Free chapter · Read without an account

PG 13

by Khadija · ANA BARIN HALAK

PG 13

Aunty Salma ce ta ja na'nawyan ajiyan zuciya sannan ta ce"

Shin kuna san dalilin da ƙasashe kaman Saudia, American da kuma sauran ƙasashen fararan fata suka cigaba??

Ba ma wannan ba.

Shin kun san dalilin da duk da arzikin da Allah ya bamu na ƙasa amma har yanzu muke shan wahala kuma mu ke fama da talauci??.

Shin kun san dalilin da yan ta'adda suka yalwata a cikin alumma??

Uhmmmm! na san amsan guda ɗaya ne.

Saboda talauci da wunya da ake ciki ko ,ko kuma in ce saboda rashin abunyi na samari da rashin godiva Allah da son zuciya ƙoƙarin dad'a wa yan da gwanmati suka kasa cika alkawarin su ko a sanda suka neman kurukun ku ko musamama na samarwa matasa sana'a ko.

Gaskiya ne babu karya a dukan hujojin da ku ka riƙewa a masayin makami to ina so na dan baku wani labari kuma dan Allah ku yan ke hukunci da hankali da tunanin ku.

Waye- waye

Shingiɗe ya ke akan tabarma ya na suraran radio da ke gefan sa ya yin da kuma iskan yammaci yake kaɗa sa a hanakali.

"Salamu alaykum!."

" Wa'alaykum salam Hajja ke ce tafe??"

"Eh baba ni ce."

"To, to amma dai lafiya ko.??"

"Eh baba lafiya amma ba lau ba."

"Uhmmmm! mata ke nan wato a rayuwa ba'a taba burje ku duk a bun da mutum ya yi bai iya ba.

To me ya faru??"

"Dama baba na zo ne dan Allah ka roki Lawal kar ya kai Yazeedu almajranci."

Tashi ya yi zaune ya na kallon ta sannan ya ja tsaki ya ce"

"Hajja! Hajja!! Hajja!!! wallahi ki ka kara magana akan karatun yaron nan zan iya tsine miki."

"Baba."!...

" Yi min shiru ai daman jiran na ke dama ina da labari akan dukan tabaran da ki ke akan karatun yaron nan kawai zuba miki ido na yi saboda na sannan za'a zo wurin,

Yazu Hajja so ki ke a ce ɗanki bai iya karatun addini shi ba.?"

"Baba ba wai haka bani ka ga Yazeedu yaro ne ɗan shekara shida kuma ga sanyi ya kuno kai karin daɗawa ba shi da lafiya to shi ne naki so ya bar shi ya kara wayo ko baɗi ne sai ya je."

"To ba zai yu ba, na ce ba zai yu ba kai wallahi Hajja idan ki ka kashe auren ki sanadiyar wanan maganan Allah ya isa ban ya fe ba."

" Baba dan Allah!ka saurare ni."

Miƙewa ya yi ya suri takalmansa sannan ya fi ce daga gidan.

"Mama dan Allah! ki yi mishi magana."

"A'a Hajja wallahi ba zan iya ba. Kawai ki tashi ki koma gidanki Allah ya yi miki Albarka ni ma zan taya ki da addu'a,ki yi haƙuri ni ma zaman haƙuri nake.

Share hawayen ta ta yi sannan ta miƙe ta koma gida jiki duk ba kwari. Yazeedu ta samu a kwace jikin sa duk ya yi zafi wan da hakan ya kara tayar mata da hankali dama tun shekaran jiya bai da lafiya ta faɗawa Mallam Lawal amma ya karyatata.

Maganin ta siyo mishi ta bashi sannan ta kara luluba mishi da bargo a kan sa jan yo shi jikin ta ta yi ya yi ga hawaye na zuba mata cikin bakin ci kaskastacen rayuwan da taki ciki na rashin galihu.

Kiran sallan magriba ne ya sa ta tashi ta fita ta ɗauro alwala dan ta yi sallah habaice kam babu kalan wan da bata sha ba amma ta danne zuciyar ta amma ranar ta kawana kuka tana hada masa kayan sa."

"Mama yanzu wai zan a kai ni ne???"

"Ka yi haƙuri babana wallahi bani da yan da zan yi ne an fi ƙarfi na ne amma ka san me ne?"

"A'a Mama."

"Ka yi min alkwari duk wuya duk rintsi bazaka yi sata , cin amana da kuma yaudara.

Ka zamo me riƙe alkawari, me gaskiya da riƙon amana ka ji ko baba.?"

"In sha Allah Mama na yi miki alkawari.

"

"Yauwa babana Allah! ya yi maka albarka."

"Amin Mama na gode.

Shafa kan sa ta yi ya yin da hawaye ke zuba da ga idanunta zuciyarta na suya.

Yan da ta ga rana haka ta ga dare cike da tunani kalan rayuwan da halin da ɗan ta duga ɗaya zai shiga a garin da bai san kowa ba huna nesan garurukan ta ke daga Hadeja wai zuwa Kaduna."

"Ya rahman, ya raheem ya zuljalalu wa ikram kai ne me kase da mam'maye ka kare min shi a ɗuk in da ya ke ka tsare hanunsa daga aikata ba daidai ba. Amin."

Washe gari asuban fari ta tashe yazeedu tayi mishi wanka ta shriya sa

"Babana ka yi ƙoƙari ka yi karatu fa kafi kowa iya wa ka ji.?"

"To Mama in sha Allah! zan yi."

"Hajja! Hajja!!wai ina ku ke ne?."

"Gamu nan Malam."

Ta faɗa a san da suke fitowa daga daƙin

"To Yazeedu Allah ya baka sa'a ya kare ka daga dukan shari na mutum da aljan."

"Uhmmmm! a hai ye duniya sabowa Lami ki na ji ko.?"

Dariya suka fashe da shi san an suka tafa.

Jan hanun Yazeedu Malam Lawal ya yi suka fita daga gidan yana mitan bata mishi lokaci da tayi.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol