka se da safe”

“Nagode sosai mu kwana lafiya “

“Ameen “ suka nufi nasu makwancin.

Washe gari da sassafe suka tashi suka yi shara da wanke-wanke suka yi mopping din ko ina a gidan tsaf sannan suka shiga kitchen suka yi breakfast.

Wanka yayi ya shirya cikin shigansa na zuwa office yayi kyau sosai sede rashin kwanciyar hankali yasa har ya ɗan faɗa. Manna mata kiss a forehead yayi bayan ya zauna a gefen gadon

“My siyam Allah ya baki lafiya can’t wait to see you on your feet again “ya faɗa yana kissing hannunta da yake rike dashi.briefcase dinsa ya dauka da car key dinsa ya fito suna jera abinci a dining suka ga saukowansa,gaishe da anty Hajara yayi su walida kuma suka gaishe sa yana kokarin fita anty Hajara ta ce

“Ahh ahh Mahmoud ya zaka fita baka karya ba,ga shi kuma an gama komai”

“Bakomai anty Hajara bana jin yunwa in naje office zanci “

“Haba Mahmoud kai da gidan ka a ce se ka fita zaka ci abinci hakan sam be yi ba,bari a saka maka a lunch box “

“Kar ki damu anty Hajara ni zan wuce kar na makara” yana gama magana ya fice duk bayan sa suka bi da kallo kana Walida tace

“Allah sarki ya Mahmoud duk ya zama wani iri saboda halin da anty Siyama take ciki Allah de ya bata lafiya”

Fadila ce ta amsa da ameen banda anty Hajara da ta tsaya kallon walida tana tambayar kanta walida kuma yaushe ta dawo fara son Siyama haka…

“Ku karya mu je dakin na ta “ ta faɗa tana zama,bayan sun yi breakfast ne suka shiga dakin Siyama nan ma aka gyara sa tsaff sannan itama anty Hajara ta goge mata jiki da towel duk abinda ake mata tana kwance kamar gawa.

Bayan isha Mahmoud ya dawo gida ya samu babu kowa a fall. wucewa bedroom din su yayi ya ajiye jakansa yana sakan murmushi bayan ya ɗaura idonsa akan Siyama yana addua Allah ya nuna masa gobe da ran sa saboda mai cire shedanu ya tabbatar musu da gobe-gobe zata farfaɗo hakan yasa yake cikin farin ciki.

Wanka yayi ya kwanta akan gadon yana mannuwa da ita wayarsa ce ya fara ringing ɗagawa yayi yaga Hajiyarsa ce waya suka yi sosai dashi har karfe tara suna waya tana tambayansa ya Siyama din da kuma tambayar sa fatan de yanzu komai lafiya babu komai,sheda mata yayı yanzu komai alhamdulillah babu wani abu da suka sake ji a cikin gidan.

Ajiye wayar yayı bayan sun gama ya musu adduar bacci yana kashe wutan dakin.

Cikin dare suna tsaka da baccin su suka ji ana buga kofan falo dake downstairs ‘bam-bam-bam’ a tare duk su ukun suka farka domin duk sun ji yanda ake buga kofan da karfi kamar za'a ɓallosa.

A hankali Fadila ta kunna wutar dakin tana mannewa da jikin gado cike da tsoro kallon juna kawai suke yi jin buga kofar yaƙici yaƙi cinyewa da wannan tsohon daren waye to ze zo yana buga kofa saboda yanzu karfe biyu ne saura.

Murya ƙasa-ƙasa walida ta ce “ to waye yake buga kofar nan da wannan daren ?”

“Nima abinda nake tunani Kenan ko zamu je mu duba ne?” Zaro ido suka yi suna kallon anty Hajara cike da mamaki

“Tabb wallahi babu abinda ze sauke ni akan gadon nan balle fita a dakin nan har se gari ya waye”

Cewar walida tana dukunkune bargo

“Wallahi anty Hajara nima gaskiya bazan fita ba tsoro nake ji”Fadila ta faɗa tana sake maƙewa a jikin gado. Har lokacin da suke wannan maganar ana buga kofar baa fasa ba girgiza kai anty Hajara ta yi ta zura kafafunta kasa tana slippers

“Anty Hajara in zaki je?”

