Free chapter · Read without an account

PG 8

by Khadija · ANA BARIN HALAK

PG8

Tun daga gate in makarata aka tare ni da ce wa Ashraf yazo, kuma hakan ya yi min daɗi sosai amma kuma ban nu na musu ba.

Ina shiga aji kai tsaye in da ya ke na nufa ina murmushi. " Yayana sannun ka da zuwa."

" Yauwa Ƙanwata an tashi lafiya."

" Lafiya kalu Alhamdulillah ya jikin ka.?"

" Da sauƙi sosai amma ta ya ya ki ka sa ni cewa ba ni da lafiya."

" Uhmmm yan da na ga kana ta hucin she karan jiya nan na san ce wa sai ka kwanta ciwo."

" Uhmmm kuma kin cin ka daidai."

" Jiya Yayana baka zo ba ƴan ajin nan suka ta min rashin mutumci wai sun ɗaura muna aure harda sadaki fa."

Dariya ya yi sannan ya ce. " Kursum kina da abun dariya wallahi kin san aure kuwa?."

" Yayana wallahi da gaske nake da kudin da suka bani nan dubu uku." Na faɗa a sanda na ke fitowa da kudin daga cikin jaka na.

" Wai dan Allah da gaske ki ke ne wai?"

" Allah kuwa Yayana."

" Su wa suka ɗaura?"

" Wai Yazeed da su Usman. Kuma na rantse cin ye kudin zan yi tun da ai auren bai ɗauru ba ko.?"

Shiru ya yi yana kaɗan kansa sanan yace. " Ƙanwata ki je kiyi harkan ki da kudin nan ki manta da wanan shriman na su."

To yau haka ayi wuni a makaranta ƴan aji mun sai labarin auran da su Yazeed suka ɗaura wai tsakani na da Ashraf har da video ko nima na kalla kuma naci dariya sosai.

To haka rayuwa ta cigaba da tafiya kawanaki da watan ni na shuɗewa har mun zo matakin da a yu muke graduating daga Diligent College ranar me inbun tarihi wan da aka bar memorable memories marasa iya ka.

Har prom ku kayi ni da Ashraf wallahi ko ba'a faɗa ba ni na san cewa munyi kyau ba kaɗan ba.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol