Free chapter · Read without an account
BABI NA HUƊU
by Ayusher Muhd · RIBAR ƘAFA
RIBAR ƘAFA
NA
Wattpad :-AyusherMohd
Arewabook:- Ayushermuhd
ŋą Ä̤ʏʊֆɦɛʀ ʍʊɦɖ🏌🏻♀️
Paid Book
Shafi na Huɗu
Adda Yagana zatai magana Kabir yai saurin cewa "Ke yayatace ba dake nake ba amma su wallahi na isa dasu kuma na faɗa babu mai tashi daga gurin nan har sai sun hura wutar nan, su kuma dafa tea ɗin, duk wani iskanci da kukeyi ai dan kunga Adda ta dawo gida ne dan da kaf cikin ku ba mai takurawa Kursum to wallahi duk iskancin ku na gaji dashi." Kallan juna sukai Hasina ita har tanta bataso kawai dai ba yanda zatai ne, da sauri ta fara ƙoƙarin kwashe gawayin Kursum ta matso tana ƙoƙarin taimaka mata, kallan da Kabir ya mata ne yasa ta ajiye tukunyar tana kallanshi, inyaso zama serious bazaka taɓa cewa shine mai shiririta ba. Alhaji Nuhu Danbatta ne ya ƙarasa shigowa ciki hannunsa ya makale a baya yana kallan saurayin dake kwance, kanshi ya nufa su kuma suna ganinshi suka fara kifi-kifi da ido, bai tanka musu ba sai dai ya amsa gaisuwar da Kursum keyi kafin ya wuce inda yaran yake, da sauri Kabir ya koma gun ya ɗan sunkoyo yace "Baba kaga yaran nan mu maida shi gun danginshi kar ya mutu a hanun mu."
Alhaji Nuhu yasa hannu kan kafadarsa ya ɗan taɓa shi sai dai bai tashi ba, juyi yai ya cigaba da bacci, kallansa yai yace "Bacci yake kamar ko?"
Kabir ya girgiza kai alamun takaici yace "Baba yaran nan fa akwai mystery a tattare dashi."
"Mas me? Kaga ni bansan guntun turancinka me kake nufi?"
Waigawa yai ganin yan mata ba kallansu suke ba yace "Ban yadda dashi ba, ko dai barawo ne ko kuma aljani." Tsaki Alhaji Nuhu Danbatta yai yace "Tashi ka goyashi ka sashi a ɗakin ka inya tashi sai mu wuce."
Ido ya zaro ya waiga yace "Kursum ɗazu wannan buhun shinkafar dana zo jawoshi kan tabirma bayana bai kusa balewa ba?"
Kallan Baba tai tace "Baba kasan Yaya Kabir ba karfi shiyasa." Harara ya zabga mata yace "Kinfa gama rainani yarinyar nan in saurayinki yazo zance ki tambayeshi wa ke tare musu faɗa." Fuska ta tamke ta ɗau kayan shayar data wanke tana cewa "Kai ka sanshi ni ban sanshi ba."
Baba ne ya katseshi da cewa "Ka tashi ka goyashi ko sai ka tabbatar mana bakada karfin?" Tahowa Adda Yagana tai sum-sum ta durkusa ta gaida Alhaji Nuhu wanda ya amsa mata fuskarsa sam babu wargi dan hankalinshi ma nakan Kabir wanda yake jiranshi ya ɗaga saurayin, haka ya tashi da kanshi dakyar aka iya ɗau rawa Kabir shi a baya, wani uban kara ya sa yace "Baba shikenan baya na ya ɓalle." Dariya Umma tasa harda tsalle tana cewa "Kabiru kaima kanada yaro ne?" Kamar zaiyi kuka yace "Umma in wannan yaro na ne ai shikenan ni kuma ta kare min." Da kyar yake iya takawa yana yi yana nishi haka ya karasa dashi ɗaki kifawa sukai kan katifar ɗakin tare abin da ya bashi mamaki juyi kawai saurayin yai ya cigaba da baccinsa. Saitin kuncinsa Kabir yakai hannu yanaji kamar ya tsinkamai mari sai kuma ya fasa ya miƙe, Baba dake jikin ƙofa yace kalla yace "Baba wannan wallahi da badan naji yana abin bacci ba ɗauka zanyi suma yai, nidai yaran nan tsoron zamanshi nake a gidan nan kar yasa a kamamu muma."
