Free chapter · Read without an account

18

by Rufaida Umar · ALWASHI

Sada Bilyaminu, shi ne auta a wurin Alhaji Bilyamin Bakori da Haj Zinnira Yahaya(Inna). Sun yi auren soyayya hakanan rayuwarsu irin ta wayayyun ƴan boko ce saboda kasancewar su duka biyun ƴan dangi ɗaya. Kuma iyayensu sun gaji arziƙi ne tun daga kakanni har zuwa kansu.

   Alh Bilyamin ya riƙe maƙamai da dama a gwamnati don a yadda tarihi ya zo har takarar shugaban ƙasa ya nema a lokacinsa amma kuma jam'iyyarsu ta sha kaye. Wannan ya haifar mishi da baƙin ciki da ma tsanar siyasar gaba ɗaya don ba ƙaramin kashe dukiya ya yi ba amma haƙansa bai cimma ruwa ba. Ya maida hankalinsa ga kasuwanci inda yake shigo da manyan motoci da ma ƙanana daga ƙasar waje zuwa Nijeriya.

   Yara uku kacal Allah ya nufe shi da haifa, Dakta Nuhu Bakori (Baba Dakta) shi ne babba yana zaune a Abuja, mai bi masa Haj Falmata (Dada) wacce ke auren wani shahararren ɗan siyasa a garin Kano, sai Alh Sada Bakori. Sai ko Zayha, ɗiyar ƙanwar Inna da take riƙo tun bayan rasuwar ƙanwarta wacce su biyu ne dama a gaban iyayensu. Mahaifin Zayha kuwa tun tana ciki ya rasu.

   Sun taso cikin gata da rufin asiri ta yadda koda wasa ba sa ƙaunar wani abu ya taɓa lafiyar yaran nasu. Alh Bilyamin ya so Nuhu ya karanci fannin kasuwanci ko don ya taimaka masa a gaba idan girma ya ci shi, amma koda ya kafe a kan ra'ayin karantar fannin asibiti sai bai ji a ransa zai masa tilas ba gudun ɓacin ransa. Dalili kenan da ya bar shi da zaɓinsa, ya kuma ɗauki nauyin tura shi jami'ar Oxford dake London, a can ya haɗa degree ɗinsa ya dawo ya ƙarasa abin da ya rage a ƙasarsa. Bayan aure ya tattara ya koma Lagos inda kafin daga bisani ya dawo Abuja tare da matarsa Hidaya ƴar Maiduguri dangin Shuwa Arab da yaransu biyar a yanzu. 

   Falmata kuwa tun tana matakin ƙarshe a jami'a ta samu mijin aure, ɗa ne ga abokin Alh Bilyamin mai suna Sanata Ibrahim Mamman, wanda aka yi gwagwarmayar siyasa tare, gagarumin biki aka yi daidai da irin na lokacin sadda ta kammala karatunta. A can Kano ta tare da mijinta Yakubu Ibrahim Mamman. Tana da yaranta huɗu.

   Alh Sada Bakori wanda duk ya fi su yawan iyali, shi ne ya tsaya ka'in da na'in wurin taimakawa mahaifinsu da harkokin kasuwancinsa. Ya kuma karanci fannin kasuwancin ba wai don farantawa mahaifin nasu rai ba kawai, a'a, sai domin shi ma a karan kansa abin da yake sha'awar karanta kenan kuma sai Allah ya sanya mishi nasibi a ciki. Kafin rasuwar mahaifinsu Alh Bilyamin sai da ya kasance komai na kasuwancin Bakori Investment ya dawo ƙarƙashin kulawar Alh Sada. Ko bayan raba gadonsu ma, madadin ya durƙushe sai Allah ya ƙara sanyawa abin albarka.

  Lokacin ne kuma dangi suka fara rarumo yaransu mata da zummar buƙatar ya aure su, shi kuwa a lokacin ya riga da ya yi zurfi matuƙa cikin soyayyar Salma, matashiyar budurwar da ya haɗu da ita tun wani zuwa da ta yi Katsina wurin dangin mahaifiyarta. Sanadin soyayyarta har garinsu Adamawa ya taka ya je, kuma ya samu karɓuwa soyayya har wurin danginta. Soyayya mai tsafta kuma mai cike da ƙauna da kulawa suke nunawa junansu.

  A ɓangaren Innarsa kuwa, tuni ta gama yanke aura mishi Zayha, ita ce wacce kaf duniya ta fi kaunar ta gani tare da Sada. Duk da cewa Zayha a sannan ma ta yi nisa a kogin son Sada amma kuma ta kasa nunawa a fili. Lokacin da Inna ta tuntuɓe ta wai ko tana son Sada za ta haɗa ta aure da shi, ji ta yi tamkar an yi mata albishir da gidan aljanna. Yanayin da ta nuna na kunya ne ya sa Inna ta fahimci lallai zarginta akan Zayha na son autanta ya tabbata. Ta kuwa saka a ranta Sada ba shi da mata sai ita.

Shi kuwa a nasa bangaren bai san da zancenta ba sai bayan da ya zo wa Inna da batun auren Salma da yake so a je nema mishi, anan Inna ta haɗe rai ta nuna sam ba ta aminta ba, ita Zayha take so ya aura. Toh abinka da wanda boko da kuma gata sula cakuɗe suka sangarta ya yi fushi matuƙa ya kuma kafe akan lallai shi ba zai auri Zayha ba sai dai Inna ta yi hakuri ya auri Salma.

Magana tun tana ƙarama sai da ta girmama don hatta Dakta da Falmata sai da suka sanya baki wurin rarrashin Inna da nuna mata bai kyautu ta yi wa Sada dole ba tunda babu wanda aka yi wa dole a cikin su biyun. Inna daƙyar ta sauko amma kuma ta kafe lallai sai dai ya aure su duka biyun, kuma Zayha ta kasance uwargida. A lokacin Sada ya so ya ƙara turjiya amma kuma rantsuwar da Innar ta yi ne ya sa dole ya ce ya ji ya gani.

Zayha da ta fahimci a dole Sada zai aure ta, tun a sannan ta ji nan duniya babu abin da ta tsana irin Salma. Daidai da sunan idan aka ambata ji take kamar an yi mata yayyafin wuta a ƙirjinta. Amma ta danne komai ta nunawa Inna ta amince ta haƙura a auresu su biyun. Inna ta dinga rarrashinta da nuna mata ta kwantar da hankali domin Sada ba zai taɓa auren wacce za ta so sama da ita ba.  Da wannan ta samu nutsuwa duk da har a lokacin ba ta taɓa tozali da Salma ba.

Haka kuwa aka yi, su ma ɓangaren iyayen Salma ba su ja da batun auren Sada ba, Salma ce a farko ta so ta ja baya sai dai babu yadda ta iya tunda ba ta samu goyon baya ba. Dole haka ta haƙura ta rungumi ƙaddarar auren Sada.

Watanni biyar tsakani aka ɗaura auren Zayha da Sada, bayan tarewarsu da wata uku ne sannan aka yi na Salma.

Lokacin da Sada zai koma ɗakin Salma, zuciya ne kawai Zayha ba ta haɗiya ba. A daren ko bacci ɓarawo bai yi nasarar sace ta ba. Kuka da birgima kuwa ba kalar wanda ba ta yi ba don har Innar da ke sonta sai da ta dinga ja mata Allah ya isa da ikrarin ta cuce ta tunda har ba ta saka baki Sada ya fasa auren Salma ba.

A ɓangaren masoyan kuwa, soyayyarsu suka ci tamkar babu wata halitta a gidan face su biyu. A sannan gidan gaba ɗaya ɓangare uku ne kawai, daga na Zayha sai na Salma sai ko Sada. Ita kanta Salma mace ce mai kishi amma kuma irin so da ma gudun ɓacin ran Sada din da kuma kokarin da take na neman soyayyar Inna ya sa ta danne nata kishin don ita a ganinta ma ai ita aka cutar, ita aka yi wa kishiya tunda ita ce matar so ba wai Zayha da ta kasance haɗin mahaifiyarsa ba.

  Wannan ne ya sanya ta ke ji da kanta har gobe sanin da ta yi ita ce mai fada a wurin Sada. Inda kuma ta fi Zayha din wayo kenan, ita Zayha sam ba ta iya ɓoyon abin da ke ranta, na farin ciki ko akasinsa. Wannan ya sa abu kaɗan Salma za ta yi ta shaƙa mata.

Batun halayyarsu kuwa, Zayha mace ce mai zafin kishi, kusan za'a iya cewa ma abin da ta ke ji a kan Salma ya zarce kishi don tsana ce ƙarara. Salma ta fi ta kyau, ana kuma yabon yadda take da kyauta duk da cewa ba kasafai take da sakin fuska ba sai idan tana tare da mutanen da ba ta ɗauke su a kusa ba. Girki ma kansa ba za ta nunawa Salma ba domin ta tashi ne ita cike da sangarta a wurin Inna, komai yi mata ake yi. Hatta bayan auren ma ƴar aiki Innar ta sa aka kawo mata. Sai dai ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba wurin maida hankali ta dinga koyo don ta tsani ta ji mutane na koɗa girkin Salma. Wannan ya sa hannunta ya faɗa itama amma kuma duk da haka girkin Salma din na musamman ne. Tsafta kuwa sai dai su yi gogayya domin ita ma zai wahala ka ga ɓangarenta da datti, a nan ne kam ba ta yarda lallai sai ƴar aikin ce za ta yi mata ba saboda tana da mugun ƙyanƙyami kamar mijinta Sada. Dukkansu saboda rainon Inna ne.

Salma kuwa tana da kishi amma akwai ɗan karan wayo ta yadda ba ta yarda ta nuna a fili ba, har zuciyarta kuma ba ta jin tsanar Zayha illa iyaka tsaftataccen kishin mijinta da take ji a ranta irin na mata. Ga biyayyar da take yi wa Inna duk kuwa da cewa Inna ba ta sakarmata fuska amma hakan bai sa ta fasa ba, uwa uba hidimar girke-girken da takan yi ta aikamata a wasu lokutan.

Sada kuwa mutum ne kaifi ɗaya kuma tsayayye a kan gidansa, wannan ne yake taka musu burki ta yadda koda Zayha ta yunƙuro da kalar nata rikicin, to fa ba ya zuwa ko'ina. Idan tafiyarsa ƙasar waje ya tashi, yakan je da ɗaya a cikinsu. Ranar farko da zai soma zuwa da Salma, nan Zayha ta tayar da hankalinta musamman ganin Salma din na Amarya. Kishi da borin da ta yi har ma da kai ƙara wurin Inna bai saka Sada janye ƙudurinsa ba. Tana ji tana gani suka yi tafiyarsu.

Da suka tashi dawowa kuwa, suka dawo da albishir din da ya dusashe ji da ganinta na ƴan daƙiƙu, wato na bayyanar ciki a jikin Salma. Sanadiyyar wannan cikin ya sa ta samu sassauci a wurin Inna. Hakan ya ƙara dugunzuma zuciyar Zayha. Ta kuma ci alwashin har abada babu wani abu wai shi sulhu ko zaman lumana tsakaninta da Salma.

Abu kamar wasa, sai da Salma ta haifi yara mata har biyu Mardiyya da Maryam, a cikin shekaru biyar na aurenta da Sada, Mardiyya na da shekaru uku sai Maryam mai shekaru biyu kafin kuma cikin ikon Allah itama Zayha ta samu ciki. Farin cikin da ta yi da samun cikin ba ƙarami ba domin duk sadda ta buɗi idanu ta ga irin tarairaya da ma soyayyar da Sada da yaransa da Salma ke kwasa sai ta shige ɗaki ta ci uban kuka ta share hawaye. Allah da ikonSa kuwa tashin farko ta haifo santalalen ɗanta namiji. Murna da tsantsar farin cikin da ta shiga ba a cewa komai, a take ta saka Sada ya yi mishi huɗuba da sunan mahaifinta wato Zakari amma kuma ta ce ita sam ba ta yarda a ɓoye ba. Dalili kenan da ya sa ake kiransa da Zakari. Suna gagarumi aka yi, yan uwan Sada da na ɓangarenta Mahaifinta sai da suka cika gida. Haka aka dinga yadawa Salma habaici wai ai sai yanzu aka haifo kan gida kuma Magaji. Toshe kunnuwanta ta yi har komai ya wuce.

