Free chapter · Read without an account
PG 2
by Khadija · ANA BARIN HALAK
PG2
Washe gari na iso, daidai ƙofan makarantan zan shiga sai ga shi nan ya zo zai shiga da kekensa, matsawa gefe na yi dan na bashi hanya ya wuce, tsayawa ya yi sannan ya ce.
" Ki wuce ma na."
" To nagode." Na faɗa har nazo shiga cikin makarantan na ji ya ce.
" Don Allah ko za ki taimaka min ki yi min submitting assignment di na."
Jiyowa na yi ina kallon sa, sannan na ce. " To kawo." Murmushi ya yi sannan ya fito da litafinsa ya Miƙa min na shige cikin makarantan da sauri, na haura sama na yi submitting assignment saboda kar suyi tunanin ni ma kaman su ne ina da wani tunani a kaina game da shi. Ai kuwa ina shiga ajin naga su Precious duk sun rufesa, gaskiya kam ya yi kyau saboda kalan shigan ƙananun kayan da ya yi, da ya ke first term ne kuma ana sanyi abun ban haushin ma wai har da Nabila a cikin su.
Wucewa na yi ba tare da na musu magana ba, dan bakin ciki zama na yi na fito da Qur’ani na fara maraji'a kafin malamin ya shigo a fara karatu.
Mintuna talatin kuwa akayi ringing bell alamun lokacin fara karatu ya yi, kuma abun ya yi mun dadi saboda za a baza wannan group in na rashin hankali.
Uhmmm karatun yau ya yi min dadi sosai saboda duka favourite subject dina akayi, muna cikin copying computer note an dan tsaya sai ya jiyo ya kale ni ya ce.
" Ƙanwata dan Allah zan iya ganin note din ki wallahi am lost tun dazu."
Ɗuka nayi na miƙa mishi, Bayan ya gama ya Miƙo min sanan ya ce. " Kowa na san sunan sa har ƙawayen ki amma ke kam ban san sunan ki ba."
" Kursum Yazeed Umar."
" Ki ce min ƙanwata ce da gaske tun da har surname in mu irin daya ne."
" Ai kuwa kam banbancin ku Umar ne kawai da babu a sunan ka." Nabila ta faɗa.
" Uhmmm to Wallahi daga yau ƙanwata zan dinga kiran ki ke kuma yayana."
Dariya nayi har wushriyana ya fito ina kallon sa na ce. " To shi ke nan amma za ka dinga kowa min karatu."
" Eh mana me zai hana bazan kowa miki karatu ba? To tun daga yau zan fara kowa miki karatu idan muka tashi sallah."
" To ai yau ƙarfe biyu zan tafi gida."
" Me ya sa?."
" Saboda ina zuwa hadda."
" Masha Allah to hadda so nawa ki ka suƙe?."
“ Kai to ishirin na hadda."
“ Masha Allah, Allah ya sa kafin mu gama SS3 ki hadda gaba daya."
“ Amin ya Allah. "
“ To yau she zan fara koya miki karatun?."
“ Gobe in Sha Allah lokacin break."
“ To shi ke nan ba komai, amma fa ina bulala fa idan mutum bai kawo min karatu ba.” Dariya na sake yi saboda yan da ya yi maganar cikin harshen barkwan ci.
“ To shi ke nan.” Dariya sosai aka saka cikin raha sanman aka cigaba da note in, wan da duk lokacin da aka ɗauka bai wuce minti talatin ba akayi ringing bell muka miƙe, na yi zan wuce sai na tuna cewa ina da sharan aji dan haka sai na ɗauki tsinsiya na fara Shara.
" Kanwata za ki yi latin hadda ba."
" Eh wallahi ina da shara ne yau."
" Ok to ba matsala amma ki yi sauri kar lokacin ya wuce."
To na amsa sannan na yi sauri na gama na tafi gida, ban yi wani tunani ba cewa da gaske Ashraf ya ke da cewa zai koya min karatu ba, sai washe gari da na zo makarantan lokacin break kai na ma a ƙasa ina muraji'a na da ya ke yau juma'a ne, kawai sai na tsinkaye muryansa cikin kunnuwana.
" Kawo na fara koya miki." Ɗagowa na yi na kali shi sannan na miƙa mishi Qur'ani.
" Wani surah?."
" Suratul hajj."
" Ok to Bismillah."
A hankali sautin karatu ya fara tashi a cikin ajin amma akwai ta daidai sahin da muki ne.
Wallahi ko ni ban san lokacin da na kawo haddan ba sai muryansa naji. " Barakallahu fih Masha Allah. Allah ya ƙara zakin murya da basira ƙanwata." Murmushi na yi sannan na ce. " Amin ya Allah nagode."
" Amma fa gaskiya ina da korafi."Nabila ta faɗa ta na kallon sa.
" To me akayi miki?."
" Gaskiya nima ya kama ta ka fara kira na ƙanwarka saboda in da ita best of friends ne." Dariya ya yi sannan ya ce. " To shikenan daga yau kin zama ƙanwata, amma fa ina bulala idan ba'a karatu."
"Eh mun ji."
" To ba matsala Allah ya iya mana."
Amin muka amsa gaba ɗaya, to hiramun muka shigaba har akayi ringing bell alamun break ya ƙare za'a fara karatu, in da muke da maths class.
Shaƙuwa me ƙarfi ne ya shiga tsakani na da Ashraf har a gida an san sa, saboda yan da ya ke taimaka min sosai musamam wurin hadda na, gashi kuma mutum ne mai dadin mu'amala wan da dukan ajin kai yabon sa amma kuma a duk innda mutum ya ke dole ka samu mai son da makiyin ka to haka ya faru da Ashraf, duk da yan da ake son sa Yasir baya son sa ko dan yan da ya ke da illim da basira ne oho Allah kaɗai ya barwa kansa sa ni daidai.