Free chapter · Read without an account

6

by Fatima Muhammad Gurin · KIWON KUBUBUWA

KIWON KUBUBUWA

FATIMA MUHAMMAD GURIN.            

         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

Sorry Kun ji ni shiru kwana biyu zazzaɓi na yi amma Alhamdulillah na samu sauƙi

                   PAGE 6

Washegari haka ya tashi da wani irin ciwon kai ko da ya fito duk sai da suka tausaya mishi idanunshi gabaɗaya sun ɗan suntuma sun rine ba kaman yadda suke farare tass ba, wanka yayi ya sake kwanciya yau din ma Afnaan ce ta saka shi karyawa Allah ma ya sa weekend ne, karfe wurin tara sai ga jabir masifa yayi tayi sai dai Aliyu ya ɗan mishi murmushi kaɗan ko ya kalleshi ya sake lumshe ido har ikirari yayi shima ya bar wurin kenan har Abada dama saboda Aliyu ne yake zuwa yanzu aiki zai nema.

A ranar su Kawu habu suka koma wanda hakan yayi matuƙar saka Afnaan cikin farin ciki don har ga Allah ta tsani zama inuwa ɗaya da goggo Salame, ko da yamma yayi jabir ne ya kira gidan su khadija ya ke faɗawa mamansu Aliyu bashi da lafiya ba zai samu zuwa ba ta yi mishi adu'ar samun sauƙi.

Har dare Aliyun bai sake ba sai da Baba da Mama suka sake saka shi a gaba da nasiha da faɗa tukuna ya daina sa damuwan a Ranshi Washegari kuwa ya tashi rassss har fita yayi ya zazzaga ko zai samu wani abin yi amma bai samu ba har azahar ya dawo gida ya ci abinci. A parlorn Mama suke Zaune yayinda maman take daga ciki shi da Afnaan baje yana koya mata assignment rabi surutu ne shi ko sai biye mata yake yi sai la'asar ya dube ta

"Kin ga Naanu na yi nan daga masallaci ba zan dawo ba zan wuce Tudun matawalle"

Tana tattare takardun itama ta mishi Adu'a mama ma ta mishi kan ya fice daga gidan, yau sossai ya samu yadda yake so daga yaran sun kuma mayar da hankali sun fahimta sossai har suka tashi be yi tsawa ko faɗa da duka ba Sallar Magrib a unguwar yayi ya shiga gidansu jabir itama hajiyarshi jaje ta mishi sossai sun ɗan jima yana taya shi shawarar abin da zai iya yi sbd gyaran nan ba karamin taimakonshi yake da abubuwa masu yawa ba musamman abincinsu amma yanzu gashi komai ya tsaya mishi idan aka ce yau babu wani ajiyayyen kayan abinci a gida bai san yadda zai yi ba.

Suna cikin maganar hajiyar da yake yiwa aiki take mishi ihsani sossai ta kira layinshi ajiyar zuciya mai nauyi ya sauƙe kan ya amsa

"Assalamu Alaikum"

"wa'alaikassalam warahmatullah Aliyu ya gd? Ya aiki?"

Ya mayar mata da gaisuwa bayan nan ta ɗaura da

"Aliyu na tura driver da mota a duba breaks din saboda delayn takuwa yake ɗazu har ya kusa haddasa mana hatsari sai kuma aka ce min baka nan wai ka bar aiki wurin... Ko ina ka koma? Don gsky bana jin daaɗin aikin kowa kaman kai"

Lumshe idanu yayi kaman ba zai yi magana ba sai kuma yace cikin sanyin muryarshi mai nauyi

"Ina gida dai tukuna ban samu wani wurin ba"

"Toh gobe da safe ina son ganinka"

Yace

"Allah ya kaimu in shaa Allahu zan zo"

Sallama suka yi ya dubi jabir

"J zan wuce bari dai mu ga yadda hali zai yi"

Ya amsa

"Toh Allah ya kawo babban rabo mai alkhairi"

Ya amsa da Ameen kan ya koma cikin gidan yayi wa Hajiya sallama ya fito ya wuce gida.

A tabarma ya samu su Baba suna hira shima ya jona su.

Washegari kaman yadda yayi alƙawari karfe tara na safe gidan Hajiya karima yayi mishi, har cikin sitting room aka mishi iso ya ɗan jima kadan wata  da alama mai aiki ce ta kawo mishi snacks da lemo, bai taɓa komai ba ya cigaba da zama chan sai ga takun hajiyar ta ƙaraso, macece ƴar kwalisa da alama kuma kudi sun zauna sossai don gidan ma kawai abin kallo ne, cikin girmamawa ya gaisheta ta amsa da kulawa kan tace

"A gaskiya abin da Naji jiya ya girgiza ni kwarai kuma na kasa yarda da hakan yanzu sun koreka kenan?"

