Free chapter · Read without an account

1

by Khadeejarth Sabi'u Yahyah · SO DAN RAYUWA!

***

❉্᭄͜͡𝘚O 𝘿𝔸𝑵☆  R̲A̳Yᑌᗯᗩ ♥️
         ☆♥︎L⋆o⋆v⋆e⋆ ᖴOᖇ 𐐛օv𝖊♥︎☆

𝗕Ⲩ 𝔸mmⅈ𝖊ყ ℓαуℓєян & ɴᴀɪɴᴀʀ kd♡

༆Ⴆᴬˢᴱᴰ σɳ ƈɾҽαƚιʋҽ ʂƚσɾყ!!!༻

Bɪꜱᴍɪʟʟᴀʜɪʀ Rᴀʜᴍᴀɴɪʀ Rᴀʜɪᴍ

Ɗan ɗano
  Daga Alƙaluma biyu na fasihai kuma Haziƙan ƴan baiwar marubutan nan naku wato NAINERH KD da kuma AMMEY LAYLERH TAKU✍️, Nasan dai hope MASOYANMU ba zaku bamu kunya ba don kunsan tunda tafiyar ta kasance ta gwanaye dole abin ya bada  Fire 🔥🔥🔥🔥🔥🔥 kawai.
 
_Karku Manta Khadijah Sabi'u Yahaya wato NAINERH KD'Nku itane ta gwangwajeku da ƙayatattu fitattun littatafanta irinsu SARAUNIYAR KYAU, CAPTAIN AYUSHER nadai San ba Rubutu ne da masoya mabiyanta ba zasu taɓa iya mancewa dasu ba a duniyarsu!!!_

Kamar yadda ya ita ma Ƴar Baiwar nan taku Maryam Naseer Mirrah, Wato AMMEY LAYLERH ita ne ta gwangwaje Masoya Mabiya bayanta da ƙayatattu haɗadɗun litattafan ta wanda suka haɗa da irinsu MIKIYA JALAAL AREEF dadai sauransu, to ya kuke tunanin tafiyar zata kaya???
                ♡
_What an amazing trailer launch it was yesterday! ♥️ A huge shoutout to the entire team for making this such a special moment, one that will stay with us forever! Still can’t believe it’s finally happening, yay! enjoying a peaceful life after the successful heist in Venice. However In a surprising turn of events, one of their own betrays the team.Feeling super proud to be a small part of this LOVE cast and crew who’ve absolutely nailed touching LOVE, Every character is perfection, and I really hope people fall in love with this Novel  as much as we did while making it! 🤞 Babu ladama a tafiyan....._
♡
_Shi S0 ♥️ A duk inda ƙwaya ɗaya ne takk kuma kan Mutum ɗaya shi wannan SO ɗin yake faɗawa, Se gashi Rayuka da yawa da yawa dai akan shi wannan SO ɗin ƙwaya ɗayan da mutum ɗaya ne ze iya Mallaka,
A cikin su kowa yana kallon SO DAN RAYUWA ne dan kuma baima abinda Zuciya take da muradi wato SOYAYYAR ESHERH KALTHOM. A.K.A SWEETY Sun yarda  sun ɗauka kasadan WASA da SO dan me Rabo ya samu shi da ita su Rayu, sedai kuma loƙaci ɗaya ba zato ba tsammani wata zuciyar ta kutso cikin jerin gwanon masu farautar wannan SO ɗin don shima tashi ZUCIYAR datai mugun kamuwa a matsayin ƙaunarta tashi ZUCIYAR ta RAYU ga zuciyar da  yake jin shima  itace tashi bugun Numfashin  dama rayuwarsa ma baki ɗaya. Soyayyar da kowa yake buƙata dan rayuwa, SOYAYYAR da kowa ke son ta zamo tashi dan cikon wani kudiri ko ceton numfashin juna. Wannan dai shi SO ɗin shi ne suke ganin  zayyi  sanadin Ràyuwarsu su duka wadda kowannen su yake jin zuciyarsa  ba zai iya rayuwa batare da bugun numfashin wannan SOYAYYAR BA a cikin Ƙirjinsa💔._