“Ina ruwan ki “

Ta fice a dakin ta barsu tsumu-tsumu suna jiran dawuwarta. Tana tafiya tana addua a zuciyarta har ta sauka ƙasa. buɗe kofar ta yi taga wayam babu kowa leka kanta tayi waje ta lalleka nan ma ba kowa hakan yasa ta sauke ajiyar zuciya ta ja kofar zata rufe wani hayaki ya shiga falon ta saman kofan batare da ta ankara dashi ba ta rufe kofar ta koma dakin su ta same su yanda ta barosu

“Matsorata kawai naje na duba babu kowa a bakin kofan”

“Hmmm Kenan shi kofan ne yake buga kan sa kenan?”walida ta jefa mata tambaya bata bi ta kanta ba ta kwanta tana juya musu baya su de baccin ma gaba daya kauracewa idanun su yayi saboda abin da mamaki mana duk yanda ake buga kofar nan kamar ana yaƙi amma se a je a tarar da ba kowa a gun.

Wannan hayaki da ya shigo gidan kuwa tafiya ya dinga yi a saman iska har ya shiga bedroom din su Mahmoud sauka yayi bisa jikin Siyama dake kwance lifeless.

Tashi tayi tana rike wuyanta tana tari me karfi cikin baccin sa yaji ana tari kusa dashi hakan yasa ya bude idanunsa ganin ta yayı zaune a tsakiyar gado tana rike da wuya tana tari kamar a mafarki a sukwane ya mike zaune yana kallon ta

“Siyama !?”

“Ya Mahmoud ruwa” da sauri ya kai hannunsa kan bedside drower ya dauki goran ruwan fari ya bude yana kai mata baki tunda ta kafe bakinta a goran bata cire ba seda ta shanye tass .

“Sannu my love “

“Ya Mahmoud yunwa nake ji “ dauko mata kulan abincin sa da su Fadila suka ajiye masa yayi dama sun tsaya sun ci abinci da Bilal a restaurant shisa ma da ya dawo ko ta kan abincin be bi ba. Jallof rice ne shi da kan sa yayi feeding din ta har se da tace ta koshi.

“Ya Mahmoud me yake faruwa dani ne,bana iya tuna komai kaina gaba daya nauyi ya min “

Shafa kumatunta yayi softly ya furta “babu komai my siyam kina lafiya kin ji ko yanzu komai ya zo karshe babu wani abinda ze sake faruwa “

“Allah yasa”ta fada tana kwantawa a jikinsa sun kai mintuna goma a haka babu wanda yace wa dan uwansa kalma daya se Mahmoud da yake shafa cikinta.

Saukan numfashinta ya ji hakan yasa ya gane bacci ya dauketa kwantar da ita yayı yana gyara mata Kwanciya tare da jawo ta jikinsa.washe gari be je masallaci ba shi ya jasu sallah a dakin su bayan sun idar ta shiga ta yi wanka shi ya taimaka mata ta shafa lotion tare da gyara gashinta.

“Ya Mahmoud yunwa nake ji mu je in ɗaura mana breakfast “

Murmushi ya yi yana ɗagota “in de breakfast ne nasan yanzu by this time an kammala”

Zaro manyan idanunta waje tayi cike da mamaki tace “su waye kenan suka yi ?”

“Anty Hajara,walida da kuma Fadila yau kwanan su biyu a gidan nan tare da mu”

Yanayin fuskarta ne ya sauya idonta ya soma ciko da kwalla riƙo duka hannayenta biyu yayi loooking straight into her eyes ya ce

“Why the sudden change Beb?”

