Free chapter · Read without an account
10
by Rabiatu bashir · DAN HALAK
💋ƊAN HALAK💋
MALLAKAR
UMMU MAHER(MISS GREEN)🍃
AREWA WRITER'S ASSOCIATION📚
~*Arewabooks*~
D'AN HALAK:: https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb3b80f1ef8159
~*Wattpad*~
D'AN HALAK
***
content=story_info
10
_____"nasan baki sanni ba ƴammata, amma kiyi haƙuri ki yafemin idan har na shigar miki lokacinki babu yadda zanyi ne, shiyasa har hakan ta faru dafatan abin bai sosa ranki ba"?.
Ɗaga kai tayi, lokaci ɗaya kunyar bawan Allahn da ganin girmansa suka shige ta, sai ta jiyo muryarsa yana ce wa" ƴammata nazo wajenki ne akan wani lamari duk da bana tunanin ƙwaƙwalwarki zata iya ɗaukar darasina, amma da sannu yaro ke rarrafe har ya fara tafiya kuma da sannu ƙaramar bishiya ke girma har ta kai ga cika waje, ban sanki ba ban taɓa ganinki ba amma Allah ya ɗora jarabar sonki cikin lokaci ƙanƙani".
suna cikin maganar ne Baba Kande ta leƙo tana sababi, har tana tsinewa Ummi wai ta zama karuwa tana janyo maza.daga nan ta fara dukanta har tana yaga mata riga. mutumin yana bata haƙuri amma taƙi haƙura ta dinga zaginsa har sai da ta koresa ya tafi domin tana son haɗa masa wani sharrin, shi kuwa ya wuce da sauri ba don yaso ba, domin har ya tafi bai daina kallom Ummi ba kana ganin fuskarsa kasan tausayinta yake ji.
Cigaban labari
na ƙara rungume Ummi sosai ajikina, yadda take kukan bilhaƙƙi haka zuciyata ma take bugawa da gaske, domin da gaske bana son duk wani abinda zai taɓa ƙannai na, yadda nake sonsu bana son kai na haka.
Baba kande tana ta maganganunta na ɓacin rai, babu wanda ya kulata domin har Ameera ta shiga gida abinta domin daman da wata aƙasa, biyo bayan abinda ya fari tsakaninta da Hajiya Ƙarama, wanda agefen zuciyata nima ya maƙale yaƙi fita domin nasan ba zasu yarda ba, kuma aikin Iya Abu nasan ya lalace haka zalika aikin Ummanmu ma ya lalace asara goma da ashirin.
Allah ya taimakemu Babanmu baya nan, saboda haka yanzu shawara muka cigaba da yi ta yadda za'ayi mu biya kuɗin asibiti.
Ihun Fahad ne ya katsemu daga shawarar da mukeyi, duka atsorace muka kallesa ya ƙaraso da gudunsa kan cinyata ya miƙomin ƴan bandir ɗim kuɗi.
Na waro ido waje domin sanin wanda ya basa, da ido nayi masa tambayar wa ya basa?.
"Antinmu wani ne ya bani, ya ce wai in bawa Anti wai ince mata wanda yazo ɗazu ne".
Da sauri Ummi ta kallesa har tana haɗe harshe wajen ce wa.
"me....me.... wanda..yazo ɗazu dai"?.
Yaron ya ɗaga kai.
Godiyq muka shiga yiwa Allah, daya sa aka samu zunzurutun kuɗi haka wanda aƙalla za su kai dubu ashirin ko su ɗanfi ma.
Sai alokacin ne Amira tayi magana, cike da fara'a ta ce" oh Allah mungode maka Ummi ke me sa'a ce wallahi yanzu kinga mun samu kuɗin da zamu kai asibiti a sallamo mana Ummanmu".
Tashi mukayi mu dukanmu muka shirya ƙannenmu muka ɗunguma zuwa asibiti, muka samu adaidaita sahu har asibitin murna fal zuciyata domin da bamu samu wannan kuɗin ba da yaya za'ayi kenan?.
muna zuwa kai tsaye na wuce wajen da aka tanada domin biyan kuɗi, na cake dubu ashirin na bayar dubu biyar kuma na ajje a gefen zanina dama kuɗin da muka ƙirgasu dubu ashirin ne da biyar.
