Free chapter · Read without an account
PG 22
by Khadija · ANA BARIN HALAK
PG 22
Rayuwa me cike da farin ciki ke gudana a gidan Ashraf da Kursum ya yin da kuma kasuwa sai son barka har makaranta ya sa ta.
Yusuf dan tsoho take zuwa in dan take karatun nursing sannan masha Allah tana kula da Ammy yan da ya kamata.
A kasuwa Ashraf na shago tare da Yazeed saboda shi ne ke zama idan Ashraf baya nan.
Nabila ce ta yi musu salama."
"A a mayan gari dama talaka na ganin ku??"
"Wallahi Yazeed bani da lokacin ka."
"To naji me za a ba ki?"
"Ba abu da nazo siya ba."
"To me ya kawo ki?"
"Ina ruwan ka?"
"Da ruwa na wallahi me ki ke so?."
"Kai ba wurin ka na zo ba wurin Ashraf na zo."
"Ni kuma?"
"Eh kai, ina so muyi magana ne."
"Tofa Allah ya sa lafiya."
"Uhmmm lafiya kalu kawai dai akwai magana me mahimmaci da nake so mu yi ne."
"Akan me ke nan?"
Akan rayuwanta ce."
"Nabila......."
"Kaga, ka san cewa tun muna makaranta muna sharing problems in mu wa juna mu dan haka ai ba wa ni abu bane idan har na zo gareka da matasala na ba ko."
"Haka ne kam to shi ke nan ina jin ki."
"Da kai kaɗe na ke so na yi magana."
"Ban da ni ke nan?.
Yazeed ya tambaya."
"Eh ban da kai."
"To yanzu Nabila a ina ki ke so muyi magana dan Allah ki duba fa kasuwa ne me cike da jama'a ta ko ina fa."
"Ka zo muje in da babu hananiya."
"To ina?"
"Ko ina ma."
"Kalla Nabila......
Raɗa Yazeed ya yi mishi a kunne.
Kallon ta ya yi sannan ya ce mata "muje".
Napep suka tara suka shiga sai smart kid.
A sama suka zauna bayan sunyi ordering in ice cream.
To Nabila ina jin ki.
Shiru tayi ta cigaba da shan ice cream in ta."
"Nabila me haka ne wai?
Ke ki ka ce mu zo nan kuma kin yi shiru."
"Uhmmm wai Ashraf me ka kai ci na baka na zuba ne?."
"Matata zan je ɗauka a makaranta ban so ta jira ni.
Dagowa ta yi ta zuba ma sa idanun har ya gama maganar da ya ke cikin ɗaurewan fuska sannan tace."
"Dan miƙe ma na."
Tashi ya yi ya na kallon ta fiskan sa a ɗaure.
Miƙewa tayi ta tako in da ya ke sannan ta jawo rigan sa kusa da bakin ta.
Da sauri ya ture ta sannan ya ce cikin tsawa."
Nabila wannan wani irin kallan rashin hankali ne?"
"To ya zan yi Ashraf. Ya zan yi ka gane irin kallan son da na ke maka.
Ashraf da ni ka dace ba da Kursum ba."
"Nabila anya kina cikin hayacin ki kowa."
"Uhmmmm tabbas ka ce haka amma wallahi Ashraf ina son ka."
"To bari ki ji ni ba kallan
wannan mutanan bane kuma wallahi bazan iya haɗa Kursum da wata mace midin muna duniya.
Yana gama faɗin haka ya tafi ya bar ta a wurin cikin bacin rai.
Napep ya tsayar sannan ya kai shi kasuwa."
"A a Ashraf har ka dawo.
Bai amsa ba wuri ya samu ya zauna ya na huci.
Zama Yazeed ya yi kusa da shi yana kallon sa."
"Ashraf me ya faru ne."
Iska me zafi ya fitar sannan ya ba wa Yazeed dukan labarin a bun da ya faru."
"Tab in jam ana wata ga wata."
"Kaman ya ana wata ga wata."
"Na'am ba komai."
"Kai Yazeed ban son sha-shanci faɗi abun da ke ranka malam."
"Kar ka damu ka je ka ɗauki matan ka, ka kai ta gida dai idan ka dawo zan faɗa ma koma me ne kaga lokaci ya yi."
"Uhmmmm ka yi alkawari."
"Na yi."
"To shi ke nan". Tashi ya yi ya ɗauki mashin in sa ya tafi ɗauko ta zuciyarsa cike da tunani.