Ƙarasa shiga cikin Alhaji Nuhu yai yace "Kabir ni kaina a tsorace nake, yaro mun ganshi sama ta ka, na koma inda akai hatsarin man tabbas babu motar, to naji in motar an sace wanene zai ɗauke wari ɗayan takalmins? Dan kuwa babu shi a gun nan, nifa wannan ciwon mantuwan ban taɓa haɗuwa da yaro mai yinsa ba nadai san tsofafi nayi." Shiru yai dan shi gaba ɗaya ya kasa tunanin abin yi.
"Shiyasa nace ma mu kaishi police station, Baba bamuda kuɗin kula da shi sannan in kuma yaki warkewa fa? Ko kuma daga baya aka gane yana gun mu akace saceshi mukai? Bamuda hujja tunda bamu kaishi police station ba." Jinjina kai yai alamun gamsuwa yace "Ka shirya inya tashi yaci abinci sai mu wuce, ni zan leka makaranta." Yana gama fadar haka ya juya ya fito, Kursum da sauri ta taho inda yake tace "Baba abinci, dumamenka na ɗaki a kula."
Kallanta yai ɗauke da murmushi yace "To Kursum Allah ya miki albarka, ya akai yau bakije makaranta ba? Ita dama Hasina nasan in har bana nan ba zuwa zatai ba."
Kanta na ƙasa tace "Kayi hakuri Baba wallahi tsoron barin Umma ita kaɗai nai, dama da Yaya Kabir na nan ne." Kallan inda Umma take yai tana ta wasanta da kafafuwanta kai kafe yarinyacw ƴar shekara 5, tausayin ta ya kara kamashi yace "Taci abinci ne?"
"A'a yanzu zatasha tea ruwan muke jira yai zafi." Yana jin haka yai ɗaki, yana shiga yace "Kursum zo." Ba musu ta mike ta shiga bayan ya amsa sallamarta, inda ta ajiye tuwon ta kalla ganin yatsarshi na nuna mata gun yace "Ki ɗauka ki bata ni in na fita zansha shayi, kinsani sarai bata iya rike yunwa yanzu sai kiga ta fara kuka."
Abinda ya faru ɗazu take san sanar mai sai dai sam batasan hankalinsa ya tashi, muryarta na rawa tace "Baba kaima bakaci komai ba tun jiya, sannan hannunka da alama ciwo kaji."
Kallan hannun yai ya akai ta gane? Dan ya riga ya kunce ɗaurin da aka mai saboda baisan su damu, kanta ta sunkuyar tace "Dazu da kana taimakawa abokin Yaya Kabiru naga sanda ka dan yarfe hannunka alamun zafi daga nan kuma kasa hannunka a baya shiyasa nake zargin bigewa kai."
Fuskarta ya kalla cike da tausayi yace "Allah ya miki albarka Kursum nagode da kulawa."
Har zata mike sai kuma ta koma tace "Baba nace maganar Inna dan......" yanda ya kalleta ne yasa tai shiru ta ɗau kwanan ta fita dashi, zama yai a bakin gadan ɗakin yai shiru, sai kuma ya mike ya shiga bandaki ya watsa ruwa sannan ya zura wasu kayan ya fito ya nufi makarantar islamiyar sa dake nan bayan gidanshi. Zama yai da wakilin makaranta ya tambayeshi ko akwai kuɗi a rantamai zai kai yaro asibiti, nan yace dubu ɗari kawai garesu a asusu, haka ya turamai ya fito yana tafe yana tunanin yanda zaiyi ya maida yaran nan cikin danginshi.
A gida kuwa Hasina da Raheena haka suka dafa tea aka siyo bread aka sha, suna ci suna hararar Kursum wacce abubuwansu basa damunta itadai kar su taɓa Umma kawai shine magana.
Adda Yagana ce ta kalleta tana taunar bread a bakinta tace "Kursum shi wancan saurayin da aka shiga dashi ɗaki wanene shi?" Kallan ɗakin Kabir tai ta girgiza kai alamar rashin sani kafin tace "Oho! Inaji abokin Ya Kabir ne kinsanshi da kwashe-kwashe."
Baki ta taɓe tace "Haka kawai suyi ta kawo mana kutane gida kamar gidan haya."
Itadai Kursum batace komai ba dan yau tun abinda ya faru da Umma taji batasan magana dayawa. Raheena ta kalli shanyar datai tace "Shine dan munafurci kikai wanki baki ce na kawo nawa ba?"
"Dadinta dai kinada hannun nan sannan kina da ƴan kudinki kinga kuwa in bakisan yi sai ki biya na miki dan ba dalilin da zai sani yi miki wanki baki biya ba."
