Free chapter · Read without an account
Ajnabiyya page 10
AJNABIYYA...
NA
*HAJJA CE* 👈
Arewabook@Hajja22522
Wattpad@Hajjac
Facebook@Hajjace
Page 10
Yadda ta ke buÉ—e idanuwa tana kallon hanya zaka rantse da Allah cewa abu ta yar ta ke nemansa. Nan kuwa hanya ta ke bi yadda ba zata faÉ—a cikin kwata ba. Tafiya ta keyi tana ganin yadda masu ababan hawa suke wucewa, ta fara tunanin. 'Da ace tana gidan masu kuÉ—i, waya kawai zata yi azo a É—auke ta. Ko kuma ta taho da driver ya kaita duk inda ta ke so.' Sam batayi aune ba taji an watsa mata wani abu a jikinta har zuwa fuskarta. Gabaki É—aya ta gigice ta shiga goge fuskar da hijab É—in jikinta. Ba zata iya cewa ga abinda ya faru ba.
A hankali ta buɗe ido tana ƙarewa wajan da ta ke tsaye kallo. Ta cikin hasken farin wutan da ya haske gari taga wani ruwa ne kwance a tsakiyar hanyar, alamar mai mashin ɗin da ta hango yana tahowa shine ya fantsala mata ya tafi ba tare da ya tsaya ko haƙuri ya bata ba.
"Hmmm." Ameerah ta yi tana ci gaba da tafiya zuciyarta cike da bakin ciki. Komai na talaka daban yake, tayi imani unguwar masu kuɗi ba zaka ga wannan ruwan kwance ba, sai tituna kamar ka kwanta. Haka har ta isa gida da tunani hakan kuma yasa bata ji wahalar tahowa a ƙafarta ba. A tsakar gida ta gansu Baba yana zaune akan tabarma yana cin abincin dare. Inno na kan kujera tazo sashin nasu tana yiwa Baba magana cewa zata je ta gano danginta. Haƙuri yake ta bata akan ta jira saboda bashi da kuɗi, ita kuma idan zataje sai ya kashe uban kuɗi saboda yawan tsarabar da ta ke sashi haɗa mata.
"Kabarni na yi tafiya ta dan Allah. Nan da nake zaune me nake yi banda zama da kuma kwanciya? Ina so naje gaskiya na gaji da zaman waje É—aya." Ameerah na zama kan tabarmar da Mama ke zaune tace.
"Inno sai ina?" Cikin ɓacin rai Inno ke faɗin.
"Yo banda an maida ni ƙaramar yarinya, taya za'a ce wai kamar ni sai nace zanje guri ace min a'a? Toh ko sanda mijina yana raye baya min kulle irin yadda Baban nan naki yake min. Haka kawai a dinga hana ni kamar wata ƴar ku?" Tayi maganar muryarta na rawa alamar zata fashe masa da kuka a kowanne lokaci. Jin yadda muryar Inno ke rawa yasa Ameerah sakin baki. Baba da jikinsa yai sanyi ganin yadda Mahaifiyar shi ta shiga damuwa yasa shi cewa.
"Yaushe kike son tafiya?" Ta buÉ—e baki tace,
"Ko gobe ma ni a shirye nake me zan jira?." Ya rintsa ido, ya sani dole yaje ya nemo ko bashi ne dan ya yi mata abinda ta ke so. Baya san damuwarta domin yasan bala'i ne ga rayuwarsa.
"Shikenan Allah ya kaimu goben." Tace,
"Amin Allah ya yi maka albarka." Mama da Baban suka amsa da amin. Ameerah kuwa cewa tayi.
"Inno Baba fa bashi da kuÉ—i, ina zai samo miki kuÉ—in tafiya Gwarzo? Dan Allah ki bari har sai lokacin da Allah ya hore masa sai kije, idan ma a can zaki zauna shikenan."
"Hana shi yin aikin alkairi kinji ko? Ke dai wallahi a haka kamar ta Allah. Toh bazan bari É—in ba, shi yai niya ke kuma kina son hanashi. Kuma idan naje mijin aure zan samo miki, kina gama gantalalliyar makarantar nan ki shiga É—akin mijinki kamar sauran Æ´an uwanki." Ameerah ta yi mata wani kallo, kasan cewar babu wadataccen haske sai na farin wata yasa babu wanda ya lura da fuskarta. Cikin zuciyarta ta ke faÉ—in.
