Free chapter 路 Read without an account

Ajnabiyya page 6

by Hajja ce 路 AJNABIYYA

AJNABIYYA...

NA

*HAJJA CE* 馃憟

Arewabook@Hajja22522

Wattpad@Hajjace

Facebook@Hajjace

Page 6

Tunda ta shiga cikin motar ta samu ta manne a jikin 茩ofar, wani irin sihirtaccen 茩amshi ne yake dukan cikin hancin ta. Gabaki 蓷aya sai ta tsargu taji tamkar zata lalata masa 茩amshin da motar keyi saboda ita 蓷in babu wani 茩amshi a jikinta. 'Anya bata yi kasada ba kuwa wajan shigowa motar nan? Gabaki 蓷aya ta kasa nutsuwa ji ta ke tamkar tace ya tsaya ta fita. Amma ta kasa fa蓷a saboda ganinta a cikin motar yasa taji wani irin yanayi a zuciyarta. Ji ta ke yi kamar yana iya jin yanayin warin da jikinta keyi. Sanyin ac da ke ratsa ta yasa ta fara jin wani irin mugun alfahari cikin ranta. 'Haka ya dace da ita, wannan ni'imar itace dai-dai matsayinta wallahi.' Da wani irin yanayi take jin cewa dan Allah mai kai da蓷i da蓷i? Me ake yi da wahala? Wa yake san wahala? Tuni ta fara mantawa da damuwar jarabawar da bata samu nasara akai ba. Tunanin ta ya fara lulata wata nahiyar mai cike da albarka. Shi kuwa Mubasshir Ungwaggo tuki yaci gaba da yi kasancewar ta ta蓳a gaya masa sunan unguwar da suke. 'Wai yau itace ake kawowa gida a mota. Yau itace babu shan rana babu gajiya bare tunanin a wane hali zata koma gida.

"Da alama an ta蓳a zuciyar nan taki mai cike da albarka ko? Tabbas ko waye da zanyi ido biyu dashi sai ya gane kuransa." Ya fa蓷a yana yin parking a dai-dai wani shagon lemuka da ruwa. Kashe motar yai yana kallanta yace.

"Mintuna biyar zaki aramin na shiga na fito." Ameerah bata ce komai ba, dan ita wani irin da蓷in kasancewar ta a motar ya gama rufe ta. Shagon ya nufa kai tsaye, lemo da ruwa sai jarkokin yogurt da ya siyo da different types na biscuit ya kwaso mata. Ta tagar da ta ke a zaune ta hango shi hannunsa 蓷auke da ledoji. Ameerah ta shiga gyara zama zuciyarta fal tunanin. 'Ni ya siyowa? Ko gidan su zai tafi dashi? Menene a cikin ledojin?' Nan da nan ta fara addu'a Allah yasa ita zai bawa, idan nata ne ita kam ya zatayi? Bata san ya dawo ba, ji kawai tayi yana furta.

"Sorry fine baby na barki ke kadai." Yayi maganar yana ajiye ledojin a back seat tare da 蓷akko jarkar ruwa 蓷aya ya bu蓷e ya mi茩awa Ameerah cike da kulawa. Ta kalli ruwan cike da san jin 茩arin bayani akan fuskarta. Ya gane abinda ta ke nufi. Sai da ya 蓷an saki murmushi kafin yace.

"Kisha ruwa dan naga kamar kina bu茩atar shi." Ameerah ta kar蓳a cike da jin nauyinsa ta juyar da fuskarta tana shan ruwan. Mubasshir Ungwaggo ya saki wani 茩ayataccen murmushi, kunyarta 蓷in nan tanasa shi jin nutsuwa da ita, yana jin tabbas maganin matsalarsa ce tazo 茩arshe. Yana da ya茩ini cewa akan yarinyar nan zai cika burin dake ransa. Sai da ya tabbatar ta gama shan ruwan sannan ya kunna motar. Kai tsaye suka nufi unguwar su Ameeran. Da kanta ta dinga nuna masa har suka iso 茩ofar gidan nasu. Mubasshir Ungwaggo bai wani sha mamakin ba ganin gidan su Ameerah, saboda ko a yanayin ta zaka san cewa ba abin mamaki bane dan ta fito daga irin gidan. 茦o茩arin bu蓷e motar ta yi zata fita taji ta a rufe, ta 蓷an juya ta kalleshi.