Dama kuma kuɗin asibitin dubu ashirin ne.
Sosai su Ummi suke murna, saboda ganin mahaifiyarmu cikin ƙoshin lafiya ga ƴan biyunta duk maza farare ƙal ƙal kamar Ameera domin ita duk ta fimu fari.
Umma ta tsuramin ido tana kallona, hankalina ya tashi sosai na ƙarasa kusa da ita domin jin laifin da nayi mata, ko domin na daɗe ne dana fita? ko kuma wani abun ne dai?.
na durƙusa gabanta, gamida riƙo ɗan yatsanta babba na ce" Ummanmu lafiya kuwa? ko dai wani laifin nayi ne ban sani ba? idan ma laifin nayi Umma ayafemun domin darajar ƴan biyu masu farar fuska".
Dariya mukayi mu dukanmu, sai Umma ta ce" to na haƙura Humaira h amma a ina kika samo kuɗin da kika biyamin kuɗin asibiti"?.
Caraf Ameerah ta ce" Umma wani ne ya bada kuɗin, wai yaga Ummi yana sonta to akan hakan nema akayi faɗa da Baba kande har ta yagawa Ummi riga, bayan mun dawo gida shi ne ya aiko da waɗannan kuɗaɗen, dama kuma muna ta neman hanyar da zamu samu kuɗin mun rasa to sai yanzu Allah yasa aka samu, don har gidan DEEN MARSHAL munje amma bamu samu kuɗin ba, harma mukayi faɗa da Hajiya Babba".
Da sauri Umma ta kalli Ameerah ta ce" me yasa kuka je gidan? kunsan wacece Hajiya babba kuwa? kunsan ƙarfin ikonta agidan? to ko uwar me gidan ce tace akora za'a kore ta, sannan ni ayanzu haka ma nasan ba barinmu za tayi ba, dalili da meyasa bakyason zaman lafiya Ameerah? ina yawan faɗa miki rayuwa bata yiyuwa sai da haƙuri, kayi haƙurinma ya ka ƙare ballantana akasin haka? sannan ga wannan abin da ya faru na Ummi".
ta kalli Ummi wacce kanta yake asunkuye dom kunya ta ce" Ummi shin kinsan mutumin ne? kuma tun yaushe kuka haɗu"?.
"Umma wallahi ni bansanshi ba, kuma sau ɗaya na taɓa ganinsa yau kenan amma ban taɓa ganinsa ba amma dai yana yimin kama da wata fuska wacce na santa amma na rasa fuskar waye"?.
Umma ta ɗaga kai, sannan ta ce" to duk sanda ya ganki ya tsayar dake kice yazo ya samu mahaifinki kinji"?.
ta ɗaga kai alamar taji.
Ameerah ta ce", uhum Umma wallahi kina da haƙuri yanzu duk abinda Babanmu yake miki bakya gani? har kike son wani yazo ya gansa daganan ya lalata lamari duk da Ummi yarinya ce amma ai ana aurar da yara ashekara 15, tunda babu wanda zai ce hakan saɓon Allah ne, ko don ƴan baƙin ciki ai dole a yardar masa ya turo kawai ayi, muma Allah ya zaɓa mana abinda yafi alkhairi".
"Ameerah koma dai meye mahaifinku ne, sai haƙuri kuma ba'a hannuna neman aurenku yake ba a hannunsa yake saboda haka ko inaso ko bana dole ne a nemi auranku a wajensa, uba ubane koda kuwa a turu aka cirosa".
Ameerah dai don haushi bata ce komi ba, ni ce ma na ce" hakane Umma Allah ubangiji ya ganar da Baba".
Duka suka amsa da amin.
Bayan an sallamo Umma, mun fito da taxi muka hango ƙofar gidanmu cike da mutane damƙam...............
$$$$$$
Haidar ya ɗaga wayar tamkar bazaiyi magana ba sai kuma ya amsa.
"ina jinki"?.
Hanan taɗan daidaita muryarta sannan ta ce" ka kuwa gane ni?".