'Inno kenan, ni zanyi auren haɗi? Uhmmm-uhmmm.' A zahiri kuma tashi tayi ta shige ɗaki tana sosa cikin kummanta. Da yake a ƙoshe ta ke, kuma tayi duka sallolinta tun a gidan Yaya Hanne. Dan haka hijab ta cire ta ajiye jakarta tare da karkaɗe inda zata kwanta. Kamar kullum yadda zuciyarta ta ke tafiya duniyar hasashe da kuma mafarki, duk da taso taga an bata kayanta da Mubasshir ya bata, tayi ɗinki mai kyau kamar yadda ƴan mata keyi. Kawai sai ta lula tunanin ace mahaifinta mai arziki ne, da ba wannan maganar ake yi ba ta ja mata rai akan kaya guda biyu. Bata sa maganar Inno ta nemo mata miji a cikin ranta ba. Hakan yasa ta samu damar yin bacci da wuri.
*****
Wajan karfe takwas na safe Baba ya fito tsakar gida dan samowa Inno abubuwan da zata tafi dashi. Tsaye ya yi yana karya hularsa zuciyarshi cike da tunanin ta ina zai fara? Shi ba mutum bane ma'abocin cin bashi ba, shi yasa komai na rayuwarsa yake yinsa cikin tsantseni. Sallama yaji anyi, ya amsa yana kallan yarinyar da ta shigo gidan. Ko gaisuwa babu ta shiga isar da sakon da ya kawo ta gidan cewa.
"Ana sallama da mai gidan." Baba yace.
"Kice gani nan zuwa." Ta juya tana cewa.
"Toh." Lokacin Mama ta fito, suka yi sallama dashi dan idan ya gama da bakon wuce wa zai yi ba sai ya dawo ciki ba. Kamar kullum yadda ya saba sai da ya shiga wajen Inno yai mata sallama akan zai je ya samo kuɗi ta zama cikin shiri. Inno tayi masa fatan alkairi daga nan ya fice. Wani matashin saurayi ya gani tsaye a ƙofar gidan, can gefe kuma mota ce da alama da ita yazo. Cikin girmamawa saurayin yake gaisar da Baban Ameeran. Ya amsa da sakin fuska duk kuwa da cewa bai taɓa ganinsa ba.
"Suna na Mubasshir Ali Ungwaggo. Baba ni ne wanda naga ƴar wajan ka Fatima (Ameerah) naji zuciyata ta aminta da ita. Ina ta cewa zanzo na ganka Allah bai haɗa mu ba, sai yau nace bari nayo sammako ko Allah zai sa na dace da ganinka dan na gabatar da kai na asan da ni." Yadda Mubasshir ke magana da yadda yake a kamalance yasa Baba ganin mutunci da kuma girmansa. Sake kallansa yai, kallo irin na tsab daga sama har ƙasa yana nazarinsa kafin yace.
"Oh hooo malam Mubashshir ne?! Toh..! toh..!!.. toh...!!! dama kai ne? Shikenan kai kuma haka ake yi duk sanda kazo wajanta sai ka kashe mata dukiya? Ka bari haka dan Allah Mubasshir har zuwa muga lokacin da Allah zai haɗa zuƙatan ku kai da ita. Bana san yawan kashe mata kuɗi da kake yi ya yi yawa gaskiya." Mamaki ya kama Mubasshir jin abinda Baban Ameerah ke cewa. A ganinsa mutum irinsa yana da buƙatar ganin an taimakawa yaransa. Sai kuma wani tunani yazo masa tunawa da yai bafa ko wanne talaka ne kwaɗayayye ba, ta iya yiwuwa Baban Ameerah yana cikin masu ta ka tsantsan. Cike da girmama Mubasshir ke cewa.
"Babu komai Baba, ba roƙata tayi ba. Kyautatawa ce kamar yadda Allah yace a kyautatawa mata. Insha Allah kuma za'a yi yadda kace ɗin." Baban Ameerah yaji daɗi yadda Mubasshir ya amsa masa. Dan haka cikin jin daɗi yace.