"Munzo fa ga gidan namu nan." Yace,

"Na gani, haka zaki tafi babu sallama?" Ameerah tayi murmushi karo na farko da yaga murmushinta.

"Wowww! Na siya murmushin nan, nawa zan bada?" Ameerah taji kamar ta zura yatsa a kunne ta murza saboda yadda taji kunnan nata yana motsawa tamkar wanda yaci abu mai da蓷i har da蓷in yasa kunnen motsawa. 'Da gaske biya zai yi? Shi komai tayi sai ya biya? Anya harkar nan ta gaskiya ce?' Taji zuciyarta tana tambaya, amma babu amsa dan bata da mai bata amsoshin a yanzu. Ganin tayi shiru yasa shi zaro ku蓷i daga aljihunsa ya shiga bubbuga su cikin tafin hannunsa kafin ya 蓷ora mata su akan cinyarta yana cewa.

"Na gode da wannan murmushin, sai yaushe zamu ha蓷u? Kinga dai duk wannan ba ha蓷uwa ba ce da zaki sanni na sanki. Idan nazo gida za'a barki ki fito?" Ameerah da tunda taji 蓷umin ku蓷in nan a jikinta, gabaki 蓷aya ji da ganinta suka nemi gushewa. Satar kallon ku蓷in kawai ta ke yi ta 茩asan ido, sunfi na ranar nan yawa, tuni zuciyarta ta shiga hango mata abubuwan da zata yi dasu. Dama wancan da Mama ta gayawa Baba, ya kirata yai mata tambayoyi ta gaya masa, cewa yai ta 蓷akko ku蓷in a siyo masara dan a lokacin dama ya rasa yadda zai yi ya nemo abinda za'a ci da safe. Ran Ameerah yai bala'in 蓳aci a ranar, gashi babu yadda zatayi dole ta ha茩ura ta fito da ku蓷in aka yi amfani dasu a gida. Wannan kuwa da ta ke gani akan cinyarta tasa a ranta cewa ko kyallinsu babu wanda zai gani sai dai suji labarin su.

"Ko baki fara hira da saurayi ba?" Taji ya fa蓷a cikin tsokana, dan a yadda yaga gidan nan nasu ya tabbatar irin gidan nan ne da yarinya ta gama secondary school ake mata aure. Dan haka yasan da wahala ace Ameerah bata fara tsayawa da saurayi ba.

"Ni dai bana yi." Yaji ta fa蓷a murya 茩asa-茩asa.

"Ba kya mene fine baby? Da gaske bakya tsayawa da samar?" Ta ce masa.

"Ehh ko Yayana ma baya bari." Da mamaki yace,

"Saboda me?" Tace,

"Suna so nayi karatu sosai."

"Kice dai yanzu nima komawa zanyi naci gaba da jara ko?" Ameerah tayi saurin kallansa. Girarsa 蓷aya ya 蓷aga mata yana kanne idon shi 蓷aya. Saurin 蓷auke fuskarta tayi daga kallonshi, ita kam sam bai yi mata ba. Amma kuma bata so ya barta tunda gashi ha蓷uwa biyu kacal ya kasheta da ku蓷i da bata ta蓳a ri茩e irin su ba da sunan nata. A soyayya dai ita ba taji tana son shi ba. Idan har yana ganin zai iya kulata a hakan fine. Amma bata jin zata iya auransa. Dan gabaki 蓷aya ba kalasa take son aura ya zame mata miji ba. Da wani yanayin a cikin zuciyarta ta ke fa蓷in.

