Free chapter · Read without an account

PG 23

by Khadija · ANA BARIN HALAK

PG 23

Parking ya yi a wurin parking bayan ya iso kasuwan.

Yazeed na ta ƙoƙarin salaman customers in da su kayi ma sa yalwa.

Shiga cikin shagon ya yi ya ta ya sa salaman su bayan sun gama Ashraf ya kalli Yazeed ya ce".

"Yazeed ka san kayun alkawari cikawa ko dan Allah ka faɗa min."

"Uhmmmm dazu, dazu dazu ne......"

"Dazu me ya faru Yazeed dan Allah stop beating around the bush ka yi magana kawai."

"Dazu ne bayan tafiyan ku Yasir ya zo."

"Me ya kawo shi??"

"Wai ya na so ka sake Kursum zai baka miliyan goma.

A has-sale Ashraf ya ce".

"Wato duk gargaɗin da nawa Yasir akan ya fita daga harka na yaki ko."

"Dama ya taba yi ma wannan maganar ne??"

"Uhmmmm ai ya taba dan tun lokacin da muke rigima a kotu."

"Kasan me ne?"

"A a sai ka faɗa."

"Dole sai ka tashi tsaye akan wa in nan mutanan biyun da suke tunkaro ku dan a iya zama na da su na san cewa idan suna son abu babu abun da ba za su iya aikatawa ba."

"Haka ne kam ko ni nan na karanci haka a tare da su a iya zama na da su na ƙanƙanin locaci."

"To sai kuyi a hankali da su."

"Uhmmmm shi ke nan ni zan huce gida sai da safe."

"To ba komai Allah ya kai mu."

"Amin ya amsa sannan ya tafi gida.

Da ya koma gida bai boye wa Kursum komai ba."

"Dama na san za a rina wai an saci zanin mahuciya."

"Kaman ya ke nan?"

"Ai na daɗe da fahimtan kallan son da Nabila ke ma ka kawai ni ce ban me da hankali ba."

"Ta ya ya ke nan?"

"Tun ranar birthday in ka yan da ta rungume ka a cikin aji da kuma yan da take shi-shige maka."

"Haka ne kam."

"Kuma ni ma ban faɗa ma ba Yasir she ka ran jiya ya zo wuri na da maganar a makaranta."

"Har abun ya fara kai wa haka?"

"Wallahi kam."

"Dole mu taka musu birki."

"Gaskiya kam dole ayi hakan."

Da wanan suka kwanta zuciyarsu fal cike da saƙe-saƙen mafita.

Washe gari a fallo bayan sun gama karya kumallo zaune suke suna hira suka ji ƙaran duga gate kallon ta Ashraf ya yi sannan yace".

"Tofa wa muka samu kuma haka?"

"Ka tambaye ni tare muke fa."

"Haka ne kam."

Tashi ya yi dan ya buɗe gate in.

Bai yi mamaki ganin wan da ke tsaye a bakin ƙofan ba illama ɗaure fuska da ya yi."

"Haba malam Ashraf haka ake tarban bako??.

"Gefe ya kuma dan ya basa hanya ya shiga gidan."

"Wow masha Allah premisses me kayu gaskiya gidan ka Ashraf ya saru."

Kujeran ruba guda biyu ya dako musu sannan ya ajiye musu a kar-kashin babban bishiyan gidan."

"Bismillah zauna sai muyi magana."

"To hakan ma ya yi zama Yasir ya yi ya ɗaura kafa ɗaya kan ɗaya.

Shiga ciki Ashraf ya yi ya dako mishi ruwa.

Zuba masa ya yi a ƙofi ya mika masa sannan ya zauna ya na kallon sa.

Sai da ya sha rabin ƙofin sannan ya ajiye ya kalli Ashraf ya ce."

"Na san cewa sako na ya iso gare ka kuma na tabbatar ya iso yan da ya kamata ko."

"Eh tabbas ya iso kuma yanbda ya kamata kaman yan da kayi zato."

"To nazo ne na ji hukuncin ka."

"Dariya Ashraf ya yi sannan yace."

"Anya mutumi na ka sha na safe kuwa?."

Dariya shi ma Yasir ya yi sanan ya ce"

"Kash wallahi na manta ɗuk tunanin Kursum ya hana ni wallahi."

"Wani abu ne me zafi ya soke zuciyar Ashraf amma ya shanye ya ce".

"Gaskiya kam naga alama amma gaskiya iska na wahalar da me kayan kara ko in ce dole ƙwaƙwalawa ta manta abun da ya kamata tun da zuciya ya kamu da son maso wani ko in ce matan wani.

Kuma amsa na shi ne bazai yu ba."

"Uhmmmm Ashraf kar ka bar wannan daman ta huce ka ba wai zaka sake ta bane a banza na tanade maka naira milliyan goma a masayin return."

"Ko milliyan budu dari za ka bani ba zan taba sakin matata ba dan haka ka je ka nemi wata."

"Malam Ashraf ka sake tunani dai."

"Babu wani tunani da zan yi dan ko shekara dubu ne za a yi amsa ta shi ne a a."

"To shi ke nan tun da haka ka ce."

"Eh haka nace.

Tashi Yasir ya yi ya fita daga gidan ko salama bai ma Ashraf ba.

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.