Free chapter · Read without an account
PG 14
by Khadija · ANA BARIN HALAK
PG 14
Garin kaduna , gari me ibun tarihi da mutane da suka zo daga ƙasa daban-daban a faɗin Nigeria.
Gari ne wan da ya ke kunshe da yare da ƙabilu dabandaban wan da kuma ya ke da arzikin illimi.
Ɗiran yammaci su yazeedu suka yi wa garin kaduna hada hada ake sosai a garin."
"Kai lado ka jagoranci su mana."
"To mallam." Shiga gaba ya yi ya yin da kuma sauran suka mara masa baya.
Tafiya ne ba ɗan ƙadan ba sai bayan isha suka isa idan za su je saboda a hanya suka yi magariba.
Wuri ne me cike da ƙazanta, dauɗa da datti dan har wani irin wari wurin ya ki tashi a wurin.
Ɗaki biyu ne in da almajiran su ke maƴan da ƙananan su.
Saboda yalwa su a waje su Yazeedu suka ƙawana washe gari kuma bayan sun yi karatu suka baza ma cikin gari dan neman abunci sannan idan suka samo manƴan ne suke ciyewa.
Sai sun yi aikato sannan su ke samu na abunci ko kuma dako wanbda ba kullin suke samu ba.
Yazeedu ya zage damse wurin karatu ya yin da kuma ya shiga kasuwa ya fara nema kuma Allah ya sa mishi albarƙa a ciki sosai ya ke samu.
Makartan boko ya shiga saboda hakan na matuƙar ba shi sháawa don haka ya shiga yaƙi da jahilci kuma alhamdulillah karatun ya amshe shi dan haka bai tsaya a iya haka ba sai ya cigaba har ya samu ya shiga jami'a.
Lokaci bayan lokaci Yazeed na zuwa hadeja ya na ƙewa mahifiyar sa ziyara sannan ya yi mata alheri.
A jami'a Ado Bayero Yazeed ke karatu saboda ya yi sauka tun yana secondary school dan haka ya tafi zaria karatu.
Ba ƙaramin tashe Yazeed ya yi a makarantan ba saboda kayu, illimi da kuma kudi saboda a lokacin kasuwa ta zauna sosai dan har plaza gare shi dadin daɗawa ba ya kula ƴan mata.
Masura mace ɗaya da ta birkita wa samarin ABU lisafe a ciki kuwa harda Yazeed. Sai de bai tare ta ba saboda gudun wulaƙanci.
Amma kuma sai ita ta fara mishi magana saboda a department in su taki wato articticture sai ɗai ita tana bayan su dan haka ta ke nemi taimakon sa akan abun da ya shafe makaranta.
Ɓoyayyen soyayya ne wan da babu wan da ya sa ni sai satin ɗaurin aure suka sanar.
Mutane da yalwa abun ya basu mamaki, ƴan farin ciki sun yi murna ya yin da ƴan bakin ciki kuma abun ya basu haushi.
A 9tal suka zauna sannan ta cigaba da karatun ta.
Rayuwa me cike da farin ciki suka shinfiɗa haɗe da daraja juna sannan shekaran su biyu da aure Allah ya basu haihuwa aka samu namiji wan da raɗa mishi Ashraf.
Alhaji Dallhatu babban abokin Yazeed wan da tare suka shi go almajiranci shi ma ya ɗan tabba karatun amma bai yi zurfi ba kamar Yazeed ba."
"Yazeed ya aka yi ne wae naga yau sai wani murna ka ke."
"Uhmmm abokina bari yau ina cikin farin ciki."
"Da me ya faru."
"Inna wa in nan kwantena in da na yi ordering in su kwanaki??"
"Eh wa in nan da suka zo daga Germany??"
"yauwa su ,to kasuwa ta yi kayu."
"Haba dan Allah nawa ka samu."
"Tsakanin milliyan talati da biyar zuwa arbani haka."
"Tofa yanzu me za ka yi da su??"
"To a cikin ɗaya daga cikin a bun da zan yi da su shi ne kai ga wannan."
Jakar kudi Yazeed ya ɗaura akan tebur in a gaban Dallhatu."
"Me haka yazeed?."
"Dallhatu ba na son haka naka ne wannan na samu riba sosai fa dan haka dan na ba ka wannan ai ban faɗi ba."
"To shi ke nan abokina na gode sosai Allah ya bar mu tare."
"Amin ya Allah." Miƙewa Yazeed ya yi da niyyar tafiya."
"Kar ka ce tafiya za ka yi."
"Wallahi kuwa."
"To ai ba zaka bar ni a nan ba muje ma na baka birthday gift in Ashraf."
"Ai kuwa kam ka kusa kaga ɗiran mikiya a gidan ka."
"To muje in baka.