“Yanzu ya Mahmoud ashe yau kwana biyu bana cikin hayyacina?”

“Ohhh siyam ki dena tuna abinda ya wuce komai ya zama tarihi kin ji ko? Allah ya kaddara se mun fuskanci wannan jarabawan dan haka ki dena sa kan ki a damuwa,kin ji my love “

Gyada mai kai ta yi suna riƙe da hannun juna suka sauko downstairs suka nufi kitchen saboda anan ne suke jiyo muryoyin su walida kitchen din suka shiga fuskokinsu dauke da murmushi

“La ilah anty Siyama kin farka?”cewar Fadila da karfi tana rungumeta ta. Juyowa anty Hajara da walida suka yi suna kallon su sosai suka yi farin cikin farfadowanta wanda fuskokinsa kadai sun nuna hakan

“Kai Alhamdulillah!alhamdulillah Sannu Siyama.... Allah mun gode maka Sannu mama na”

“Yawwa anty Hajara sannun ku da kokari Nagode sosai da kulawa “tayi maganar ɗauke da murmushi

“Sannu anty Siyama Allah ya ƙara sauki da kiyayewa”cewar walida

“Nagode walida me ku ke girkawa haka an gama ko baa gama ba dan yunwa nake ji sosai kamar in ci babu”

Dariya duk suka yi walida tace “masa muka yi yanzu zaa yanka ganye a yi miya “

“Tom bari in tayaku,ke kuma ɗaga min jiki katuwa dake kin wani manne min” tura baki Fadila tayi saying

“Kai anty Siyama ke baki san yanda na yi missing din ki bane”

“Au haba” ta faɗa tana daukan wuka ta janyo ganye ta fara tsinke su.

“Ayyah Siyama ki bari zamu karasa”

“Anty Hajara dan Allah kar ki hanani ina san in ɗan warware jikina ne ko ya Mahmoud?”

Murmushi yayi yace “ehh Yakamata “

Walida da Fadila zama suka yi a kitchen din shi kuma Mahmoud yana tsaye kusa da siyam dinsa dake yanka ganye,anty Hajara kuma tana sa wainar masa a kula se hiran su suke yi abun burgewa.

Kira ne ya shigo wayarsa ko da ya duba yaga sabuwar number ce hakan yasa ya fito bakin kitchen din ya daga saboda hayaniyar su Fadila baze barsa yayi waya ba.

“Assalamualaykum….da wa nake magana?”

“Sunana haladu mataimakin me cire shedanu”

“Okay malam haladu ykk ya kuma malam yake ?”

“Na Kira ka ne domin in sanar dakai gagarumin matsala na fuskanto ku,,a daren jiya uban gidana me cire shedanu ya rasa rayuwarsa a dalilin ruhin da ya cire a jikin matar ka. yaje binne ruhin a makabarta amma kafin ya isa suka yi hatsari farat daya ya mutu sannan kwalbar ya fashe. ina da tabbacin gidan ka suka dawo kuma wajen matar ka domin iddasa nufin su, tabbas bazasu taɓa Kyale ku ba har se sun ɗauki ruhin matar ka da kuma ɗan dake cikinta…wanann shine abinda na Kira in sanar dakai kayi takatsantsan sosai da matar ka domin yanzu sun dawo ne a fusace zasu iya kashe ta a take ko su kashe wayanda suke kusa da ita na barka lafiya.” Kitt ya kashe wayar sa bayan ya gama sanar dash abinda yasa ya kirasa.

Wani irin zufa ne yake ketowa Mahmoud kallo daya zaka masa ka fahimci yana cikin tsananin tashin hankali dakyar ya iya juyawa yana kallon Siyama da ta ke yanka ganye ta juya masa baya.

