Free chapter 路 Read without an account
Chapter 14
*IMARA 馃拫 馃拫*
Mikiya writers asso...
Chapter 14
4:30pm
*Da茩ayyawa*
Zaune take kan kujerar katako tana tu茩in tuwo, gaba蓷aya hankalinta baya wajen aikin da take, har yanzu mutuwar Granny bata saketa ba, wani yaro ne ya yi sallama ya shigo yana gara taya, amsa sallamar tayi ya ce"wai ana sallama da matar gidan nan" "sallama kuma?" Tafada tana kallon yaron, "Eh haka ya ce" tashi tayi ta rufe tukunyar tana kallonsa ta ce"je ka ce ina zuwa" da gudu ya fita daga gidan, hijab ta 蓷auko a 蓷akin, ta tsaya tana kallon Imara wacce ke zaune tana wasa 蓷aukanta tayi ta ce"sarkin ha茩uri muje ki rakani" kallonta kawai Imara ta yi ta shiga ta蓳a mata fuska, murmushi goggo Asiya tayi sannan tayi waje. Tsaye ta sameshi jikin bishiyar 茩ofar gidan ya juya mata baya, sallama tayi ya amsa yana juyowa, zabura goggo Asiya tayi ta koma cikin gidan da gudu tana rufe bakinta da hannunta kukan na neman cin 茩arfinta, shigowa gidan ya yi tayi saurin shigewa 蓷aki ta saka sakata cikin kuka ta ke fa蓷in
"Dan Allah kayi ha茩uri, ka barmu da ran mu, wannan yarinyar bata san komai ba, kada ka cutar da rayuwarta, kun kashe kowa nata ku barta ta rayu da wannan ba茩in cikin kawai, dan Allah kayi mata wannan alfarmar... Ka taimaka yaro... Dan...Allah!..."
Ta 茩arashe maganar tana rushewa da wani sabon kukan, tsaye yake har sannan a tsakar gidan hannayensa zube cikin aljihu sai kallon gidan yake ta cikin glasses 蓷in dake ma茩ale a fuskarsa. Shirun da Goggo Asiya taji yasa ta tsagaita da kukan har sannan tana rungume da Imara wacce tafara kuka, a hankali ta bu蓷e 茩ofar ta fito, turus tayi ganinsa zaune kan tabarmar dake shinfi蓷e a 蓷an tsakar gidan, jikinta ne ya fara rawa tana 茩o茩arin komawa ya ce"da kin tsaya kin ji abin da ya kawo ni baba" cak ta tsaya jin sunan daya anbaceta dashi da kuma sanyin murya irin nasa, cikin rawar murya ta ce
"Me zaka cemin yaro?, dan Allah kar kace zaka kasheta" 蓷an murmushin gefen baki ya yi idanunsa na kallon gabansa ya ce
"Idan da naso kashe yarinyar nan da tun ranar na kasheta, idan da banso cetar rayuwarta ba da bazan ce miki ki gudu ba, ban zo nan da niyyar cutar da ita ba, saboda haka ki zauna ki saurareni dan Allah!"
Shiru Goggo Asiya tayi dan gaba蓷aya jikinta ya yi sanyi, tabbas ta yarda ta maganganunsa da yaso cutar da Imara shine zai nuna inda take, zama tayi a hankali har sannan Imara na jikinta, hannunsa ya mi茩o ya 蓷auki yarinyar kasancewar ta saba da 蓷aukar babanta ta wangale masa baki tana dariya, murmushin shima ya yi yana kallonta ya ja mata kumatu. Zaunar da ita ya yi kan cinyarsa ya 蓷auko mata chocolate a aljihu ya mi茩e mata, kar蓳a tayi tana wasada ita, sai a sannan ya mayar da hankali wajen Goggo Asiya wacce ke kallonsu tun 蓷azu.