Ya basar ya cigaba da aikinsa saboda sam bayason yin waya da kowa ayanzu saboda shi kaɗai yasan halinda yake ciki, wanda kuɗi ko mulki ba zai iya bayarwa ba domin ayanzu haka aƙwance yake yana fama da ciwon cikin dake azalzalarsa wanda yake motsa masa duk bayan wani lokaci, wanda likitoci suka tabbatar masa rashin aure ne ya janyo masa.
Hanan taɗan dakata da magana, saboda taji kamar yana cikin wani yanayi ne saboda haka ta ce" kayi haƙuri bansan kana cikin wani yanayi ba, ko zan iya taimaka maka da wani abun?".
bai katse kiran ba, kuma bai ce mata ƙala ba saboda haka har Hanan ta gama maganarta bai san abinda take cewa ba.
Da ƙer ya lalubo lambar Hammud, bugu ɗaya ya ɗaga yana jin yanayin aminin nasa hankalinsa ya tashi sosai da sauri ya sanya jallabiyyarsa ya fito daga ƙerarran gidansa wanda ya gamasa ƙwanannan.
***
Yana zaune gaban likita, yayi shiru yana jin dukkanin bayanansa har ya kai ƙarshe Yana kallon yadda hankalin Hammud ya tashi sosai.
"likita yanzu meye mafita?".
Cewar Hammud wanda baki ɗaya hankalinsa yake atashe.
likitan ya gyara farin gilashinsa sannan ya ce" solution dai ɗaya ne yayi aure domin wannan matsalar tasa babu wani magani ko tablet da zamu basa yayi masa magani kawai dai gwara yayi haƙuri ya daure yayi auren shi ne magani, sannan kada ya daɗe ahaka ba tare da yayi auren ba komi zai iya faruwa".
Hammud ya kalleni, na rintse idona inajin wani irin suya araina.
Hammud ne ya kamani muka fito, dai dai wani ɗan desk naso faɗuwa yayi saurin ruƙoni yana ce wa" sannu Haidar kayi ahankali".
Hammud wannan wata irin ƙaddara ce? anya kuwa zan iya jure wannan ƙaddarar? ace ina da lafiya ta da komi Allah ya horemin komi na rayuwa amma Allah bai sanya nayi aure ba, saboda wani dalili wanda aka shafamin kashin kaji, idan ma laifina dana zo duniya ne ai ba ni na aikata laifin ba, sannan Allah ne yaso inzo ta wannan hanyar"!!.
na faɗi maganar tawa cikin ƙaraji.
Hammud ya ce" kash! Aminina bai kamata adingajin wannan kalaman masu muni daga bakinka ba, kamata yayi ace ka mayarda komi ba komi ba ka cigaba da addu'ah komi yayi farko yana da ƙarshe kuma in sha Allah komi zai zama kamar ba ayiba, kuma auren ma ƙwanannan zaka yisa in sha Allah".
Haka dai ya dinga rarrashina har muka dawo gida, allurar da suka yimin ta fara ratsa ƙwanyata, barci me nauyi yayi awon gaba dani.
HANAN
wani malolon baƙin cikine ya kusa kasheta atsaye, wannan wani irin ɗan rainin hankalin namiji ne? ace da ranta da lafiyarta namiji yana wahalar da ita? gaskiya doleta ta samowa kanta mafita, tun kafin gari ya waye mata.
Yayarta Asabe ta kira, kirab farko ta ɗaga tayi mata bayanin komi.
Yaya Asabe ta ce" aikin banza aikin hofi au dan ɗan wannan ƙaramin alhakin shi ne kika tada
hankalinki?"............................
WELCOME TO UMMU MAHER BUSINESS CENTER
_____¥¥¥¥¥¥¥
TIME TABLE NA KOYON SANA'A
CLASS 1👇🏻
____________
KOYON MAYAFI NA BEAD WORK BEAD WORK
MAYAFI NA STONE WORK
HULUNA
RIGUNA
FANTIS
WANDO JEANS
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
~Naira~ 800
CLASS 2👇🏻
______________
INVITION CARD
3d logo
3d mockup
3d render
Cover book
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
~Naira~ 800
CLASS 3
_________
Turaren wuta
Humrah
Gyaran jiki
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
~Naira~ 1k
a tuntuɓi ummu maher ta lambarta👇🏻
***
DOMIN SHIGA WHATSAPP GRP ƊINMU👇🏻
***
thThNQx
UMMU MAHER