Free chapter · Read without an account

12

by Fatima Muhammad Gurin · KIWON KUBUBUWA

KIWON KUBUBUWA

FATIMA MUHAMMAD GURIN.             

         (Gureenjo)

ADABI WRITERS ASSOCIATION

                   PAGE 12

"Tsarki ya tabbata ga ubangijin da ya halicci wannan kyakyawar surar"

Idanunta ta ɗan waro tana kallonshi yadda ya jingina da motar ya wani harde kafafu ya naɗe hannayenshi a kirji.

"Kina mamakin gani na a irin wannan lokaci ko?"

Tayi shiru tana cigaba da kallonshi don tabbas kam ta shiga cikin mamaki.

"Wallahi da ke na kwana maƙale cikin zuciyata, Naji babu abin da nake son karyawa dashi irin kyakyawar fuskarki, na ji duk duniya babu abin da zan gani ya sa ni cikin nishaɗi irin murmushin ki, gashi ma na zo ana min rowar shi"

Bata san ta ɗan murmusa ba har lokacin bata yi niyyar magana ba sai da ya furta

"Tun da dai Muryar ma rowa ake min bari na fara kai gaisuwa an tashi lafiya sweetheart"

Da sauri tace

"Ina kwana?"

"Lafiya ƙalau, kin ga kan hanya muke zagayo ki shiga in ajiye ki school din sai mu tattauna a hanya"

"Amma Ya..."

Katse ta yayi

"Shhhhhh kema kin san ba zan taɓa cutar dake ba, sauƙe ki kawai zan yi ba wani abu ba Don Allah ba don ni ba kar ki ƙi"

Ya haɗa hannayenshi alamun roƙo.

Haka ta zagaya shima ya zagaya da sauri ya buɗe mata ta shiga kan ya rufe ya dawo ya shiga ya tada motar suka nufi hanyar makarantarsu

"Afnaan na kula rowar muryarki kike yi min baki san hakan zai iya cutar da ni ba ko?"

"Ka daina magana irin haka Yaya Tahir suna yi min wani iri"

Murmushi mai kyau ya saki

"Saboda baki taɓa soyayya ba ko?"

Da sauri ta kalleshi yayi murmushi

"Na sani ne saboda yanayin da na karanta akanki daga jiya zuwa yau, Ni kuma gashi Allah ya jarabceni da tsananin soyayyarki da ina me tabbatar miki na rasa ki zan iya mutuwa"

Wara ido tayi yayi dariya.

"karatu ne a gabana yanzu, duk burin Yayana ya ta'allaka ne ga inganta rayuwata kuma na mishi alkawarin zan yi karatu sossai idan kuma na tashi aure shi zai min zaɓin mijin da ya dace da ni"

Numfashi ya sauƙe yace

"Aure bai taɓa hana karatu ba Pretty, kin ganni nan zan iya barin matata ta ga har ƙarshen biro in dai a boko ne saboda anfanina ne tunda na yarana ne, maganan yayanki ya zaɓa miki miji kuwa ina ga ba daidai bane saboda ke a karan kanki kike bukatar zaban wanda zuciyarki ta natsa dashi, wanda kike jin zaki iya rayuwa dashi ta har abada ko yayanki ne zai zauna miki a gidan?"

Tayi shiru.

"Aure fa sunnar ma'aiki ne mai girma kuma wallahi ni da aure nake sonki"

Nan ma bata ce komai ba har suka isa makaranta ya fito ya zagaya ya buɗe mata.

"Sa min layinki a nan"

Ta kalli wayan ta sauke numfashi

"Bani da waya"

Ya wara idanu

"babba dake?"

"Ya haidar yace ba yanzu ba"

Idanu ya ɗan runtse yana taɓe baki Meyasa Haidar ɗin nan ke da tsauri ne? Kafada ya ɗaga ko da shi ke shi yayi wa kiwo mai kyau yanzu in ya ɗauketa tabbas zata mishi biyayya yadda yake so.