Lumshe idanu yayi na seconds kan yayi uttering

"uhmm"

A ƙasan makoshi alama baya son ko tuna zancen fahimtar hakan ya sa ta kau da maganan

"Idan babu damuwa ina son offering ɗinka job ne, akwai ɗiyata da ta gama secondary a London to sun dawo nan gabaɗaya da mai gidan kuma ta samu admission a Alqalam University idan har zaka iya aikin tukata zuwa har ta saba da garin sai mu ji don dama ina planning samar mata driver wanda hankalina zai kwanta da shi"

Sossai take yabawa kamewa da natsuwar shi da wannan yanayin miskilancin nashi kila ya iya da jawahir.

"Zan yi shawara Hajiya"

Ya amsa a takaici

"Toh babu damuwa amma don Allah ina saurarenka"

Kira tayi sai ga mai aikin nan ta dawo da leda ta miƙa mata ita kuma ta karɓa ta miƙe ta bashi kin karɓa yayi sai da ta mishi dole ya mata sallama ya fice, direct gida ya koma a parlor ya samu ahalin nashi Naanu na kwance cinyar mama tana bacci yayinda mama da baban suke kallon sunna Tv a ƴar tvnsu bayan sun gaisa ya miƙawa mama ledar

"Toh me muka samu gadanga?"

"Ko buɗewa ban yi ba Mama wata customer ta ce ta bani"

Bayani ya musu na yadda suka yi baba ya girgiza kai

"Aliyu me zai hana mu sake cigaba da neman wani wurin na aiki? Aikin direbanci ba wai ba abu bane me kyau amma kana da lafiya da kuriciyarka sannan da sana'arka irin wannan aiki sam bana tunanin za'a haifi ɗa mai ido da kai"

Mama ma cikin ba da goyon baya tace

"Da gaskiyar mahaifinka sai dai kuma in kana ganin zaka iya ɗin za mu bika da Adu'a ne da Fatan alkhairi"

Numfashi ya ɗan fesar tunaninshi yadda zai yi da jarrabawowin Afnan ne masu zuwa, sannan abincinsu da lafiyar baba idan har ya cigaba da garari ba aiki komai zai iya zuwa ya mishi zafi. ya dubi baba

"Baba mai zai hana ko na wata guda ne tunda yanzu samun wani garejin su dauke ni ma aiki ne? In ya so ina yin wannan ɗin ina nema har Allah ya sa in dace."

Su ma sun duba abin da ya hanga don haka suka amince akan yayi na ko da wata guda ne.

Ledar Mama ta buɗe ta fiffido robobin cikin farare kusan biyar glazed pufpuff ne ɗaya, samosa roba ɗaya, meatpie roba ɗaya, cookies roba ɗaya, spring rolls roba ɗaya sai stickmeat a jikin toothpick a roba ɗaya a jere gwanin kyau, sai wasu kalar robuna farare da aka zuba zobo da kunun Aya.

Jinjina karamcin matar suka yi, ko shi Aliyu bai san abubuwan ci bane ciki kuma duk wanda aka ajiye mishi ne a gidan bai ci ko guda ba bayan ruwa da ya ɗan kurba.

La'asar na yi ya wuce Tudun matawalle mutanen nashi sun fara sanin shi don haka suna kan kiyaye dokokinshi kuma sossai suke fahimta a yanzu da suke ɗan natsuwa yana ɗan sake musu fuska Dukda ba dariya ko wasa dasu yake ba sai dai baya tamke fuskar yadda ya saba, mahaifiyarsu ma tana jin daaɗin fahimtar sauye sauye daga yaran.

Bayan kwana biyu da maganansu da Hajiya karima yau yana shagon wannan Alhjn yana sauke kaya wayanshi ya shiga ƙira bai duba ba kasancewar buhu ne bisa wuyanshi sai da ya gama sauƙe su tass kan ya matso wurin Alhjn ya kirga kudadenshi ya bashi, gaba ya ɗan yi ya kira mai pure water ya sayi biyu ya sha ɗaya kan ya watsawa fuskanshi dake ta tsatsafo da gumi ɗaya, Kasar bishiya ya samu ya zauna ya tabbatar da su Baba sun san yana wannan aiki ba zasu amince ba amma shi a ganinshi tunda karfinshi zai iya abu mai sauƙi ne, wayanshi ya zaro yana dan lumshe fararen idanunshi dake cike tab da gajiya ganin Hajiya karima ya sa ya miƙe ya ƙarasa wani shago kusa da shi ya sayi katin ɗari ya bi kiran bata ɗaga ba har ya tsinke, yana kokarin mayar da wayan aljihu ya ji ta ɗauki ruri dagawa yayi suka gaisa cikin mutunci kan ta ɗora da

"Aliyu ina ta zuba idanu ban ji ka ba"

Ɗan numfashi ya sauƙe yana saisaita girman idanunshi yace

"Zan yi Hajiya"

Daga muryarta yaji farin cikinta ya rasa Meyasa take son shi da aikin, ɗan taɓe baki yayi bayan ta mishi sallama akan gobe ya soma zuwa zai ga kuɗin abin hawan shi na zuwa da komawa da zata tura mishi na watan yayi anfani da su a kullum tunda ba gidansu zai koma ba da zama ba.