Kayayyakin barka da ta aikawa Zayha kuwa, haka aka maido mata da su wai ta riƙe abin ta ba a so. Idan ta ce abin bai mata ciwo ba ma ta yi ƙarya. Daga ƙarshe ta tattara ta ƙara yin watsi da lamarinta don ta kula ba za su taɓa daidaitawa ba.

Zakari na da shekaru biyu a duniya, itama ta haifi Areef. Yaron da ya ɗauko fari da kyawunta. Wasu ma ɗan balarabe suke kiransa da fari. Zayha kuwa sai ta saki jikinta tun daga Zakari babu ruwanta da wani ba da tazara irin na lokacinsu, haihuwarta sai ya zamana a kai - a kai, burinta kawai shi ne ta tara yaran da dole za ta amsa sunanta na Uwargidan Alh Sada. Bayan Zakari, ta haifi Nasreen, Zahra, Fadila, Khalid. Sai da ta jero su biyar kafin Salma ta haifi Benazir da take sa'anni da Nabeel ɗa na shida a wurin Zayha, sai ko ta ƙara haifo Afrah sa'ar Lubnar Zayha. Daga nan Salma ba ta ƙara haihuwa ba sai ko Zayha da ta rufe da autanta Yasir.

A taƙaice dai Zayha na da yara takwas, Salma kuwa yaranta biyar cif.

Rayuwar ta yi ta tafiya a hakan, a lokacin kuma da Salma ke ɗauke da cikin Afrah ne, Sada ya ƙara aure. Wannan auren ya faranta ran Zayha sosai don ba ƙaramin daɗi ta ji ba. Ta dinga yadawa Salma habaici, ta kuma tsaya tsayin daka a hidimar biki don a cewarta ai ita bayan ma aure, yar uwa ce ga Sada. Don haka tudu biyu take ci. Ya auro Nafisa haifaffiyar garin Kano. Tana da wata uku ne Salma ta haifi Afrah.

Yaran Nafisa uku ne kacal a gidan, ƴan biyunta Amir da Amira, sa'annin Yasir autan Zayha, sai ko ƙaramarsu Waheeda.

***

Yaran sun taso cike da gata da samun kulawar iyayen nasu, ga kuma a gefe Kakarsu Inna mai yi musu son duniya saboda su ne jikokinta da ke kusa da ita a gari ɗaya, don ta yaran Dakta da Falmata, zai wahala ka gan su a garin Katsina idan ba hutu suka zo ba, shi ma hutun jifa-jifa.

Muguwar sangartar da Zayha ta yi wa Zakari ne ya yi sanadin gurɓacewar rayuwarsa, mahaifi ba ya kwaɓa, ita ma ba ta yi. Inda suke da bambanci da Salma kenan domin duk kaunarta da yaranta, idan suka yi ba daidai ba za ta yi musu hukunci. Kuma ba koyaushe ne take bin abin da yaranta ke so ba.

Mugayen abokai suka yi tasiri sosai a rayuwar Zakari ta yadda hatta da makarantar da aka tura shi yi tare da Areef a can London bayan kammala sakandire dinsu (domin ajinsu guda dalilin maimaicin aji da Zakari ya yi) bai nutsu ba. Ban da shaye shaye da yawan club babu abin da ya sa gaba, wannan ne ya sa ba shiri Alh Sada ya yanke masa hukuncin dawowa gida. Yana kuma daga cikin abin da ya tsayawa Hajja Zayha a ƙoƙon rai don a ganinta ba Zakari ne kawai ya tozarta ta ba, har da Alh Sada. Ta kuma saka a ranta Salma dariya take musu a ɓoye.

Koda mugayen ayyukan Zakari ya ci tura sai da aka haɗa da miƙa shi gidan horo domin a yaƙi mummunan halayyarsa ta shaye shaye. Aka ci sa'a kuwa ya rage kaso mai yawa amma kuma bin mata kam, sai abin da ya yi gaba.

