Free chapter 路 Read without an account
Chapter 15
IMARA 馃拫馃拫
Mikiya writers asso...
Chapter 15
Da sauri Mubarak ya 蓷ago idanunsa yana kallon Mommy, harararsa tayi ta ce"Eh ka kalleni da kyau!, wlh saidai ka za蓳a ko Suhaila ko kuma yarinyar kaji na fa蓷a maka!" Ta 茩arashe maganar tana haki, girgiza kai Daddy ya yi yana kallon Suhaila ya ce"ke tashi ki bi mijinki, kai kuma Mubarak ka nemawa yarinyar mai raino kamar yanda nafa蓷a maka" har 茩asa ya sunkuya cikeda ladabi ya ce"Nagode sosai Daddy, Allah ya 茩ara girma" "Ameen" cewar Daddy yana cigaba da kallon labaransa, tashi ya yi yana kallonta ganin yanda take tura baki gaba kallon iyayen nata tayi sannan ta yi waje fuu kamar zata tashi sama. "Gaskiya yalla蓳ai wannan ba shawara ba ce ya yarinya zata kawo kuka miji ya yi mata abin da bai dace ba sannan ka ce mata ta koma without taking any action, nan gaba idan ya sake mata abu ai ba zata ji kwarin gwiwar dawowa gida ba"
"Kwarin gwiwar!?, au daman akwai wata kwarin gwiwa a yin yaji?, mene ne abun tashin hankali anan?, dan ya ce zai ri茩e yarinya shine ya yi laifi?, tunda su Allah bai basu haihuwar ba, ba zasu 蓷auki na wasu su raina ba kenan?, saboda ku mata 茩wa茩walwarku 茩arama ce!"
"Amma yalla蓳ai..."
"Kar na sake jin bakinki akan wannan maganar, na rufe babinta" shiru Mommy ta yi ba tareda ta so hakan ba.
***Yana gama parking 蓷in motar tayi waje kamar zata tashi sama da, da idanu Mubarak ya bita har ta shige gidan, ya girgiza kansa kawai sannan ya gyara parking 蓷in motar ya fito. A parlon ya sameta tana zaune ta ha蓷e kai da gwiwa tana kuka, zama ya yi gefenta yana kallonta ya ce "Suhaila nayi tunanin komai ya wuce ai?" Tashi tsaye tayi tana watsa masa wani kallo ta ce"ya wuce yaje ina?, to bari kaji babu abinda ya wuce wlh, muddin wannan yarinyar na cikin gidan nan to ka dinga gamuwa da 蓳acin rai kala-kala kenan, idan kai baka fasa ba nima bazan fasa ba!" ta juya ta bar parlon, dafe kansa ya yi na rashin sanin abin yi, tunawa ya yi da Imara hakan yasa ya tashi ya 蓷auki car key 蓷insa ya yi waje. Gidan ma茩otansa ya yi sallama bayan an yi masa iso ya shiga, zaune ya samesu suna hira Imara kuma na gefenta sai wasa take abin ta, zama ya yi suka sake gaisawa sannan yayi musu godiya, murmushi Sulaiman ya yi ya ce "haba ai babu komai Mubarak, duk abinda Suhaila zata iya maka ai Fatima ma zata yi maka shi" jinjina kansa ya yi yana murmushi ya ce"ai ko Nagode sosai, yanzu daman wata alfarma nake nema a wajenki Fatima"
"Alfarma kuma?"
Jinjina kansa ya yi ya ce, "Eh, dan Allah idan babu damuwa inason ki samo min wacce zata dinga rainon Imara, amma irin babba mai hankali nakeso wacce zata ri茩eta da amana" murmushi Fatima tayi ta ce"indai wannan ne babu damuwa bari yanzu na kira wacce take kawo min yan aiki naji", ajiyar zuciya ya sauke ta samun sau茩i, ko babu komai zai bawa Imara irin kulawar da yake son bata, duk da zuciyarsa cike take da tunanin yanda rayuwarsa zata kasance muddin oga ya gane baya tare da su, har aka kira wayar yana wannan tunanin, bayan matar ta bata tabbacin za'a samu, sosai ya yi farin ciki sannan ya gode musu ya tashi zai 蓷auki Imara
"Tunda dai nasan yanzu Maybe fita zaka yi to wajen wa zaka barta a gidan?" Fatima ta fa蓷a tana kallonsa, girgiza kansa ya yi fuskarsa 蓷auke da damuwa ya ce"to ya zan yi, da tafiya zanyi da ita" girgiza kai tayi ta ce"a'a a wannan sanyin, kawai ka barta anan zan kula da ita har anjima mai rainonta ta zo" murmushi ya yi ya ce"Nagode sosai da karamci Fatima" murmushi ta yi bata ce komai, sukayi sallama da Sulaiman sannan ya fita yana tunanin ina ma Suhaila ce ta ke yin haka.