Cikin Central market ya shiga yayi musu sayayya duka sai da ya ƙarar da kuɗin da ya samu yau din kan ya nufi gida, sannu da albarka iyayen suka yi ta saka mai bayan ya zube kayan a karamar store ɗinsu da suke rufewa da key, wanka ya shiga bayan ya fito ya ci abinci kan ya ɗauko wayanshi sai ya ga 15k daga Hajiya karima ɗan saƙon godiya ya tura mata kan ya fice daga gidan zuwa gidan lesson ɗin shi.

Washegari bayan yayi Sallar asuba yayi shara kaman yadda yake al'adarshi a gidan ya shirya cikin riga da wando baƙi da dark green suma duk sun ɗan kode rigar yayi fari amma bai damu ba, turarenshi ya ɗan fesa sai gashi yana kamshi abinshi kowa ya san Aliyu ya san shi mutum ne mai son kamshi da tsananin tsafta yana da kyankyami na bugawa a jarida a yadda yaken nan ba komai yake ci ba kuma ba a ko ina yake iya cin komai ba, fuskanshi a kicin-kicin ɗinta yau ya tashi wayanshi kawai ya zara ya nufi cikin gida, Afnaan ya samu tana cin ɗan wake da suka yi da safen, gefenta ruwan lipton ne da basa rabo dashi da safe idan yana da kuɗi har yar madara yake saya musu su sha don duk suna kaunar ruwan zafi, tea ɗin ya ɗauka ta turo baki tana ɗan kallonshi

"Ya haidar naka fa na parlorn Mama"

Bai kula ta ba sai ma kaiwa baki da yayi ya soma sha.

"Maama..."

Kan ta kai ƙarar ya katse ta da cewa

"Ba kin ga 'yar fara na min rowar baƙin shayi ba.."

Kaman zata yi kuka tace

"Mama fa wanda kika saisaitamin ne ya san nashi da zafi sossai kuma ba iya shan mai zafi nake ba shine yake shanye min nawa"

"ka ga gadanga ban son neman faɗan da ka saba ka bata kayanta kaje ka sha naka a parlor"

Maƙogoro ya buɗe yayi one sip da ya zuƙe kusan gabaɗaya tea din sai ya ajiye mata kofin kukan Shagwaɓa ta sanya tana cewa

"wlh mama ya shanye"

Tuni ya shige parlorn yana murmushi yana ji tana cewa

"Ɗan baƙi kawai kuma sai na rama"

Daga ciki yace

"za dai ki rame yarinya... Zauna nan ki cigaba da sakalci sai kin je an zaneki a school ni dai ba ruwana"

Miƙewa tayi tana ƙurbe wanda ya bari ta dubi baba dake musu dariya tace

"Baba aka zaneni saboda shi zaka rama min ko?"

"Sossai ma, riƙe min shi zaki yi in rama miki tass"

Cikin tsalle tayiwa kofar da yake ciki gwalo kan ta musu sallama ta fice daga gidan suna dariyar ta.

Sharp Sharp ya karya ya fice shima suna mishi adu'ar Allah ya tsare, direct gidan Hajiya karima ya yiwa tsinke, me gadi ne ya nuna mishi motar da zasu ke fita dashi ɗin bayan sun gaisa, tsumma ya ɗauka Dukda a wanke motar take tassss fara kal da ita ya sake cigaba da gogewa bayan ya gama ya ɗane bayan ya zauna ya ɗan fiddo ƙaramar wayanshi yana ɗan game sbd rage lokaci ya kusa awa ɗaya wurin har ya soma gajiya don lokaci lokaci sai ya ja tsaki, da ya faɗi a game ɗin sai ya fita ya duba time tara har ya wuce ɗago kan da zai yi karo na kusan biyar sai suka faɗa kan wata yarinya, baka ce kuma a kamanni sossai suke kama da Hajiya karima tsiririyace, ta ci wasu irin riga da wando baƙi da ja da ya kamata sossai gashin kanta a tufke hannunta rike da abin da ya tabbatar hijabi ne ruwan kasa sai wani karamin school bag da ta rataya, kafafunta wasu hills ne da in ka kalla sai ka ji mata tsoron faɗuwa, tayi kicin kicin da fuska Bakinta na taunar cingam ta ƙaraso sai ta ja ta tsaya, cigaba da game ɗin shi yayi kaman yadda bata yi magana ba shima bai nuna ya san akwai wata halitta a wurin ba.