Sallama ta mishi ta shige school ya shiga motar shi yayi kasuwa shagunanshi masu girma uku  a jere na atmphophi, turaruka da kuma jewelries yayiwa tsinke inda ya zauna owners corner yana ta juyawa cikin nazarin yadda zai saye zuciyar yarinyar nan.

A ɓangarenta kuwa haka ta yi papern sukuku da kyar ta yakice tunanin da Tahir ya sanya mata sai dai tana fitowa kuma ta sake cin karo dashi, kaman ta rusa ihu haka dole ya ɗauketa ya maida ta gida a hanya ya zare time table ɗinta yayi snapping daga nan kullum take da paper zata same shi waje haka in ta gama zata koma zata same shi babu wanda ya sani bata gayawa kowa ba hatta Yayanta saboda sai da ya san yadda yayi ya sanya mata tunanin soyayya ba zai hanata karatu ba, ya kuma nuna mata yana son ta zai iya yin komai saboda ita, kuɗi kuwa duk yadda yayi kokarin kashe mata zata nuna bata so saboda bata san me zata ce a gida ba, har waya ya saya mata mai tsada ta ƙi karɓa sbd tsoro, ita ko ɗaukarta da yake ya kaita a mota ya dawo da ita wani abu ne da bata saba dashi ba sai kuma yadda za'a yi ta kallonta da shaawa in ta fito zata shiga motar sai yake mata daaɗi.

A hankali ya fara idan ya ajiye ta bayan ta jima da shiga shima zai shiga ya gaida Mama har ma duk abin da yake so yaje mata sai ya isar ta nan su yan makulashe sai yace tsarabar su Afnan, sam Aliyu bai sani ba kuma bai kula ba don babu abin da ya chanza daga yanayin Afnaan ɗin, bai tashi kula ba sai da Afnaan tayi zurfi sossai a soyayyar Tahir irin soyayyar nan da yake nuna maka komai kake so zai maka kuma ko menene kake so zaka samu, yayi mata alkawarurruka da dama wanda ta san ko da zata shekara nawa tana tara kuɗi a yadda suken nan burikan ba cika zai yi ba.

Yau jawahir ta zo gidan suna zaune a parlor Mama ta aike ta sayan alaiyahu a bakin hanya hakan yasa jawahir ɗin ta miƙe don raka ta suna cikin takawa Jawahir ta dube ta

"Afnaan na kula da cewa kwana biyun nan kaman bakya cikin natsuwar ki, menene matsalar? student in suna gama jarabawar karshe farin ciki suke amma ke tunda ake maganan saura kwanaki kadan ki gama neco sai kike ta rashin walwala why?"

Shiru ta ɗan yi cikin nazari haƙiƙa tana buƙatar tattaunawa da wani kaman yadda Tahir ya faɗa mata wani ba yayanta ba idan ma ta kama mace ƴar uwarta, bata da ƙawa ita bayan mama da Ya haidar babu wanda take faɗawa matsalolinta Toh amma wannan ɗin dole ta nemi shawarar Jawahir a hankali ta soma magana

"Ina cikin ƴar damuwa ne Jawahir" ta fara bata labarin farkon haduwarsu da Tahir har kawo yanzu

"Ina tsoro ina tsoron Ya haidar muddin ya ji zamu matuƙar samun matsala da shi gashi ni kuma bana jin zan iya rabuwa da Tahir yanzu, yayi min sabo da komai nashi idan na gama paper ban san ta yadda zamu cigaba da haɗuwa dashi ba kuma"

"kin tabbatar kina son shi Afnaan?"