Washegari da safe bayan sun gama breakfast ya shiga gidan Sulaiman ya samu har mai rainon ta zo, babbar mace ce kuma kana ganinta kaga mai hankali, da alama ba yar 茩auye ba ce dan babu alamar hakan a tattare da ita tsananin kuncin rayuwa ne kawai, zama ya yi ya lissafa mata abubuwan da yakeson ta dinga yi wa Imara kuma ta amince da hakan, sannan ya dan茩a mata Imara a hannunta. Godiya ya sakewa Fatima sannan suka bar gidan, a corridor 蓷in gidan ya nuna mata wani part suka shiga, parlon ne madaidaici sai kitchen a cikinsa sai wani 蓷akin kwana mara girma da ban蓷aki a ciki, kallonta ya yi ya ce "yawwa Baba nan ne inda zaku dinga zama" jinjina kanta tayi ta ce"tom Alhaji mun gode" murmushi ya yi ya ce"babu komai, zuwa anjima zan fita nayi muku siyyayar abinda zaku ci da kuma na amfani, nidai fatana kawai ki ri茩e yarinyar nan da amana dan marainiya ce" girgiza kanta tayi ta ce"Allah sarki, Allah ya ji茩an iyayenta, in sha Allah ba zaka samu wata matsala daga 蓳angarena ba zan kula da ita iyakar iyawata in sha Allah" sosai ya ji da蓷in haka ya yi mata sallama ya fita. Kai tsaye 蓷akinta ya shiga tana tsaye jikin curtains 蓷in 蓷akin ta kalleshi murya kasa 茩asa ta ce" wace wannan wacce ka shigo da ita?" yana cire agogon hannunsa ya ce"wacce zata raini Imara ce tunda ke ba zaki iya ba!" harararsa tayi tana ta蓳e baki ta ce"Eh bazan yi ba tunda ba dolena ba ce, ba zan raini 拼ar da bansan taya aka haifeta ba" a fusace ya 蓷ago yana kallonta cikin wata kakkausar murya ya ce"ki dinga sassauta kalamanki akan yarinyar nan Suhaila idan ba haka ba zan baki mamaki wlh"
"Me zaka yi!?, Na ce me zaka yi?, zaka sakeni ne?, idan zaka iya sakeni Mubarak!, na ce ka sakeni!"
Kwafa ya yi sannan ya juya ya bar wajen ba tareda ya tanka ta ba, harararsa tayi sannan ta fice daga 蓷akin itama.
6yrs later (Bayan shekaru shidda)
Zaune take tsakar gidan tana wanke-wanke, banda ta蓳a kwanukan babu abinda take yi dan babu alamar tama iya wanke-wanken, gashin kanta ne duk ya rufe mata fuska hakan ya sa ta mi茩e tsaye tana tsalle sai kuma ta fashe da kuka, da gudu ta fito tana kallonta ta ce"Imara lafiya?, me ya saka ki kuka?, wane ya sakaki wanke-wanke?" 茦arasawa wajenta tayi tana kuka ta ce a shagwa蓳e "Umma gashina ne!, gashina ne!, ni ki ha蓷e min shi" ta 茩arashe maganar tana bubbuga 茩afa, murmushi tayi ta ce"Allah ya yaye miki wannan rigimar" turo baki tayi, girgiza kai Umma tayi sannan ta ha蓷e mata gashin kan nata irin na larabawa sak ta 蓷aure mata waje guda, nan fuskarta ta fito sosai, kyakkyawa ce ajin farko dan ko ba'a fa蓷a maka ba kasan ma jinin yan Nigeria ba ce ba, kallon idanunta wanda suka kasance manya tayi sannan ta ce "me ya sameki a fuska?, naga tayi ja?" Turo baki ta yi ta ce "ba Aunty ce ta dakeni ba, kuma ta ce nayi mata wanke-wanke, kuma ta ce idan na fa蓷awa Daddy sai ta yanka niii!"
"What!?"
