Free chapter · Read without an account

PG 18

by Khadija · ANA BARIN HALAK

PG 18

Zaune Ashraf ya ke cikin saƙe-saƙen a bun da zai yi

ya san dai yan da akwati uku wan da kuma ba laife ya sa kaya iyakacin ƙarfin sa saboda tun sanda ya ji su usman sun ɗaura musu aure a makaranta ya fara tanadi dan zuwan ranar hakan.

Salaman su kawunsa ne tare da na Baba Jabir shi ya dawo da shi daga duniyar tunanin da ya tafi.

Guri suka samu suka zauna sanan Ashraf ya gaisar da su suka amsa sannan kawu ya ce"

Dama Ashraf dalilin zuwan mu shi ne Jabir ne ya zo ya same ni kan cewa yana son sati me zuwa a yi biki kuma munyi magana da shi na fahimta kan cewa hidimar biki kawe za a yi bai buƙatan komai a wurin mu dan hata gurin zama ma a wani gidan sa zaku zauna."

"Baba jabir ina godiya da dukan karamcin ka a gare ni amma ni ina da inda zamu zauna kuma na hada lafe na."

"Ta ya ya kuma a inna ka samu kudi da har ka siya gida?"

"Kawu kai ka sa ni ba sana'ar saida giya ba ne ƙade na ke yi ba harda saiyar da wayoyi sannan ina tsaron wani shagon kayan hasi duk karshan wata ana biya na kudi da daddare ne na ke zuwa nightclub in to kuma ka tuna gidan da na siya a gangare ai da kudin sauran sano'ina na siya ba na giya ba shi na giyan asibiti na ke kai innata da shi."

Shiru sukayi da dan mitina sannan Baba Jabir ya ce ba"

"To ba lefi zan iya ganin akwatin??"

"Eh bari in ɗauko ma."

Tashi ya yi sannan ya fito da su ɗaya bayan ɗaya duk da ba wani kaya me kudi sosai bani amma ya yi iya ƙarfin sa kuma ya sa duk a bun da ake buƙata baba Jabir ne ya ce"

"Mash Allah kaya ya yi kayu sai dai Allah ya sanya alheri idan mun yanke lokaci zamu sanar da ku ranar da za'a kawo kayan."

"To madallah mun na godiya."

"Ba komai yi wa kai ne."

Miƙewa dukan su sakayi a tare suka yi wa Ashraf salama sannan suka fita dan kawu ya raka Baba Jabir.

Sai bayan sallahan isha ya shiga gida.

Aunty salma ce kaɗe a fallo tana shayar da ma'arof."

"Sanu da dawowa."

"Yauwa sanun ki ya gidan??"

"Lafiya kalu."

"Masha Allah."

"Salma."

Na'am Abban Ma'arof."

"Me ne nai tunanin ki akan hukuncin da na yanke akan Kursum.

Amma kafin nan me ya sa ki ka boye min gaskiyan tun tashin farko baki fada min ba.?"

"Baba ne ya hana ni a cewan sa idan har Allah ya kaddarda ita matar sa ne ko me zai faru sai sun zauna dan haka nayi shriu ne na zuba wa sarautan Allah ido."

"Haka ne kama yan/da gaskiya."

"Amma Abban Ma'arof me ya sa ka yanke hukunci ba tare da kayi shawara ba?"

"Da su waye kai nan?

Jabir ya tambaya."

"Da su Yaya Ayuba."

"Mtswwww ragamar rayuwan Kursum a hanunna yake" ya faɗa sannan ya tashi ya bar fallon.

Yau dai babu hira sam a gidan saboda kowa zuciyarsa ya yi nauyi cike fal da tunani sannan yan da suka rana haka suka ga dare a wurin Ashraf ma haka yake ko ƙadan bai rinsa ba.

Washe gari ƙarfe shida barrister Kamal ya kira Jabir."

"Hello engineer sorry na tashe ka ko?"

"Aa ba komai barrister dama ai tun-tuni na tashi."

"Ok to dama akan maganar mu ne"

"Ok ina jin ka."

"Alkali ya maidar da zaman mu na sirri sannan ya ce ra'ayin yarinyar zai bi duk wan da ta zaba a cikin su shi za a bata."

"Masha Allah barrister nagode sosai da ƙoƙarin ka i really appreciate it thank you so much."

"Ba komai yi wa kai ne jibi insha Allah za'a zauna so sai ku shriya."

"Ba komai godiya na ke.

Salama sukayi suka kashe wayan.

Wanka ya shiga sannan ya shriya ya fito fallon.

Aunty Salma ce kai ta ƙoƙarin shriya dinning tebur."

"Goodmorning love".

"Morning. An tashi lafiya?".

"Lafiya kalu and You?".

"Same. Ina Ma'arof?".

"Yana wurin kursum."

"Ok to ga check in kudi a ɗaki ku je kasuwa yau kuyi siyaya kayan kitchen idan ma bai isa ba ki kira ne."

"To ƴallabe godiya muke ."

"Ba komai sannan ki je shago ki dauki muku atamfa guda shida ke da ita ki kai muku wurin ɗinki.

Fari Salma ta yi da ido sannan tace".

"Godiya muke Allah ya kara arziki da nisan kwana."

"Amin ya Allah thanks ni zan fita."

"Wallahi baka isa ba ka fita ba ka ci komai ba tab ba da ni ba.

Dariya ya yi sannan ya ce"

"Am sorry my queen zuba min na ci yau me aka yi mana ne?"

"Meatpie ne da madara."

"Wow fantastic ai dole ma na ci.

Hudu ta sa miki meatpie in sannan ta cika mishi kofi da madara wan da sai da ta tabbatar ya cika cikin sa sannan ta bar sa ya fita.

Yana fita aunty Salma ta haura sama ɗakin Kursum.

Goye take da Ma'arof a bayan ta ya yin da ita kuma ta kifa.

Tana shiga ɗakin tace mata."

"Kursum tashi ki zauna."

Zama Kursum tayi tana fiskantan aunty Salma.

Labarin yan da sukayi da Babanta kab ta bata sannan da ɗaura da cewa

"Ke kin san me ne yanzu wanka zamuyi mu shirya mu shiga kasuwa."

To aunty Kursum ta amsa sannan ta mika mata Ma'arof ta shiga wanka.

Siyayya sosai sukayi na kayan kitchen sannan kuma suka ba da ɗinkin su.

Want the next chapter?

ui.create_a_free_arewapen_account_to_save_progress_unlock_paid_chapters_fol