Areef ya taso da wata irin nutsuwa da maida hankali a karatun boko da Arabi, don ko kafin su kammala sakandire yana da haddar Alkur'ani mai girma da ma wasu litattafan addini. Faɗin irin so da ƙaunar da hakan ya siya masa a wurin Alh Sada da ma yan uwan Alhajin nasa, Baba Dakta da Dada Falmata, abin ba a cewa komai. A gefe guda kuma Kakarsu Inna, saboda za ta iya bugar kirji ta ce koda ba ta jin Salma sosai a ranta, to fa tana kaunar abin da ta haifa. Amma kuma ba ta taɓa nunawa a gaban Salma ɗin musamman dayake suna zargin da sa hannunta a lalacewar Zakari. Dangi kaf Zayha ta gama nunamusu ai jifa ne aka yi wa ɗanta wanda ya yi sanadiyyar lalacewarsa.

Mardiyya aka fara yi wa aure tana tsaka da karantar Nursing a makaranta, wani kwararren likitan ƙashi ne ya aure ta. Shekararta biyu da aure itama Maryam da ta kammala nata karatun a fannin Accounting, ta auri wani ɗan attajiri ɗa ga abokin Alh Sada a nan Katsina.

A lokacin ne kuma Nasreen ɗiyar Zayha itama ta yi aure irin wanda Zayha ke so, gidan sarauta domin Yariman Sarkin Katsina ta aura. Wannan ya ƙara fasawa Zayha kai. Zahra auren gida ta yi, ɗa ga ƙanin mahaifin Zayha tunda matashi ne mai rufin asiri kuma ɗan kasuwa mazaunin Kano ya sa Zayha amincewa. Sai ko Fadila wacce ta ɗan samu jinkiri kafin ta yi aure, a ka yi bikinsu tare da na Benazir ɗin Salma. A shekarar ne kuma Sameera ta fara zuwa gidan domin yin kitso. Benazir ta tare a Abuja, Fadila kuwa a cikin garin Katsina take zama.

Zuwa lokacin Alh Sada ya siye gidajen dake kusa da gidansa ya ƙara faɗaɗa gidan ya yi shi wata duniya guda a unguwar Barhim. Ya fidda bangaren samarin yaran nasa daban, sai ko na shi da na matan kowanne daban. Sai garden mai ɗauke da shuke-shuke da kuma wurin wasan yara da ma ƙorama ƙarama mai sanyi sai ko ƴar bukka mai kyau da yakan zauna a wasu lokutan musamman idan ya yi baƙo.

Areef koda ya kammala haɗa Masters ɗinsa a fannin kasuwanci kai tsaye Alh Sada ya fara ɗora shi a wasu harkokin nasa. Tare suke shi da Fareed ɗan aminin Alh Sada, tun suna ƙanana suke abota har girmansu. Haka ya sa koda su Areef suka wuce London karatu, ba musu shima Mahaifin Fareed ya tura shi. Shaƙuwarsu na burge kowa.

Areef mutum ne ba mai yawan magana ba amma fa cikin yan uwansa akwai hira da zolaya. Haka za a zauna a yi ta dariya ana labari. Yana da sakin fuska da girmama wanda ya fi shi. A gefe guda sam ba shi da zafi, ba kuma shi da fushi. Yana furzar da abin da ke ransa to shikenan ta wuce. Hakan ya sa ko wani aika-aikar yayansa Zakari ya yi, shi Sada ke ɗorawa a kan case ɗin. Ya sha zuwa ofishin ƴan sanda yo belin Zakari idan an kama su a club da ma cases mabanbanta. Wannan ya ƙara rura wutar ƙiyayyarsa a zuciyar Zakari da Hajja.

Faruwar ƙaddarar can ne ya sauya Areef gaba ɗaya. Ya koma mutum mai shiru da rashin sakin fuska, hirar ma gaba ɗaya ya rage ta. A shekarar da abin ya faru ya tafi, aka yi auren Zakari, Fareed shima a shekarar ya yi auren duk da yaso a ce tare da na Areef aka yi. Amma kuma ya fi kowa sanin Areef tun can ba shi da wacce yake so sai ma su rububin sonsa, balle kuma da wannan kaddarar ta afkamasa, sai ya ƙara nisanta kansa da ƙasar gaba daya don ko bikin Fareed bai halarta ba. Yanzun ne suka samu ya waiwayo gida baki ɗaya.

Wannan Kenan!

***

Want the next chapter?

Create a free ArewaPen account to save progress, unlock paid chapters, follow this author, and keep reading across web and the Android app.