Suka ji saukar muryarsa a bayansu, girgiza kai Imara ta shiga yi ta rufe bakinta da 蓷an 茩aramin hannunta, 茩arasowa gabansu ya yi ya kama hannunta cikin sanyin murya ya ce"me Aunty tayi miki?" Girgiza kanta ta yi, ya daka mata tsawa. Fashewa tayi da kuka ta shige jikinsa jikinta na rawa, rungumeta ya yi yana shafa bayanta ya ce"shikenan ya isa fa蓷amin me tayi miki?, laifi kika yi mata?" Girgiza kanta tayi cikin shasshe茩ar kuka ta ce"indomie nakeso shine kuma babu anan, na shiga ciki zan 蓷auka shine ta mareni ta ce nayi mata wanke-wanke, amma dan Allah Daddy karka fa蓷a mata ta ce idan nafa蓷a maka sai ta yanka ni, ni banason na mutu Daddy!!" Sosai ransa ya 蓳aci bai ce komai ba ya kama hannunta suka shiga gidan, zaune suka sameta tana cin cake tana kallon draman da ake a MBC Bollywood,
"Me tayi miki da har zaki 蓷auki hannu ki mareta?, a matsayinki na wa?, akan me zaki sakata aikin da yafi 茩arfin shekarunta?, ke koma aikin da zata iya ne ki a matsayinki na wa zaki sanyata aiki?" Tashi tsaye tayi tana kallonsa baki a bu蓷e,
"Bari kiji bakisan wahalarta ba, baki raineta ba, babu abin da ya ha蓷aku saboda haka karna sake jin kin shiga harkarta, idan ko haka ba wlh saina 蓳ata miki rai!"
"Okay, saboda na saka yar da ake ri茩o a gidana aiki shine laifi?, ko kuwa dan na hukuntata?, kenan babu wanda ya isa ya gyara mata idan tayi ba daidai ba?, naga..."
"Akwai mana!, akwai mutanen da suka dace su gyara mata idan tayi kuskure, amma ke bakya 蓷aya daga cikinsu, bakida wannan damar, baki isa ba!, ke baki kai ba, saboda haka ki kama kanki, idan har kika cigaba da irin wannan nuna kin isan da ita zan baki mamaki!"
Yana gama fa蓷in hakan ya kama hannun Imara suka yi waje, part 蓷insu ya mayar ya daina ya zauna yana kallonta ya ce"kiyi ha茩uri kinji, bari zan fita sai na siyo miki man zafi, kinyi karatu sosai a school ko?" Murmushi tayi har saida beauty point 蓷inta ya loma ta ce"Eh Daddy, uncle John ya ce nafi kowa 茩o茩ari a class 蓷in mu, naji da蓷i Daddy" murmushi ya yi ya ce"yawwa, that's my girl, keep it up kinji, inason kiyi karatu sosai ki zama lawyer "
"Lawyer kuma Daddy?, why not Doctor?" Girgiza kai ya yi ya ce"No, lawyer nakeson ki zama kinji" gya蓷a masa kai tayi ta ce"your command is my wishes Daddy" girgiza kansa ya yi yana dariya ya ce"yawwa Baby na, yanzu bari naje nayi wanka, zan zo muje shopping" tashi tayi tana tsalle ta ce"yehh, daman inason siyan chocolate da Pringles" murmushi ya yi ya ce"oyha je ki shirya ki zo mu tafi " da gudu ta shige bedroom 蓷in ya girgiza kansa sannan ya yi waje.
***Kallonta tayi ganin har sannan batayi shiru ba ta ce"wai ke idan ba zakiyi shiru ba ki tashi ki bar nan, tunda kika zo kike kuka, nayi miki maganar duniya kin yimin banza, tun da ba zaki fadi abin da ya kawo ki ba sai ki tashi ki bani guri" shasshe茩ar kuka ta fara tana kallonta ta ce"Mommy wlh nagaji, nagaji da abin da Mubarak yake yimin akan yarinyar nan, kwata-kwata baya kulani, idan kinga ya yi min magana to saidai akan yarinyar nan, yana fifitata akan komai Mommy, ni bansan me nayi masa ba, kuma ban isa na hukunta yarinyar ba sai ya hau yimin bala'i kamar zai dakeni, ya zanyi Mommy?, ya zan masa, nagaji wlh, idan babu dama sai na ha茩ura da auren nasa!"
"Ki ha茩ura!?, ki ha茩ura fa kika ce?, bama kida hankali, kenan wannan yarinyar da aka haifeta a gabanki ita zata fitar dake daga gidan mijinki, to idan kin fito sai ki auri wa?, kinsan dai babu mai aurenki bakya haihuwa shima 蓷in saboda yana cin arzikin ubanki yake zaune dake, amma badan haka ba tuni wani zancen ake. Ke bakida wayo, cikin ruwan sanyi zaki fitar da ita, akwai wata 茩awata wacce ta ta蓳a sakawa aka yimin aiki akan Alhaji naga bai ci ba na ha茩ura bari na kirata ta zo ta rakamu muje ayi ta ta 茩are"
Goge hawayenta tayi ta ce"ni Mommy so nake kawai a kasheta kowa ma ya huta, ko kuma a haukatar min da ita".
# Bestnovel
# IMARA 馃拫
# Heart touching 馃挃
# Nanameera
# 2025.