Murya na rawa ya ce “Si..siyamaaaa” Duk kallon sa suka yi banda Siyama da take yanka ganye da karfi

Kallon ta suka yi suka kalli kuma Mahmoud din ganin tashin hankali ɓaro-ɓaro akan fuskanshi

“Mahmoud me yake faruwa ne”

“Sun dawo”wannan shine iya abinda ya iya furtawa ya shiga kitchen din yana rungumeta ta baya da karfin tsiya ya juyo da ita nan yaga yanda ta yayyanka hannunta jini se zuba yake ganyen kansa duk ya gauraye da jini.

Kokari yake yaga ya kwace wukar a hannunta dan kar ta kuma yiwa kanta lahani amma ya kasa saboda tafi karfin sa nesa ba kusa ba. Riƙe wajen kaifin yayi ya kwace da karfi se de cikin rashin saa ya yanka hannun sa.

“Innalillahi wainnailaihi rajuun”shine kawai abinda suke faɗa cikin tashin hankali ganin yanda Siyama da Mahmoud suke kokuwa inda daga karshe tayi wurgi dashi cikin cabinet ya faɗi ƙasa kwanuka suka hau zubo masa akai

“Ita din mallakin mu ce bazamu taɓa barın ta ba ruhinta ya zamo mallakin mu”ta faɗa da karfi nan take kwanukan glass da duk wani abu da yakasance na glass a kitchen din ya fara tarwatsewa. Ɗaga idanu tayi ta ta dubi su anty Hajara da suke tsaye a bakin kitchen jikin su rawa kawai yake yi kamar mazari. wuka ta ɗauka ta wurgi walida da shi da azama ta sunkuya wukar ya faɗi a ƙasa,nufo su tayi da wata katuwar wuka Mahmoud dake kwance hannunsa duk fasassun glass sun yanka shi ya miƙe ya damki kafanta

“Ku gudu” be gama rufe baki ba suka nufi falo da gudu shi kuma ya soma kokarin kwatan wukan hannunta da be san inda ta samo sa ba.

“Innalillahi nashiga uku ina wayata take “cewar anty Hajara tana neman wayar ta a kiɗime, dakyar ta hangosa ta ɗauka ta danna kiran hajiyar su Mahmoud ringing daya aka daga nan fa ta kwashe Komai ta fada mata.

A kitchen kuwa Mahmoud gaba daya ya galabaita saboda azabtar dashi da take yi bana wasa bane tunawa yayi da baba ya mata addua kwanaki ta suma hakan yasa ya soma kwararo duk wani addua da ya zo bakinsa aiko ko minti uku baa yi ba ta faɗa jikin sa a sume.

Ɗaukan ta yayi dakyar saboda jikinsa ba karamin ciwo yake masa ba ya kai ta Falo ya kwantar akan kujera 3 seater su Fadila duk suna tsaye akanta sun yi jugum.

“Ya Allah na tuba,meyasa Siyama ?meyasa zasu azabtar min da mata?wani laifi muka yi musu? Da wahalar da ita da kuke yi ku dawo kaina ku min duk abinda ku ke so.ba ruhi ku ke bukata ba ni ku ɗauki nawa amma dan Allah ku har min matata na roƙe kuuuu” ya karasa maganar yana fashe wa da kuka kamar karamin yaro yana tsugunawa a gaban Siyama dake kwance kan kujera yana yin ta ya soma sauyawa irin na baya. riƙe hannunta yayi yana ci gaba da kuka sosai,saboda komai yake faruwa ya ɗaura wa kan sa laifi,na farko ya gane rashin bin umarnin hajiyarsa da beyi bane Allah ya kamasa,na biyu kuma rashin yarda da Siyama da ta sanar masa da akwai mugayen abu amma ya rufe ido yaƙi amincewa da duk wani abinda ta sanar masa.

Sosai jikin su yayı sanyi ganin yanda Mahmoud ke kuka gurfane a gaban matarsa.