"Ban sani ba gaskiya. Kuma kaga yanzu dai jarabawa zamu fara yi ta fita daga makaranta. Kuma ni Yaya Ammani masifa yake min idan namiji yazo gidan mu yace yana nema na. Da kanshi yake fita ya kore su. Idan kuma baya nan suka zo, idan Baba yana nan shi yake fita, shima ya basu ha茩uri yace karatu nake yi sai dai idan na kammala." Mubasshir Ungwaggo ya yi murmushi wanda ya bayyanar da ha茩oransa. Sai da ya sake kallanta yana jin wani irin yanayi a kanta yace.

"Ni nazo a sa'a kenan, tunda gashi kina matakin karshe a karatu ba bayyana a gareki, kinga kenan kina da sa'a Allah ya aiko miki da miji kina gama Neco sai biki." Ameerah kanta a 茩asa, duk wasu kalamai da yake mata ba ta jin su a zuciyarta. Daurewa tayi dan a ganinta dama ce ta samu da zata samu ku蓷i a jikin guy 蓷in ta morewa rayuwarta. Ta 蓷an kalleshi in second ta janye idanunta dan cikakken kallo ma bata san yi masa tace.

"Nima ban sani ba sai abinda Baba yace."

"Ni zan zo nayi magana da Baban karki damu. Kawai dai ina so ki kula min da kanki, kinga ke 蓷in ba irin matan nan bane da zasu yi ta ballagazar da kansu a gari suna kula maza anyhow. Ki kula da kanki dan ina da kishi sosai." Bata gane inda maganar shi ta nufa ba, saboda hankalinta gabaki 蓷aya yana kan ku蓷in dake kan cinyarta. So kawai ta keyi ya barta ta tafi dan yin hira dashi ba faranta mata takeyi ba. Kamar yasan abinda yake ranta, ya mi茩ar da hannunsa ya bu蓷e mata 茩ofar yana cewa.

"Ga wa蓷annan kayan ki shiga dasu ciki." Ameerah ta juya tana kallan unguwar su, ganin mutane sunyi mata caaa yasa taji wani iri a jikinta. Mai da idanunta tayi kan Mubasshir Ungwaggo da yake kwaso ledojin dake backseat yana dawo dasu kan kujerar da ta tashi. Da haka zata ce masa a'a ya barshi, amma sai wata zuciyar tace mata. 'Ina ruwanki da 拼an unguwar ku? Zasu baki ne su 蓷in? Idan fa baki kar蓳a ba shikenan kinyi wa kanki' Sai ta kasa fa蓷ar cewa ya barshi, tasa hannu ta 蓷auki ledojin duka tana yi masa godiya. Yana tsaye har ta shiga cikin gidan su. Ya lumshe ido yana sake jin ransa na tabbatar masa da cewa tabbas Ameerah itace irin wacce yake nema ido rufe, gashi kuma Allah ya bashi cikin sauki, dan yaga alamar ba zai wani sha wahala akanta ba.

Tana shiga zauren gidan ta tsaya ta zaro dubu biyar ta soke ragowar da bata san ko nawa bane ba a cikin jakar makarantar ta. Bata saba irin wannan halin ba, toh ina ma ta samu ku蓷in bare tayi hakan? Yanzun ma ganin yadda aka yi mata ranar ne yasa wannan idea 蓷in tazo mata. Fuskarta babu fara'a ta shiga cikin gidan. Da kyar ta yi sallama tana bin wajan girkin su da kallo cikin zuciyarta tana wata irin dariya mai tattare da yau ko a jikina.

"Yauwa Ameerah naji da蓷in shigowarki, tun 蓷azu nake jiran yaro yazo ya 蓷akko mana ni茩an dawar can a inji ban samu ba. Maza-maza ki ajiye jakar ki kizo kije 拼ar albarka ki 蓷akko." Mama ta fa蓷a tana kallan Ameerah sa茩e茩e da ledoji a hannunta. Baki sake ta ke kallanta tana san jin 茩arin bayani, zuciyarta tafi bata cewa kyauta ce taci a makaranta su. Sai da Ameerah ta shiga cikin rumfarsu tana zare hijab 蓷in jikinta tare da ajiye ledojin take cewa Mama.

