Free chapter · Read without an account
3
by Rufaida Umar · ALWASHI
ALWASHI
***
03
Adam bai samu zuwa asibitin ba wajen matarsa sai dare. Su biyun nan dai matan su ne tare da ita, sai da ya ji ta ba shi tausayi. Ya sani da ace tana da danginta a kusa to fa ba za ta fuskanci waɗannan kalubalen ba. Daya bayan ɗaya ya ɗauki yaran, farare ƙal masu cikar suma. Haka ya bi kowacce ya yi mata huɗuba, ya ba su suna Sameera da Laila. Ba don ma ɗan zaren da aka ƙulla a ƙafar ita Sameera ba, wanda shi ya bambance su, to fa zai wahala a yanayi na halittar fuska ka iya bambanta su.
Washegari kuwa aka sallame su da safe suka tattara zuwa gida. Su Nene da yaranta kuwa babu ko leƙe, haka aka dinga shigowa Kubra daga makwabta ana mata ta'aziyyar rashin Gwaggo da kuma barkar haihuwa. Koda ranar suna ta zo babu wani taro, raguna manya guda biyu Adam ya yanka sai abinci da aka raba na sadaka. Nene sai a lokacin ta zo gidan ta iske Kubra zaune tana shayar da 'yan biyunta, gaba ɗaya ta rame sai ko hasken da ta ƙara tamkar wacce jinin jikinta ya ƙare.
"Allah ya isa tsakanina da ke Kubra! Shegiya kawai mayya! Ki sani kin cuce ni da ki ka auri ɗana, kin cutar da ni da kika sanya na haɗa tsatso da ke. Mutuniyar da ba a san asalinta ba! Har abada na tsane ki! Na kuma tsani waɗannan 'ya'yan da ki ka haifa! Kuma mu zuba ni da ke sai na shayar da ke mamaki!"
Tana kai wa nan ta fice daga gidan ta bar Kubra da zafin ƙirji da zubar hawaye sosai. Wannan ya ba ta tabbacin cewa har abadan fa Nene ba za ta taɓa sonta ba. Koda ba su ma furta ba ta gani, babu wani ɗan cikin Nene da ya shigo mata barka, ta ƙara rungume yaranta a ƙirji tana kuka kamar ranta zai fice. Adam da ke tsaye a hanyar shiga ɗaki, ya ji komai, tun sallamar Mahaifiyarsa ya miƙe daga biyan bashin bacci da ya tara tun rasuwar Gwaggon bai samu ya yi ba.
Tun kuma rasuwar da wata ɗaya sai Adam ya koma wani shiru-shiru, ba shi da aikin da ya wuce tunani, ko ya shige dakinsa ya yi ta rubuce-rubuce. Kubra da ta gaji ta tunkaresa don neman ba'asi. Murmushin yaƙe ya bi ta da shi kawai ya girgiza kai.
"Kewar Gwaggo ce ke ɗawainiya da ni ba komai ba Kubra. Sai ko ɓangaren aikina, nan da kwanaki uku zan yi tafiya zuwa Abuja, zamu je ne hira da mataimakin shugaban ƙasa. Dalili kenan da ki ka ga ina ta shiri."
Ya ƙarashe da mata nuni da takardun da ya tattare su dab da za ta ƙaraso ɗakin. Sai a lokacin da ta ɗan sami nutsuwa har da sauke ajiyar zuciya.
"Allah ya tabbatar da alheri. Allah ya jaddada rahma ga Gwaggo ya sa tana kyakkyawar makoma."
Ya amsa da amin.
Kwana biyu tsakani, Adam ya soma shirin tafiyarsa. Ana gobe zai wuce har wuraren uku na dare ba su yi bacci ba da Kubra suna hira. Kusan gaba ɗaya hirar yana ba ta labarin irin yadda ya tsallake hare-haren da abokan adawar siyasa na juna ke kawo masa saboda kokarin bankaɗo sirrikansu ta hanyar tambayoyi ko kuwa a cikin shirin Dimukuradiya da yake gabatarwa a gidan rediyo. Idan ya yi wata tambayar ma, sai su yi ta zarginsa da sanin wani babban sirrinsu. Ita dai Kubra gaba ɗaya jikinta sai ya yi sanyi, babu kamar jin cewa har yunƙurin watsa masa Acid a fuska an yi amma Allah ya tsallakar da shi.
"To nikam na ji aikin nan naka ya sire min gaba ɗaya. Ka tausaya min da yaranka ka ajiye shi hakanan, na gwammace ka koma kasuwa hankalina zai fi kwanciya."
Adam ya yi dariya gami da gyara Sameera dake gefen abin lulluɓinta da ya yaye, sai da ya sumbaci goshin yaran nasa ɗaya bayan ɗaya kafin ya maido duba ga Kubra ya riƙe yatsunta na duka hannayen ya ce,
"Kina tunanin idan na yi haka shi ne zai sa na tsira? Um um Maman Twins, wanda fa ke bibiyarka a sharri komai za ka yi ba zai fasa ba. Ke dai kawai duk inda zan shiga na fita, ki taya ni addu'ar gamawa da kowa lafiya kamar yadda iyaye da ni kaina nake yi. Babu sana'ar da ba ta cike da ƙalubale da hatsari."
Ta sauke ajiyar zuciya.
"Hakane, Allah ya dafamaka ya ƙara baka kariyarsa."
Ya shafi gefen fuskarta gami da amsawa da amin.
Daren ranar sun raba shi ne suna hirarraki, yana ta lallaɓa ta gami da ba ta baki akan zamantakewarsa da mahaifiya da yan uwansa, yana nuna mata watarana za'a wayi gari ko don dalilin yaran nan, Nene ta kaunace ta. Murmushi kawai ta yi masa, amma ba ta hasko hakan a abin da zai iya faruwa ma. Akwai tsanar da watarana ke gushewa komai ya wuce, amma ban da irin na Nene. Saboda gorin asali take mata, ita kuma ta fidda ran ganin dangin mahaifinta, balle kuma na mahaifiyarta da ba ta da wani makusanci da ya yi saura a doron ƙasa.
Ta saka hannu ta ɗauke hawayen da suka zubomata ba tare da ta yarda ya gani ba.
Koda ya tashi tafiya Abuja, ranar Kubra sai da ta ji tamkar an mata mutuwa, gaba ɗaya jikinta ya yi sanyi. Haka suka yi sallama bayan Adam ya rungume yaransu a ƙirji ya kuma sumbaci kowaccensu yana ta murmushi kamar kar su rabu. Ya dago ya dubi Kubra yace,
"Sai Allah ya ƙaddara saduwarmu Maman Twins. Ki kularmin da kanki da yaranmu a koyaushe. Ki kuma taya ni addu'ar kammala aikin da zai kai ni lafiya har na je na dawo in sha Allah. Zai iya kai ni yin sati ɗaya ko biyu, amma zan dawo da zarar mun kammala. Nasan kuɗaɗen da na ajiye za su ishe ki har na dawo da yardar Allah ko?"
A hankali ta gyaɗa kai tana ɗan tura baki lokaci guda hawayen da take maƙalewa suka kwaranyo. Ita gaba ɗaya sai tafiyar ta fice mata a rai. Gani take yi kamar Adam yana mata sallamar barin duniyar ce gaba ɗaya ma ba wai gari ba. Ita ba ta son irin zantukan nan nasa sai ta ji kawai rabuwarsu ce ta zo.
Ashe kuwa hakan ne, tafiya ce da za ta kawo rabuwarta da shi har abada.