Free chapter 路 Read without an account
Chapter 39&40
*IMARA 馃拫馃拫*
39&40.
***.
Mikiya writers asso...
Ajiyar zuciya Abaan ya sauke yana kallon Abbiey ya ce"Abbiey why?" Girgiza kai ya yi cike da damuwa ya ce"Muhammad abun ne ya fi 茩arfina ka dai san halin kakarka, bansan mene ya sameta ba da har ta yanke irin wannan hukunci, ba zan iya yi maka dole akan auren Jidda ba amma ina tunanin abin da zai je ya dawo. Shiru ya yi yana kallon Abbiey kafin ya mi茩e tsaye ya yi hanyar fita daga parlon
"Ka aikata abin da Jadda ta umarceka Abbiey"
Da sauri Abbiey ya juyo ya kalleshi zuwa sannan kuma ya fice daga falon. Ajiyar zuciya ya sauke yana godiya ga Allah domin da Abaan bai yarda da auren nan ba bai san abin da zai ce da Jadda ba.
***Tun da ta shiga 蓷aki ta nemi waje ta zauna, haka kawai ta ji ba ta jin da蓷i zuciyarta na bugawa da 茩arfi, bu蓷e 蓷akin a kayi ta 蓷aga idanun ta kalli Nana wacce ta shigo 蓷akin, zama ta yi gefenta tana murmushi ta ce"shine yau ki ka 茩i zuwa makaranta ko?, muna ta jiranki baki fito ba" cikin sanyin murya Imara ta ce"to ai na je wajensa ne kuma shine ya ce ba zan je makarantar ba"
"Wane haka?"
Turo baki ta yi ta ce"wannan mana, babban yayan gidan nan" tuntsirewa da dariya Nana ta yi ta ce"wai Yaya?" Gya蓷a mata kai ta yi, Nana ta ce "lallaima, to Yaya Abaan sunan sa, Babban soja ne da kike ganinsa kuma ba 蓷an 茩asar nan bane" ta蓳e baki Imara ta yi, kamar an tsikareta kuma ta gyara zamanta tana kallon Nana ta ce
"Ki ka ce Soja ne?"
Gya蓷a mata kai Nana ta yi, Imara ta tashi tsaye ta fara tafiya a 蓷akin tana murmushi, biyo bayanta Nana ta yi tana kallon ikon Allah, ganin kamar ta samu matsala yasa ta 蓷an dafata can 茩asa da murya ta ce
"IMARA"
Juyowa ta yi sai kuma ta rungumeta tana dariya ta ce"wlh ina son shi, shi nakeso ni, ina sonshi sosai wlh, kuma shi zan aura"
A fusace Nana ta ture ta daga jkinta tana yi mata kallon kin yi hauka ta ce"me ki ka ce?, kina cikin hayyacinki kuwa?, Yayan ki ke so?, Yaya Abaan 蓷in?, kinsan kuwa wane shi?"
茒aga kafa蓷a Imara tayi irin bai dame ta ba ta ce"ni fa babu ruwana da ko wane shi, jami'in tsaro nakeso na aura kuma gashi na same shi, I'm so lucky wlh"
Nana was speechless, sai bin Imara take da kallo tamkar wata zararriya. Girgiza kanta kawai ta shiga yi dan da alama wasu aljanun sun shiga jikin Imara ba tare da kowa ya sani ba.
***Around 9pm ya shigo hannunsa ri茩e da wasu ledoji guda biyu, kai tsaye apartment 蓷in Jadda ya shige, zaune ya sameta kan ladduma tana jan tsazbaha, zama ya yi a 茩asa kusa da ita har sai da ta idar sannan ta juyo ta kalleshi, murmushi ya yi ya ce"Jadda" ajiyar zuciya ta sauke ta shafa kansa ta ce"Abaan, sannu ka ji, sannu da 茩o茩ari, Allah ya yi maka albarka" lumshe idanunsa ya yi ya 蓷ora kansa bisa cinyarta, sosai ta ji tausayin sa, a duk san da ya yi mata haka ta gane kewar mahaifiyarsa yake. Shafa kansa ta shiga yi tana karanto masa addu'o'i, tana jin yanda yake sauke numfashi a hankali har bacci ya yi gaba da shi.
Sanye take cikin wata doguwar riga ta atampa, a-shape ta rufe gashin kanta da wani veil ya zubo ta bayanta, a hankali take tafiya fuskarta fal murmushi. Zaune ta sami su Umaima suna cin abinci ta zauna a kusa da Umaima tana kallon Nana wadda ke yi mata wani irin kallo kamar me tsoronta. Dariya Imara ta yi, Umaima ta kalleta ta ce"Lafiya dai Imara?" Nuna mata Nana ta yi wadda ke faman zare ido. Dariya ita ma Umaima ta yi ta ce"lafiya me aka yi mata?" shiru Imara tayi har sannan murmushi take. Harararta Nana ta yi ta ce "ni ki daina kallona" gwalo ta yi mata ta ce"na kalla 蓷in, ni zo ki ga" a hankali Nana ta taso ta dawo inda take zaune ta zauna ita ma, kallo Umaima ta kunna a wayarta hakan yasa suka fasa aikin suka maida hankalinsu kan kallon da suke. Kiran wayar Umaima a aka yi hakan yasa ta tashi ta bar wajen, murmushi Nana ta yi ta ce"ki ce masa ina nan ina jiransa a Naija" harararta kawai ta yi ta shige kitchen da sauri. Kallon Imara Nana ta yi ta ce
"Wai ke ina wayarki ne?"
