Free chapter · Read without an account

PG 11

by Khadija · ANA BARIN HALAK

PG 11

" Salamu Alaykum."

" Waalykum salam."

" Aunty."

" Na'am." Zama ta yi a gefan katifan da nake zaune sannan ta kale ni ta ce.

" Kursum baffan ki ya bani labarin komai amma ke kuma wa ki ke so a cikin su.??"

Shiru na yi kai na a ƙasa dan har ga Allah ina son a bar min aure na.

" Wallahi duk da baki firta ba shirun ki ya tabbatar min da ce wa mijinki ki ke so, amma shawara ke din ga tashin sallah dare kina addu'a haɗe da niman zabin Allah tsakanin su."

" To Aunty In sha Allah kuma ke ma dan Allah ki taya ni da addu'a."

" Kar ki damu In sha Allah zan taya ki.”

To duk yan da muki tunani abun ba haka ya ke ba, dan Inna ta tubure akan wai sai na rabu da Ashraf na aure min Salisu ɗan yayanta, kuma sauran baban ni na sun goya mata baya a cewan su wai bazan aure kaɗo ba.

Sanman a cikin wannan rigimar wani tashin hankali ya shigo wan da ko ni nan ya kiɗima ni sosai, Ashraf na gani a kan hanya ya na layi cikin maye, wallahi ranar da na ganshi ban iya yin bacci ba saboda tashin hankali.

Washe gari kiran duniya ya yi naki ɗagawa sakonin sa ba addadi duk naki kulawa saboda a lokacin naji duk ya sire min bana son ganin sa.

Rigima sosai ya balle tsakani mu da su Ashraf akan sakin, wan da sai da hakan yansa aka je kotu dan alkali ya raba auren nikam a yanzu bani da ta cewa sai dai ido.

Kotu ta saurare dukan bangarori guda biyu akan shari'an Ashraf da Kursum, wanda kotu ta baiwa Ashraf yazeed wa'adin sati daya da ya sake ta kuma kotu ta faɗa da kanta da haka aka buga tebur aka tashi.

Tashin hankali rudu da damuwa ne baro baro na gani akan kwayan idon sa a san da yazo min magana na kwace.

Saura kwana uku wa'adin da kotu ta bada, a wa inan kwanakin na manta da dandano abunci saboda ko yunwan ban na ji. Da dadare muna fallo nida Aunty Salama tana bani haƙuri akan halin da nake ciki, kawu ya shigo fuskar sa ba annuri.

Na gaishe da shi sannan na miƙe da niyar barin fallon sai ya ce. " Kursum ga sako daga Ashraf yace ki karanta sannan ki sa shi a addu'a wallahi ya gamu da wani mumuna hatsari yanzu haka yana asibiti emergency."

Dam naji gaba na ya faɗi, ya yin da jiki na ya ɗauki rawa a sanda na amsa envelope da ya ce min wai an kawo min saƙo a cikin.

Da na shiga ɗaki na buɗe envelope in wani litafi ne ya faɗo sanman sai wani wasiƙa. Buɗe wasikan nayi wan da ya kunshi takaitatcan saƙo a ciki.

" Aslm da fata kina cikin koshin lafiya na san kina jin haushi na akan abun da ya faru kuma ina me baki hakuri akan haka alfarama nake so ki mulin shi ne ki yanke mun hunci da zuciyar ki." Cen daga ƙasan number paper naga an rubuta " Ki duba litafin nan." ɗauka na yi sannan na buɗe na fara karantawa....

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.