Free chapter · Read without an account
PG 21
by Khadija · ANA BARIN HALAK
PG 21
Zaune suke a fallo suna karya kumallo Kursum ce ta kalli Ashraf ta ce".
"Yayana wai yau she Umma zata dawo gidan nan ne wai?"
"Uhmmmm wallahi kaman kin shiga zuciyata ko ni nan ban ji daɗi idan na tuna bata kusa da ni.
Amma bari in sha Allah kwanan nan."
"To shi ke nan amma dai dan Allah ka sa kan ka ka yi wa kawu magana ka ji wallahi idan ka fita ni kaɗe kaman mayya wallahi."
"Kar ki damu insha Allah zan ƙoƙarta.
"Dama ina so na fada miki shago fa ya kammala."
"Masha Allah a in na ne?"
"A kasuwan kawo wallahi."
"To me aka zuba a ciki?"
"Kayan hasi da mai sai kuma su majji."
"To masha Allah Allah ya sanya alheri ya kawo kasuwa mai albarka."
"Amin ya Allah."
"To yaushe za ka fara fita?"
"Yau insha Allah."
"To kar a manta dai ayi addu'an ne man sa'a."
"Insha Allah."
Miƙewa Ashraf ya yi sannan yace".
"To ni zan fita."
"A dawo lafiya."
"Allah ya sa."
"Ameen ya Allah."
"Me ki ke so na kawo miki?."
"Ko me ma."
"To shi ke nan."
Da ya isa shago kafin ya duɗe sai da ya tsaya ya karanta"
Lahuwla wala uwata illabilla.
Lahuwla wala uwata illabilla.
Lahuwla wala uwata illabilla.
Lailahaillah wahadu la sharikala lukullmunku wallahu hamdu yuhiyi wa yu mid wa huwa khairi la yamud bi ya dihiri khairi wahuwa ala kulli shairi kadir."
A hankali ya buɗe shagon ya shiga ya zauna.
Alhamdulillah ya yi ciniki a masayin sa na sabon shiga kasuwa kuma customers in sa na ɗayan shagon sun biyo sa sabon wurin na sa.
A gajiye ya koma gida dan sai wurin ƙarfe tara na dare ya isa gida."
"Sanu da dawowa."
"Yauwa sanu ya gida?"
"Lafiya kalu Alhamdulillah."
"To masha Allah ga wannan."
Bakin leda ya mika mata.
Amsa ta yi tana dubawa.
Kilishi ne a ciki.
Godiya tayi masa sannan ta miƙe ta hada masa ruwan wanka saboda yan da ta gansa ta tabbatar ya yi matukar gajiya."
"Ga ruwan wanka."
"To nagode". Tashi ya yi ya shiga wankan ,da ya fito ya shriya ya fito fallo mamaki ne ya hana sa magana.
Abunci take bata a baki suna wa sa.
Wai-wayowa tayi ta kalle sa sanan tace"
"Gibaɗo zo mana."
A hankali ya tako in da su ke ya zauna kusa da Ammyn sa."
"Wallahi Gibaɗo ta iya griki sosai kuma da daɗi."
Kallon Kursum Ashraf ya yi yana murmushi.
Abuncin ammyn sa ta kawo bakin sa.
Shi kuma ya buɗe bakin sa ya amsa abuncin tabbas kam abuncin ya yi daɗi.
Da wayo Kursum ta bar fallon dan ta bar su suyi hira."
"Kursum, Kursum ina Kursum take."
"Na'am ga ni nan."
Fitowa fallon ta yi ta same su a in/da ta bar su.
Zama tayi kusa da ita a gefan daman ta ya yin da shi kuma yake gefen hagun ta .
Ledan naman ya buɗe a ɗaura akan plate ya sa musu a tsakiya suna ci.
Tun tana shiru har ta biye su aka fara hiran da ita."
"Amma Kursum wa ya kawo Ammy gidan nan??"
"Dazu ne da naje gidan kawu dan zaman haka ya ishe ni shi ne ta biyo ni".
"Ok to ya yi".
"Ai Gibaɗo mun yi wa kawun ka wayo muka gudu.
Dariya ya yi sannan ya ce"
"Gaskiya kam kun mai wayo."