Free chapter · Read without an account
p-18
by Rabiatu bashir · DAN HALAK
💋ƊAN HALAK💋
MALLAKAR
UMMU MAHER(MISS GREEN)🍃
*AREWA WRITER'S ASSOCIATION📖*
AREWABOOK
https://arewabooks.com/book?id=6631fffa0eeb
3b80f1ef8159
WATTPAD
***
content=story_info
Ina masu son shiga adashe Amma kuna fargaba🤔yar uwa ki tsarkake zuciyan ki kizo kiyi adashe cikin aminci da kwanciyan hankali insha Allah Babu rigima ko tashin hankali kwanciyan hankali zaki Yi adashen ki Kuma mu gama lfyh da yardan Allah..🥰🤝
30k weekly parking 300k
1)Haj Maryam✅
2)Ada umar/hafsat yahya✅
3)Usman
4) barrister hauwa'u
5)shafa bello/baby daura
6)
7)
8)
9)
10)
Akama slotd
***
RmuDuL
18
________"Ni Ifkam na bada shawarar haɗa yaranmu aure, musamman da ayanxu muke da ƴammata kusan goma a gidan nan sannan ga samari ma saboda haka a madadin bakin mai martaba na yanke wannan hukunci, duk kuma wata ko wani da zai zo daga baya ya ce hukunci bai masa ba, to ya kuka da kanshi domin hukunci Sarki shi ne dai-dai sannan ko kusa ba muyi hakan domin zalunci ba, ilahu yasan manufarmu ta yin hakan".
Kallon-kallo aka shiga yi a wannan babban ɗakin, nan da nan fuskokin wasu suka juye zuwa baƙin ciki, wasunsu kuma akasin hakan domin har yau har gobe wasu suna ɗaukar hukunci sarki abu mai yiyuwa, sannan duk abin zancen da zai fito daga bakin Waziri Ifkam sun san tabbas wannan ba ƙaramin abu bane wanda zai sa suyi fatali da shi, domin a wannan masarautar ana matuƙar girmama maganar shi, duk da shi dama Waxiri Ifkam ya kasance ɗan uwa kuma kaka a cikin wannan babbar masarauta, kuma a yanzu ɗan ɗan uwanshi ne yake wannan sarauta, kuma shi da kanshi Ifkam ɗin yana matuƙar girmama al'amuran wannan babbar masarauta.
Ganin kamar a wannan karon kowa ya yi shiru baka jin ambaton Alhamdulillah ya Allah, yasa ya ƙara motsi sannan ya gyara zaman shi akan kilishi wanda ya kasance tamkar doki wajen yake, domin an zana hoton doki sak da daƙwa daƙwan gwala-gwalai sai sheƙi yake sannan aka ɗora kilishi akai, sai abun ya bada wani irin mugun haɗi amma ba ana nufin haɗin gambiza ba.
"Kamar yadda na faɗa babu wata ko wani da zai ce wannan hukunci bai yi ba, sannan kuma wannan aure bama so ya wuce wannan watan da muke ciki, babu ruwanmu da wani biki ko kaɗe-kaɗe hakan nan za a yi wannan biki cikin salama, domin idan mun tuna da shekarun baya muna duk al'adunmu na wannan babbar ƙasa wajen yin shagalin biki, amma yanzu dole ne a tsayar da komi domin ganin abin da ya faru a baya wanda ya zana babban allon da har yanzu bai goge a cikin allon zuciyoyinmu ba, wanda nima shaida ne kuma shaida ne saboda a yanzu zan faɗi wannan haɗi da ya kasance".
SHAHID WA ZEINEB
ƘASIM WA JAWAHIR
LUƘUMAN WA ZEHRATU
RABIAAT WA TANIM
FARUƘ WA BILQISS
ASSADIƘ WA MINAT
HILAL WA BINTU
SAGIRR WA ESHAT
BILAL WA KUBRAT
NURRR WA NURATU
Ai kafin ya gama rufe baki wajen ya fara kaurewa da surutu mai ƙarfi har aka fara jiyo muryoyin wasu suna yiwa juna ƴan gore gore da habaici, wasunsu kuma har da kuka wiwi tamkar dai iyayensu sun mutu ne, ganin hakan yasa Ifkam ƙare musu kallo sosai yana nazarinsu da kalamansu, masu yin kuka ma ba a barshi a baya ba kallon idanuwansu yake ganin hango tsagwaron baƙin ciki tamkar dai zasu balbalawa wajen wuta, mutane biyu ne yaga suna farin ciki da wannan aure amma in ka cire su biyun nan sauran duk cikon aji ne, ma'ana duk ƴan daɗawa wuta fetur ne wasu kuma rabon faɗa suke amma sai su ɓuge da shigarwa wani ɗan uwansu mafi kusa.
Ifkam bai hanasu ba har suka yi suka gaji sannan ya ce"kowa ya tashi ya tafi mun sallame shi, idan da akwai abin da kuke so ku yi da kuɗi kowa ya yi magana za a bashi ba a cire mutum ɗaya ba, domin gudanar da hidima".