~Ku sani cewa ita zuciya tamkar ƙabari ne, wanda yake cikinsa shi yasan abin dake damunta, kamar yadda bakasan ranar mutuwarka ba, haka SO yake shiga zuciya ya zauna daram, SO tamkar  tsawane cikin damuna baka sanin loƙacin da yake faɗowa, SO tamkar jini ne ajikin ko wanne ɗan Adam kamar yacce babu zuciyan da zata  iya rayuwa batare dashi ba, SO halittace da baka iya gane gabansa ko bayansa, SO tamkar iskane baka sanin loƙacin da zaka shake shi, SO halittace yana cikin jikin duk wani abu me rai awannan duniyar, SO shine kesa mutum ya kasance cikin farin ciki aloƙuta da dama, SO shi ne ke sanyaya zuciya kuma shi ke zafafa zuciya kuma shi ne ke sa mutum kukan fili dana ɓoye, SO shine ke sa mutum ya zama tamkar mahaukaci, An halicci so tun farkon kafa duniya ko an kashe kowa SO na nan ajali baze ganshi ba, Abu mafi girma a zuciyata shi ne ƙaddarar soyayyar wani wanda kuma shi ɗin ba nake bane ya hau kanka a hasalin nan ake gane bugun bugun ZUCIYAR Wanda ya kamu da SO dan ALLAH kuma SO ɗin ba nashi bane~

𝙎𝙾 ᴰᴬ𝙽  𝓡𝔸𝕐𝕌𝕎𝔸💘  labari ne mai cike da soyayya, yaudara,  jarumtaka, Cin Amana, A cikin wannan labari za a ga yadda soyayya ke iya zama mafarki mai ƙyau ko kuma mafarki mai ban tsoro, dangane da wanda mutum ya zaɓa ma kanshi. Shin waɗan nan sauran zuciyoyi zasu gane   cewan ba su bane a gabanta kafin loƙaci  ya ƙure? Ko kuwa zasu ci gaba da  sake zurfafa kansu a inda ba nan ne muhallin su ba?

Shin tayaya kuke kallon  zasu fuskanci rayuwar da ƙatoton  ƙalubalen  dake gabansu  su dukan akan SO💌 ƙwaya ɗaya?

Karfa ku Manta sunan wannan zazzafan LITTAFIN naku  𝙎𝙾 ᴰᴬ𝙽  𝓡𝔸𝕐𝕌𝕎𝔸💘💕!!!

