Free chapter · Read without an account
PG 10
by Khadija · ANA BARIN HALAK
PG10
" Tsarki ya tabbata ga ubangijin talikai, wan da shi kaɗai ya san hikiman da ya sa ya kaddara haka."
" Haka ne kam amma to yanzu ya za'a yi."
" To a ganina tun da dukan su yara ne kawai a raba auren....."
" Uncle dan Allah kar ku min haka."
" Ashraf wannan wani kalan shrime ne...."
" Aa malam Ismail ka tsaya muji hanzarin sa, ya ka ke so a yi."
" A gaskiya Baba idan nace muku bana son Kursum nayi ƙarya, dama ina ta ne man daman da zan faɗa mata amma kuma ban samu ba."
" To kai zaka iya rukon aure ne??."
" Eh zan iya"
" To shi ke nan za....."
" Aa Jabiru kar ka fara dan ba zai yu ba."
" Kaman ya kenan??"
" Ka manta akwai alkawarin wani akan ta."
" To Rabi ya za'ayi da hukunci da Allah ya yanke."
" A raba auren kawai."
" Saboda??"
" Bazan iya zuba ido wani ya aure Kursum ba Salisu ba."
" Akan wani dalili?"
" Saboda tun tana simma aka yi musu alkawarin aure."
" Uhmmm wallahi Rabi baki da dalili da zaki ja da kudiran Allah, yaran nan ba ka alfasha aka ce suka yi ba aure suka yi kuma akwai shaidu da sadaki."
" A biya shi sadakin sa."
" Uhmmmm Rabi ke nan me ya sa ki ke so ki haramta a bun da Allah ya kurdirta ki ai kata a bun da Allah da ya halata kai matukar fishi da shi idan aka aikata. Da ƙarancen shekarun yarinyar nan ki ɗaura mata zawarci."
" Ka fahimce ni ba haka nake nufi ba amma ana barin halak dan kunya ko."
" Uhmmm malam Ismali kuje ku gyara in da zaku saka ta aure ya ɗauru kuma babu rabuwa ku girmar da kan su ai ni kin taimake ni da haka ki ka aika ta ba wai kin zubar da mutumcin ki ba."
Miƙewa su malam Ismali suka yi sannan ya ce. " To shi ke nan mu yanzu zamu tafi su sake shawara de."
" Aa babu wani shawara da zamuyi kar ka damu ai, yarinya a hanunna take kuma ni nace nayi amana to kar ka ji komai akan haka."
" Ango aje a fara shirin zuwan amarya ko."
" Uhmmm wallahi sai de a mafarkin sa."
" Na gode sosai baba." Ashraf ya faɗa sannan suka wuce.
Bayan tafiyan su Baba Jabiru ya kalli Kursum ya ce. " Ki je ki shriya mu tafi.”
Jiki a sanyaye na miƙe na shiga ciki na haɗa kayana dan wallahi Allah kaɗai ya san me zai faru idan na kwana a gidan.
Fitowa nayi na mata salama ya huce duk da ban ji amsawan ta ba wan da na tabbatar min da cewa ran ta ya baci