Free chapter · Read without an account
PG 6
by Khadija · ANA BARIN HALAK
PG6
Yau geography teacher mun bata zo ba dan haka free period muke da shi. Ashraf ne a gaban aji sai barkwan ci ya ke ta yi a na ta shan dariya, a na ihu a na shewa dan ko ni nan ina daga cikin su, wallahi ba mu san san da double period in ya ƙare ba aka shiga Short break wan da kai cin miti arbani.
" Ƙanwata yau ba ki kawo mana abunci ba ne?."
Murmushi nayi sannan na ce. " Wallahi yau ina sauri ban samu na yi girki ba."
" To shi ke nan ai bari in dan leƙa wajen na ga me ke faruwa."
" To a dawo lafiya." Kaɗa kansa ya yi sannan ya fice daga aiji.
Ihu sosai da shewa ake saki a waje dan haka da na ga ana fita dan ganin me ke faruwa ni ma sai na fita. Wai a she Ashraf ne ya ci kollo shi ne ake shewa ni kam komawa aji na yi dan jin hakan saboda na san tabbas sai dai in Nabila bata shigo ba, amma na san komai kaman ina wurin aka yi shi dan an ga an fara shigowa aji sabida anyi ringing in bell ana zo wurin tururuwan shigowa, aikuwa Yasir ya turi Ashraf har sai da tabarun sa su ka faɗi da ya durkusa, sai Yasir ya taka mishi hanun wan da sai da ya yi mishi targad'e ɗago kansa ya yi ya kali Yasir ya ce. " Haba Yasir me haka??."
" Dan uwar ka uban me ya faru da ka ke ce min me haka?."
" Baka gani ka ture ni kuma na durƙusa daukan tabaru na ka taka ni."
" Kutuma to dan uwar ka a yaushe na ture ka har tabarun ka suka faɗe."
" Yasir duk abunda za mu yi da kai kar ka ƙara zagin iyaye na."
" An zaga din me zaka yi?"
" Ni de na faɗa maka kar ka ƙara. To shi ke nan." Ashraf ya faɗa a sanda ya ke ƙoƙarin sa ke ya wuce.
Tas,tas,tas ƙaran mari ne a jire, sai da ƙaran ya huce aka fahimci ashe wai Yasir ne ya mari Ashraf. A bun da ya bata wa kowa rai kar rin ramawa ma da Ashraf bai rama ba ya wuce ya dawo sit ya zauna amma fa sai huci ya ke alamun faɗa ya ke da zuciyar sa akan kin ramawa da ya yi.
Yazeed ne ya rama me, wan da faɗan kuma ya koma tsakani Yazeed da Yasir, dama dukan su aji kai su ke da juna. Da kyar aka raba faɗan amma kuma ragowan period da akayi anyi shi ne ana zaje zaje tsakanin Yasir da Yazeed, har suka shirya cewa idan an tashi su haɗu ayi dambe.
Da farko Yazeed ya yi shiru ya dai na kula Yasir, amma kuma Yasir bai dai na zajin sa ba ganin Yazeed ya ƙi kula shi, ya danno wata zagi ya ɗana wa Yazeed wan da hakan ya sa Ashraf ya ce. " A ina ka ke so a haɗu in an tashi din???"
" Ƙaraman ƙofa bayan makarata ."
" To shi ke nan consider it done."
" Yayana dan Allah kar ka biye shi?."
Kallo na ya yi ta gefan ido ba tare da ya ce min komai ba, wan da haka ya nu na min ƙarara babu a bun da zai hana shi zuwa, dan haka na ja bakina na yi shiru a rai na ina addu'an Allah ya kawo a bun da zai hana wanan faɗa, saboda gaskiya ina matuƙar tsoron Yasir saboda yana yawo da makami.
To har aka yi ringing bell na tafiya na gida wanbda su kuma suka nufi ƙaramin ƙofan dan su yi faɗan. Tafiya nake ina wai waye hankalina a tashe ina zulumin a bun da zai faru.