"Da farko ina sauraranshi ne saboda kirkinshi da taimakon da yayi mini a sadda nake tsananin bukatar hakan amma a yanzu wallahi ina son shi sossai, har waya ya saya ya bani akan in ajiye a ɓoye muke yin magana na ƙi karɓa don ban san me zan ce a gida ba"

"Kin cika tsoron Yayankin nan"

Girgiza kai tayi

"Na fa riga na mishi alkawari babu daaɗi yaji na karya"

"Toh ki karɓi wayan Tahir ɗin, kuma ya dinga zuwa kaman yadda yake ɗan zuwa akai akai akan wurin mama ya zo idan zai fita kiyi kaman kin raka shi ku ɗan fara tsayuwa tare na tabbatar Yayankin zai iya zuwa ya iske ku hakan zai nuna mishi kin tsayar da wanda kike so, ya tambayeki kuma ki faɗa mishi kyawawan halin Tahir ki kuma nuna mishi shi kike so"

"kina ga ba zai ji haushi na ba?"

"Haba ke ce fa shalelen Yaya Haidar ko ya ji haushinki ma na lokaci kaɗan ne"

A ranta kuwa fata take su yi baram-baram dalilin hakan har ma kusanci da kaunar da suke yi wa juna ya ja baya.

Washegari kuwa da take da last paper haka bayan ya kaita ya dawo daukarta cake ne mai hawa uku ya taho dashi da su kayan makulashe tana shiga motan ya fara mata congratulations on her final paper Finally an gama makaranta, sai murmushi take nuna mata yayi ta hure wutan ta kuwa hure ya ajiye ya mata tafi yace ta yanka, ta ɗaura hannunta kan dan karamin wukan shima ya ɗora nashi a kai ta ɗan firgita sbd zata iya cewa bayan Baba da Aliyu babu wanda ya taɓa rike mata hannu amma sai ya matse dole suka yanka a tare ya yanko ya saka mata a baki, yace ita ma sai ta mishi da kyar ta iya yi mishi ya dubeta

"Pretty ba karamin kewanki zan yi ba please ba don ni ba ki amshi wayan nan ko muryarki nake ji kila zan samu sauƙi"

Kallon wayan tayi Iphone ne Dukda bata san wanne ne ba amma ta tabbatar yana da tsada, numfashi ta sauƙe kan tace

"Yanzu idan aka gani a gida fa? Wlh ban taɓa shiga da abu gida ban sanar ba ina jin wani iri idan Yaya ya gani in ce me?"

"Zaki bari ya gani ne? Ai ba zaki bari ya gani ba yanzu fa duniya ta chanza kai ya waye ki zama wayis mana... Irin dabarar matan nan dai ki ɓoye shi muke magana da dare nima ba zan kira ba sai kin yi flashing"

Haka ba yadda ta iya ta karɓa ta sanya cikin jakanta, amma fir sauran cake din ta ki karɓa sai choculate ɗaya da ta ɗauka shima suka yi sallama ta fita jabir dake tsaye daga nesa jikin wani shago ya kalleta da mamaki, sai dai bai kawo komai ba ya karɓi abin da zai karɓa yabi bayanta don yau Aliyu bai je lesson ba sbd ɗan rashin jin daaɗi da baya yi.

Tana shiga ta san Yayanta yau yana gida kofan shi a buɗe labule ne kawai a sauƙe tsabar rashin gaskiya haka ta wuce bata leƙa ɗakin ba tayi cikin nasu ɗakin tayiwa wayan kyakyawar ɓoyo ta sauya kaya ta fito ta ɗauki abinci duk zuciyarta fal tsoro.

A chan kuwa ɓangaren Jabir yana shiga ya ɗan bugi bayan Aliyu dake kwance a kife yace

"Malam wallahi ka zo kayi aure ka huta da wannan ciwon cikin bala'in"

Tsaki ya ja yace

"Ni na ce maka cikina ke ciwo daga bani da lafiya kawai sai ciwon ciki?"

Jabir na dariya sossai ya furta

"Ka rantse da Allah ba ciwon ciki bane? Haba Aliyu ba fa tun yau na san ka ba na kuma jima da fahimtar inda ka dosa gashi kuma Allah ya yi ka baka son kula mata bare a ce akwai wacce kake so da aure ko dai mu zaɓar maka ne mu maka auren jeka ga ɗakin ka don wannan azabar na yawa"

Miƙewa yayi zai kai wa jabir ɗin duka da sauri ya kauce yana dariya tsaki Aliyu ya sake ja.