Ta蓳e baki ta yi ta ce"ya kwace min, ni so ma nake na ganshi" harararta Nana ta yi ta ce"wlh ki fita a harkarsa tun kafin ki jawowa kan ki Tom, gwara ma ki cigaba da magana da sir sai ya fi miki, 蓷azu ma na ganshi ya shiga apartment 蓷in Jadda kuma har yanzu bai fito ba" zumbur Imara ta mi茩e ta bar wajen, da idanu kawai Nana ta bita sai kuma ta girgiza kanta.
***Wani ihu Umaima ta saki wanda y saka Nana shiga kitchen 蓷in da sauri. Tana ganinta ta rungumeta tana dariya ta ce
"Yaya ya dawo, Yaya ya dawo Nana, I'm so happy wlh" ihu suka sake saki a tare daidai nan Mamah ta shigo kitchen 蓷in, kallonsu ta yi ta ce
"Mene haka?, meke damunku?"
"Mamah Yaya Kamal ne ya dawo daga Uk kinga kuwa dole mu yi murna, yanzu ma zamu fara tunanin abin da zamu yi masa gobe idan ya zo ne"
Numfasawa Mamah ta yi ta ce"to sannun sa da dawowa, amma dare ne wannan ihun ya yi yawa, ku je ku kwanta" to kawai suka ce sannan suka yi hanyar fita.
"Ina Imara ne?"
"Taje apartment 蓷in Jadda"
Okay Mamah ta ce sannan ta cigaba da abin da take.
***A hankali ta tura 茩ofar falon ta shiga bakinta 蓷auke da sallama, zaune ta hangi Jadda, shi kuma har sannan yana kwance akan cinyarta. Murmushi Jadda ta yi ta ce"au Yarinyar kirki ke ce anan?" gya蓷a mata kai Imara ta yi sannan ta 茩araso inda take ta zauna tana murmushi ta ce"daman zuwa nayi na gaisheki Jadda"
"Da gaske, kai amma na ji da蓷i sosai Yarinya, Allah ya yi miki albarka" murmushi kawai Imara ta yi, Jadda ta ce"kuma ina da wani alkaki da aka yomin, gashi wannan sangartaccen yaron ya zo ya wani kwanta min a jiki" dariya Imara ta yi ta ce"to ki tashe shi Jadda man" girgiza kai Jadda ta yi ta ce"a'a fa, ai ba'a tashin sa yana bacci tun yana yaro" jinjina kai Imara ta yi sai kuma ta le茩a fuskarsa, ha蓷e rai ta ga ya yi ta 蓷ago ta kalli Jadda ta ce
"Wlh Jadda yana ji ba bacci yake ba, kinga ya motsa ko?"
Da sauri Jadda ta kalli inda Abaan yake sai kuma ta ce"ke bacci man yake, ina jin saukar numfashinsa 蓷azu"
"N rantse Jadda ya tashi, bari kiga" tana fa蓷in haka ta tashi ta koma daidai inda fuskarsa take ta kwalla 茩ara. Da sauri Abaan ya tashi zaune ya shiga bin ta da idanu. Tuntsirewa ta yi da dariya tana kallon Jadda ta ce"kin gani ko, wlh ya tashi daga baccin fa" kallonta Jadda ta yi sai kuma ta kalle shi ta ce"kaga 茩aton banza, kai yanzu da ba baccin gaske ka ke ba ka bi ka taushe min 拼ar ragowar cinyar tawa" langwa蓳ar da kai ya yi kamar 茩aramin yaro ya ce"Jadda bacci fa nake ji"
"Sai ka tashi ka je 蓷akin ka ka kwanta ai. Amma da ka bi ka danne ni, ga nauyi kamar me Allah na tuba. Yarinyar kirki na gode miki, zauna anan na kawo miki abin da蓷i"
Gya蓷a mata kai Imara ta yi tana murmushi, kwafa Abaan ya yi ya kalleta kawai bai ce komai ba, wata robar dambun kaza Jadda ta kawo mata, ta ajiye a gabanta. Ganin yanda yake ganin robar yasa Jadda ta ce"tashi ki je kitchen ki 蓷auko leda ki 蓷an sammasa ko ka蓷an ne kar mu shiga ha茩茩insa ido guba" kallonsa Imara ta yi taga ya yi murmushi, turo baki ta yi batasan yi wa Jadda musu ya sa kawai ta tashi ta shiga kitchen 蓷in. Mi茩ewa Abaan ya yi ya kalli Jadda ya ce"sai da safe, na tafi" ri茩e ha蓳a ta yi ta ce"au ba zaka ci dambun kazar ba?" Kallon robar ya yi sai luma ya saka hannu ya 蓷auke duka ya yi waje, daidai nan Imara ta fito daga kitchen hannunta ri茩e da farar leda. Kallon Jadda ta yi ta ce"Jadda ina ya tafi dashi kuma?"