"Mama dan Allah yau dai abar yin tuwon nan haka. Bari muga meye a cikin nan 蓷in sai muci shi kawai." Tayi maganar tana 蓷aga abubuwan dake cikin ledojin. Da mamaki Mama ke cewa.

"Wannan kuma fa?" Ameerah dake jin yanayin sauyawar muryar Mama a jikinta yasa nan da nan kuwa itama ta ha蓷e rai cikin ranta tana cewa. 'Uhm-ummm nifa wallahi wannan zanci, ga sauyi yazo mana har gida ace na ajiye? Yogurt fa? Yaushe rabo? Dan ma dai wani lokacin Yaseer yakan siya mana, amma ai ba irin wannan bane ba.' Yawun bakin ta ne taji ya tsinke. Tabbas yanzu ta samu irin na masu ku蓷i. Yanzu ne aka fara nuna mata ainahin yadda ya kamata ta kasance. Lallai kam zata morewa rayuwarta amma gashi taji Mama na neman kwafsawa wanda hakan bata tunanin mai yiwuwa ne.

"Ko baki ji tambayar da nayi miki bane Ameerah?" Cewar Mama idanunta still yana kan Ameerah. 

"Naji Mama, wannan mutumin ne da ya ta蓳a bani dubu goma kwanaki. Toh yau da shi muka zo har nan 茩ofar gidan yace zai zo suyi magana da Baba saboda na gaya masa Yaya Ammani baya bari na tsaya da maza." Jin yazo har 茩ofar gida ne yasa hankalin Mama kwanciya. Amma duk da haka bata saki fuskarta ba, kallan kayan kawai ta keyi tana cewa.

"Sai ki kwashe su kije ki kai 蓷akin Baban ku idan ya dawo ya gani sai a rarraba. Kizo yanzu ki wuce ki 蓷akko min ni茩an nan shi nake ta jira." Ameerah tayi shiru kuka ya cika mata ido. Wannan kalar rayuwar ta gidan su gabaki 蓷aya batayi mata ba. Saboda rayuwa ce marar 拼anci, a takure komai yake zuwar mata. Ji tayi Mama tazo ta kwashe kayan ta wuce 蓷akin Baba dasu tana fa蓷in.

"Ki tashi ki wuce kije ki 蓷akko min, yana nan zaki ganshi a cikin farin buhun nan da nake kai 蓳arjin masara idan zamu yi dambu." Ameerah ta tashi a fusace tayi waje ri茩e da jakarta. Tana tafiya zuciyarta kamar zata fashe. 'Har sai yaushe ne za'a barta tayi yadda take so ne? Gashi da alama kamar tana da sa'a tunda gashi ha蓷uwar ta da Mubasshir Ungwaggo sau biyu kacal, amma har ta fara hango canje-canje a tattare da ita. Nan gaba ka蓷an tasan zata kerewa sa'a, zata yi rayuwa irin ta 拼an gayu.' Saboda tsabar tunani da rashin nutsuwar zuciya bata ma san tazo wajan injin ba, abu 蓷aya kawai zata iya tunawa shine ganinta a gaban injin yana ta 茩arrr.

Lokacin nata akeyi dan sai da aka gama yin na farar masara sannan aka fara yiwa masu na dawa. Gangarawa tayi can gaba da injin ta shiga wani shagon provision. Wani irin nisha蓷i ta ke yi tana jinta wata daban. 'Kenan da ta fito da ku蓷in duka haka Mama zata kwace su shikenan ita da su sai kallo?' Ta bu蓷e jakarta ta zaro dubu biyar tace abata madara 拼ar sachet zare guda. Sai sukari gwangwani biyu. Milo ma zare guda. Sai lipton kwali 蓷aya. Yadda ta ke yin siyayyar kawai sata farin ciki yake yi, ji ta ke kamar ana bu蓷e mata duniya da abinda yake cikin ta ana cewa ta zabi duk abinda ta ke so. Har ta fara tunanin barinshi haka sai ta hango Indomie da sabulun wanka da na wanki tace a bata Indomie 蓷in guda biyar sauran kuma 蓷aya-蓷aya. Duka kayan aka saka mata a leda ta biya ku蓷in sannan ta juyo.