Wata harara Raheena ta zabga mata tace "Kefa yanzu bakida kunya gaba ɗaya tunda Inna tabar gidan nan kika feɗare na rantse da Allah duka zan miki kuma na da ki banza dan yanda kike a bushen nan in na makeki kila sai na balla ki." Dariya ce ta kwace mata ba tare da tace komai ba, mikewa tai bayan ta gama ta wanke kwanukan da suka ci abinci tasa ruwan abincin rana tanayi Umma na zaune tana wasa a gefenta.
Alhaji Nuhu Danbatta ne ya dawo kallo ɗaya zakamai kasan a wahale yake dan tunda ya fita har wannan lokacin kudin daya samu ɗazu kawai shi ne a hanunsa ya rasa motar da zai samu suje su dawo, shi kuma nauyin tambayar aro yake dan a rayuwarshi ba abinda ya tsana irin ya ɗau rawa wani nauyi, da sallama ya shigo kafin ya fara kwallawa Kabiru ƙira. Tunda Kabiru ya fito ya saki baki yana kallanshi, mamaki gaba ɗaya ya cikashi ganinsa sanye da kayan saurayin nan, ya kwama trainers dinshi wanda gefenshi duk ya cinye, sai wani bouncing yake shi a dole ɗan gaye. Hannu Alhaji Nuhu Danbatta ya ware alamun zagi yace “Ungo nan, kai ni meke damunka? Taya zaka ɗau ki kayan yaro ya ka saka? Ko kunya ma bakaji? In kuma kayan dashi iyayensa zasu ganeshi fa?” Bayan kansa ya shafa yace “Baba indai da kayan zasu ganeshi to alamu ne na masu hali kaga shikenan sai nai fuska nace nine.” Fuska a tamke yace “Ka wuce ka bashi kayansa ko sai nazo na kifama mari? Shashasha kawai.”
Baki Kabiru ya turo ya koma ɗaki inda saurayin ke zaune sanye da kayan Kabirun na ɗazu kallansa yai ya kalli shinkafa da waken da aka kawomai wanda haryanzu baici ba yace “Kaga in ba yunwa kake ji ba cire kayan nan ka bani mu wuce.” Kallansa yai kamar bai gama gane abinda yake nufi ba, Kabir ya ɗaga shi yace “Kayana zakaban, zan amshi wannan in zamu barka a police station.” Kai kawai ya ɗaga alamun to sannan ya canza kaya, tare suka fito dan shidai ya koshi shi wannan tunda baisan cin abinci shiya sani.
A waje ya tadda Baba na jiransu kallan saurayin yai yace “Yaro ka tashi? Ba inda ke ma ciwo?” Murmushi ne a fuskarsa ya girgiza kai alamun babu. Kabir yace “Kai magana mana sai ai ta tambayarka kana ɗaga kai kamar wani kurma.”
“Kai dai ka fiya neman magana ai dai baka taɓa ji yayi magana ba sai ka bari muji ko ma yana magana.”
Da sauri ya dawo gaban saurayin yace “Baba yaran nan wallahi yana magana, kai ɗazu bakawa Kursum magana ba? Harda wani guntun turancinka.”
Jin haka Alhaji Nuhu ya kalleshi yace “Kana magana?” Kai ya ɗaga alamun eh “Sunan ka fa? Ka tuna?” Kai ya sunkuyar tare da girgiza kai alamar a’a, baki Kabir ya taɓe yace “To meya hanaka magana yanzu? Baba dan Allah muje ni wallahi kaina ya fara ciwo.”
Fitowa sukai suka nufi tasha, mota suka hau golf suka zauna a baya su uku aka samu ciko mai kota yaja suka tafi, ana fara tafiya ko minti goma ba’ai ba saurayin nan ya fara bacci. Mamaki ya kama Kabir yace “Baba wannan baccin nashi anya na lafiya ne? Yini fa yai yana bacci.”
“Kabir ba wannan ba, Aminu Kano ya kamata mu fara zuwa a tabbatar dame ke damunshi kafin muje police station.” Zaiyi magana Alhaji Nuhu ya katseshi da cewa “Hakkin mu me mu tabbatar munyi duk abinda ya kamata, kada ka manta hatsari mukai kuma ni ke da laifi.” Shiru yai dan yasan bashida amsar maganaa. Shiru sukai kowa da abinda yake sakawanhar suka iso Aminu Kano.