"Toh Allah ya tabbatar da alkairi tsakanin ku. Yanzu dai tana matakin ƙarshe a makarantar gaba da primary. Ina so ka ɗan bata lokaci ta samu tayi jarabawarta cikin nutsuwa kafin ta faɗa tarkon soyayya." Mubasshir ya yi murmushi yana sosa ƙeya jin abinda Baban ya faɗa. Nan fa ya gaya masa ko wanene mahaifinsa da sana'ar mahaifinsa da unguwar su da komai da ya kamata Baban ya sani. Nan Baban Ameerah ya tabbatar masa da cewa zai yi bincike akan komai kamar yadda addini ya shar'anta a neman aure. Daga nan suka yi sallama Mubasshir ya ciro kuɗi dubu ashirin ya bawa Baban amma yaki yadda. Ganin zasu tsaya jayayya bayan kuma shi Mubasshir ya yi niya sai kawai ya ajiye masa kuɗin a ƙasa ya nufi mota da sauri. Daidai kuma lokacin Yaya Ammani ya nufo Shi, ganin kuɗi a ƙasa yasa shi ɗauka baki a buɗe yake kallan mahaifinsa yana kuma kallan yadda Mubasshir yabar wajan.
"Baba waye wannan?"
"Saurayin Ameerah ne." Yaya Ammani ya É—an ja da baya yana ware ido.
"Kaiiii..! Wannan wanda yake kawo ababan arzikin?" Baba ya kalle shi yana zabga masa harara. Duk da hakan sai da Yaya Ammani ya ƙarasa maganar da ta ke cinsa.
"Ina ma ina wajan nan yazo, nasan da har ni zai bawa kuɗin." Ya faɗa yana ƙoƙarin ƙirga kuɗin hannunsa. Baba ya miƙa masa hannu alamar ya bashi. Yaya Ammani ya kalleshi yana lankwasa kai yake cewa.
"Dan Allah Baba ko Æ´ar dubu biyu ce ka bani. Wallahi ko sisi bani dashi ga wanki ina so nayi." Da mamaki Baba yake cewa.
"Wai kai baka jin kunya ne? Kamar ka ƙaton saura ba sana'a ba komai sai zaman majalisa kuna gulmar jama'a? Toh da ba'a bada wannan kuɗin ba, gaya min ya zaka yi da kayan naka? Ammani kana tunanin wannan zaman banzan da kake yi yana burgeni? Allah ya shirye ka. Ungo nan." Ya faɗa yana ciro dubu biyu ya bashi. Yaya Ammani ya karɓa bai ji haushi ba yana ta godiya. Maimakon ya shiga gidan sai ya juya ya koma inda ya fito. Baba kuwa wani irin farin ciki ne ya kamashi yana sake yiwa Allah godiya na kawo masa wannan kuɗin. Wajan Inno ya shiga ya sameta tare da tambayarta abubuwan da ta ke so ya siyo mata wanda zata tafi dashi. Nan fa ta shiga lissafowa harda adadin yadda ta ke so. Bayan ta gama faɗa masa ya tashi ya shiga wajan Mama yake nuna mata kuɗin tare da cewa zai ranta ya yi amfani dasu idan Ameerah tazo tasa kuɗin a cikin lissafin da yace ta dinga rubutawa. Daga haka ya fice daga gidan. Lokacin da Ameerah ta dawo daga ɗibar ruwa Mama ta gaya mata abinda Baba yace. Ameeran tace,
"Nifa Mama ba abinda nake rubutawa wallahi."
"Amma kinsan yace ki rubata dai ko? Bana san jan magana Ameerah ki shiga ki ɗakko takarda da biro ki rubuta bana san taurin kai." Jin haka yasa Ameerah ta tashi, cikin ɗakin ta shiga ta janyo jakarta ta makaranta ta rubuta duka abinda Mubasshir ɗin ya bata, har wanda ta taɓa ragewa sai da ta rubuta, sannan ta yiwa littafin wani irin mugun ɓoyo. Tashi tayi ta shirya zuwa gidan Yaya Hanne yadda za'a sha hira da ita. Tana gamawa ta yiwa Mama sallama ko wajan Inno bata je ba ta fice.
Yaseer yana kan lifan É—in Baban su an aike shi ya hango ta tana tafiya. Har zai wuce sai kuma ya zagayo inda ta ke. Da sauri ta É—ago dan ganin waye. Murmushi tayi masa tana cewa.
"Har kasa naji tsoro." Yace,
"Sorry ban zaci hakan ba. Sai ina kuma haka?"
"Gidan Yaya Hanne."