"Banida kalaman da zanyi magana dasu wajen baki ha茩uri, ita rayuwa ba kai kake da ikon za蓳awa kanka yanda zaka yita ba, nasan abin da aka yi ba'a kyauta ba kuma ba daidai bane, amma haka Allah ya 茩adarta, wannan yarinyar Allah ne ka蓷ai yasan abin da ya 蓳oye a cikin rayuwarta, naji sanda mahaifiyarta ke yiwa kakarta wasiyyar ta kula da ita, na barsu sun tafi dukda na hangesu kuma inada ikon na kashe su a wannan lokacin, wannan sana'ar tawa ba abun arziki ba ce, ban ta蓳a nadama ba sai a lokacin da naga yanda mahaifiyar yarinyar nan ke kukan rabuwa da yarta, an kashe su ba tareda sun aikata wani laifi ba, tun daga sannan nayi al茩awarin barin wannan harkar ta kashe-kashen rayukan al'umma, na biyo su 茩auye ne dan ganin inda yarinyar take kuma na taimaketa idan nasamu dama, sai gashi cikin ikon Allah nasamu damar tseratar da rayuwarta" numfasawa ya yi sannan ya cigaba da fa蓷in
"Inason na nemi alfarma a wajenki, dan girman Allah ki bani yarinyar nan na ri茩eta koda hakan zai sanyayamin zuciya, munyi aure da matata shekaru biyar baya amma ko 蓳atan wata bata ta蓳a yi ba, ki taimaka ki bani yarinyar nan na kula da ita, zan sakata a makaranta kamar yanda mahaifiyarta ta bada wasiyya, nayi miki al茩awarin babu abinda zai samu rayuwarta muddun ina raye, sannan lokaci zuwa lokaci zan dinga kawo miki ita ki ganta"
Tunda ya fara magana Goggo Asiya ke kuka, kallonsa tayi taga shima kukan yake idanunsa zube akan Imara da keta wasa da ledar chocolate, cikin shasshe茩ar kuka ta ce"wlh tsoro nakeji, wannan yarinyar amana ce a wajena, amanarta aka bar min, idan har nayi abin da zai cutar da rayuwarta Allah bazai barni ba, kuma nima bazan yafewa kaina ba, bazan iya kare kaina ba a ranar lahira, duk da zan zo tayi ilimi kodan ta 蓷auki fansar abun da aka yiwa iyayenta amma wlh ina tsoron baka ita, bansan wace rayuwa zata je tayi ba, yarinya ce 茩arama wacce ta gamu da 茩addarar rayuwa tun tana yar 茩aramarta, wa yasan me gobe zata haifar?, bansan wace rayuwa zata fa蓷a ba idan ta bar hannuna ne, wane wanda zai zame mata bangon da zata jingina?, dan Allah kayi ha茩uri!..." Ta 茩arashe maganar tana fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya.
Tashi ya yi ya tsuguna akan gwuiwarsa ya ha蓷e hannayensa biyu waje guda alamar ro茩o yana kuka ya ce
"Ki taimaka ki yimin wannan alfarmar, ki bani yarinyar nan na raineta, ki taimakeni na aikata wannan koda shine ka蓷ai abin Alkhairin da zanyi a rayuwa, ki rufamin asiri kamar yanda Allah ya rufa miki, nayi miki al茩awarin ni zan zame mata bango wanda zata jingina, zan bata kariya da rayuwata, zan bata farin ciki iyakar iya wata, dan Allah ki taimakeni na fito daga cikin wannan 茩angin, ki taimakeni na aikata aikin Alkhairi "
Ya 茩arashe maganar yana kuka, above 5mins kafin Goggo Asiya ta kalleshi cikin sanyin murya ta ce"shikenan zan baka ita, amma dan Allah karka barta tayi kuka a rayuwa, kuma a duk sanda kaga ka gaza da rainonta ka dawo min da ita, zan cigaba da kulawa da ita, ita 蓷in*AMANATA* (upcoming novel) ce, kaji yaro" . Gyara zamansa ya yi yana kallonta ya ce"Nagode sosai Baba, in sha Allah zan kula da rayuwarta kuma zan kawo miki ita a duk sanda kika bu茩ata, ni a cikin garin Dutse nake zaune kinga bamuda nisa Kenan, zan baki lambata da address 蓷in gidana ko dan halin rayuwa" jinjina kai tayi ta ce" tom shikenan, Allah ya baka ikon sauke nauyin da ka 蓷auka" murmushi ya yi ya ce"Ameen ya rabbi" tashi tayi ta shiga 蓷aki ta 蓷auko jakar ku蓷in da granny ta bata ta fito, ajiye masa tayi a gabansa ta ce" wannan iyayenta ne suka bayar saboda a kula da rayuwarta, ka tafi dashi duk abin da take bu茩ata ka siya mata" murmushi ya yi ya tura mata jakar gabanta ya ce" cewa nayi zan 蓷auki nauyin ta, idan har na kar蓳i ku蓷inta kenan ba 蓷aukan nauyin nata zanyi ba, ki ajiye mata wannan ku蓷in watarana idan ta girma zai mata amfani, amma yanzu dai babu bu茩atar su" girgiza kanta tayi ta ce"to, Allah ya yi maka albarka yaro, amma ya sunanka?" Murmushi ya yi ya ce"sunana Mubarak" "to, Allah ya rayaka kaima" "Amen ya rabbi" ku蓷i ya zaro a aljihunsa ya ajiye mata yana tashi ya ce"Baba gashi ba yawa" girgiza kanta tayi kafin tayi magana ya ce"karki damu wannan ba ku蓷in da ake bani bane, wannan da gumina nake nemosu, dan Allah kiyi amfani da su " murmushi kawai tayi dan daman abin da take tunani kenan, 蓷aukan ku蓷in tayi ta ce"To Allah ya biyaka" "Ameen " ya fa蓷a yana murmushi. 茒aukan Imara ya yi a hannunsa ta rako shi har 茩ofar gidan sannan suka yi sallama ya tafi bayan ya bata lambar wayarsa. Ajiyar zuciya ta sauke sanda ya shige motarsa ya bar 茩ofar gidan, girgiza kanta tayi ta ce a fili
"Dan Allah Maryama ki gafarceni, ina nema mata kyakkyawar rayuwa ne".