“Mahmoud kayi hakuri in sha Allah komai ze zo karshe Matar ka zata samu lafiya kadena daura wa kan ka laifi”

Be ce mata komai ba shi tashin hankalin da yake ciki ma bayajin ze barsa ya fahimci abinda take magana akai sallaman su hajiya ne yasa suka maida kallon su bakin kofan falo hajiya ce da ya ibrahim,Bilal,ya Usama da matarsa safiya,suna shigowa suka zauna suna kallon Mahmoud da kuma Siyama,basu jima da shigowa ba Iyayenta suka shiga suma da wani babban malami kana ganin sa ka ga malami na kware.

Kallo daya zaka wa wayannan ahalin ka fahimci duk suna cikin damuwa.

“Sannu Mahmoud Sannu da kokari”cewar mama cike da tausayawa take kallon su.

Buɗe taro da addua malam yayi ya soma da kallon Mahmoud “ a gaskiya duk wanda ya siyar maka da gidan nan ya munafurceka be faɗa maka komai dangane da gidan ba,duk da komai ya faru da bawa mukaddarine da ga Allah amma akwai ganganci.tabbas kafin mu fara gabatar da komai muna bukatar da ka kira mana dillalin wannan gida,wanda ka siya gidan ta wajen sa”

“Bari na kira sa” Bilal ya faɗa yana danna kiransa bayan ya daga yace dashi in ba damuwa suna bukatarsa da yazo.

Bayan iso wan sa ne malam ya fara yi masa tambayoyi kamar haka

“Shin malam yusuf ka san abinda yake faruwa da wanda ka siyarwa wannan gida?”

“Gaskiya ban sani ba saboda tun ranan da suka tare bamu sake waya ba har rana me Kama ta yau”

Jinjina Kai malam yayi sannan ya kwashe duk abin da ya faru ya sanar masa sosai jikinsa yayi sanyi

“Yanzu kai tsakanin ka da Allah malam yusuf zaka ce baka san abinda yake kunshe a cikin gidan nan ba?me yasa son zuciya ze sa ka kai wasu ga halaka?”

Gyara zama yayi ya ce “kamar yanda na faɗa muku sunana Yusuf Ɗan Ladi kuma ni dilalin gidaje ne dana filaye. Alhaji turaki ne ya siya wannan gidan a hannun daya daga cikin jikokin asalin mamallakin wannan gida wato Attajiri Tahir. Wato tunda Alhaji turaki ya siya wannan gida duk ɗan haya da ya shiga gidan se mugun abu ya faru dasu hakan yasa aka dena kama hayan gidan daga karshe Alhaji turaki ya same ni da batun yana so ya siyar da gidan kwatsam se Alhaji Mahmoud ya nu na ze siya,bayan ciniki ya faɗa ya biyani kudin komai da komai har da saukan da ya bukaci a yi a wannan gidan na koma gida na da niyan washe gari zan turo a yi saukan Qur’ani amma a wannan daren aka min barazana da cewa matukar na sa aka yi sauka to karshen rayuwata ya zo. Wannan yasa na tsorata sosai shine kawai nace musu an yi saukan. Amma ban taɓa sanın akwai mugun a wannan gida na Attajiri Taheer ba”

Tabbas sun gamsu da bayanın sa da kuma gaskiyarsa.

Siyama da tun da ya furta sunan Attajiri Taheer ta buɗe idanunta da suka koma jaaa jini cike a cikinsa ta miƙe tsaye

“Attajiri Taheerrrrr yana ina?ina Attajiri taheer yake bakin azzalumi mara tausayi yana ina ne”

Duk miƙewa suka yi tsaye ganin yanda take magana rai a matukar bace ga jijiyoyin kanta da na wuya ya fito ɓaro-ɓaro ga idanunta da suka sauya nan suka fahimci ba Siyama bace.