Bangaren imaging suka nufa suka hau layin CT sai da sukai awa ɗaya da rabi sannan aka ƙirasu, har lokacin yaran nan sai dai ya zauna shiru sai yatsun sa da yake ta matsawa, sunshiga akace su jira shikuma aka bashi wani kayan, sai daya canza sannan aka shiga dashi, Likitan abokin wanda ya turosu daga Danbatta ne, bayan ya gama ya sa aka ƙira su kallan Alhaji Nuhu yai bayan ya nuna mishi hoton yace “Zaka iya faɗa min meya faru?” Nan ya kwashe kaf abinda ya faru ya sanar mai, shiru yai kafin ya juyo da computer ɗinshi saitinsu yace “Alzheimer’s disease baya nunawa ta CT scan, sai dai zamu iya detecting shrinkage daga ciki wanda sign ne na memory loss, wanda muke zargin tsoro da trauma na abinda ya faru shine yasa memory ɗinshi tafiya, sai dai da alama bazai daɗe ba zai dawo, ku samu ku nemi family ɗinshi ku maidashi dan zama cikin gurin daya saba rayuwa yana daga cikin abinda zai dawo da memory ɗinshi da sauri, b ciwo bane da za’asha magani a warke, ciwo ne wanda sai anyi hakuri.” Alhaji Nuhu Danbatta ya kalleshi yace “Muna tunanin kaishi police station daga nan, tsorona kar muryarsa ma ta ɓace dan ni haryanzu banji yayi magana ba.”
Kabiru da sauri yace “Baba yayiwa Kursum ɗazu na faɗa ma.”
Dr ɗin ya waiga yace “Tana ina? Tazo da alama zata taimaka gun buɗe bakinsa wanda shi zai taimakawa kwakwalwarsa.”
“Mun barta a gida, yanzu zamuje police station ɗin mungode.” Nan suka fito suka biya kuɗi sannan suka nufi police station lokacin har yamma tayi.
Shidai yaran nan binsu kawai yakeyi, police station ɗin unguwa Uku sukaje dan kuwa Dr ne ya basu wannan shawarar, ya kuma basu number DPO ɗin police station ɗin akan yantai maka musu. Suna sanarwa sune wanda aka turo aka kaisu gunshi, nan ya ɗau ki hoton yaran ya kuma sake musu tambayoyi, sai daya tabbatar da komai sannan yace “Yanzu zamu sa shi a cigiya amma bazamu barshi a gunmu ba dan bamuda inda zamu ajiyeshi amma ku koma dashi kubar numberku in muka baza cigiya aka samu wanda ya sanshi sai kuzo dashi.” Da sauri Kabir ya mike yace “Sorry DPO amma gwara ya zauna a gunku dan mu muna tsoro bamusan wanene shi ba wasu halaye yake dashi da zamu….” Jan bayan rigarsa Alhaji Nuhu Danbatta yai ya koma ya zauna kafin shia yai gyaran murya yace “Babu wata hanya data wuce wannan? Muna tsoron kar wani abu ya sameshi a gun mu.”
“Maganar gaskiya yaran nan yanzu dole ya zauna a gunku, har sai munsan su waye danginshi, zamusa cigiya gidan radio da tv zakuma mu samar da ragowar police station dan na tabbatar ko sati baza’ai ba zamu ji daga garesu indai suna raye.”
Alhaji Nuhu Danbatta ya jinjina kai yace “Shikenan mungode.” Numbersa ya bada daga Kabir wanda takaici duk ya hanashi magana.” Haka suka fito shidai yana binsu daga gefe, suna ɗan yin nisa Kabir ya waigo ya zare mai ido yace “Malan kama gabanka wallahi kaji na faɗa ma.”
Yana gamawa ya fara tafiya, waigowa yai ga mamakinsa yaran na binshi yana ganin zai waigo ya tsaya, kallan Alhaji Nuhu Danbatta yai yace “Baba kasan Allah mu gudu ya zamu ɗau ki yaran da bamusan ko dan fashi bane mukai gida?”
“Kai yanzu in akace ka tafi ka barshi anan tafiya zakai?”
“Da gudu ma kuwa, kana ganin fa yaran nan kasurgumin dan iska ne, haryanzu yaki mana magana ko likita yaki kulawa amma yawa Kursum magana.”
Alhaji Nuhu Danbatta ya kalli inda yake tausayin yaran ya ratsashi yace “Kai ka sani nidai haryanzu banjishi yana maganar dakace ba dan haka ka wuce mu tafi mu munyi iya namu sai muyi addu’ar Allah ya kawo iyayensa nan kusa.
Ayusher Ce🏌🏻♀️