Free chapter · Read without an account

BABI NA BAKWAI

by Fatima Eshak · SAFEENATU

SAFEENATU

NA

UMM ASGHAR

Arewa books @UmmAsghar

BABI NA BAKWAI

Tunda aka ce muje mu shirya nake kuka. Kuka nake yi sosai har da shesheƙa.

A haka nayi wanka na shirya a cikin atampar embellished super gold background dinta blue sai ratsin lighter shade of yellow da brown, na nannaɗe jikina da farar laffaya mai adon flowers kalar light blue. Ya Aisha da Ya Zainab suna tsaye akan mu muka shirya, wani oil perfume mai azaɓar ƙamshin daɗi Ya Zainab ta bamu tace mu shafa a jikinmu. Bayan mun gama kuma ta bamu wani abu a cup tace mu shanye yanzu mu bata cups ɗin. Ni dai har na gaji da irin wannan gyaran da ake yi mana, tunda lokacin bikin ya ƙarato yayyenmu suke tsaye akan mu wajen gyaran jiki. Anty ma ba'a barta a baya kuma komai zata yi mini tare da Khadija take haɗawa. Duk abinda tasan na amfani ne tare tayi mana sai ɗan abinda ba za'a rasa ba.

Wajen Baba aka fara kaimu yayi mana nasiha tare da sanya albarka ya danƙa mana mukullen motocin da ya mallaka mana ni da Khadija ƙirar Toyota Camry, daga nan aka miƙa mu wajen Mama muka yi mata sallama sannan wajen Anty. Kowaccen su tayi mana nasiha bakin gwargwado, ana ɗaga ni za'a fitar dani daga ɗak8n Anty na tafi na rungumeta ina sakin wani irin kuka. A yadda nake ji da za'a ce an fasa auren na zauna a gida tsaf zan yarda saboda wata irin kewa nake ji ta taso ta lulluɓe ni.

Ni dai an fito dani ina ta kuka haka aka sakamu a cikin motar Baba wacce a ita za'a kaimu gidajenmu, daga ni sai Khadija da wasu Goggonnin mu guda biyu sai Yaya Umar dake driving motar.

A cikin gidansu Yaya Hamza dake sharaɗa nndc quarters zamu zauna a apartment ɗin shi da aka ware mishi a gefe guda a cikin gidan nasu. Kasancewar shi ɗa ɗaya tilo namiji da suke dashi yasa Umman shi tace sam bata yarda yayi nisa da ita ba.

Ni aka fara kaiwa kafin aka wuce a kai Khadija. Sai da aka fara sadani da part ɗin iyayen mijina aka damƙa musu amanata kamar yadda yake ga al'ada kafin aka dangana ni da nawa part ɗin.

Ƴan rakiyarmu basu wani jima ba suka tafi saboda akai Khadija nata gidan don haka ko ƙawaye ban samu sun zauna dani ba sai mutum biyu sauran duk sun wuce rakiyar Khadija.

Bayan ƴan kawo amarya sun wuce ne kawata Hafsa ta yaye mini lulluɓin da nayi da laffayar tana cewa "buɗe fuskar ki haka nan ki sha iska kin ji."

Murmurshi nayi mata ina ƙarewa ɗakina kallo, a gaskiya Baba ya kashe kuɗi wajen saya mana furniture sai dai mu bishi da addu'ar fatan alkhairi. Sosai aka narka dukiya wajen ƙawata mana gidajenmu, dama tun ana jere naji ana maganar irin kayan da aka zuba mana da yadda gidajen suka yi kyau. Komai da aka saka mana mai tsada ne tun daga kayan ɗakunamu har zuwa parlour da kitchen, komai mai tsada ne.

Muna nan da friends ɗina Hafsa da Bahijja muna ƴar hirarmu nan da can abokan ango suka rakoshi lokacin nan ƙarfe 9:30 na dare.

Dama parlour muka dawo muka zauna don haka anan suka same mu. Ina jin sallamarsu gabana yayi wata mummunar faɗuwa. Haka nan nake jin fargabar haɗuwar mu a yau ɗinnan da Albi yaci burin zuwanta gashi cikin hukuncin Allah ya nuna mana ranar.

Kan kujerar da nake zaune yazo ya zauna ya kamo hannayena duka biyu ya riqe a cikin nashi. Sunkuyo da kanshi yayi daidai kunne na cikin muryar raɗa yace "welcome to our humble abode, baby."

Kunya ce ta lulluɓe ni ganin bamu kaɗai bane amma ya iya riƙo hannuna a gabansu har yana yi mini raɗa.

Ina ji abokanshi nayi mishi tsiya wai wa yaga sabon shiga shi kuma yana mayar musu da "idan kun ji haushi goben nan naga invitation card."

Sai da suka gama barkwancinsu kafin suka yi mana ƴar nasiha da addu'o'i suka tashi zasu tafi bayan sun sallami su Hafsa da kuɗin sallamar ƴammata.

Hamza ne ya nemi dasu tafi dasu su ajiye su a gida. Sallama suka yi mini, godiya nayi musu sosai don sun yi mini halacci a harkar bikin nan.

Ina zaune anan inda ya bar ni ya dawo daga rakiyar da yayi musu.

Hannu yasa ya ɗagoni tare da bude mini lulluɓin fuskata don tun shigowarsu dana rufe fuskar ban buɗe ba har yaje rakiyarsu ya dawo.

"Masha Allah," yace tare da sumbatar goshina very lightly. Rungume ni yayi a jikin shi yace "i'm so happy Feenah, yau Allah ya cika mini burina daya nuna mini wannan ranar da kika zama mallaki a gareni. Ina fata Allah ya bamu zaman lafiya tare da zuri'a ɗayyiba." A zuciyata na amsa "Ameen," ɗin.