# Reader's FAN'S
# reelschallenge

Page 1

ABUJA

   Lekki phase 1

♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡

Kwance take saman ƙayataccen  bed ɗin ta da ya gama jin  haɗuwar duniya d kuma wani irin gyara na musamman kai ba kace Mutum me Numfashi na rayuwa a wurin ba.
Mayuka da sabulan gyaran jiki kala kala masu kyau da tsada. Dan juyi ba da yawa ba tayi kafin Ahankali ta shiga buɗe  sleeping eyes nata da suka mata wani kalan nauyi kana kuma suka ƙanƙance,  dishi dishin da take gani acikin su ne ya sanya ta  maida idanun nata ta rufe su ruf, sosai taji kanta na wani irin bala'in sara mata, wanda take da ta cikakken tabbacin  rashin baccin da bata samu ba ne a daren jiya ya haifar da hakan. dan haka take jin gaba ɗaya jikinta yayi weak haɗi da kasalan jiki  ga kanta da take jin har yanzun yana mata wani kalan fitinannen  ciwo. Hannu tasa tana ɗan  dafe kan  dake mata ciwo kaman zai rabe biyu,still idanunta masu gama da na mashayiya ko kalan like irin wanda aka janye su ɗin nan, Ahankali ta ɗan motsa jikinta tare da soma ƙoƙarin ɗaga kanta  da takejin yayi mata  nauyi sosai, wanda kuma tasan hakan bai rasa na saba da tsakanin tunanin  da ta kwana yi,jingina bayanta da jikin fuskar gadon tayi  tare da sakin ajiyar zuciya tana miƙewa da ƙyar tare da nufar bathroom ɗin dake cikin bedroom nata.
           Shower kawai ta sakamar kanta  tare da tokare hannuwanta duka biyu da jikin toiletry ɗin. haka ruwan shower'n  ya shiga dukan jiki da kuma kanta, jin numfashinta  na neman ɗaukewa ne ya sanya ta janye jikinta  da ƙyar. idanunta jajur alamar  har yanxu komai nanan daram a yadda take jin komai ɗim kuwa.  Ahankali ta fara ziro fararen sawayenta daga cikin bathroom ɗin, ɗaure da towel me ɗan girma komi ahankali takeyi, Anutsenta tazauna gaban mirror kan stool,  blow drying gashin kanta tayi  tai parking nashi a ƙasan ƙeyarta, ta ɗauki wasu sprays masu tsada da ƙamshi ta feffesa ma gashin,kai tsaye ta nufi wurin clothing nata  da jibgin kayanta  ke ciki, walking slowly take tafiyan fuskar nan babu walwala samm ko kaɗan a saman kyakkyawar fuskar tan,  Kaya marassa nauyi ta sanya kasancewar tasan yau ɗin babu inda zata ta fi.Sosai take jin cunkushewar zuciya tattare da lamarin da har kwanan  yau bata iya samun damar cikakken me bata amsar WAYE MAHAIFINTA? Kafin tabar duniyar  don rayuwarta saura ƙiris Numfashin ta na dab da barin gangar jikinta,  Shi yasa take son kafin wa'adin ta yau ko gobe ya cika tasan waye ainihin MAHAIFINTA? Bawai taci gaba da amsa sunan mahaifiyarta a matsayin Mahaifinta ba. Tana son koda iyaka sunan shi ta sani koda bata ganshi ba tana son jin sunan sa ta yacce Rana daya takk sunanta ya tashi daga ESHERH KALTHOM JEDDY's ba. Ta na da tsohon burin ganinta zagaye yau da dangin pa'apah'nta wanda tun kamin tasan zata ganshi a cikin zuciyarta take ƙiransa da hakan. Wato PA'APAHH!!!.
Tayi nacin bi diddigin ahalin Maama'nta kaff  su faɗa mata koda iyaka sunan mahaifinta ne amma abu ɗaya take fuskanta daga gare su shine Ɓacin Rai, Ɓacin Rai shi ne take fuskanta daga kowa na Ahalin mahaifiyarta,sunce meta nema ta rasa a cikin duniyar ta da dolen dole take son Sanya ma kanta cutar rashin mahaifi a kusan ta? Sun ce  a cikin wannan duniyar meta nema ta rasa? Sun bata  duk wani kalan jin daɗin duniyar  sun zagayeta da tarin ƙaunarsu gareta.  Sake lafewa a cikin lallausan fari ƙal ɗin duvet cover ɗin ta tay tana yi  shiru, tana sake lulawa duniyar tunanin gano koda gaskiya ne daya daga mahaifin tan, Sama ta sake  ƙura ma idanunta sosai tamkar wata mai kallon wani abin ko wanne anan ne zata sama duka amsan tambayoyin da suka mata karen tsaye a ƙahon zuciyarta.
        Wata ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya ta kawo loƙacin da taji jiniyar car's nashi sun  karaɗe gaba ɗaya gidan wanda take da tabbacin har dama cikin qnguwar baki ɗaya.
  Daga can compound na gidan kuwa wasu shegun  jiga jigan manyan motoci ne suke ci gaba da sakin jiniya a cikin ESTATE ɗin. Mahaukaciyar Black car ɗin da tafi kowacce kyau da tsaruwa a cikin su wani soldier yay saurin buɗe masa wata shegiyar luxurious  car sanfurin ƙirar Roll R Rayce Sauran  bodyguards din dake tsaitsaye gaban manyan motocin  da suka kasance launinsu bakake tikk su kuma suna sanƙamewa. Tsaye ya tsaya cakk kan diga digansa loƙacin da matashin saurayin mamallakan wadan nan tarin car's din ya fito.Sara may sukai loƙacin da ya gama bayyana kansa garesu suna sake red na hannayensu dake  riƙe da wasu shegun bindigu irin  waɗan da basa saɓa saitin nan