Ya nuna musu sam baisan abin da suka yi yanzu a gabanshi ba, sai jikinsu ya yi mugun yin sanyi domin har yau hat gobe basu manta waye Ifkam ba, in har ya zartar da hukunci ko akan waye sai anyi ko da kuwa ɗan cikinsa ne.
sosai wannan babbar masarautar ta yamutse, kowa cin karanshi ba babbaka yake kullum a cikin tashin hankali tun bayan da Ifkam ya zartar da wannan ɗanyen hukuncin, domin a ganinsu ai wannan ɗanyen aiki ne idan ba haka ba abar yaransu su zaɓa mana, amma sai ace za a y musu dole saboda an tsane su?.
Ɗakin cike yake da ƴan taro, Omer sai zagaye ɗakin yake yana hawaye mai sosai zuciya, ganin wannan hawayen ya ƙara sanya jikin kowa yin sanyi ya murza idonsa wanda yake yi masa matuƙar nauyi ya ce" tabbas a yau muna cikin alhini, tabbas Ifkam ya rusa mana dukkanin abin da muka rufe, domin yana ganin shi ne babba kuma shi ɗin ba wanda zamu iya taɓawa bane wallahi tallahi ba don shi bane da wani ne da sai inda ƙarfin takubban mu suka ƙare, tsabar tozarta wai kamar Ƴata Nurata wai ita ce za a haɗata da Nurrr yaron da har yanzu bai daina shirme da shiririta, kullum cikin yawon ƙasa-ƙasa yake yana neman ƴar iskar da zai shaƙata da ita, saboda shi ba a yo shi da mutunci ba sannan mu nan duk bai ɗaukemu da mutunci ba, hatta shi sarkin ba wai yana ganin mutunci shi bane amma shi ne za a jajibo shi a haɗa shi da ƴata"?.
Abu Nurrr ya yi saurin ce wa "kai Omer ka iya bakinki, akan mi za ka dinga zagin ɗana? Yaron da ko a yanzu bai haura shekara 30 ba shi ne ake yiwa irin wannan zagin ɗibar albarkar? Domin kawai son kai, ita ɗiyar ta ka wani irin iskanci ne ba ta yi? Ko an faɗa maka bamu sani ba ne? To har da boka tunfafiya tana lalatar ta dashi, wanda ya kasance ƙazami kuma faƙiri sai ni za a dinga zaginmu saboda bamu kai ka kuɗi ba, to idan ma domin kuɗi ne ai har yanzu baka kai shi Sarkin ba duk da ana haɗawa dana sat..."
Wata irin shaƙa Omer ya kaiwa Abu Nurrr sannan wajen ya kaure da bala'i, mai makon abarsu suyi faɗansu faɗan mutun biyu sai ya zama faɗan mutane sa yawa waje ya hau sowa, abin ka da ɗakunan gidan sarauta manya-manya sai ga shi an jiyo faɗansu tun a babban masarauta idan ka kasa kunne za ka ji.
babu shiri aka buga busar giwa, nan da nan suka ja munafukan bakunansu suka yi shiru domin sun tabbatar suka bari aka ƙara buga wannan sarewar to fa kashinsu ya bushe, duk da haka basu daina aikawa juna mugayen kallo ba saboda Ƙabilar Turam akwaisu da taurin kan tsiya yadda kasan mutanen farko, ga su da mugun yawa domin iya su gidan masarauta za a haɗa gari biyar awaje ɗaya kuma ba ƙaramin gari ba a a babban gari wanda yake ji da tumbatsar mutane.
ƘASAR NIM
Babbar ƙasa ce mai tafe da mutane da dama, sannan idan ka gansu saboda kyau sai ka ɗauka su ne da kansu suka ƙera kyawunsu ba manya ba yara, gasu da kyawun halitta yadda kasan larabawa haka suke sai dai har sun fisu ma fari da haske su ɗin mutane ne masu yare da al'adu da dama, suna wani yare wanda ake kira YIMAN yaren kamar larabci yake amma ba larabci bane, sannan suna yin yare da dama a garin har yaren da baka tunanin ji ba sai ka ji shi a ƙasar, kusan mutanen duniya da dama suna zuwa ƙasar domin yawan buɗe idanuwa domin Allah ya yi musu kyawun gine gine, kyawun furanni,shuke-shuke albarkatun gona. Sannan suna da dukiya sosai ba kaɗan ba idan nace ba kaɗan ba ina nufin sosai ɗin nan. Ta yadda ko da za suyi shekara malala gashin tunkiya suna raba kuɗa ɗe ba zasu ƙare ba, domin kullum arziƙinsu gaba yaje ba baya ba saboda Allah ya sani suna cinikayya da haɗakar dukiyoyi da ƙasashen africa dama na yamman duka, shi yasa sam ko asara idan ta hau su basa damuwa domin suna da bila adadin ɗinsu a bayan ƙasa.