Ɗauka ta yayi gaba ɗaya in bridal style ya shiga dani ɗakin, bai direni a ko ina ba sai akan gado.

Fita yayi ya shigo da ledojin da ya bari a parlour.

Zama yayi a kusa dani ya sanya hannayenshi ya zagaye ƙugu na, hanshin shi ya kai saitin wuyana yana sunsuna a hankali.

Kunya ce haɗe da wani baƙon yanayi suka ziyarceni a lokaci guda. Ba tare da nayi aune ba kawai na tsinci bakina a cikin nashi yana kissing ɗina. Ƴar ƙarama suma nayi domin kuwa ya kaini wata duniya ne da ban taɓa zaton akwai ta ba by mere kissing kawai.

Mun ɗan ɗauki lokaci a hakan kafin ya iya zare bakin shi daga nawa, gaba ɗayanmu numfashi muke saukewa da sauri-sauri. Sai da ya samu nutsuwar shi ta dawo sannan ya sauka ƙasa ya zauna akan rug ɗin dake shimfiɗe a tsakar ɗakin ya buɗe ledojin da ya shigo dasu.

"Bismillah" yace mini tare da miƙa mini hannunshi.

A kunyace na sanya hannuna a cikin nashi sannan na sauko ƙasan ba tare dana yarda na hada idanu dashi ba. To ta ina ma hakan zai faru bayan abinda ya wakana a tsakaninmu yanzu-yanzu.

Ban iya sakewa naci naman nan ba duk kuwa da yunwar da nake ji don fa rabona da abinci tun breakfast amma zullumi ba zai bari na sake na iya cin naman nan ba, fresh milk ɗin ce ma na sha rabin kofi.

Bayan mun gama ne ya umurceni dana shiga bathroom nayi alwala yayin da ya tattare kayan da muka gama amfani dasu ya fita.

Tashi nayi na shiga bathroon ɗin, sai da nayi brushing haɗe da kuskure bakina da mouthwash kafin nayi alwalar na fito.

Zama nayi a bakin gado ina jiranshi.

Babu dadewa sosai ya shigo ɗakin yana sanye cikin silk pyjamas riga da wando kalar light brown.

Sallaya ya shimfiɗa tare da umurta ta da na tashi muyi sallah.

Bayan mun idar ya dafa kaina ya karanta wannan addu'ar

"Allahumma inni as'aluka khairaha wa khaira ma jabaltaha alaihi wa a'udhu bika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi."

Tashi yayi ya miƙar dani tsaye kafin yasa hannu ya warware naɗin laffayar dake jikina ta zube a ƙasa. Wardrobe ya buɗe ya fito mini da cotton kayan bacci gajeren wando da riga kalar lemon green and pink ya miƙo mini.

A kunyace na karɓi kayan na shiga bathroom na saka, sai dai kuma na kasa fitowa daga banɗakin. Ina matuƙar jin kunya da nauyi ya ganni a haka.

Na jima a cikin bathroom ɗin ina saƙa da warwara na yadda zan yi na fita a yadda nake, sai can dabara ta faɗo mini don haka na ware zanin da na cire na rufe jikina dashi kafin na fita.

Yana kwance akan gadon kwanciyar rigingine yana kallon ceiling.

Ina fitowa ya tashi ya taroni tare da karɓar kayan hannuna ya ajiye cikin wardrobe, daga nan kuma ya ɗauke ni gaba ɗaya yayi kan gado dani. Shiru nayi ina jin zuciyata tana wani irin bugawa da ƙarfi. Gaba ɗaya tsoron shi ya gama kama ni. Tashi yayi ya kashe fitilar ɗakin kafin ya dawo kan gadon ya kwanta

A hankali naji hannayenshi suna bin sassan jikina, gabaki ɗaya jikina ne ya ɗauki rawa amma Albi bai kula ba, bakinshi ya ɗora akan nawa yana kissing ɗina a zafafe hannayen shi kuma sun kasa tsayawa wuri ɗaya, kafin wani lokaci ya ruɗa mini jikina yana nema ya fitar dani daga hayyacina.

A taƙaice dai a wannan daren Hamza bai ɗaga mini ƙafa ba sai da ya mayar dani cikakkiyar mace, na zama shi ya zama ni. Wahala iya wahala na sha ta saboda abinda ya faru a tsakaninmu baƙon al'amari ne a gareni.

Da taimakon shi na samu na kimtsa jikina da asuba. Fitowa nayi ina tafiya a hankali don sai nake jin jikina yayi wani fayau tamkar babu ƙarfi a tare dani. Dauriya sosai nayi wajen yin sallah. Ina idarwa na ɓingire anan wajen da nayi sallar wani nannayan bacci yayi awon gaba dani ko addu'a ban samu nayi ba. Farkawa nayi na ganni a kwance akan gado cikin jikin Albi.

Ban sani ba ko ya jima da farkawa ko kuma motsina ne ya tashe shi.

"Good morning sleepy head," yace tare da kissing dina a goshi.

Murmushi nayi cikin jin kunya ina mai ƙara nutsa fuskata a cikin ƙirjin shi. Ɗagoni yayi muka haɗa ido, wani annurin farin ciki naga yana fita daga fuskar shi. "Thank you for giving me the most amazing gift. Allah ya bamu zaman lafia haɗe da zuri'a masu albarka."

Ƙasa-ƙasa na amsa mishi ina mai jin wani irin farin ciki yana ratsa zuciyata.

"Tashi kiyi wanka sai muje muyi breakfast ko, don yunwa nake ji." Ƴar dariya nayi ina mai miƙewa sai dai fa nima ɗin yunwar nake ji don haka ban yi musu ba na shige wankan kamar yadda ya buƙata.....

UmmAsghar

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.