Free chapter 路 Read without an account

43

by Aminatu nazeer 路 HALIMATUS'SADIYAH

A gidan Alh inuwa, girkin Umma ne yau, bayan ta kai mashi abinci ta tsaya har sai da ya fito ya fara cin abinci ta mashi mgn a kan Asif da Nur.

Bai ce komi ba har sai da ta gama. Ya sidai yatsun da yagama cin nama sanan ya ce "Eh wannan shawara ce mai kyau."

Sannan ya mike ya je wurin sink ya wanke hannun sa ya dawo ya zauna ya ce "Sai a fidda ranar da za a sa auran, idan ita Raihana ta wa mijin na ta mgn."

Umma ta ce "Toh shike nan, da

man na fara tuntubar ka kafin a tuntubi mahaifin yariyar."

Ya ce "Ba damuwa ay shi ya na da hankali ba kamar dan uwansa ba, shi ya dauko daidai da shi yar mutunci yar arziki ba matsiyata ba masu bamu bamu.

Ke ma sun shayen ki har da biya mata kudin flight wanna ay asarar kudi ne da albazaran ci."

Ta ce "Alh na ga komi ya wuce yaron na yana son matar shi kuma suna zaune lfy babu wani tashin hankali kuma bani bani da ka ke cewa family din su h

Halimatu ba su da kwadayi da son zuciya, mutane masu wadata wadda wannan wadata sai wanda Allah ya cida."

Ya dagatar da ita da hannu ya ce "Ya isa, Yayi na shi ya san wannan yarinya ko badan badai sai sun rabu na kyale shi ina sa mashi ido."

Daga haka ya mike ya wuce daki. Ta bishi da ido.

Bayan shigar shi ta sauke ajiyar zuci a ranta ta ce "Allah ya fi karfin ka, yana son matar shi ka raba shi da ita sbd son zuci, mahaifin yarinya ba ya ma fika kammala da wadata mi a ke yi da mai son kudi irin ka."

Haka ta cigaba da masifar ta a zuci har ta isa part din ta.

Readers kun ji fah abinda Alhaji inuwa ya xe ko badan badadai sai Asim ya saki Halimatu馃檳馃檳馃檳

Mi kuke tunanin zai faru??

Anya Asim zai saki masoyiyar shi??

"Ba kudi ba ne wadata, wadatar zuciya ita ce wadata kuma ita ce arziki.."

Allah ya karamana wadatar zuci, containtment with what you have.

HALIMATUS'SADIYAH(sakayya)

Love, conspiracy & revange

Don't forget to vote, comment and invite others馃檹

Countless grateful for your time馃憤鉂わ笍

Meenamajeed love you馃拫馃拫

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol