Free chapter · Read without an account
PG 9
by Khadija · ANA BARIN HALAK
PG9
Wayan da ke gefe na ne ya ɗauki ruri a hankali na kai hannuna na ɗauka, duk da ban duba me kiran ba amma na san cewa Ashraf ne, kuma ko da na duba shi ne murmushi na saki sannan na ɗauki wayana na kara a kunne.
" Salamu alaykum."
" Wa'alykum salam Ƙanwata ya gida."
" Lafiya kalu wallahi alhamdulillah ya shriye-shriye kuma?"
" Lafiya kalu alhamduillah"
" To Allah ya nu na mana da rai da lafiya masha Allah buri ya cika ko?"
" Wallahi kuwa."
" To Allah ya sa albarka a karatun ki ya sa dan baya muma mu haddace."
Dariya nayi sannan nace." Wallahi Ashraf baka rabo da sokana ko?"
" Eh mana yauwa kin ce mun Ishaq ya miki magana ko?."
" Eh Yaya."
" To me ya ce miki?."
" Wai ya na so na."
" Hahaha to wani amsa ki ka bashi?."
" Nace sai nayi shawara. Amma kai ya ka gani."
" Bari idan ki ka dawo haiyacin ki zamuyi magana kin ji."
" To."
" Uhmmm Kursum dan Allah idan za kiyi addu'a ki roka min Allah ya karkato da hankalin ta kai na."
" Wacece?"
" Kursum na faɗa soyayya. Soyayya me matuƙar ƙarfi me hana sukuni da hana bawa baci, wallahi Kursum yau kwana uku bana iya baci."
Wani irin abu ne naji ya sauƙa min a zuciya amma kuma bai dame ni sosai ba sai da mukayi salama da shi abun ke damu na. Sauran wurin ranar nayi shi ne cikin damuwa duk da in da na shiga kowa sai ya jane da wasa amma wallahi ƙarfin hali kawai na ke.
Rana bata ƙarya sai de uwar ɗiya taji kunya. A yau take ranar da nake suƙan haddan Al-qurani mai grima, dangi maza da mata sun halarci taron farin cikin da nake ciki bata misaltuwa.
Bayan suƙan ne da sati uku Yayan baba na baba Jabiru ya zo gidan ranar wata alhamis da uwar safiya, nikam ko baci safi ma ban tashi ba.
" Rabi kuyi haƙuri na tashe ku ko? wallahi dole ne ya sa."
" Aa ba kome Yaya Jabiru amma lafiya na gan ka haka."
" Lafiya kalu in an juma kaɗan za'a yi baki ban son mu zo ace wani ya fita ina son dukan ku ku zamo kuna nan."
" To amma lafiya kuma su waye za su zo?"
" Kar ki damu ke dai ku shirya tarbar baki idan sun zo zaki ji me kai tafe da su."
" To shi ke nan Allah ya kawo su lafiya."
" Amin.” Ya amsa sannan ya juya ya fita.
Wallahi tun da naji zuwan sa gaba na ya yanke ya faɗi wan da sai da ya sakar min ciwon kai.
Ƙarfe uku daidai bakin suka iso ina ɗaki a san da suka shigo. Mama ce ta shigo ta kira ni fallo din da bakin su ke.
Mamaki ne ya cika ni a san da na ke ganin fiskokin wa in da suke zaune a ƙasa, ni ma samun wuri na yi a ƙasan kusa da yayata na zauna mamaki fal rai na.
" Kursum"
" Na'am Baba."
" Ɗaga kan ki ki kalle wa ɗin nan kin san su?.”
Ɗagowa na yi a hankali na kalle su sannan na kaɗa kai na alaman eh.
" Me sunayen su?"
" Asharf, Yazeed, Usman da kuma Lukman."
" Da kyau, Me alakan ki da su?."
“ Ƴan ajin mu ne."
" Masha Allah za ki iya tuna a bun da ya faru a makaranta ranar sha takwas da watan mayu ƙarfe goma na safe."
" Eh kawu."
" To bamu labarin."
A hankali na basu labarin komai cikin rawan murya dan hantar ciki ya gama kaɗawa.
Wani irin shiru ɗakin ya ɗauka ya yi da she shekan kukan da nake kai tashi cikin she she kan na ce.
" Baba dan Allah ku yi haƙuri."
" A a kursum baki yi lefen komai ba, illa iya ka a bun da zan faɗa miki shi ne auran da wa in nan ƴan ajin naku suka ɗaura sakanin ki da Ashraf ya ɗauru tun a locacin kin zamo matar sa..