"Ina da Matata a hannu Jabir lokaci ne kawai nake jira"

"Da gaske Don Allah? Wacece haka ban santa ba? A ina take?"

Ko ci kanka bai ce ba ya fice daga ɗakin ruwan sanyi yaje ya watsa ya dawo sanye da jallabiyarshi sai lokacin jabir yace

"Yauwa ni na ga wani ya sauke Afnaan a mota ko waye shi?"

Dan tsayawa yayi daga zaman da yake kokarin yi kan ya juyo ya kalli jabir.

"Afnaan dai? Wani? Ya yake?"

"Fari haka dogo"

Tsammm Aliyu ya sake yi

"Ka tabbatar jabir?"

"Zan maka karya ne, ka san ban taho da mota ba na sauka bakin hanya in sayi Credit kan in ƙaraso bayan na saya na juya kenan na ganta kuma tana gabana har muka shigo cikin gidan nan bare in ce wata na gani"

Dakewa yayi bai ce komai ba ya soma shafa mai kaɗan kaɗan a jikinshi alhali cikin kanshi kuwa tunani ne fal Meyasa Afnaan zata shiga motar wani? Waye shi? Ajiyewa yayi akan bari yaga zata bashi labari? Don ya santa bata ɓoye mishi komai kuma bata iya shiru idan abu ya faru da ita sai ta bada labari ko bata ba wa mama ba zata bashi.

Har dare jabir na gidan sai bayan isha suka ci abinci ya tafi, kuma har lokacin Aliyu na sa ran zata mishi wani magana sai dai bai ji tayi ba har Washegari da safe ya shirya ya wuce shago yana ƙara shiga rudani da mamaki, yau ma Magrib ya dawo har Bento cake ya saya mata na murnar kammala secondary school tayi farin ciki Dukda bai kai na Tahir girma da tsaruwa ba sai kuma ta tuna matsayi ba ɗaya ba ina Ya Haidar zai iya sayan wanchan ai sai ya yi ciwo ya saya sbd tunanin kuɗinshi ta karɓa tana godiya yana ta sa ran ta mishi maganan wanda ya sauketa a mota amma bata yi ba har aka sake kwana, da yamma sossai suna zaune kitchen da mama suna aiki suka ji sallama, Indo ce ta leƙa ta dawo tana cewa wai wani ne yana neman izinin shigowa, hijabs suka saka kan ta mishi iso sossai gaban Afnaan ya faɗi ganin Tahir cikin girmamawa ya gaida Mama haka ta amsa cikin fara'a tare da mishi Adu'a ya ajiye ledan da ya zo dashi yace mata dama ya zo ne ya gaisheta daga haka ya miƙe zai fita

"Afnaan babu rakiya?"

Hakan da ya faɗa yasa ta miƙe ta bi bayanshi da kallo mama ta bi su yanayin fuskanta na ɗan sauyawa kaɗan zuwa mamaki ko tsoro.

"Me ya hana ki kunna wayan nan Afnaan? Kin kuwa san ya nake bacci? Kina so ciwo ya kama ni ko Pretty?"

Ta girgiza kai

"Don Allah ki rage wannan tsoro kin girma fa, yanzu fa kin shiga 18yrs already akwai wanda ya isa ya miki dolen wani abu ne? Babu so please take a chill pill ki mori rayuwarki to the fullest"

Numfashi ta sauƙe

"Zan kunna kayi haƙuri"

"yauwa ko kefa ko in turo ne hajjin bana ayi damu daga nan mu wuce honeymoon?"

Da suri ta rufe fuska tana Dariya daidai nan Aliyu ya iso kofan gidan.

Na gode*

                        

                           🖤Gureenjoh🖤

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.