“Bazaku faɗa mana inda yake ba ???”ta faɗa a tsawace tana kai dubanta kan dillali Yusuf hannu ta sa a wuyansa ta masa shakan da ko da wasa baze iya kwace kansa ba ta ɗaga sa sama kafafunsa na lilo a iska

“Kai ne nan na ji ka ambaci sunan wannan la’anannen ina yake yanzu yana ina ?????????ka faɗa mana ko kuma ka bar wannan duniyar “ idanunsa ne suka kankance suka koma ciki sun yi jawur numfashinsa na fita dakyar tsabar azaban da yake sha.

“Ku sake sa mu yi magana “ cewar malam

A fusace ta juyo tana kallon malam din tana huci “bazamu taɓa sake sa ba har se ya sanar damu a ina ne Attajiri Taheer ya je ya boye kan sa.”

Furzar da iska malam yayi lokacin da ya fahimci bayan aljanu akwai fatalwaye masu yawa a cikin jikinta wanda suke cike da son ɗaukan fansa.

“Attajiri Taheer yau shekarar sa 49 da barın wannan duniyar Allah ya masa rasuwa “

Gani suka yi ta sako dillali yusuf ya faɗo ƙasa timm ita kuma ta soma ja baya idanunta ya fara zubo da hawayen jini kafin ta zube akan guiwowinta ta fara kuka mara dadin ji muryoyi da yawa ne suke fitowa daga jikinta suna kuka da kururuwa. kuka suke yi me tsuma zuciya wanda zuciyar kowa se da ya karye domin kukan da suke yi kuka ne me ɗauke da ciwo da kunci.

“Meyasa ze mutu ?meyasa ya mutu batare da mun ɗauki fansar mu ba,ya zalunce mu ya rabamu da ta mu rayuwar shine shi ze yi mutuwa cikin sauki,a wannan gidan ya rabamu da ran mu sannan ya kulle ruhinmu a cikin sa har na tsawon shekaru hamsin bazeyu baaaaaaaa dole se mun biya bashin gabanmu da duk wanda yazo hanyar muuuuuuu” ta faɗa da karfi tana dukan tiles nan take inda ta daka ya dare

“Wannan ba dede bane sam. wani ya biya laifin da wani ya aikata wannan shine ake kira da babban zalunci. Attajiri Taheer shine nan ya aikata muku laifi kuma Allah ya karɓi rayuwarsa Allah ne kaɗai ze iya muku hisabi a ranan gobe kiyama. Yanzu wannan duniya da ku ke cikin ta ba na ku bane. dan haka ku bar wayannan ma’aurata su yi rayuwarsu kamar na kowa”

“bazamu Kyale ta din ba,ruhin su ya rigada ya zama namu yanda muka bar wannan duniya haka ita da ɗan cikin ta suma zasu barshi saboda da kyautan ruhine kaɗai zamu samu cikekken ƴancin da muke bukata… shin kun san abinda wannan azzalumin ya aikata kuwa?kun san ahali nawa ya sanya cikin kunci dan kawai ya samu biyan bukatarsa?”

“Na fahimce ku,na fahimci irin zafin da ku ke ji…. Ni ban San Attajiri Taheer ba sunan sa kawai nake ji. Shin ko zaku iya bamu tarihinsa?”

Tana gurfane a ƙasa ta ɗago da idanunta da suka yi jawur ga hawayen jinin da ya bushe a fuskarta ta dube sa

“Mallakar mana da ruhin su shine ze sa mu Kyale mijinta mu kuma zamu tafi duniyar da ya fi cancanta da mu”

“Wannan bashi ne abinda na tambayeku ba muna da bukatar tarihin Attajiri Taheer domin mu san ta inda zamu bullowa abun”

“Bazamu sanar dakai komai ba,idan kana son jin tarihin sa dole se jinin sa shine ze sanar daku komai akan sa”

“Malam Yusuf shin a ina ne zamu samu ragowar ahalin Attajiri Taheer ?”

Don’t forget to share,comment and like 👍

Se mun haɗu Monday in Allah yakaimu da rai da lafiya❤️

Kamar yanda ku ka sani bana posting on weekends in aka yi Friday se kuma Monday 🥰

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.