"Bishi duk in da ya yi, karki kuskura ya cinye ya bar ki"
Da gudu Imara ta bi bayansa, saidai bata same shi ko a falo ba, hakan yasa ta haye sama da sauri. Zamewa ta yi, tayi baya zata fa蓷i ya ri茩e ta, 蓷agowa tayi ta kalleshi sai kuma ta sunkuyar da kanta ta ce "ina yini"
"Lafiya klao Imara, wannan gudun fa?, so ki ke sai kin ji wa kan ki rauni?" Girgiza kai ta yi ta ce"abu na zan amso, bana son ya cinye ina zuwa" daga haka ta shige ta bar Khalil tsaye a wajen. 茦ofar apartment 蓷in Abaan ya ga ta shige sai kawai ya ja ya tsaya a wajen yana jiran fitowarta.
***Babu kowa a falon hakan yasa kai tsaye ta shige 蓷akinsa, dan ba ba茩onta bane, kama 茩ugu ta yi ta rike ganin nan ma baya nan, 茩arar zubar ruwan da ta ji a ban蓷aki ya sanya ta nemi waje ta zauna a gefen gadonsa. Above 10mins kafin Abaan ya fito daga wanka yana sanye da bathrobe, sarai ya ganta sai kawai ya 蓷auke kansa ya 茩arasa wardrobe 蓷insa, wasu pyjames White colour ya 蓷auko sannan ya dawo gaban dressing mirror ya fara gyara gashin kansa, tana zaune har sai da ya kammala duk wasu abubuwan dake gabansa sannan ya sanya rigarsa. Runtse idanu Imara ta yi ta sanye hannayenta duka biyun ta rufe fuskarta, duk abin da take yana kallonta ta mudubi bai kula ta bar ya kammala nan da nan 蓷akin ya 蓷auki wani sassayan 茩amshi. Remote ya 蓷auka ya 茩aro gudun AC, lumshe idanu Imara ta shiga yi tana jin wani bacci na san蓷arta. Fridge ya bu蓷e ya 蓷auko ruwa ya sha sannan ya dawo ya zauna akan sofar dake 蓷akin ba tare da ya kalleta ba, ganin yanda ya shareta ya sa Imara ta taso ta dawo kan kujerar da ya zauna ta zauna itama tana kallonsa ta ce"ka bani dambuna in ji Jadda"
"Mene haka?"
Kwa蓳e fuska ta shiga yi tana shirin fashewa da kuka, rangwashinta ya yi akai ya ce"babu kyau mutum zai saka kaya a dinga zama a 蓷akin kin ji ko?" Gya蓷a masa kai tayi jin yanda ya ri茩e mata kunnenta. Cikin rawar murya ta ce"ni ka bani dambuna na tafi, bacci nake ji" da hannu ya nuna mata inda ya ajiye robar ta tashi da sauri ta 蓷auko sannan ta dawo inda yake zaune. Amsa ya yi ya bu蓷e ya 蓷ebo da yatsun hannunsa ya mi茩o mata, da idanu kawai Imara ta bi shi bai ce mata komai ba ya girgiza kai ya kai bakinsa, lumshe idanunsa ya yi saboda da蓷in da dambun ya yi masa. A nutse ya cigaba da cin abin sa ba ta re da ya sake kallonta ba. Ganin yana shirin cinyewa ya sanya ta jawo masa riga hawaye na zuba akan fuskarta ta ce"ka bani na ci to" kallonta ya yi kawai ya sake 蓷iba ya kai bakinsa. Fashewa tayi da kuka ya 蓷ebo ya zuba mata a baki. Tsit Imara ta yi shiru ta shiga tauna naman, sosai ya yi mata da蓷i itama, a haka suka cigaba da ci yana bata a baki saida ya rage sauran ka蓷an ta yi saurin kar蓳e robar tana taunar naman ta ce
"Ni ka bar min wannan, ai ni ce 茩arama"
Harararta ya yi ya kar蓳e robar ya ce"tashi ki tafi to" kallonsa ta yi kamar ta fa蓷a masa abin da ke zuciyarta sai kuma kawai ta tashi tayi hanyar waje. Murmushi ya yi ganin ba ta sake magana ba ya mi茩e tsaye, taku 蓷aya ya 茩araso inda take ya juyo da fuskarta yana kallonta, sunkuyar da kanta ta yi ya 蓷ago fuskar yana murmushi ya ce "tafiya babu sallama?"
# *IMARA 馃拫*
# *Bestnovel*
# *Nanameera*
# *2025*.