Free chapter · Read without an account
PG 25
by Khadija · ANA BARIN HALAK
PG 25
Ƙawanaki hudu da suka shafe a rayuwan Ashraf na wannan shafin ya yi shi ne cikin bakin ciki da tashin hankali tare da damu.
Ya rame ya yi baki saboda damuwan da yake ciki duk wan da ya gan sa sai ya tausaya me saboda yan da ya koma su Baba Jabir ne ke ta lar-lashin sa akan ya rage damuwa a ransa.
Wata safiyar asabar dukan su sun hadu a gidan Ashraf ana kara magana akan matsalan wayan Ashraf ne ya dauki ruri da sauri ya dauka."
"Hello da fatan ina magana da malam Ashraf."
"Eh da shi ka ke magana ."
"To masha Allah an since wata mata a nan maraban jos so sai ka zo ka duba ko ka san ta."
"To, to ga mu nan zuwa".
Tashi Ashraf ya yi ko ganin gaban sa da kayu ba iya yi.
Riƙo sa Baba Jabir ya yi saboda ya san cewa baya iya ganin gaban sa.
A motan Jabir suka tafi maraban jos in.
An taru sosai a wurin daƙer suka samu suka ƙusa ciki dan-dazon mutanan da suke wurin.
A lulube take da wani zanin da ko kafan ta bai karasa rufewa ba.
Jikin Ashraf babu in da baya rawa daƙer ya durƙusa ya bude fuskan ta.
Wani irin zabura ya yi cikin tashin hankali daga nan kuma bai kara sanin inda yake ba.
A hankali ya fara bude idanunsa wani irin sara da ciwon kansa ke yi masa a hankali ya tuna a bun da ya faru bai san sanda wa su zafafan hawaye suka zubo masa tabbas mahifiyarsa ne ƙwance a wannan wurin anyi mata kisan hulakanci."
"Kayi haƙuri Ashraf haka rayuwa ta ke kayi haƙuri ka amshi kaddaran ka yan da yake."
"Haba Kawu wannan wani kallan kaddara ne."
"A a Ashraf kayi shiru kar kayi sako."
Shiru Ashraf ya yi ya yin da wa su siraran hawaye ke zuba daga fuskansa.
Wayan baba Jabir ne ya dauki ruri kowa sai da hantar cikin sa ya kada.
Jikinsa na rawa ya daga wayan shiru ya yi ya yin da gumi ke zuba daga ko ina a jikin sa a hankali ya sauke wayan ya tashi ya fita daga ɗakin ba tare da ya cewa kowa kome ba.
Ashraf ne ya fizge drip in da aka sa mishi suka bi bayan baba Jabir shi da kawun sa.
Kawu Jabir bai yi zato ba suka shiga cikin motan."
"A a Ashraf me haka baka da lafiya ba."
"Baba dan Allah muje.
Kuna motan ya yi suka nufi asibitin da aka Kwantanta masa.
Parking ya yi a haraban asibitin suka fito sannan suka nufi emergency in asibitin.
Wani ɗaki aka shigar da su dan su duba.
Dukan su sankarewa su kayi a wurin an kasa samun wan da zai je ya duba dan kowa tsoro ya cika sa.
Ashraf ne ya yi ƙafin hali ya yi addu'a sannan ya yi shahada ya bude jakan da aka sa gawan.
Tsayawa ya yi ya ƙafe fiskan gawan da idanun."
"Ashraf ba itace ba ko??
Kawunsa ya tambaya.
Bai amsa ba illa ma dariya da ya fashe da shi."
"Kawu da ranta barci take, wallahi barci take kaga ma har wannan murmushin take idan na dame ta tana barci.
Jin haka baba Jabir ya fara salati ya yin da jiri ke diban sa.
Anyi janaizan Kursum tare da Ammy bayan aibiti sun gama binciken su.
Ashraf kam bin kowa ya ke da ido ya ki magana ya ki cin abunci daga karshe ma aka neme shi aka rasa.