"Kai..!"

Ta faɗa bayan shafe kusan mintuna biyar a haka, ko motsi bai yi ba sai ma ɗaure fuska tamau da ya sake yi.

"Kai ƙasƙantaccen driver da kai fa nake...!"

Idanu ya ɗan runtse kaɗan ya buɗe don sarai ya ji kalmar ƙasƙantaccen har cikin zuciyarshi.

"A'ah Aliyu baku tafi ba?"

Sai a lokacin ya ɗan ɗago ya kalli Hajiya karima da ta iso wurin, dira yayi ya gaisheta fuskan nan a matukar haɗe kallo ɗaya ya yiwa Jawahir sai ta ɗan sha jinin jikinta don yana da matuƙar kwarjini, tsaki mai karfi ta ja tace

"Mommy wannan kuwa da kika jajibo min anya yana ji da kyau? Ko dai kurma ne?"

"Wani irin kurma baki ji mun gaisa ba?"

"Ni ce kenan ya raina, Mommy kin san halina kika kwaso min wannan banzan ina masa magana yana share ni?"

"Jawahir...!"

Hajiya karima ta ɗan mata tsawa

"Kin dai san a girme ya girme ki, sannan a musulunce duk wanda ka zo ka samu a zaune kai ne zaka mishi sallama"

Tsaki ta ja hajiyar tayi saurin Buge mata baki sai ta fashe da kuka ta buɗe motar ta shiga tana buga kofan.

"Kayi haƙuri Aliyu, nima nan hakurin nake mahaifinta da yaddikonta sun riga sun lalatata da fitsara"

Girgiza kai kawai yayi ya mata sallama, driver seat ya buɗe ya shiga har lokacin tana kuka ya ja ya bar gidan.

Yana ji ta ƙira waya

"Dad sai da na ce maka mom bata ƙaunata amma ka dage ka turoni wurinta tun jiya buguna take akan ƙasƙantattun talakokin nan, yanzu akan wani banza driver ta fashe min baki"

Tana kai nan ta sake rushe wa da kuka, ɗan lumshe idanu Aliyu yayi ya buɗe yana sake damke stirring, a hankali ya jefa lip ɗin shi na kasa a baki ya fara ciccizawa kaɗan kaɗan, bai san me na ɗaya ɓangaren ke cewa ba amma da alama haƙuri ne yake bata don sai Shagwaɓa take yi.

Har suka isa makarantar kan ta sauƙe wayar a kusa da senate building yayi parking yayi shiru, itama shiru tayi abin ta sai ya sake ɗauko wayanshi ya fara game

"Wannan wani kalar kuturun wulakanci ne zaka wani tsai da ni anan alhali ka san ina da lectures?"

Da kyar ya iya furta

"Say the hall name"

Ɗan wara idanu ta ɗan yi jin wai ashe ya iya turanci tsaki ta ja kan ta faɗa, ciki ya nufa har gaban hall ɗin ya tsaida motar.

"Wai baka san cikin aikin ka har da buɗe min mota da rufewa ba?"

Ta sake faɗa cikin dan hargagi

"Ki kwana nan"

Yana kai nan ya fice ya je bayan motar ya ɗane ya zauna abin shi.

Iya ƙuluwa ta ƙulu haka ta warware hijabin da take ji kaman ta mutu in ta ga uban yawan waenda Mom ta jibge mata wai makarantar ba'a sa gyale sai taji duk ta tsani kanta da ƙasar gabaɗaya, sakawa tayi ta fito ta bar murfin buɗe tayi tafiyarta.

Da kallo ya bita har ta ɓace masa,(hmmm Aliyu Allah ya hanaka aikata abin da na sani) don tsaff idan ba Adu'a yake na rage zafin zuciyarshin nan ba wata rana zai iya fasa bakin yarinyar nan, gabadaya Ranshi baƙi kirin yayi in ya tuna sunan da take kiranshi hmm.

Sama da awa biyu kan ta fito yadda ta bar motar haka ta same shi, sai dai bata ganshi a inda ya zauna ba kenan motan ta ya bar mata a wangale yayi tafiyar shi, wani irin baƙin ciki ne ya zo mata wuya nan ta ja ta tsaya kusan mintuna goma sai gashi ya bullo bai mata magana ba ya buɗe gaba ya shiga.

"Kutttt"

Ta faɗa idanunta a waje....

                       

                           🖤Gureenjoh🖤

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.