Zaune yake a 茩asa yayinda shi kuma yake zaune kan kujera yana ka蓷a 茩afa
"Sir duk abin da ka umarce mu muyi mun aikata shi, yanzu babu wani abu wanda ya danganci Major Ahmad wanda bai zama tahiri ba" murmushi ya yi yana kallonsa ya ce"good job, yarinyar da aka gudu da ita akan kamota?" Shiru ya yi sai kuma ya jinjina masa kai ya ce"yes sir, mun kasheta harma da wacce ta tafi da itan" wani killer smile ya yi ya ce "haka nakeson ji" wata jaka ya 蓷auko ya ajiye masa a gefensa ya ce" ga shi nan kowannensu ya 蓷auki 5millions, kai kuma ka 蓷auka 7m" dur茩usawa ya yi yana murmushi ya ce"godiya muke mai gida, Allah ya ja zamaninka, duk wanda zai shigo hanyarka sai mun tabbatar da cewa mun kawar dashi, mu naka ne har abada oga" jinjina masa kai ya yi ya 蓷auki wani glass cup dake gefensa ya ce"you can leave" tashi ya yi ya 蓷auki jakar ya sake masa godiya sannan ya yi waje.
Tun da ya fara magana take kallonsa har ya gama, tashi tsaye tayi hawaye fal idanunta ta ce"yanzu me kake nufi Mubarak?" cikin sanyin murya ya ce"ina nufin mu raineta har ta girma tunda mu Allah bai bamu haihuwar ba!" Girgiza kanta ta shiga yi tana kuka ta ce"wato abin har ya kai haka?, saboda ban haihu ba!?, dan har yanzu ban haihu ba shine kaje ka 蓷auko tsintacciyar yarinya kace na raina?" With so much surprised Mubarak ke kallonta zai yi magana ta cigaba da fa蓷in " bafa zaka rainamin hankali ba Mubarak!, kai kayi ka蓷an, ni bari kaji ma wlh ban yarda iyayenta ne suka mutu ba saidai idan can kaje ka yi cikinta wata ta haifeta yanzu ta baka yarka, ni kuma na zauna haka har 茩arshen rayuwata saboda kawai ina sonka to wlh bazai yiwu ba!, baka isa ba!, na rantse bazan ri茩e ta ba!"
"Inna'lil lahi wa ina ilayhi raji'uun, Ni Suhaila!?, Ni!, Ni kikewa kallon mazinaci?" Turo baki tayi tana harararsa ta ce"to ai abune a duhu wa ya san abin da kake aikatawa" ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce"abar wannan maganar, ni ba tashin hankali nakeson muyi dake ba, bance sai kin shayar da ita ba, zan dinga siya mata madara har ta isa yaye, amma dan Allah ki dinga yi mata wanka kina saka mata kaya, ta zauna a wajenki idan na fit..."
"Na rantse da Allah bazan yi ba!"
Ta katse shi kafin ya 茩arasa fa蓷ar abin da ya yi niyya. Rasa me zai ce mata ya yi kawai ya tsaya yana kallonta, harararsa ta yi cikeda tsiwa take fa蓷in
"Bari kaji, idan kanason zaman lafiya dani to ka fita da wannan yarinyar daka cikin gidan nan, idan ko ba haka ba zakaga abin da zan yi yanzun nan" tashi tsaye ya yi yana kallonta ya ce"me zaki yi?" Kallonsa ta yi ta ce"babu abin da ya dameka da abin da zan yi, kuma ba sanar dakai zanyi ba, abin da nakeson ji shine zaka fita da ita ko bazaka fita ba?"
"Bazan fita da ita ba!"