Cikin zuciyarta tana al茩awarin kayan nan Mama ba zata ga irin su ba bare ta hanata yin amfani dasu. Lokacin da ta koma an gama ni茩an 蓷auka kawai tayi tana tafiya tana jin farin ciki. Gabaki 蓷aya mantawa take akwai buhun ni茩a a hannunta. Ji take duka ledoji ne masu 蓷auke da kayan shopping a ciki. Tana shiga gida ta wuce sashin Inno da sauri, Allah ya taimake ta Inno tana can wajan bawa kaji da awakin ta abinci. Ameerah ta shige 蓷akin. Inda ta ke ajiye kayanta ta 蓷aga kwalayen ta zuba ledar ta sannan ta fito da gudu ta nufi sashin su. Mama na ka蓷a miya yau ba sabun ba busasshiyar kubewa aka yi. Ameerah ta ajiye ni茩an ta shige cikin 蓷aki. Kaya ta cire ta 蓷aura zani tasa hijab. Mama bata kula ba ta fice zuwa sashin Inno. Tana shiga Inno tace.

"Wato kika shigo min waje babu sallama, kawai ina juyowa na hango ficewar ki. Me kika 蓷aukar min a cikin 蓷aki?" Ameerah na shiga ciki ta ke cewa.

"Inno meye abin 蓷auka anan fisabillahi?" Da mugun haushi jin kalamanta Inno ke cewa.

"Ehh tunda ga fa茩iriya da bata ajiye ba bata bawa wani ajiya ba ko? Ina gaya miki idan kika sake zuwa min babu sallama sai na kwankwashi kan nan naki." Ameerah ta yi dariya kawai tana janyo sabulu ta fito tana fa蓷in.

"Wanka zanyi a nan."

"Da wane ruwan? Ina ce tun jiya nake fama kizo ki 蓷ebo min, da yake kin rai na ni kika gudu? Toh bani da ruwan da zaki wanka anan, tafi can gidan ku kiyi." Inno ta fa蓷a tana ture Ameerah daga wajan ruwayenta. Cike da mita taci gaba da cewa.

"Idan wankan ya zame miki dole kiyi shi anan. Toh kije ki samo ruwanki ga ban蓷aki nan ba hanaki shiga zanyi ba." Ameerah ganin da gaske Inno rashin mutunci take yi mata, sai kawai ta juya tana cewa.

"Shikenan na tafi Inno ga ruwanki nan na bar miki."

"Eh naji abar min abu na. Ke yarinyar nan yanzu kin fara fan茩are mana wallahi."

Mama na tanka蓷e Ameerah ta shiga. Ko kallan wajan ba tayi ba ta 蓷auki bokiti tana 蓷ibar ruwa Maman tace.

"Idan kin huta zuwa anjima zaki shirya kije Yaya Mari na kiranki." Ameerah cikin rashin damuwa dama tun 蓷azu ta ke neman hanyar da za'a barta ta fita, sai gashi ta samu cikin sauki. Dan haka ba wani 蓳acin rai ta ce da Maman.

"Toh." Mama ta kalleta da mamaki dan ta zata sai tayi ta fama da ita, musamman ma da ta ga yau ma ta hanata ta蓳a kayan saurayinta. Tana kallo ta shige ban蓷aki bata sake cewa komai ba. Yau kam ta da蓷e a ban蓷aki tana wanka, yo an samu sabulun eve ana sa蓳ashi 茩amshin na ratsa mata cikin hanci yana sanya mata nutsuwa. Yau ba da ragowar wanki ake yi ba, hakan yasa har ta da蓷e ba ta sani ba. Tana gamawa ta maidashi kwalinsa ta 蓳oye ta fito. 茦amshi ya cika hancin Mama ta dinga bu蓷e hanci, da mamaki ta ke kallan Ameerah tana cewa........

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.