Wannan rigimar da aka fara sarki yasa aka buga ƙahon giwa ya yi ne saboda kawo ƙarshen tarzoma, domin shi da kanshi ba magana zai yi musu ba saboda sam ba ya son surutu ko hayaniya a tsakanin mutanen shi, ya fi son ya yi musu shiru yaga iya gudun ruwansu saboda sai suyi fin wata ma ba tare da sun sanya idanuwansu akan sarki ba, suna gida ɗaya mai sassa daban-daban kuma duniya daban tunda kowa ba ya ganin kowa tsakanin inda suke, da inda sarki yake a ƙalla ana samun tafiya mai nisan gaske wacce idan a ƙafa za kaje sai ka yi tafiyar awa ɗaya.
HMM KA DA KUGA LABARI YA JUYA, TI BAI JUYA BA YANA NAN DAI AKAN ƊAN HALAK ƊIN SHI KU DAI KU CIGABA DA BIYO NI
HUMAIRAH
Babu mutanen da ba a aikawa Babanmu ba, akan mu koma gidan shi ya yi haƙuri, amma ya murzawa udanuwanshi kwalli ya ce sam ba zamu koma mishi ba, idan munga dama mu shiga duniya ma amma shi ba shi ne ya haifemu ba, tunda mu ba zamu zauna lafiya ba.
Wannan maganar da ya yi ta ƙara tunzura zuciyoyinmu, musamman ma su Ameera Umma ma taji haushin furucin sosai.
Muna zaune a tafkeken tsakar gidansu Umma, ni Ummi, Ameera, Anti Salamatu, Matan gidansu. Duk hira ake akan Iyan Salame wato mahaifiyarsu Umma wacce take ƙasar larabawa shekaru goma kenen amma har yanzu ba ta dawo ba taje aiki. A nan ne ma ake ƙara tattaunawa kan matsalarmu, Anisa ce ta shigo tana kuka wato ƙaramar ƙanwarmu, idanuwanta sun yi jawur ga ƙafafunta babu takalmi, raina ya yi mugun ɓaci idanuwana suka kawo ruwa domin duka-duka shekarar Anisa uku, amma mahaifinmu ya yi tsallen baɗake ya ce ba za a ɗaukar mishi ƴa ba, domin kada mu koya mata mugun hali irin na mu da uwar mu. Ni daman nasan za a rina wai an saci zanin mahaukaciya domin ni nasan Baba ba zai iya kula da ƙannen mu ba balle kuma Anisa da take yarinya ƙarama, ga hantarar Baba kande da dukan da take musu.
Da gudu ta rungume ni tana ce wa"Yaya unwa ina ji, cicina ciwo ake mini".
Sosai na fara hawaye na ce"Sannu baby Anisa zo ki ci abinci". Na ɗakko sauran gadin kwakin da muka sha na fara ba ta tana ci, hannu baka hannu ƙwarya tamkar dai za ta haɗa da ƙwanon saboda gunwa. Kowa ya dinga kallon yarinyar cike da tausayi, tana gamawa na ɗebo mata ruwa tasha na ɗora ta akan cinyata ina shafa kwantaccen gashinta mai kyau da sulɓi, dama ga Anisa da son jiki sai ta ƙara shigewa jikina na fara tambayarta? "Baby Ani tun yaushe rabon ki da abinci"?.
"Yaya tun da chafe da Baba kande a bamu ɗumamen tuwo".
Da sauri Ameera ta ce" tun da safe Ani? Yanzu fa la'asar ake kira? Inna lillahi wa inna ilaihi raji'un".
Muka saki kuka, amma banda Umma domin tabbas abin ya girgizata shi yasa ma ta kasa magana saboda baƙin ciki.
muna zaune matan gida suna ta zagin Babanmu da matarshi da ta gama mallake shi, sai kuma wani tashin hankalin ya riskemu domin kuwa Anisa ce ta fara wani irin amai tamkar za ta amayar da kayan cikinta, ga bakinta sai kumfa yake...
KEMA HAKA KI KE ZAUNE BA KIDA SANA'A? KO KUWA KINA YI SAMU NE BAKYA YI? KO KUWA KINA CIKIN MATA MASU ƘIWA?
TO KU BUƊE KUNNUWAN KU DA KYAU, SANNAN KU SANI SANA'A ITA CE JIGON RAYUWA MUSAMMAN MU MATA, UMMU MAHER TA SHIRYA TSAF WAJEN KOYA MUKU WAƊANSU SANA'O'I KAMAR
BEAD WORK🧶👚🧵
GRAPHICS✍🏻
MAGUNGUNA NA MU NA MATA🍃
RIBOMS NA YARA DANA MANYA💇🏻♀️💇🏻♀️
IDAN KIN SHIRYA KOYON DUKKANIN WAƊAN NAN SANA'O'IN KI YI MIN MAGANA TA NO ƊINA KAMAR HAKA;
***
$IFKAM
$HUMAIRA
$AMEERA
$UMMA
SHARE
COMMENTS MY FANS
CHART NO CALL ***