Ya fa蓷a yana kallonta, waro manyan idanunta tayi tana kallonsa, tunda suke bai ta蓳a yi mata irin haka ba, baya ta蓳a zallake maganarta saboda irin yanda suke son junansu, sai gashi yau suna fa蓷a akan IMARA. Kuka Imara ta saka ya juya yana kallonta, zaune take kan kujera tana sanye da wasu sabbin kaya daya siya mata, 蓷aukanta ya yi yana jijjigata, 茩arar da cikinta ya yi ya tabbatar masa da yunwa take ji ya dafa cikinta cikin sanyin murya ya ce
"Sorry marh gurl, muje na siya maki madara" daga haka ya fita daga cikin parlon ba tareda ya sake kallon Suhaila ba, da gudu ta shige 蓷aki tana kuka kamar ranta zai fita.
***Around 8am ya shigo gidan hannunsa ri茩e da Imara sai wasa take da doll 蓷in daya siya mata, siyayya sosai ya yo mata ta kayan sakawa da mayuka sannan ya siyo mata madarar dan baiga alamar tana cin wani abu ba, a parlon ya ajiyeta ya shiga kitchen ya ha蓷o mata madarar ya dawo ya zauna yana bata, tunda ta kafa kanta jikin feedar bata cire ba sai da ta shanye tass, cirewa tayi ya kalleta yana murmushi ya ce" a 茩aro?" Kamar taji me yace ta gya蓷a masa kai tana 茩ura masa idanu, wata ya sake ha蓷a mata ya bata tasha. Tana gama sha kamar wacce ke jira tafara bacci hankalinta kwance, tashi ya yi ya kai ta 蓷aki sannan ya shiga 蓷akin Suhaila amma ga mamakinsa sai ya samu bata ciki, fita ya yi ya dawo dan duk zatonsa tana ban蓷aki saidai har yayi wanka ya shirya ya dawo Suhaila bata fito ba, sunanta ya kira yaji shiru hakan yasa ya tura 茩ofar ban蓷akin amma sai yaga wayam babu ita babu dalilinta, duk inda ya kamata ya duba a gidan saida ya duba amma bai ga Suhaila ba, har ma茩ota ya shiga bai ganta ba hakan yasa ya dawo gida ya 蓷auki waya ya shiga kiranta, ringing 蓷in duniya bata 蓷auka ba daga 茩arshe ma sai ta kashe wayar tata. Zaunawa ya yi a parlon ya dafe kansa ko ba'a fa蓷a ba yasan Suhaila gidansu ta tafi, dan damar gwanar 茩orafi ce. Daren ranar haka ya kwana a parlon ba tareda ya yi bacci ba, da yaga lokaci na tafiya a banza ya tashi ya 蓷auro alwala ya fara salloli yana ro茩on Allah ya gafarta masa zunubansa, har akayi sallar asuba yana zaune sai a sannan ya tashi ya le茩a 蓷akin da Imara ke kwance, bacci ya tarar tana yi har sannan sai kawai ya rufe mata 茩ofar ya fito harabar gidan wacce batada girma ya shimfida sallaya ya bi jam'in anan.
***Around 9am ya yi parking a 茩ofar gidan, a hankali ya fito daga motar ya shiga gidan yana tunanin abin da zai je ya tarar, a babban compound 蓷in gidan ya tsaya ya aika mai gadin domin ya yi masa iso,saida aka ce ya shigo sannan ya shiga. A parlon Daddy aka kaishi bayan sun gaisa ya kalleshi ya ce"Mubarak me ya ha蓷aka da Suhaila?" Cikin ladabi ya bashi labarin duk abin da ya faru, Daddy bai ce masa komai ba yasa akayi kiranta suka shigo ita da Mommy idanunta ya kumbura da alama taci kuka, bayan sun zauna Daddy ya kalleta ya ce"yanzu Mamana mene a ciki dan kin ri茩e marainiya?, kinsan ladan ri茩on maraya kuwa?" fashewa tayi da kuka ta ce "ni wlh Daddy bata yimin ba, kuma kawai ya mayar da ita wlh indai ni ce bazan ri茩eta ba!" Kallonta Mubarak ya yi bai ce komai ba, Daddy ya ce"ya maidata ina?, ki ma bar wannan maganar, kawai magana 蓷aya ce yanzu kai Mubarak tunda kanason ka ri茩e yarinya to ka samo mata mai aiki wacce zata dinga rainonta har zuwa sanda zatayi hankali ke kuma ki koma gidan mijinki"
"Ta koma ina?, wlh babu inda zata je!, indai har bazai mayar da wannan shegiyar yarinyar da ba'a san asalinta ba saidai ya saketa!".
# Bestnovel
# IMARA 馃拫
# Lolo
# Nanameera
# 2025.