         Cikin nitsuwa Matashin dake  tahowa sanye da farin rigar sport designer ta companyn NIKE mai ɗauke da cap da dogon wando alaman daga street warming execise ya ke, tun da yanzun sanyin safiya ne hakan ya sanya kai tsaye nan ya fara nufowa kafin komawa gidansa dake Barack.  Ko ina ya ɗauki shirun safiyar ranar ga sanyi irin mai ratsa jikin nan sosai. Daga inda take tsaye bayan jin tsaiwar motocin nashi zuciyan ta taƙi ci gaba da bata haɗin kwarin gwiwan kin kallonsa. Sosai ta ƙura masa kyawawan idanunta daga yanayin yadda yake takunsa da cikakken ƙarfi na hasali zaka san cewar ehhhh lallai shi ɗin matashi  ne mai ji da lafiya, cikakken namiji ne wanda a kallah zai iya kai 33 year's haka  a duniya,  hair'nsa yana kwance  ya sha gyara irin na Manyan soldier's din nan masu ji da gayu da kuma samartaka. Yana tafe yana shafan woyansa me ƙirar apple iPhone,ɗayan hannun nasa kuma  na ɗaure da wani haɗadden  diamond watch,  Cikin tafasar jini yake takunsa  yana sake nufo ganinta  kai tsaye, Wani irin ajiyar zuciya ta sauƙe tare da ƙara mannewa da jikin door  window'n tana jin shin a wanne mataki ne ma ya kamata ta sanya shi?  Tabbas tana jinsa sosai har cikin zuciya da ruhinta sedai gangar jikinta yaƙi bata haɗin kan jin kasantuwa tare dashi a matsayin ƙarƙashin Inuwa daya. "What are you doing there Shalele? Inata ta magana shiru baki jina!" Haka taji sauƙarn muryan mahaifiyanta take tsaye a bayanta tun ɗazun tana ta mata magana shiru. A ɗan  tsorace ta juyo don batay tunanin wanzuwar maama'n ba a irin wannan loƙacin, tun da tafi kowa sanin cewan ita ba mutum bace me karya dokan da duk ta riga ta gindayama kanta. Ijiyan zuciyan hakan ta sauƙe tana juyowa gaba ɗayanta. "Ina kallon Woje ne Maamah!!!" Ta furta tana son fuskewa abinta. Daidai kuma da loƙacin da yake shigowa har cikin bedroom ɗin, Kuma kai tsaye mayen ƙamshinsa ne ya fara sanar mata da hakan wanda baya taɓa ɓuya koda kuwa a cikin dubu yake.
   Daga bakin bed ɗin Maah ta koma tana zama gefe da inda yama kansa mazauni. A kan cushion ɗin dake gefe dap da gadon ta zauna tana sake lafewa luff tmkar wata ƴar mage.
cikin nutsuwa ta ce. "ESHERH KALTHOM JEDDY's wannan ba loƙaci bane na ɓoye wata damuwa daga gareki ko dan lafiyan jikinki! Ina so duk wani tunanin da baya da amfani a cikin rayuwanki ki shafe babinsa daga cikin brains naki, inason kamar yacce na sanki da jarumtaka da shanye komi to a wannan karon ma ina so  ki tsaya sosai ki jajirce ki yi aiki da tunani da kuma hankalinki kinji Shalelena, INSHA ALLAH babu abinda ze farun min da rayuwanki Shalelen Maah ɗin ta"
     Kan  ta tai nooding  kamar kan ƙadangaruwa alamar ehhhh ta ɗauki komai. "Good girl, to kada ki yi wasa kin ji? Maza ga Fawaz nan yazo bara na barku Ni zan fita ne yanzu tafiya ta kamani zuwa Lagos" idanunta manya da har yanzu suke ba a daidai ɗan su ba ta gyaɗa tana jimƙe hannuwanta wuri guda. Har taje dap da ƙafan fita ta dawo cikin ɗan hanzari tana furta "Shalele kinga ma Omer na ƙirana mebi kuma ya kira taki woyan ne a kashe se kuyi magana" daga haka ta sanya kanta tana barin bedroom ɗin ba tare da tayi duba da sanda yanayin fuskan Fawaz ta sanja ba. Zubama woyar idanu sosai ESHERH  tayi tana  kallonta tamkar me nazartan woni abu daga cikin ta,  "Wannan ba ƙoƙarin bane na biye shirmen banza oya maza bani magungunan ki" haka taji dakakkiyar muryansa  me kama da bada umarni.A kuma daidai loƙacinne wani sabon ƙiran ke sake shigowa woyan dake gefe da bed ɗin.tsamm ya miƙe tsaye  yana nufar saman mirro'rnta da kai tsaye ya hanji tarin drug's nata. Wani kalan yatsine farar fuskanta  tay tana juyar da kanta gefe. A kuma lokacin yake dawowa. "Uncle Fawaz pls ka bari zuwa anjima" ba tare da tasan se tanka mata ba ya furta. "Ya jikin ki?, hope dai kan ya rage ciwon sosae kuma idon baya miki shi wannan zogin?"   Wani kalan sake lafewa a cikin cushion din tay tana janye idanunta baya..........

Thank you for sharing your nuvel  with the world and enriching our lives with your beautiful fam 💃💐. May this special day bring you as much happiness as you bring to others. Wishing you endless love, success and fulfillment in all that you do. ❤️ All my love 😍

BY AMMEY LAYLERH ✍️
        &
*NAINERH KD✍️☑️*

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.