"Lafiya dai ko? Nasan ba zumunci gareki ba." Ameerah tayi Æ´ar dariya tana faÉ—in.
"Karka yi min sharri wallahi. Toh haihuwa tayi."
"Ahh na san dama haka kawai bazaki je ba. Allah sarki Allah ya raya."
"Amin."
"Muje na rage miki hanya dan nasan tafiyar nan a dole kike yinta Æ´ar gayu ce ke." Ameerah ta harare shi tana faÉ—in.
"Ka kai ni dai wane irin ka rage min hanya?"
"Haka nake nufi ai." Ya faÉ—a yana É—an matsa mata dan tazo ta hau. Babu musu ta haye suna tafiya yana janta da magana har suka isa.
"Nagode kaga da tuni ina hanya ina ta tafiya." Bai bata amsa ba sai cewa yai.
"Ɗazu naga motar saurayinki a ƙofar gidan ku. Kice har da safe yake zuwa?" Yaseer ya yi maganar da wata irin siga wacce tasa Ameerah yi masa kallon da ita kanta bata san tana yinsa ba. Ya ɗaga mata girarsa alamar tabbatar da abinda ya faɗa yana lasar lips ɗinsa na sama kamar yadda ya zame masa jiki.
"Yaseer kasawa guyen can ido fa. Toh menene naka a ciki ni kam?" Yaseer ya sauke numfashi tare da kura mata ido tayi saurin janye nata yace.
"Na rasa gane wai aure zaki yi ne? Keda Meenal kunce sai kunyi karatu. Amma ke har kin fara rushe tsarin da aka fara ginawa."
"Dame zanyi karatun Yaseer? Kaida Meenal kunci jarabawar nan. Ni kuma fa? Ina son karatu Yaseer, amma ba irin wanda ni zan sha wahala. Iyayena ma su sha wahala ba. Idan har auren zai zama farin ciki a rayuwata zanso yinsa a lokacin. Kudai ina muku fatan karatu lafiya." Ta faÉ—a cikin karyewar murya idanunta na kawo kwalla. Shi kansa Yaseer jikinsa yai sanyi yace.
"Ki bari mu kammala jarabawar mu please. Insha Allah za'a samu mafita. Nida Meenal ma zai yi wahala muyi amfani da scholarship É—in da za'a bamu. Gwara mu ci gaba da rayuwar mu yadda muka taso." Ameerah ta kalleshi. Duk da ba wani girman arziki garesu ba dan Ameerah da Meenal É—in shekeran su goma sha bakwai. Yaseer kuma yana da 20years. Amma suna da wani irin tunani da kuma soyayyar son junansu. Tana girgiza kai ta ke cewa.
"Bazai yiwu ba Yaseer, iyayan ku ma bazasu yadda ba. Karka damu dani ina addu'a komai Allah ya zabar min zanyi godiya na yi."
"Insha Allah zaki karatu Meerah." Ya faÉ—a cikin karfafa mata guiwa.
"Nagode." Ta faÉ—a tana juyawa ta shige gidan. Shi kuma yaja lifan É—insa yabar unguwar zuciyarsa cike da haushin rashin samuwar nasarar jarabawar Æ´ar uwar tasu.
*****
Baba kuwa sai da ya siyawa Inno komai da tace, sannan ya dawo gida lokacin ta gama shiryawa shi kawai ta ke jira. Yana zuwa kuwa ta fito shanye cikin mayafin ta na atamfar jikinta ta yiwa Mama sallama suka fito. Har tasha yaje ya ɗorata a mota ya biya kuɗin motar tare da bata wasu ta riƙe a hannunta. Bai bar wajan ba har sai da motar ta tafi sannan ya nufi wajan sana'arsa. Ameerah yau ma bata dawo gida ba sai da tayi sallar isha'i a gidan Hanne. Suna zaune ita da Mama ta yi ƙasa da murya tana cewa.
"Mama kayan nan a bani su na É—inka zan saka ran sunan jaririn Yaya Hanne." Mama tace,
"Toh Baban ki yace sai yaje kasuwa ya tambayo kuɗin su sannan zai baki. Yace shi duk abinda zai fito daga hannun saurayi tsoran sa yake saboda gudun wulakanci da rashin mutunci." Ameerah ta sunkuyar da kai ƙasa bata san lokacin da tace........
Chat.... ***